FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · A DUNIYAR MU
A DUNIYAR MU Page 1&2Bismillahir'rahmanir'raheemWata macece wacce ba zata wuce shekara ashirin ba cikin wani ma daidaicin gida daidai na talaka mai rufin a siri, shara take da sauri da sauri wani wajan yana sharuwa wani wajan kuma ana wuce shi, tana gamawa ya yadda tsintsiyar ta nufi ɗakin ta, tana shiga ta fito sanye da hijab da ƴar post a hannun ta ta fice daga gidan tasa mukulli ta rufe,tafiya kaɗan tayi ta iso ƙofar gida mai ƙaramin get ƙofar a buɗe take don haka ta shiga da sallama, wasu mata ne a cikin gidan ko wacce ta cire hijab wata ma vest ce ajikin ta wata kuma kayan bacci, shewa aka saka lokacin da ta shigo wata daga cikin su wacce da alamun ita ce matar gidan tace "" a'a kaga amare yau ango bai fita da wuri bane ko? sheƙewa ragowar matan gidan sukayi da dariya suna tafawa, bata ce komai ba ta nemi waje ta zauna tana cire hijab ta buɗe post ɗin hannun ta ta ciro' agwaluma ta fara sha, ƙura mata ido sukayi kamar zasu cinye ta,"'Shukrah me zan gani haka ? kardai kice har kinyi ciki? cewar wata mata wacce duk ita kaɗaice mai kaya complete a cikin su tana yauƙi tace ""chaɓ lallai kinshiga layin ƴan jagwal ""bangane jagwal ba cikin shine jagwal?, naga haihuwa abun nema ce kuma bakiga yanda yake farin ciki ba kamar ya goya ni, """hehehe cewar matar tana gyara zama ta ce ""ai dole ya nun miki farin cikin sa tinda an ɗakko hanyar da zai ƙara aure furzar da ƙwallon a gwalumar tayi zuciyar ta na bugawa tace "" haba maman Nabila ya daga yin aure zaki fara yi min zancen kishiya? gaskiya banji daɗi ba,""nasan ba zakiji daɗi ba amma dole saina faɗa miki idan banda ƙuruciya irin taki da rashin wayewa daga yin aure wata biyar har kin bari ya banka miki ciki? to wllh tin wuri kisan abinyi don kina haihuwa kinzama mama zaki lalace shi kuma ya auro wata su cigaba da chilling kina ji kina gani kinzama uwar ƴaƴa, haba kalleki fa black beauty ga diri amma ace tin yanzu har zaki fara tarwa kanki tension, ki dube ni ki gani shekara ta shida da aure ƴata ɗaya saida na shekara biyar ma sannan na bari na haihu kuma nasan ke shaida ce yanda miji na yake ji da ni saboda har yanzu kallon budurwa yake min, amma da na tara yara fa? da yanzu ina da kishiya""To yanzu ni ya zanyi? Shukrah ta tambaya tana bada attension ɗin ta ga Maman Nabila,saida ta ɗan yamutsa fuska sannan tace "" a zubar da shi kawai,""what? kina nufin inje a zubar da cikin daga nan na mutu ko? kujera Maman Nabila taja ta zauna sannan ta ce "' ku ke nan da ake raina muku hankali amma ni waye ya isa ya raina min wayo? waye ma yace miki ana mutuwa? da ana mutuwa da ban mutu ba,A tare mutanen gidan suka haɗa baki wajan cewa kina nufin kin ta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.