Chapter 11
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 11*
Kusan a tare suka isa inda Jannat take zaune shida Mufeedah ya bud'e gaban motar yana fad'in, "Jannat lafiya meya same ki?." Ta kifa kanta a kan cinyoyin ta hakan ya saka Mufeedah bata da fuskar ta ba a lokacin sai maganar ta take ji tana fad'in, "Yaya mu tafi kaina."
"Ciwo kan yake miki?." Ya sake tambayar ta cikin rud'ewa yana so ya d'ago ta amma tak'i bada damar hakan sai sake b'oye fuskar ta da take a tsakanin cinyoyin ta. "Ai ba gida ya kamata a tafi ba gwara muje asibiti a duba ta." Mufeedah ta fad'a tana kallon sa zaiyi mgana tace, "A'a nidai muje gida, kazo mu tafi." Ta sake fad'a cikin kuka sosai ba shiri ya kulle inda take ya zagaya ya shiga ya kunna motar ya bar wajan da sauri dan shi ya manta maganar da sukayi da Mufeedah a lokacin.
Ajiyar zuciya Mufeedah tayi ta koma ciki jikin ta sanyaye sosai.
Tunda suka tafi yake ta aikin jera mata sannu tana jin sa tak'i kuma d'ago kanta sai kuka da take tayi mai sauti, "Jannat ki bar wannan kukan ko shi zai k'ara miki ciwon ai." Bata iya magana ba ba kuma daina kukan ba dan yadda take jin zuciyar ta in bata yi kuka ba baza ji zatayi kamar lokacin mutuwar tane yayi.
A haka suka k'arasa gida ya bud'e mata ta fito suka shiga gidan a tare kamar koda yaushe Gwaggo na zaune ita kad'ai tana shan iska, ganin su sun shigo tabi Jannat da kallo kafin tace, "A'a Imrana lafiya?."
"Gwaggo kanta ne yake ciwo, ina maganin ta?." Ya fad'a bayan yaga ta zauna yana kallon Gwaggo.
"Yana d'aki." Tana fad'ar hakan ya shiga ciki ya dawo tare da maganin ya kawo mata had'e da ruwa tasha, Gwaggo ya kalla yace, "Gwaggo bara naje na dawo." Ya fad'a yana fita ta bishi da kallo tana aiyana abubuwa da yawa a ranta.
Mik'ewa Jannat tayi ta shiga band'aki tayi alwala ta shige d'aki dan gabatar da sallar i'sha.
Imran kuwa yana fita suka had'u da Nura yace, "D'an halak fitowar da nayi kai nake niyar kira." K'arasawa sukayi wajan k'aramin dakalin dake k'ofar gidan suka zauna Nura yace, "na d'auka ai ka manta ma munyi zamu had'u dan kai in kana tare da Jannat baka ji baka gani." D'an murmushi yayi kad'an kafin yace, "to kaga laifi na? Ita kad'ai ce fa k'anwa ta ai dole naji da ita sosai dan ita d'in ta musamman ce."
"Ni dama zaka bani auren ta wallahi da naji dad'i." Murmushin dake kan fuskar sa ya nema ya rasa a lokacin ya d'ago idon sa ya kalli Nura yace, "mu bar maganar Jannat, meye kake nema na?."
Nura yayi murmushi mai cike da tarin ma'anoni yace, "daman abinda ya kawo ni wajan naka kenan ai, son Jannat nake kuma da aure." Imran ya kasa cewa komai sai kallon Nura da yake yi cikin rashin sanin abinda zaice masa, ganin hakan Nura ya saka shi yace, "kayi shiru ko baza ka bani ita bane kake kallo na?."
"Har nawa Jannat d'in da take da zakayi min maganar auren ta? Infact bana son yi mata maganar soyayya yanzu sai ta kusa kammala karatun ta sai dai in zaka jira." Nura da yake kallon sa yace, "me zai hana na jira abinda nake so ne fa, amma ka bani number wayar ta dan Allah gaisawa kawai zamu dinga yi tasan kuma dani a masu son auren ta." Tsaki yaja wanda bai san ya fito ba yace, "na fad'a maka bana son abinda zai raba mata hankali ka bar maganar nan please."
Dariya Nura yayi sosai kafin yace, "to duk meya kawo wannan fusatar haka?." Imran ya kalle shi ya harare shi baice komai ba dan wani irin zafi yake ji a k'asan zuciyar sa.
"Imran kenan, na fad'a maka wallahi kana son Jannat so na aure amma sai kace ba haka ba gashi yau kana nuna kishi k'arara a kan nace ina son ta, kwantar da hankalin ka wasa nake wallahi domin nasan indai kana raye babu wanda Jannat zata aura in ba kai ba dan itama son naka take yi."
Kallon sa Imran yayi yace, "nifa bawai kishi nake ba kawai bana son a raba mata hankali dan nafi kowa sanin yadda take qaunar karatun ta, kuma waye yace maka Jannat na sona?." Nura yace, "ai basai ta fad'a ba labarin zuciya ai a tambayi fuska, wallahi tallahi kana son Jannat haka itama tana son ka da aure, kai taurin kanka da musun tsiya ya hana ka gani ita kuma rashin furtawar ka ya hana ta furta maka."
D'an jimm Imran yayi kafin yace, "kai Nura wannan ai kutse ne da bin diddigi in ba haka ba ta yaya zaka san abinda yake raina ko yake ranta? Nida Jannat babu soyayyar aure a tsakanin mu sai soyayyar Yaya da k'anwa kawai."
"Haka kake gani kuma kake cewa amma ba haka abinda yake a bad'ini ba, kayi tunani dakyau ina tabbatar maka zaka fahimci abin kake ji a kan Janant ba soyayyar wa da k'anwa bane ba, kana kishin ta sabida kar maza su dinga ganin ta ya saka ka kwashe komai naka ka siyi mota na farko kenan, na biyu ka hana ta hawa napep sabida baka son a had'a ta da namiji a wajan zama, na uku ka hana ta kula kowa kace sai ta kusa gama karatu, na hud'u ko waye yazo ya same ka a akan yana son ta baka bashi fuskar koda kula ta, na biyar....." kafin ya k'arasa Imran da jikin sa yayi sanyi yace, "Dakata Nura dan Allah, duk abinda ka lissafo haka ne amma bawai dan ina son ta da aure bane ya saka nayi hakan, ina kishin ta matsayin ta na mace kuma k'anwa ta."
"Meyasa baka jin hakan akan ko wacce mace sai ita kad'ai kawai? Imran ina fad'a maka gaskiya ne gwara ka farka daga baccin da kake yi tun yanzu kafin lokaci ya k'ure maka, kun dace da kai da Jannat sabida dukkanin ku kuna son junan ku." Da mamaki Imran ya kalle shi yace, "na shiga uku ni Imrana, wai waye yace maka ita Jannat d'in sona take yi ne?."
"Wai sai an fad'a min zan gane? Labarin zuciya a tambayi fuska haka hausawa suka ce kuma hakan ne, kayi tunani dakyau akan lamarin ta zaka gane komai da kanka indai ka nutsu ka fahimci komai yadda yake da kanka zaka gane ta jima da fad'awa tarkon qaunar ka, kana son ta kaima gwara ka furta tun kafin kwad'o yayi maka k'afa."
Imran ya yake k'okarin fad'awa duniyar tunani yace, "shikenan naji, yanzu dai meke tafe da kai?." Nura yace, "gobe zaka raka ni gidan su wacce zan aura zamu gaida iyayen ta."
"Gobe da yaushe kenan?."
"Kamar da yamma in ka dawo daga aiki."
"To Allah ya kaimu, ni bara na shiga gida." Ya fad'a yana mik'ewa tsaye dan yana buk'atar keb'ewa yayi tunani.
Shima mik'ewa yayi yace, "to mu kwana lafiya a gaida Umma." Kai kawai ya d'aga masa ya shiga gida shi kuma ya wuce.
Kasancewar tara ta wuce yasan Umma ta kwanta zuwa lokacin ya shiga d'akin sa yayi shirin bacci ya kwanta, duniyar tunani ya fad'a akan abinda Nura ya fad'a masa, mik'ewa zaune yayi lokacin da ya tuno maganar Jannat inda take tambayar sa yana da budurwa, yadda sukayi da ita lokacin da bata da lafiya ya sake fad'o masa a rai lokacin da take cewa wanda take so ya mutu, kansa ya dafe da hannayen sa ya tuna yadda tayi k'ara a lokacin da Mufeedah tace tana son sa, "kenan da gaske Jannat na sona da aure? Hakan yana nufin duka a kaina take shan wannan wahalar? Hasbunallah ya akayi ban fahimta ba sai yanzu?." Ya fad'a a fili yana mik'ewa tsaye.
Wayar sa ya d'auka ya kiran number Jannat ya kara a kunne, Jannat tana jingine a jikin katifar ta ta kulle ido taji k'arar wayar ta ta kalla taga Yaya na hakan ya saka ta jawo wayar ta d'auka tare da karawa a kunne.
Daga can b'angaren yace, "Jannaty."
"Na'am Yaya."
"Bakiyi bacci ba?."
"Uhum banyi ba."
"Me kike yi har yanzu baki kwanta ba? Ko jikin ne?."
Sai da ta d'an sauke numfashi ta sake rik'e wayar a kunnen ta tace, "A'a naji sauk'i kawai bana jin baccin ne." "Meyasa bakya jin baccin bayan gobe kina da lecture?."
"Nima ban sani ba Yaya kawai ji nake bazan iya bacci ba." Shiru yayi baice komai ba yana nazarin ta yaji tace, "Yaya!." Ta fad'a cikin sanyin murya wanda hakan ya saka shi lumshe idon sa ya bud'e can k'asan mak'oshi yace, "Na'am Jannaty." Sai da ta had'd'iye saliva sannan tace, "wacce muka je wajan ta d'azu wacece?." D'an murmushi yayi kad'an ta ta jiyo sautin sa yace, "wacce nake aiki a k'ark'ashin tace, wani abun ne?."
"Kaima kana son nata kamar yadda tace tana sonka?." Ta fad'a muryar ta na rawa kamar zatayi kuka. Zama yayi a gefen shinfid'ar sa yace, "bana ce ba dai gaskiya."
"Yauwa Yaya kar ka sota dan Allah." Ta fad'a a lokacin hawaye suna sakko mata a idon ta.
"Meyasa kika ce kar na sota?."
"Sabida ni bana so naga mace ta fara cewa tana son namiji kamar rashin aji ne hakan."
"Waye ya fad'a miki rashin aji ne Jannat?."
"Kawai nice na gani."
"Ba rashin aji bane ai barin kashi a ciki baya maganin yunwa sai dai ya zama cuta, haka barin magana a zuciya baya maganin matsala sai dai ya haifar da ciwo gwara ka fad'a ka huta."
Ajiyar zuciya tayi har ya jiyo sautin ta sannan tace, "Amma in ka furta kuma yace baya sonka ai kaga babu dad'i kuma ka riga ka fad'a gwara ka barshi a ranka yafi."
Shiru yayi wani tunani ya fad'o ransa yace, "shiyasa ke kika ki fad'awa wanda kike so har ya bar duniya kenan?." Kamar yana gaban ta ta share hawayen ta tace, "Uhum sabida ina jin tsoron kar yace baya sona shiyasa nayi alqawari koda son sa zai kashe ni bazan fad'a masa ba." Jinjina kai Imran yayi ya sake gasgata maganar Nura yace, "Yanzu misali nine wanda kike so d'in zaki kasa fad'a min nima?."
Shiru tayi tana raba ido gaban ta ya fad'i tana tunanin karfa ya gano tane ya saka yake mata tambaya haka, maganar da ya sake yi ya saka ta dawo hankalin ta tace, "Ai ba kai din bane bama." Sai da yayi murmushi kana yace, "ai a misali nace miki."
"Ko kai d'in ne bazan iya fad'a ba gaskiya." Kamar tana gaban sa ya zaro ido yace, "kin yadda silar hakan kiyi rashin lafiya a akan ki fad'a min? Nifa ba kamar kowa nake ba ki tuna."
Dafe gefen zuciyar ta tayi sabida bala'in bugun da take mata ta daure tace, "Gaskiya bazan iya ba." Jinjina kai yayi wani bala'in tausayin ta mai had'e da soyayyar ta ya shige shi ya sake tausasa murya yace, "Amma ni kuma inda ni d'in ne in na gano a kai na kike rashin lafiya bazan ji dad'i ba zan kuma yi fushi dake a kan hakan." Bata ce komai ba sai hmmm ta kawar da zancen tace, "To yanzu Yaya meye matsayin ita shugabar taku a ran ka?."
"Bata da wani matsayi a waje na amma ina tunanin zan mata matsayin." Sautin kukan ta yaji hankalin sa ya tashi yace, "Jannat meye na kuka kuma muna hira?."
"Dan Allah Yaya kar ka mata wani matsayi ka bata hak'uri kar ka sota dan Allah." Ta fad'a cikin muryar kuka sosai. Dafe kansa yayi sannan yace, "Shikenan Jannaty kwantar da hankalin ki bazan bata ko wanne matsayi a raina ba bayan na shugaba ta da take dashi, ki daina wannan kukan bazan yi ba tunda bakya so." Sassauta kukan tayi tace, "nagode Yaya na."
"Abinda kike so shi nake so Jannaty, na bar miki zab'i ki zab'a min duk wacce kike ganin mun dace da ita kinji ko?." D'aga kanta tayi tace, "to Yaya na."
"Yanzu ki kwanta dare yayi gobe zaki je makaranta amma kafin nan kiyin alqawarin baza ki kwana kina kuka ba." Hawayen idon ta ta share tace, "bazan ba nayi alqawari."
"To shikenan ki kwana lafiya, kuma gobe in Allah ya kaimu akwai wani abu na ban mamaki da nake so zan nuna miki shi."
"Allah ya kaimu Yaya na ina jiran naga meye, Allah ya tashe mu lafiya." Ya amsa da amin tare da kashe wayar.
Da baya ya kwanta a kan katifar yana jin wani irin zafi a zuciyar sa wanda bai san dalilin sa ba, "yanzu kenan ta tabbata sabida ni Jannat jinin ta hau? Kenan sabida ni duk take shiga damuwa har haka? Meyasa ban fahimci tana sona tun farko ba na barta tana shan wahala." Ya fad'a a bayyana kamar yayi kuka dan ba k'aramin tausayin ta yake ji ba.
Da wannan tunanin shima bacci ya d'auke shi bayan ya jima yana saqa da warwara.
Washe gari da wuri ya shirya ya fita dan yasan Jannat bata da lecture sai sha biyu na rana hakan ya shi bai neme ta ba ya yafi company.
Kamar komai bai faru tsakanin su ba haka yake aikin sa dan so yake yayi ya gama yaje ya kai Jannat makaranta, yana tsaka da aikin wayar da take gefen table d'in sa tayi k'ara ya d'auka kamar yadda yayi tunani itace tace yazo office.
Baice komai ba ya ajjiye ya nufi office d'in nata kamar koda yaushe sai da ya fara kwankwasa k'ofar sannan yayi sallama ya shiga, had'a ido sukayi yayi saurin dauke idon sa dan gani yayi idon ta ya k'ank'ance alama ne na wacce bata samu bacci sosai ba ko wacce ta kwana tana kuka.
Zaiyi magana tace, "kar kace min madam dan Allah, call me Mufeedah." Maimakon yayi abinda tace sai yace, "akwai abinda kike so kika kira ni?."
"Imran amsar ka ta jiya nake so, na kwana cikin fargaba da tashin hankalin abinda zaka ce min yau dan Allah ka tausaya min wallahi da zuciya d'aya tak nake son ka."
Ajiyar zuciya yayi kad'an ya kalle ta dan zuwa lokacin ta mik'e tazo gab dashi yace, "kiyi hak'uri Mufeedah ina da wacce nake so nake kuma burin aura sabida haka gaskiya baza ki samu wani gurbi a zuciya ta ba a yanzu."
Baya tayi kamar zata fad'i Allah ya bata sa'a ta dafa table ta sunkuyar da kai tana kallon table d'in, jiri take ji yana d'aukar ta sabida har cikin k'asan zuciyar ta taji abinda yace bata san lokacin da hawaye suka fara sauka a idon ta ba sai d'umin su taji a fuskar ta.
Kallon ta yake cikin tausayawa duk sai jikin sa yayi sanyi ganin yanayin da ta shiga lokaci d'aya amma baya so yayi mata k'arya shiyasa ya fad'a mata gaskiya, "kiyi hak'uri ban fad'i hakan dan na saka ki cikin yanayi mara dad'i ba, na fad'a miki ne domin bana son nayi miki k'arya ya zama kamar na yaudare ki ne, nasan zaki ji babu dad'i a zuciyar ki domin ko wanne d'an adam baya fatan ya nemi abinda yake so wata rana ya rasa shi musamman a b'angaren soyayya balle kuma ke mace, bana b'oye gaskiyar da take raina shiyasa na sanar dake b'oye miki yafi fad'a miki cutuwa, nagode sosai da soyayyar ki a gare ni bazan kuma tab'a mantawa dake ba har k'arshen rayuwa ta."
Zuwa lokacin kuka take sosai kamar ranta zai fita bata damu da kayan da suke jikin ta ba ta fad'i a kan tiles d'in office d'in tana kuka sosai ta kasa furta ko wacce kalma, hankalin Imran yayi bala'in tashi sam bai d'auka lamarin yayi zafi haka ya k'arasa inda take ya rage tsayin sa yace, "Mufeedah!."
Duk da halin da take ciki hakan bai hana taji saukar muryar sa a tsakiyar kanta ba hakan ya haifar mata da lumshe ido ba tare da ta kalle shi ba bata ce kuma komai ba, "kiyi hak'uri ki daina wannan kukan domin ba shine magani ba."
Sai a lokacin ta samu kwarin guiwar kallon sa idon ta yayi kaca-kaca da hawaye tace, "Allah ya halatta maka auren mace sama d'aya Imran ba lallai sai nazo a ta farko ba na amince ko a ta hud'u ne indai zan zauna da kai matsayin mata ina so, ka tausayawa zuciyar da bata tab'a fad'awa tarkon so ba sai a kanka, ka tausayawa zuciyar da bata san wani abu wai shi so ba sai a kanka, ka tausayawa zuciyar da ta saudaukar da kanta gare ka, ina sonka Imran, ban tab'a son ko wanne namiji a duniya kamar yadda nake son ka ba dan Allah kar ka barni." Ta k'arasa fad'a cikin sautin kuka sosai.
"Ya rabbi." Shine abinda Imran ya furta can k'asan mak'oshi ya tsuguna a gaban ta yana kallon yadda idon ta yake zubar da hawaye farar ta ta koma ja sabida kuka, kawar da kansa yayi gefe zuciyar sa na bala'in bugawa kafin ya dawo da kallon sa gare ta yace, "Mufeedah ba nak'i karb'ar tayin soyayyar ki dan na wulaqanta ki ba sai dan bana son cutar dake ne, ina da wacce zan aura in na karb'i soyayyar ki na yaudare ki kuma Allah sai ya kama ni da hakkin ki, kiyi hak'uri dan Allah ki cigaba da addu'a komai zai zo da sauk'i."
"Meye dani da baka sona? Meye a jiki na?." Ta fad'a tana kallon sa cikin kuka.
"Babu ki da komai Mufeedah bance miki kuma bana sonki ba wannan dalilin dana fad'a miki shine kawai dalili na."
"Shekara d'aya, shekara biyu, uku, hud'u, biyar, har fiye da haka zan iya jiran ka ka zauna da matar ka ta farko ka auro ni a ta biyu, ina da burin zama matar ka tun ranar da Allah yasa na d'ora ido na a kanka Allah ya saka min son ka da qaunar ka har na kasa b'oyewa, ka tausaya min kar ka juya min baya."
Ajiyar zuciya Imran yayi yace, "in har Allah ya rubuta ke matata ce a cikin k'addara ta wallahi sai na aure ki shiyasa nace ki cigaba da addu'a komai zai zo da sauk'i."
Mik'ewa tayi kan guiwowin ta tace, "Alqawari nake so kayi min akan zaka aure ni duk tsanani." Zaiyi magana tace, "dan Allah nace ba dan ni ba kayi min wannan alqwarin shine kawai zan samu sassauci a cikin zuciya ta a kan abinda nake ji yanzu."
Hasbunallahu wani'imal wakil, shine abinda yake furtawa a zuciyar sa domin ya shiga tsaka mai wuya a lokacin, shiru yayi kawai yana kallon ta domin shi ba mutum ne mai son d'aukar alqwarin da yasan bazai ciki shi bane dan yasan Mufeedah tafi k'arfin sa nesa ba kusa ba, "kai nake jira in zan samu hakan? in bazan samu ba tsaf yau nasan zaka iya samun labarin na kwanta a asibiti ko na mutu ma."
Ya kasa furta komai sai kallon ta kawai da yake yi, "nasan baza kayi min ba daman, shikenan nagode amma ina so ka sani kome ya faru dani koda mutuwa nayi alhakin hakan yana kanka, kuma indai ba kai ba wallahi bazan yi aure ba in kuma nayi sai na kashe kaina na kashe mijin kaji kuma nace maka wallahi."
"Subahanallahi meyasa kike fad'ar haka kamar ba musulma ba? Ki tuna ba komai kake nema ka samu ba in nayi miki alqawari ya zama Allah bai rubuta ni mijin ki bane bafa?." Ya fad'a cikin tausasawa dan yaga kamar ta fara fita a hayyacin ta.
"Dan Allah kayi min alqawarin hakan dan Allah." Ta sake fad'a a gigice tana kallon sa.
"Shikenan nayi alqawari indai har Allah ya rubuta ke matata ce zan aure ki na zauna dake mata." Lumshe ido tayi ta fara sauke numfashi a hankali ta koma baya ta jinjina da bango kusan minti biyar tana a haka kafin ta bud'e ido ta ganshi a tsaye a gefe tace, "Nagode sosai, zan jira ka daga nan zuwa ko Shekara nawa ne, ina sonka ina fatan na mutu da sonka."
Murmushi mai kama da yak'e yayi mata ya kalli agogon hannun sa yace, "Ina zuwa." Daga haka ya fita ta bishi da kallo cikin tsantsar farin ciki domin kuwa alqawarin da yayi mata ya yaye duk wata damuwa da ta shiga a d'azu.
Zuciyar sa duk babu dad'i haka ya koma gida ya kira layin Jannat ta fito ta shiga motar bai ce komai ba suka fara tafiya.
Ganin ko kallon inda take baiyi ba sai tuk'in sa da yake yi sai jikin ta yayi sanyi itama ta kasa furta komai har suka kusa zuwa makaranta sannan yace, "ki tuna da alqawarin na da yake kanki, kar ki sab'a Jannat, kar ki bari wani abu ya had'a ki da Mushin ko meye shi."
tace, "insha Allah Yaya bazan sake kallon inda yake ba." Daga haka bai sake cewa komai ba har suka isa bakin gate d'in makarantar yayi parking har zata fita yace, "In kin koma gida anjima zamu tattauna kamar yadda nace miki, ki shiryawa hakan." Ya fad'a yana kallon ta da murmushi.
Saurin sunkuyar da kai tayi gaban ta na fad'uwa ganin irin kallon da yake mata wanda bai tab'a yi mata irin saba tunda suke dashi ga murmushi mai kyau a fuskar sa duk da ta fahimci baya cikin walwala, d'aga masa kai tayi kawai ta fita ta shiga shi kuma ya bar wajan.
Koda ya koma bai yadda sun sauke had'uwa da Mufeedah ba duk da ita tana kallon sa ta tv amma shi bai bari sun had'u ba aikin sa yake har akayi la'asar ya bar company.
K'arfe biyar da rabi Jannat ta dinga gwada number Imran amma tak'i shiga gashi ya hana ta hayo napep haka ta zauna har magariba ta kawo kai hakan ya saka kawai ta yanke shawara ta hau napep ta koma gida.
Maimakom ta shiga gida sai ta shiga gidan su dan ta fad'a masa shine yak'i zuwa kar yaga laifin ta amma abin mamaki baya nan, ta kalli Umma da take zaune tace, "Umma Yaya bai dawo ba?." Umma tace, "bai dawo Jannat na d'auka ma tare kuke."
"A'a Umma tun d'azu nake jiran sa nima shiru shiyasa na tawo."
"To jekii gida ki huta yau dai yayi nisan kiwo."
"To Umma kiyi shaida kinga dai shine ya dad'e shiyasa na tawo." Umma tayi dariya tace, "to Khadijah."
Abu kamar wasa har dare yayi babu labarin Imran an kira shi kuma wayar a kashe zuwa lokacin hankali ya fara tashi amma ana jira aga abinda zai biyo baya, Jannat ce ta koma gidan Umma dan su kwana tare kasancewar shi baya nan, haka kowa ya kwanta zuciya cike da al'ajabin abinda ya hana Imran dawowa gida ana ta addu'a da fatan yana lafiya a duk inda yake.
Safiya tayi Umma tana tashi ta lek'a d'akin sa amma yana nan yadda yake a daren jiya, gaban ta ya fad'i domin tasan ko awa d'aya Imran zai k'ara a waje sai ya sanar da ita balle har ya kwana.
Jannat ko makaranta bata iya zuwa ba domin babu kuzarin hakan a tare da ita sai aukin kuka da take tana fatan duk inda Yayan ta yake yana lafiya.
Sai K'arfe sha biyu na rana Nura yayi sallama ya shigo gidan, suka gaisa da Umma yace, "Umma Imran yayi tafiya ne?." Umma tace, "babu inda yaje Nura tun jiya da ya fita bai dawo ba har yanzu."
"Kuma bai fad'a miki zaije wani wajan ba Umma?."
"Bai fad'a min ba hasali ma ko jimawa yayi bai dawo ba sai ya sanar dani."
"Jannat ke fa?". Ya fad'a yana kallon Jannat da take baya a rakub'e.
Hawaye ya sakko mata ta girgiza kai alamu A'a. Ajiyar zuciya Nura yayi kana yace, "yanzu muka tsinci motar sa a can bayan company su babu kowa a ciki hatta wayar sa na ciki amma an kashe ta." Gaban Umma da Jannat ya fad'i a tare suka furta, "to shi yana ina?." Nura yace, "bamu ganshi a ciki ba."
Anty Surayya da take shigowa gidan taji abinda akace tace, "mun shiga uku, Allah kasa ba y'an garkuwa da mutane bane suka sace shi." Nura ya sauke numfashi yace, "Gaskiya hakan muma muke tunani dan yanayin abin yayi kama da irin nasu."
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine abinda suka furta gabad'ayan su, k'arar fad'uwar abu suka ji a baya hakan ya saka suka kalli wajan a tare.
Wattpad@Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.