5
by @autarmama
🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼
*DAGA ALƘALAMIN*
ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♂️🧚♂️🧚♂️.
*P. 5*
Hannunshi ya juya mata, kafin ya juya gurin Ƙannanshi, idanunshi jaaazir, Umarni yy musu da su daukeshi, Part dinshi, suka nufa da shi.
Kan kujera suka ajiyeshi, Umarni ya ƙara musu da su dauko mishi Madara peak da cup a fridge, da sauri suka dauko suka dawo, karɓar madarar yy,ya ɓula bakinta da Key din mota , gaba daya madarar ya juye cikin cup din, Sayyid-maleeq ya kalla kafin yace "Zuma and Spoon", ya fada yana daura tafin hannunshi a goshin Zayn_maleeq , da ta dauki wani mugun zafi sosai.
da sauri Sayyid ya je yy abun da Shehi ya Umarceshi da yy, bayan ya kawo ya haɗa Zumar, ya jujjuya , tare da tallafar kan Zayn ya fara zuba mishi haɗaɗɗiyar madarar da Zuma , a bakinshi cikin ikon Allah yake shiga cikinshi, har ya shanye tasss.
tafin hannunshi, ya kama ya matsa, zazzafan numfashi ya sauke, tare da ƙaƙarin Amai, dagoshi Shehi yy ya ƙarashi da jikinshi,amai ya shiga kwararawa baƙiƙƙirin .
shafa mishi bayanshi ya shiga yi , yana fesar da iska mai zafi, sai da Zayn ya amai gaba daya abun da ya ci kafin ya koma jikin Shehi, yana sauke numfashi, cikin kakkausar murya da gargadi yace "kai kunnen kashe ne da kai ko ??,ba na haneka da karɓar wani abu ba hannun yan cikin masarautar nan?,ka ci gaba da shishige musu kana karɓar abu a hannunsu kana ci, ba mutuwa ake tsoro ba wahalar da zaka sha ita de abun gudu", dafe kanshi yy yana jin yana wani mugun sara mishi.
zameshi yy daga jikinshi ya wucewarshi Upstairs. dai-dai nan Umma Jakadiya ta shigo palon a tsorace, da sauri ta isa gurin Zayn , tana tattaɓashi a firgice take cewa "fatan dai bb abun da ya sameke ko ?" ta fada a firgice, idanunshi da suka kasance irin na Shehi ya dan bude tare da yin luuuu da su irin dai yarda Shehi yake yi, idan baya son hayaniya ko baya jin dadi.
taɓa wuyanshi yy, jikinshi bb zafi, numfashi ta sauke tare da cewa "Alhamdulillah", kallon Sayyid da Abdul tayi, tace "ku kamashi ku kai shi Bedroom ya kwanta, ya huta, kafin na sama mishi abin da zai ci", ta fada tana miƙewa.
Yaa Shehi na shiga bedroom dinshi, ya kwanta kan bed, yana sauke wani wahalalan numfashi,cikin rashin yake ayyana tunda sun gama abun da ya kawosu garin dole su tattara su barshi, kafin ayi Sanadiyar rai abu mafi soyuwa a gareshi.
zazzafan numfashi ya sauke yana jin wani zafi tun daga cikin jikinshi, har saman gashin kanshi,a hankali ya miƙe ya zare Alƙyabbar jikinshi, ya zame rawanin kanshi ya ajiye akan bed din, tare sa nufar bathroom, tsakiyar shower ya tsaya, tare da kunnawa.
ruwan sanyi ne ya fara dukan kanshi, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tura yatsun hannunshi tsakiyar kanshu, yana barbaza gashin kanshi . ta yarda ruwan ya ke shiga dukkan jikinshi.
sai da ya tabbatar da cewar zafin ranshi, har ma da zafin jikimshi yy ƙasa kafin ya fito kashe shower din, ƙaramin towel ya daura a kanshi, yana tsane gashin kanshi da yake lirif da ruwa,a hankali yake takowa . sai da ya zo gurin ƙofa kafin ya zare lallausa kuma tattausar ƙafarshi daga cikin bathroom slippers din, bude kofar yy ya fito, yana fitowa ya daura ƙafarshi akan welcome carpet da yake shimfiɗe a ƙofar fitowa bathroom din.
da Sunan Allah ya fito ya fara shiryawa cikin Arebiyan Jallabiya Back mai kyan gaske, gaban dressing mirror ya tsaya, hand dryer, ya fara busar da gashin kanshi, da har rufe mishi fuska yake, tsabar yawa da sulɓi, a hankali ya tattare gashin ya mayar da shi baya , yana fesar da sanyayyar ajiyar zuciya, turarenshi na Huge boss ya dauka, ga fara feshe jikinshi da shi.
har sai da ya fara hawar mishi kai kafin ya ajiyeshi, yana juyawa daga gaban mirror, gurin Pray mat ya matsa, tare da zama, ya tankwashe ƙafafunshi , Al-qur'ani ya dauka ya fara karantawa.
Yaa Shehi bai fito ba sai gabanin Magrib, a hankali ya fara saukowa, wannan ƙaron yana sanye da Jallabiya Fara ƙarr sai hula fara, ƙafarshi na sanye da wasu tausasan slippers masu kyau da sukawa ƙafarshi ɗas.
A hankali yake saukowa daga Upstair yana cewa "```Allahummaj al fiy kalbiy nu`ran, wa fiylisa niy nu`ran, wafiy basari nu`ran, wamin fauki nu'ran, wamin tahti nu`ran , wa an yami`ni nu`ran , wa an shima`liy nu`ran, wa min ama`mi nuran, wa mankhalfiy, waj al fiy nafsiy nu`ran, wa aazim liy nu`ran , wa azzimliy nu`ran , waj al liy nu`ran , wa nu`ran , Allahumma aadiniy nu`ran , waj alfiy asabiy nu`ran, wafiy lahmiy nu'ran , wafiy damiy nuran , wafiy shaariy nu`ran , wafiy bashariy nu`ran```" , bai ko yi musu magana ba sai nuni da yy musu da su tashi lokacin Sallah yy.
har ya kuaa fita Umma Jakadiya tace "Yaa Shehi mai za'a haɗa maka ??.", hannu ya ɗaga mata alamar yana dawowa, Zayn_Maleeq da ya warwarw ne yace "Ummu Tuwan Shinkafa da miyar Kase", yaba fada ya bi bayan Yan uwanshu haka suka fice yana gaba suna binshi a baya, har suka ƙarasa Masjid din bb wanda yy wa wani magana.
ko da suka ƙarasa bakin Masjid din, suka yi Addu'ar shiga Masallaci, lokacin Yaah Shehi har ya shige ciki, kasantuwar lokaci ya tafi da yawa.
kafin su ƙarasa shiga cikin Masjid din har ya ƙwala kiran Sallar Magrib cikin zazzaƙar muryarshi mai dadin Sauraro , cikin yar Azama suka shiga Masjid din, suka tsaya a sahun gaba daga bayanshi.
cikin Zazzaƙar muryarshi ya fara karatun Al_qur'ani mai girma, har ya idar a cikin Suratul Ma'eedah , Ƙarin karatun da ya soma yi musu jiya yy musu ,har lokacin Sallar Isha yy , Bayan ya Jasu Jam'in Sallar Isha, suna idar wa, ya miƙe tare da yin hanyar waje, ganin hakan yasa da sauri Sayyid_Maleeq da Zayn_maleeq da Abdul_Maleeq suka biyo bayanshi.
jerawa suka yi su huɗu a bunsu suna tafiya, ko wane tasbhi yake, haka har suka ƙarasa sashen Matan Sarki da tun zuwansu basu leqa ba, sashen Babbar Matar Sarki Hajiya Lami suka fara shiga,ba laifi ta sakar musu fuska sosai, dan kusan Ƙawar Ammiensu ce kafin ta bar duniya, bayan sun gama gaisheta, suka nufi sauran sassan gidan.
duk in da suka shiga bb wani sakin fuska hakan, yasa basu wani damu ba, san sun saba da yana yon gidan Sarautar nasu,Asalin Sarautar tasu ce, amma gaba ake musu da mugun kwulli a kanta.
su basu ma damu da Sarautar ba kwata-kwata amma an damar musu rayuwarsu, hakan yasa basa jin dadin zama cikin gidan ko kaɗan, wanda har zaman Abroad ya fiye musu zaman gidan , dan ta ko wane ɓangare hari ake kawo musu, duk kuwa da cewar Sarautar ba hannunsu take ba sun riga da sun Miƙata ga Ƙanin Mahaifinsu.
daga nan Ɓangaren Sarki suka nufa, cikin sanyayyiyar muryar Shehi yy Sallama cikim palon Lamurɗe,cikinshi ne yy wani mugun murɗawa, zuciyarshi tayi wani mugun bugawa, tunaninshi ya so gushewa daga cikin jikinshi, dakyar ya tattare gaba daya natsuwarshi guri daya, har suka ƙaraso cikin palon shi bai amsa Sallamarsu ba kuma bai dauke idanunshi daga kallon da yake musu ba.
har suka ƙaraso su Zayn suka zauna ƙasa Yaa Shehi ya zauna saman kujera, amma Lamurɗe bai dauke ganinshi garesu ba, da alama ma baya cikin cikakken natsuwarshi, gyara murya Yaa Shehi yy, tare da cewa "Fatan Lafiya Abba ..?", da sauri ya dauke idanunshu daga garesu yana sakin dan ƙiƙirarran murmushi, tace "Uhmm hhhhmm lpy lau Yaa Shehi", ya fada yana dai-daita natsuwarshi.
Haɗa baki su Zayn suka yi gurin cewa "barka da dare Abba ", dan murmushin da iyakarshi laɓɓa yy tare da cewa ''barka dai Yaran Albarka", jim suka dan yi kafin Yaa Shehi yace "Uhmmm na zo faɗa maka cewar gove zamu koma", ya fada yana dan sauke numfashi. ɓoyayyiyar Ajiyar Zuciya Lamurɗe ya sauke tare da cewa "to..to...to. Madallah Allah shi kai mu goben", ya fada yana dan murmushi.
sun jima a gurin Lamurɗe yana jaansu da fira su kuwa suna san biye mishi, har dai ya gaji shima ya tsuke bakinshi, sai da Zayn kawai yake Yar fira , dan Zayn din shine Uban surutu. amma sauran da dan su za'ayi surutu da ba'ayi ba, dan ko mai zaka ce musu a gajarce suke amsa maka.
sai gurin 9pm kafin suka miƙe gaba dayansu suka fice, part din Yaa Shehi da dama nan suke gaba dayansu suka koma, lokacin da suka shiga Umma Jakadiya na ƙarasa shirya Wormers akan dining table, da murmushi kan fuskar Zayn Maleeq yace "Yawwa Umma kamar kin san da yunwa nake tare", girgiza kanta tayi, dan tasan gogan dama baya wasa da tunburƙumarsa.
kan dining ya wuce ba tare da ya tsaya cikin palon ba, tsayawa yy yana ƙarewa Dining din kallo, su Sayyid kuwa suna tsaye cikin palo, in da Yaa Shehi yy Upstairs .
Kallo Umma Jakadiya yy yace "Umma taho ki haɗa min Yaa Shehi", tun da ta ji haka tasan tare zai ci Abin cin da Shehi dan wani lokacin tare suke ci, matsawa tayi dining din ta shiga haɗa mishi cikin babban tray mai kyau sosai.
miƙa mishi tayi tace "gashi na gaban goshin Yaah Shehi", ta fada tana murmushi, murmushin shima yy, tare da ƙarɓa ya haye Upstairs din zuwa palon Yaa Shehi.
Zaune ya sameshi, ya tanƙwashe ƙafafunshi, idanunshi a lumshe yana ta Istigifari , da Sallama a bakinshi ya ƙarasa gaban Yaa Shehin da ya lumshe idanunshi, a hankali ya amsa Sallamar Zayn chan ciki, wanda in ba ka saurara da kyau ba ba zaka ji sadda ya amsa Sallamar ba.
gaban Shehin ya ƙarasa tare da ajiye tray din a ƙasa, yace "Sannu da hutawa Yaa Shehi..!", bai bude idanunshi ba, kuma bai Amsa mishi ba. gefenshi Zayn_Maleeq ya zauna ya nannaɗe ƙafafunshi ya dan jaaa numfashi, yana kallon Shehi.
kusan 10minutes Yaa Shehi bai bude idanunshi ba,bai kuma yi mgn ba, kallonshi yy yace "Yaaa Shehi Yunwa",ya fada yana dan yatsina fuska,bude idanunshi yy tare da jaan tray din, ya fara bude plate tare da ajiyewa a ƙasa. wormers din ya fara bubbudewa, Tuƙaƙƙen Tuwon shinkafa da ya haɗe jikimshi yana daure a leda ya bayyana, daya ya dauka tare da budewa ya daura akan plate, dan bowl ya dauka, tare da bude ƙaramar Wormer kalar babbar Wormar din da ya fiddo tuwon.
buɗe Wormer din yy lafiyayyiyar miyar Kase ce ta bayyana,sai kamshi take ta ji name zuƙul-zuƙul sai turiri yake, hannu Yah Shehi ya dauraye cikin wata yar tasa, tare da gutsiro tuwon, ya sanya cikin miyar ya fiddo tare, da nufar bakin Zayn_Maleeq, da sauri Zayn ya gyara zamanshi, ya dawo gaban Yaa Shehi sosai, bude bakinshi yy, cikin soyayyar Yan Uwantaka ya fara bashi tuwon yana ci, har ya cinye leda daya, kallonshi yy tare da mishi lamar ya ƙoshi girguza kanshi yy .
hakan yasa ya kara bude wani, tare da gutsirowa, jin da zafi yasa ya dan busa mishi da iskar bakinshi, ya ci gaba da bashi,zufa ce ta fara tsatsafowa Zayn_maleeq na ƙoshi, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da cewa " ```Alhamdulillahi Ala kullu Halin ...!``` ", ya fada yana dan jaaa baya, sanyayyayen Lemun Kwakwa da yaji madara Yaaah Shehi ya zuba mishi , dauka yy ya sha, yana lumshe ido sa boda sanyin da ya ratsa maƙogwaronshi.
baya ya Jaaa tare da jingina kanshi da jikin kujerar da Yaa Shehi yake zaube ya fara sauke numfashi, tuwon shima ya ci kaɗan dan ko loma biyar bai yi ba, duk kuwa da cewar yana jin yunwa dan tun Coffeen safe bai ƙara cin komai ba.
Amma kasantuwarshi na ba ma'abocin cin Abin cin mai nauyi bane, musamman in zai kwanta bai iya cin Abin cin ba.
bayan ya gama ya tattara komai cikin tray din ya miƙawa Zayn_Maleeq , ba tare da yace komai ba, ganin ya miƙa mishi gabanshi yasa ya dauka yy Downstairs domin mayar da kayan abin cin.
bayan ya ajiye ya zauna gurin Sayyid da suke zaune suna kallon ball....
sai guraren 11pm kafin ya miƙe yy Sama suma bin bayanshi suka yi, yana zuwa ya tarar da Yaaa Shehi na Bathroom hakan yasa suka kwanta akan bed dinshi, sai da suka yi Addu'o'i kafin su rufe idanunsu, suna Tasbhi kamar yarda Yaa Shehi ya koyar da su dan basa barci matsawar basu yi Tasbhi ba, barcin ma gaba daya baya zuwa amma da sun fara sai ya daukesu.
har suka yi barci bai fito ba, sai da ya ɓata kusan 1 hour kafin ya fito, cikin Jallabiya Maroon da tayi mishi masifar kyau, idanunshi da suke cike da gajiya da barci ya dan jaanye tare da lumshesu, ƙarasawa yy gurin bed din, sai da ya sake musu wata Addu'ar ya shafe musu jikinsu, ya jaaa musu duvet kafin ya kwanta a gefensu, kashe glove yy tare da fara karanta "```SUBHANALLAHIWA BI HAMMADIHI SUBHANALLAHIL AZEEEM```", haka ya ringa mai maimatawa, hae barci mai dan nauyi ya daukeshi.
```Washe gari```