FANSAR FATALWA 009
*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️ )
_Tsarawa/Rubutawa_
*© SHAMSIYYA MANGA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*SADAUKARWA*: _Wannan book ɗin gaba ɗayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .
*Free book*
-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*
*009*
____________________________
Duk irin gudun da Amira take bata ji ko alamar gajiya ba balle kuma ta ji a ran ta wai ko zata tsaya.
Tayi Gudu mai nisa kasancewar makarantar ta su a bayan gari take ya sanya bata samu damar ƙarasowa inda take so ɗin ba sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana wannan gudun.
A dai-dai bakin wani gini naga taja tunga ta tsaya, a hankali kuma ta shiga mayar da numfashi kaɗan-kaɗan sannan naga ta ɗaga kai ta dubi ginin inda ta kai duban ta kan rubutun saman ginin ashe ma police station ne.
Tafiya ta fara yi cikin sauri har ta ƙarasa bakin police station ɗin inda ta shiga bubbuga ƙofar police station ɗin da sauri da sauri kamar an aiko ta.
Jin irin bugun da ake yiwa wajen ne ya sanya ƴan sandan da suke aikin kwana a wajen saurin miƙewa tare da ciro bindigogin su sannan suka nufi bakin ƙofar wajen ɗaya daga cikin yana furta.
"Waye a nan wajen".
Ya faɗa yana saita bindigar a saitin inda Amira take tsaye.
"Dan Allah ku taimaka ku buɗe ƙofar na zo ne domin naga DPO".
Amira ta faɗa cikin rawar murya.
Jin muryar mace da ƴan sandan suka yi ya sanya su saurin nufar bakin ƙofar amma duk da haka ba su mayar da bindigogin na su ba.
Ƙarasawa bakin ƙofar su ka yi sannan suka buɗe ƙofar, ai suna buɗewa kamar abun da Amira take jira kennan ta fara ƙoƙarin ture su dan shiga cikin police station ɗin ko tsoron bindigar hannun su bata yi ba.
Cikin sauri suma ƴan sandan suka riƙe ta tare da hankaɗo ta waje har sai da ta faɗi ƙasa, cikin fushi ɗaya daga cikin ƴan sanda ya dube ta sama da ƙasa sannan yace.
"Ai ni sai yanzu na lura ashe da mahaukaciya mu ke magana ban san ni ba, Kofur Audu ka kalle ta fa ƙafa ko takalmi ba bu wai take iƙirarin ta zo ganin DPO, to ke an gayamiki cewar DPO ɗin mutumin banza ne da zaki ɗebo dattin ƙafafuwan ki da wannan tsakiyar daren wai kin zo ganin DPO, ko an gayamiki haka kawai ake zuwa kai tsaye a ce za'a ga DPO ɗin? ".
Ya faɗa yana nuna ƙafar Amira yadda ta yi bututu kamar an tono ta daga rami tare da fashewa da dariya.
Shima ɗayan ɗan sandan dariya ya fara sannan ya tako ya iso har inda Amira take yashe wadda tun da suka cillo ta waje bata miƙe ba.
"Ke mahaukaciya mai ya kawo ki nan wajen?".
Ya faɗa da alamar izgilanci domin kuwa su har ran su sun ɗauka mahaukaciyar ce da gaske.
Wani abu ne ya taho ya tokare wutan Amira saboda takaici amma kuma ta sanyawa ran ta in sha Allah duk wani rashin mutunci da zasu mata zata jure shi har sai ta aiwatar da abun da ta ta yi niyya.
Miƙewa tsaye tayi tare da karkaɗe jikin ta sannan ta share hawayen takaicin da suka zubo mata tare da ƙara runtuma a guje ta hankaɗe su ta shige cikin police station ɗin tana cewa.
"Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, DPO dan Allah ka fito kana ina wallahi kai nake son gani".
Amira ta faɗa tana ƙarasa shigewa cikin police station ɗin tare da fara ƙolawa Dpo ƙira.
Wani ɗan sanda ne ya fito daga cikin wani office sanye da Kayan ƴan sanda sakamakon hayaniyar da ya ke ji ɗin ya sa ya farka daga baccin da yake ɗin.
A dai-dai wannan lokacin ne kuma waɗannan ƴan sanda guda biyun suka ƙaraso wajen kamar an jefo su inda suka fara ƙoƙarin kama Amira za su sake fitar da ita.
Ai Amira tana ganin haka ta nufi wannan ɗan sandan da yake tsaye tare da ruƙunƙume shi tana cewa.
"Yallaɓai wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, wallahi DPO na zo gani dan Allah ka taimaka kar ka bar su su fita da ni, idan kuma kai ne DPO ɗin ka sanar dani na ganka".
Amira ta ƙarasa maganar tana ƙara ƙanƙame shi domin kuwa ji take kamar waɗannan ƴan sandan za su fitar da ita waje.
"Yallaɓai ka gani ko wallahi wannan yarinyar mahaukaciya ce dan bana tantama cewar ba daga dawanau ta tsinko ta gudo ba".
Cewar Kofur Audu ɗin yana ƙoƙarin ƙarasawa wajen Amira domin ya kamo ta ya fito da ita daga wajen.
Hannu wannan ɗan sandan ya sanya ya ɓamɓare Amira daga jikin shi wadda tun daga yanayin yadda ya ganta ya tabbatar da cewar ba a hayyacin ta take ba.
Ai Amira tana ganin ya ɓamɓare ta daga jikin shi ta fashe da wani irin kuka sannan ta fara magana.
"Dan Allah ka taimaka mun wallahi matuƙar ban ga DPO a yau ba,rayuwa ta tana cikin matsala, dan Allah kar ka karo ni na rantse maka da Allah ina da hankali, wallahi mai hankali ce ni, dan Allah ka haɗani da DPO".
Amira ta faɗa tana zubewa a wajen tare da ƙanƙame ƙafafuwan wannan ɗan sandan.
Da sauri ya ɗago ta sannan ya kamo hannun ta tare da kai ta kan wata kujera ya zaunar da ita sannan yace.
"Kin ga ƴanmata ki nutsu, ki dawo hankalin ki sannan ki sanar da ni mai ke tafe da ke".
Shiru Amira ta yi tare da kafe gefe guda da ido sannan ta fara ƙoƙarin yin magana amma sai gani aka yi jikin ta ya shiga rawa,inda ta shiga nuna musu wani dungu a cikin police station ɗin tana zaro ido waje lokaci guda kuma ta sulale ƙasa ta sume a wajen.
Murmushi Amrah ta yi wadda take tsaye a dungun da Amira ɗin ta nuna cikin wata irin mummunar siffa, haƙoran ta zaƙo-zaƙo ga wani gashi da ya fito a duk wani sashi na jikin ta, hawaye take amma kuma hawayen jini kamar yadda ta saba kullum, cikin wata iriyar murya mai matuƙar tsoro tace.
"Kash!! Amira ban zo wannan wajen da niyyar cutar da ke ba, domin kuwa da kina daga cikin waɗanda zan ɗauki Fansa a kan su da ba zan bar ki har ki kawo wannan lokacin ba, ai ke baki cutar da ni ba kawai laifin ki ɗaya da ki ka kasa fitowa ki yiwa duniya bayani a lokacin da aka cutar da ni aka jefa rayuwa ta cikin tashin hankali wannan shine kawai laifin da ki ka mun, dan haka ni ba zan cutar da ke ba sai dai nasan dole daman idan kin yi arba da ni ki tsorata".
Amrah ta na kaiwa nan a zancen da take ɗin wanda ita kaɗai ta san mai take faɗa ta yi wata irin girgiza sannan ta bi ta jikin ginin police station ɗin ta fice daga wajen.
Ganin wannan halin da Amira ɗin ta shiga ya sanya wannan ɗan sandan umurtar Kofur Audu da ya miƙo mishi ruwa da gaggawa.
Aikuwa ana kawo mishi ruwan ya ɗeba a hannun shi tare da watsawa Amira a fuskarta.
A firgice Amira ta farka tana sakin wani irin gigitaccen ihu tare da miƙewa da gudu zata fice daga wajen tana cewa.
"Wallahi idan har ba ku yi gaggawar haɗa ni da DPO ba ku ka bari har ta yi nasarar hallaka ni kamar yadda ta hallaka ƴan uwana to tabbas alhakin mutuwa ta ya rataya a kan ku".
Da sauri ƴan sanda biyu nan suka kamo ta tare da zaunar da ita ganin da gaske fa ta fice a hayyacin ta.
A wannan lokacin duk wani mai rai da yake kusa da cikin police station ɗin sai da ya farka hatta waɗanda suke cikin cell a rufe sai da suka farka suka tashi suka zazzaua, sakamakon ihun da Amira ɗin take ba na wasa bane, inda wasu suka shiga leƙowa dan bawa idon su abinci gashi lokacin ƙarfe uku har ta yi.
Wayar shi wannan ɗan sandan ya zaro sannan ya shiga contact ɗin shi ya binciko wata number tare da yin dialing ɗin ta.
*****
A can Clinic ɗin makarantar su Amira kuwa bacci mahaifiyar ta take ba ta san abun da yake faruwa ba sakamakon yadda baccin na ta ya yi nisa duba da yadda kwanakin biyun nan bata samun rintsawa, yau ɗin ne kawai ta samu ta rintsa da yawa har haka.
Can wajen ƙarfe uku kamar wanda aka zabure ta, ta farka firgigit sakamakon wani mummunan mafarki da ta yi, inda taga Amira ɗin a cikin wani mummunan yanayi.
Wannan mafarkin ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba inda ta farka cikin sauri tare da miƙewa zaune tana kai duban ta kan gadon da Amira ɗin take kwance.
Kasancewar wutar lantarkin ɗakin a kunne take shi ya bata damar hango gadon da Amira ɗin take kwance wanda yake wayam ba alamar mutum a kai.
Daram gaban ta ya bada wani irin sauti mai ƙara lokaci guda kuma ta dafe ƙirjin ta tare da miƙewa tsaye tana furta.
"Innalillahi wa'innailaihi rajiun mai nake gani haka!, Ina Amira ta shiga kuma?".
Ta faɗa tana nufar hanyar toilet dan dubawa duk kuwa da cewar bata ga alamun cewar akwai mutum a cikin toilet ɗin ba.
Sai da ta fara ƙwanƙwasa ƙofar sannan ta fara ƙira sunan Amira ɗin.
"Amira kina jina kuwa".
Ta faɗa tana kasa kunne a jikin ƙofar ko zata ji alamar motsin mutum, sai dai shiru ba alamar da mutum a cikin toilet ɗin.
Tura ƙofar tayi inda ta shiga cikin toilet ɗin sai dai wayam ba alamar cewa ma wani ya shiga cikin toilet ɗin.
"Hasbunnallahu wa ni'imal wakil innalillahi wa'innailaihi rajiun" .
Su ne kalmomin da suka shiga fitowa daga bakin mahaifiyar Amira ɗin wadda hankalin ta ya yi masifar tashi, lokaci guda kuma ta ji wata irin hajijiya tana shirin kwasar ta, da sauri ta dafe jikin bangon toilet ɗin sannan ta fara sulalewa a wajen tana yin zaman ƴan bori.
Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga biyowa ta kuncin ta cikin kuka ta fara magana.
"Shikennan abun da na daɗe ina gudu ya faru ya faru!, Shikennan Amira kema sun kashemin ke!, Ai ni daman tun da naga an kashe aminan ki jikina ya ban ba za'a ƙyale mun ke ba, innalillahi wa'innailaihi rajiun, yanzu wannan wana irin tashin hankalin ne hak, yanzu wana la'annanne ne yake bibiyar ku ɗaya bayan ɗaya shin mai ku ka aikata mishi haka?".
Ta ɗauki tsawon lokaci a zaune a bakin ƙofar toilet ɗin kafin wata zuciyar ta ce mata.
" _Kinga zama bai kama ki ba, kamata ya yi ki tashi ki fita ki duba waje ko Allah zai sa ki ganta_ ".
Aikuwa tana kaiwa nan a zancen zucin nata ta miƙe da sauri sannan ta fice daga cikin ɗakin, Kasancewar dare ne ya sanya bata haɗu da kowa ba a filin makarantar.
Kai tsaye bakin gate ta nufa inda taje ta tarar da jami'an tsaro a tsaitsaye kamar masu jiran ko ta kwana.
Tun da Inspector Rasheed ya hango mace ta nufo inda suke ɗin cikin sauri kamar zata kifa da bakin ta jikin shi ya bashi ba lafiya ba.
Gaba ɗaya jami'an tsaron ido suka zuba mata suna jiran su ji da wacce ta zo.
Tana isowa wajen ta fashe da kuka sannan ta buɗi baki cikin rawar murya ta fara magana.
"Yallaɓai sun sace Amira na tabbatar da cewa a yanzu sun riga da sun hallaka ta kamar yadda suka hallaka sauran ƴan uwan ta, yallaɓai ku taimaka dan Allah nikam ko gawar ta a kawo mun na ganta kaf.......".
Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon wani kuka da ya ci ƙarfin ta.
Dafe kan shi Inspector Rasheed yayi cikin tsananin tashin hankali, anya kuwa makashin ƴan mata nan mutum ne?, Idan kuwa har mutum ne to tabbas a cikin makarantar nan yake rayuwa, domin kuwa abun shikam ya fara bashi tsoro ya za'a yi a ce suna tsaye a wajennan ko rintsawa ba su samu damar yi ba amma ace an shiga har cikin Clinic ɗin an kashe yarinyar, to amma yanzu kana da tabbacin an kashe ta ɗin ne?, Wata zuciyar ta jefa mishi wannan tambayar.
Aikuwa cikin sauri ya kawar da tunanin da yake sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira ɗin da take dirzar kuka kamar ran ta zai fita yace.
"Kin ga ki nutsu ki mun bayanin abun da ya faru da Amira ɗin".
Goge hawayen ta tayi tare da sanya bakin hijab ɗin ta ta fyace majinar da ta zubo mata sannan ta fara mishi bayani tun daga farkawar da tayi bata ga Amira ɗin ba har zuwa yanzun da take tsaye a gaban su.
Hankalin jami'an tsaron wajen ba ƙaramin tashi yayi ba, musamman Inspector Rasheed.
Har ya buɗi baki zai yi magana sai kuma ƙira ya shigo wayar ta shi, ganin wanda yake ƙiran nashi ya sanya ya yi saurin ɗaga wayar tare da karawa a kunnen shi.
*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .