FANSAR FATALWA

FANSAR FATALWA 010

by @shamsiyyamanga

*FANSAR FATALWA*

( _Horror Story_ 💀☠️).


_Tsarawa/Rubutawa_


© *SHAMSIYYA MANGA*


*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*


*SADAUKARWA*: _Wannan book ɗin gaba ɗayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.


*Free book*


-------------------------------------------

*Bissimillahir rahmani rahim*

*010*

____________________________


*Not Edited* .

Shiru Inspector Rasheed ya yi ina sauraran abun da ake faɗa mishi a cikin wayar kafin daga bisani naji yace.


"Ok to shikennan ku barta a wajen kar ku barta ta tafi ina zuwa nima akwai ƴar wata matsala ce da ta ta so in sha Allah idan na shawo bakin ta zan shigo zuwa nan da asubah, amma kasan DPO a wannan lokacin ko ka ƙira shi ba samun wayar shi zaka yi ba,so kar ka ƙira shi ka bari mu ga zuwa safiya".


Inspector Rasheed ya faɗa, ban ji abun da aka ce mishi a ɗaya ɓangaren ba sai ji nayi yace.


"Ok to shikennan duk yadda zaku yi dai kar ku ƙyale ta ta tafi".


Yana kaiwa nan a zancen na shi ya katse wayar sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira da har a wannan lokacin bata daina kukan da take ɗin ba.


"Uhmm Mama dan Allah ki daina wannan kukan kiyi haƙuri in sha Allah daga yanzu zuwa safiya zamu yi duk ƙoƙarin da zamu yi domin ganin mun gano wanda yake da hannu a wajen ɓatan Amira ɗin".


Ya ƙarashe maganar cikin sigar rarrashi.


"Yallaɓai ni wallahi a yanzu buƙata ta ko gawar Amira na kalla domin kuwa na tabbatar i zuwa yanzu sun daɗe da hallaka ta,na tabbata ba zasu ƙyale ta ba itama kashe ta zasu yi kamar yadda suka kashe sauran ƴan uwan ta, Allah ya ji ƙanki Amira ya saka muku a kan duk wanda yake aikata muku wannan zaluncin".


Mahaifiyar Amira ta faɗa tana durƙushewa a wajen sakamakon kukan da yaci ƙarfin ta.


Shikam Inspector Rasheed rasa abun da yake mishi daɗi yayi wannan bala'in har yaushe, tabbas duk wanda suka kama da hannu a wannan aika-aikar ba zasu mishi da daɗi ba,har ya hango irin hukuncin da za'a zartar mishi.


Da ƙyar dai ya lallaɓa mahaifiyar Amira ta tashi daga wajen sannan suka sanya ta a mota suka mayar da ita gidan ta.


*****


Lokacin da suka mayar da ita gidan nata har asubah ta kawo kai domin kuwa a lokacin har ƙarfe biyar ta yi dan haka suna kai ta gidan nata suka dawo wani massallaci da yake ɗan gaba da gidan kaɗan suka gabatar da sallar asubah kafin suka miƙe suka nufi police station ɗin.


Shigar su cikin police station ɗin ne suka yi arba da abun da ya yi matuƙar ba su mamaki.


Amira suka gani a zaune a bakin kanta ta kafe ƙofar shigowa cikin police station ɗin da ido ko ƙiftawa bata yi.


Wata zabura Kofur Bala yayi ya maƙale a bayan Inspector Rasheed yana furta.


"Yallaɓai Fatalwa, innahu min sulaimanu wa innahu bissimillahir rahmani rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, yallaɓai ka ga abun da idanuna suka gane mun kuwa".


Ya ƙarashe maganar yana ƙara shigewa jikin Inspector Rasheed ɗin domin kuwa shi har ran shi yayi tunanin Fatalwa ce kuma yayi tunanin shi kaɗai yake ganin Amira ɗin.


Tsawar da Inspector Rasheed ɗin ya buga mishi ne ta dawo dashi daga haukar da yake ɗin.


"Wai kai Kofur Bala mai yasa wani lokaci lamarin ka sai a hankali ne, yanzu fisabillillahi ina Fatalwar take a wannan wajen?, Ko kuma an ce maka ita wannan ɗin gawa ce?, Kuma wai a hakan kana iƙirarin kai jami'in Ɗan sanda ne ko?, Dallah ni malam sakar mun kaya".


Inspector Rasheed ya faɗa yana ɓamɓare hannun Kofur Bala ɗin daga jikin shi.


A sannan ne kuma waɗannan ƴan sandan suka fito daga wani ɗaki alamar salla suka yi.


"Inspector Rasheed har kun iso kennan?".


Da sauri Inspector Rasheed ya ƙarasa wajen shi yana riƙo hannun shi suka nufo wajen da Amira take rakuɓe sannan ya fara magana fuskar shi da alamun mamaki.


"Asp Sadiq a ina ku ka samo wannan yarinyar?".


Murmushi Asp Sadiq yayi sannan ya nuna Inda Amira take yace.


"Wannan ai ita ce yarinyar da na ƙira ka a kan ta wadda na sanar da kai cewar ta zo tana son ganin DPO".


Wata doguwar ajiyar zuciya Inspector Rasheed ya sauƙe tare da furta godiya a Ubangiji a fili.


Kllon shi Asp Sadiq ya yi fuskar shi da alamar tambaya sannan yace.


"A'a ya naji kana sauƙe numfashi haka ko dai ka santa ne?".


"Tabbas kuwa na santa, ina case ɗin da yake hannu na na waɗannan ƴanmatan da aka kashe har guda uku a jami'ar Ahmadu Bello?".


Inspector Rasheed ya faɗa yana kafe Asp Sadiq da ido.


"Ƙwarai kuwa na gane,kar fa kace mun wannan yarinyar tana da hannu a cikin wannan kisan da ake yi ɗin?".


Ya ƙarashe maganar cikin zaro ido waje.


"Ko kaɗan ba hannun ta a ciki asali ma yanzu haka rayuwar ta tana cikin haɗari domin kuwa gaba ɗaya waɗanda aka kashe ɗin tana da alaƙa ta kusanci sosai da su,idan ka yi duba da irin zazzafan amintar da take tsakanin su ba wanda bai san irin ƙawancen na su ba,yanzu haka maganar da nake maka mahaifiyar ta tana can hankali a tashe a tunanin ta an kashe mata ƴa kamar yadda aka kashe sauran abokanan ta, to amma abun da ya bani mamaki shine mai ya kawo ta police station ɗin?".


Inspector Rasheed ya faɗa yana kai duban shi inda Amira take rakuɓe wadda har a wannan lokacin idanun ta ba su daina zabur da hawaye ba.


"To gaskiya ni dai ban ba zance maka nasan takamaiman abun da ya kawo ta nan ba domin kuwa lokacin da ta zo ta sanar da mu kawai ita Dpo take son gani".


Shiru gaba ɗaya suka yi kafin a hankali Inspector Rasheed ya ƙarasa wajen Amira da take ta rarraba idanu kamar a ce mata firit ta ruga da gudu.


"Amira".


Inspector Rasheed ɗin ya ƙira sunan ta yana mai tsugunawa a kusa da ita.


Ɗago ido Amira ta yi ta kafe shi da ido ba tare da tace uffan ba.


"Amira kina jin yunwa a kawo miki abinci".


Saurin jijjiga mishi kai ta yi, wanda sai a wannan lokacin ta samu damar yin magana cikin rawar murya tace


"A'a bana son in ci komai, dan Allah buƙata ta nidai kawai ku haɗani da DPO saboda nasan wallahi nima ta kusa kashe ni, nasan ba zata bar ni ba kashe ni zata yi dan haka tun kafin lokaci ya ƙure ku haɗani da DPO domin na bayyana mishi wata ɓoyayyar gaskiya wadda burin ku shine ku gano ta".


Ta ƙarashe maganar cikin sakin wani irin marayan kuka.


"Kin ga Amira ki nutsu in sha Allah ba wadda zata kashe ki, yanzu ki nutsu ki sha ruwa sannan kimun bayanin abun da yake tafe da ke".


Inspector Rasheed ya faɗa yana tsiyayo ruwa a cikin wani kofi da Kofur Bala ya kawo mishi sannan ya miƙa mata.


Karɓar ruwan Amira ta yi amma bata sha ba sai ma kafe ruwan da ta yi da ido sannan ta ɗago kai daga bisani tace.


"Ina mahaifiya ta?".


Kallon ta Inspector Rasheed yayi cike da mamaki kafin daga bisani yace.


"Mahaifiyar ki tana nan cikin ƙoshin lafiya tana gida".


Ɗan shiru ta yi kafin tace.


"Ina son kafin na sanar da ku abun da ya faru dan Allah ina son na nemi wata alfarma daga wajen ku".


"Ok to shikennan ki faɗa in sha Allah za'a miki ita".


"Ina son dan Allah a ƙira iyayen su Afrah da Azra da Anisa da kuma Anwar domin a gaban su ne kaɗai zan iya bayyana irin mummunar aika-aikar da ƴaƴan su suka aikata har yake bibiyar su".


Kallon Asp Sadiq Inspector Rasheed yayi sannan kuma daga bisani ya mayar da kallon shi kan Amira yace.


"Meyasa sai a gaban iyayen su zaki iya sanar da mu abun da yake faruwa?".


"Saboda hakan ne kawai zai wanke musu raɗaɗɗin kisan da aka yiwa ƴaƴan su, sannan kuma hakan zai sa su gane cewa kowane abu aka yiwa ƴaƴan su su suka janyo, kuma hakan zai sa su daina ganin laifin wanda yake kashe mu su ƴaƴan su daga haka sai su koma ganin laifin ƴaƴan su domin kuwa ko mai ne su suka janyo wa kan su, idan da hali ma ina buƙatar a gayyato ƴan jarida da kuma hukumar makarantar mu domin a samu a yaɗa labari a duniya ko hakan zai sa masu son zuciya irin ta su su shiga hankalin su".


Mamaki ne ya kama su Inspector Rasheed inda suka shiga kallon-kallo da kuma mamakin kalaman Amira ɗin.


Duban agogon hannun shi Inspector Rasheed inda ya ga har ƙafa shiga ta gota sannan ya dubi Asp Sadiq yace.


"Asp bari naje gida na yi wanka daga can zan biya ta gidan iyayen yaran can dan na sanar da su ko zasu samu damar zuwa dan mu ji abun da yake tafe da wannan yarinyar".


Inspector Rasheed ya faɗa yana mikewa daga tsugunen da yayi da sauri Asp Sadiq ya dube shi yace.


"Ai nima tare zamu wuce domin kuwa kaga jiya ban kwana a gida ba, wallahi wasu yara aka kawo wanda yasa dole aka ƙirani na zo to kuma na zo kennan ban daɗe ba wannan yarinyar ta zo ta".


Asp Sadiq ya faɗa yana bin bayan Inspector Rasheed ɗin inda su kuma sauran ƴan sandan suka tsaya jiran ma su aikin safe su zo su karɓe su suma su tafi.


Sai da Inspector Rasheed ya fara biyawa ta gidan su kasancewar ba shi da aure, wanka ya fara yi kafin ya fito ya je part ɗin mahaifiyar shi inda ya same ta zaune ta kammalla haɗa breakfast.


Waje ya nema ya zauna a gefen ta kafin ya shiga gaishe ta.


Amsawa tayi sannan ta dube shi tace.


"AbdulRasheed naga kwana biyu wannan case ɗin da ka ke gaba ɗaya ya sa ka fara fita a hayyacin ka, ni dai dan Allah abun da nake so da kai kuma wanda kullum na sha faɗa maka shine ka kula kuma ka riƙe gaskiya da amana kar a baka kuɗi ko wani abu wanda zai sa ka danne haƙƙin mai gaskiya har ka bawa marar gaskiya gaskiya, sannan addu'a kullum ina faɗa ma addu'a ita ce jagaba a komai idan har ka riƙe addu'a to tabbas ka riƙe babban makami wanda zai kare ka daga dukkan wani sharri dan haka ka kula kaji".


Sosai maganar mahaifiyar ta shi ta shige shi inda ya dube ta yace.


"In sha Allah Ummu kamar yadda kika sanni a da to ba zan taɓa sanjawa kuma addu'a ina kan yin ta zan kuma cigaba da yi in Allah yarda".


Bayan sun gama cin abincin addu'a ta mishi sosai kafin kuma ya miƙe ya mata sallama, lokacin ƙarfe takwas da rabi sannan ya fita, duk da irin baccin da yake ji amma haka ya fita, kai tsaye gidan su Afrah ya fara nufa.


A dai-dai bakin gate ɗin gidan su Afrah ɗin suka ci karo da mahaifin ta da kuma yayan ta Aliyu sun fito zasu tafi wajen aiki.


Gaisawa suka yi da Inspector Rasheed ɗin cikin sakin fuska kafin Inspector Rasheed ɗin ya dubi mahaifin Afrah ɗin ya fara mishi bayanin abun da yake tafe da shi ɗin.


Ɗan shiru suka yi daga mahaifin Afrah ɗin har yayan nata kafin daga bisani kuma mahaifin Afrah ɗin ya ɗago ya dubi Inspector Rasheed ɗin yace.


"To amma Inspector a ganina meye dalilin yarinyar na ganin dole sai a gaban mu zata sanar da komai?".


"To Alhaji nima abun da na kasa fahimta Kennan amma ina ganin ku yi haƙuri mu je idan ya so mu ji abun da yake tafe da ita ɗin".


"To Shikennan Inspector bari na shiga na sanar da mahaifiyar ta sai ta shirya mu wuce".


"To ni dai yanzu idan kun shirya kwa same mu a can police station ɗin domin kuwa yanzu haka ma zan wuce gidan sauran iyayen yaran ne".


Inspector Rasheed ya faɗa yana juya sannan ya shiga motar shi ya nufi gidan su Anwar bayan ya karɓi address ɗin shi a wajen Aliyu.


Lokacin da ya je wajen Anwar ɗin bai wani samu damuwa dashi ba, haka a ɓangaren mahaifin Anisa ma inda shima yace zasu shirya su biyo su daga baya.


Daga gidan su Anisa gidan su Azra ya nufa sai dai bai tarar da mahaifin ta a gida ba inda mai gadin gidan ya sheda mishi cewar ya tafi office, wayar shi ya ƙira amma bai ɗaga ba dan haka kawai ya yanke shawarar ya je ya same shi a office ɗin.


Hakan kuwa aka yi inda ya nufi office ɗin Justice Kabir ɗin, bai wani samu matsala wajen ganin Justice Kabir ɗin ba sai dai kuma inda gizo ke saƙar shine Justice Kabir ya daga tsallen aradu yace.


"Ni ai daman na san wallahi makashin ƴata a cikin shegun yaran nan yake,watau sai da ta bisu ɗaya bayan ɗaya ta kashe su tukunna zata wani kai kan ta police station ɗin ai cuta kam an riga an gama cutar mu, dan haka wallahi itama ta shiryawa karɓar nata hukuncin dan kar ta ga ta kai kan ta police station ta yi tunanin cewar hakan zai sa a sassauta mata hukunci, to ba zai yiwu ba wallahi sai ta tafi inda ta aika mun ƴata".


Shi dai Inspector Rasheed haƙuri ya bashi sannan ya lallaɓa shi suka tashi suka nufi police station ɗin.


A zazzaune suka tarar da kowa ya hallara a office ɗin DPO ɗin su kawai ake jira, ga Amira kuma a zaune a gefe ido yayi jawur tun da suka shiga cikin office ɗin DPO ɗin mahaifin Azra yake jefawa Amira mugun kallo ji yake kamar ya shaƙe ta ta mutu.


Gyaran murya DPO yayi bayan kowa ya nemi waje ya zauna sannan yace.


"To yanzu dai Alhamdulillahi mun hallara kamar yadda malama Amira ta buƙata dan haka muna sauraran ki shin mai yake tafe dake?, ga dai iyayen yaran da aka kashe nan a gefe suna sauran ki, ga kuma ƴan jarida kamar yadda ki ka buƙata su ma sun zo, ga wasu daga cikin hukumar makarantar ku su ma sun samu damar halartar wannan wajen, kowa ya baza na zumaye da na mujiyar shi yana sauraran abun da zaki faɗa".


DPO ya faɗa yana mai zuba idon shi a kan Amira.


Ɗago jajayen idanun ta ta yi tare da sanya hannu ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta fara magana cikin kuka.


A dai-dai sannan kuma ƴan jarida suka saita camera ɗin su da abun ɗaukar sauti a dai-dai fuskar Amira ɗin.


*MANGA* ✍️.

_Comment_

_Share_

_Fisabillillahi_.