ZANEN ZABUWA

Chapter 12

by @nanahaleema11

*ZANEN ZABUWA*


    ©️ *Nana Haleema.*



*Book 1*


*Page 12*




Da gudu suka yi inda take Anty Surayya ta d'ago ta jikin ta ragowar pure water da yake a gefe aka zuba mata a fuska ta sauke dogon numfashi ta fara k'okarin bud'e idon ta amma hakan ya gagare ta.


"Kuce min mafarki nake yi, Yaya babu inda yaje kar kuce min ba'a ganshi ba." Idon ta a kulle take fad'ar hakan Umma da Anty Surayya suna rik'e da ita sai Nura da yake kallonnta da tausayi sai Gwaggo da ta shigo a lokacin.


Nura yace, "Umma zan je company su yanzu bamu sani ba ko sune suka tura su wani wajan bai samu ya sanar damu ba." Girgiza kai Anty Surayya tayi tace, "Babu ta yadda za'ayi a aika shi wani wajan bai sanar da Umma ba, koda ma aika su d'in aka yi sai ya bar motar sa akan titi da kuma wayar sa a ciki?."


Shiru Nura yayi bai amsa ba dan yasan abinda tace gaskiya ne yace, "Za dai muje ba'a san inda za'a dace ba, sai na dawo." Ya fad'a yana fita su suka juya ga Jannat da take kwance har lokacin bata bud'e idon ta ba.


Koda Nura ya isa company tun a gate yayi musu bayani suka yi masa iso wajan Manager dan daga bakin ta za'a ji ko ta aike shi wani wajan, da sallama Nura ya shiga ta amsa tana kallon sa har ya k'araso ya zauna yace, "barka da rana." Ta amsa da fad'in, "barkan ka." 

"Suna na Nura ni abokin Imran ne da yake aiki a wannan company."


Jin an ambaci sanyin idanun ta ya sanya tayi murmushi mai kyau tace, "kai ya aiko bazai samu damar zuwa ba kenan, ina ta kiran layin sa sai naji a kashe lafiya yake dai ko?." Jin abinda tace ya saka jikin Nura sake yin sanyi ya sauke numfashi kana yace, "gaskiya ba lafiya ba hasalima tun jiya da safe da Imran ya bar gida har yanzu bai koma ba shiyasa muka zo wajan ki a tunanin mu ko daga nan company aka tura shi wani wajan."


Mufeedah da ta zuba masa ido tana kallon sa har ya kai k'arshe kamar an dasa ta a wajan ta kasa koda motsi sai bugun zuciyar ta da take ji na shiga kunnen ta, a rarrabe tace, "me kake so kace min?." Nura yace, "a tak'aice dai an nemi Imran an rasa duk inda ake tunanin za'a same shi an neme shi an rasa shi, a bayan companyn nan kuma aka tsinci motar sa da kuma wayar sa a ciki hakan ya tabbatar mana da sace shi akayi." Table d'in da gaban ta buga da k'arfi cikin tsawa tace, "kar ka kuma cewa an sace min Imran d'ina, Imran d'ina yana nan babu wanda ya isa ya sace shi." Sai kuma ta fashe da kuka.


Shi kam Nura bata ita yake ba hakan ya saka shi ya mik'e har zai fita idanun sa ya sauka akan tv nan yaga tana haska ko ina na company ya dawo, har zai mata magana sai kuma ya fasa kawai ya d'auki remote ya fara canjawa har ya kai inda yake haska bayan company ya dawo da abinda ya wuce yana gani, hasko Imran akayi ya tsaya ya siyi apples da kankana a wajan mai siyarwa dake wajan ya dawo mota ya bud'e zai shiga sai ga wata mota babba bak'a babu lamba a jikin ta ta tsaya kusa da motar sa kamar zata matse shi a jikin motar, d'uf sai wajan ya d'auke bai sake dawowa ba sai bayan wasu mintina sai aka ga babu Imran sai motar sa.


Nura da idon sa ya ciko da kwallah shima ya ajjiye remote d'in domin yanzu hasashen sa ya zama gaskiya sace Imran akayi, Mufeedah da ta kalli komai itama hankalin ta ya sake tashi ta dinga kuka kamar ranta zai fita Nura kam bai sake bi ta kanta ba ya fita domin shima ba'a hankalin sa yake ba.


Tun ana d'aukar abin kamar wasa sai gashi anyi kwanaki har bakwai babu Imran babu labarin sa, an kai cigiya gidan radio da gidajen tv amma shiru domin Nura bai sanar dasu abinda ya gani a company ba sabida kar hankali ya tashi yayi shiru akan in masu garkuwar suka kira suka nemi wani abun sa sani.


Jannat ta rame sosai kamar ba ita ba tayi bala'in yin bak'i bata cin abinci sai an mata dole bata zuwa ko ina hatta makaranta ta ajjiye ta bata da wani aiki sai kuka kullum cikin ciwo take dan cikin sati d'aya sai da ta kwanta a asibiti sabida tashin hankalin da zuciyar ta take ciki.


Labari ya zaga dangi da unguwa kowa ya sani ana ta addu'a da fatan Allah ya bayyana shi cikin k'oshin lafiya.

Ta b'angaren Mufeedah ma haka abin yake y'an gidan su gabad'aya sun kasa samun kanta tayi bala'in ramewa ga damuwa ko aikin ta daina zuwa kullum tana gida tana aikin kuka da tunani, ta saka police a cikin maganar amma shiru sabida ba'a bar wata hujja mai k'arfi da za'ayi amfani da ita wajan gano wanda suka sace shi d'in ba.


Yau ta kama ranar laraba wanda yayi dai-dai da sati biyu cif da b'atan Imran Mufeedah tana zaune tayi tagumi tana kallon waje d'aya hawaye na sauka a idon ta Muhsin da yake sakkowa daga sama ya gano ta ya k'araso a hankali ya zauna kusa da ita yace, "Haba Mufeey wai baza ki daina sakawa kanki wannan damuwar ba? Mun fad'a miki in sha Allah zamu yi iya bakin k'okarin mu wajan ganin an ganshi ke dai ki cigaba da addu'a kawai."


Kallon Yayan nata tayi da jajayen idanun ta tace, "Yaya a ranar da yayi min alqawarin zai aure ni a ranar na rasa shi, a ranar da yayi min alqawarin zai rayu dani a matsayin matar sa a ranar na rasa shi, kuma kake cewa na daina kuka Yaya? In banyi kuka ba me kake so nayi?" Ta fad'a tana sake fashewa da kuka tare da kwantar da kanta a kafad'ar sa.


Tausayin ta yaji sosai ya shafa kanta yace, "ki daina kuka Mufeey in sha Allah Allah zai bayyana shi za kuma muyi k'okari wajan ganin an nemo shi da izinin Allah." Mummy da fitowar ta kenan daga d'aki ta k'araso wajan tace, "yauwa Muhsin ka dinga yi mata fad'a tayi hak'uri kullum cikin kuka take ko aiki ta daina zuwa."


Kallon Mummy yayi yace, "Abinda nake tayi mata kenan Mummy kuma in sha Allah zamuyi iya bakin k'okarin mu wajan ganin an nemo shi." Mummy tayi ajiyar zuciya tana kallon autar tata tace, "Allah ya amince." Ya amsa da amin ya mik'e ya fita Mummy ta maye gurbin inda ya tashi.


Zuhra ce ta shigo falon da sallama suka gaisa da Mummy ta tashi ta basu wajan, Zuhra ta kalli k'awar tata ganin yadda ta rame ta lalace lokaci d'aya tace, "Kinga yadda kika rame kuwa Mufeedah? Meyasa baza ki karb'i k'addara ba?."

"Zuhra na karb'a inda ban karb'a da yanzu na zauce, ni kad'ai nasan abinda nake ji a zuciya ta daurewa kawai nake." Girgiza kai Zuhra tayi tace, "mun san dole kiji ciwo a ranki amma addu'a itace maganin komai kuma Allah yana sane da duk abinda yake faru shine ya k'addara hakan."


Share idon ta tayi tace, "da mota kika zo?." D'aga mata kai tayi alamun eh, mik'ewa tsaye tayi ta kwance d'ankwalin kanta ta yafa tace, "Muje ki kaini gidan su." Zuhra ma ta mik'e tace, "muje muyi me a gidan su?." Mufeedah tace, "shiga gidan su zai saka hankali na ya kwanta ko yaya ne." Ta fad'a ta fita daga falon dole itama Zuhra tabi bayan ta.


Kasancewar tunda ta saka a fara neman sa har address d'in gidan su ta sani bata sha wahala ba suka isa k'ofar gidan sai dai confusing da take wanne ne nasu tsakanin guda biyun, wani yaro ta gani zai wuce ta sauke glass tace, "kai dan Allah ina ne gidan su Imran?." Baice komai ba ya nuna mata ya wuce abinsa ita kuma ta fito bata tsaya jiran Zuhra ba ta nufi gidan.


Da kallo Zuhra take bin gidan tana girgiza kai cike da mamaki da al'ajabi ta furta, "tabbas so makaho ne in ba haka ba ina Mufeedah ina fad'awa soyayya da wanda ya taso a wannan gidan kamar akurki?." Ganin ta kusa shigewa gidan ya saka ta fito daga motar ta biyo bayan ta ta same ta a soro a tsaye suka shiga ciki da sallama.


Umma, Gwaggo, Yaya Binta da Anty Surayya duka suna zaune a falon gidan suka amsa a tare Mufeedah da Zuhra suka shiga ciki, zama suka yi daga gefe aka gaisa Umma tace, "Sai dai ban shaida fuskar ku ba." Mufeedah ta d'ago da kanta tace, "suna na Mufeedah a company mu Imran yake aiki."


Umma tayi murmushi tace, "Allah sarki, kamar ma naso na gane fuskar ki a wani waje." Mufeedah tace, "eh mun tab'a had'uwa asibitin murtala." Umma tace, "ba shakka anyi haka."

"Ya muka ji da abinda ya faru?."

Suka had'a baki dukkan su suka ce, "an gode Allah."

"Allah ya bayyana shi yasa yana cikin k'oshin lafiya." Ta k'arasa fad'a muryar ta na rawa alamun zatayi kuka.


Suka amsa da amin Gwaggo tace, "An gode Allah ya bada lada." Kallon Zuhra tayi a hankali tayi mata alama da ta bata kud'i in akwai a jakar ta ita kuma ta d'au haske ta gano abinda take nufi.


Mik'ewa Mufeedah tayi bayan Zuhra ta fito da kud'in ta ajjiye musu itama ta mik'e, "har da wahala haka?." Gwaggo ta fad'a tana kallon su. Murmushi Zuhra tayi tace, "babu komai ai an zama d'aya, sai anjima Allah ya bayyana shi." Suka amsa da amin tare da godiya su kuma suka fita.


Suna fita Jannat ta fito daga wanka hannun ta rik'e da kanta sabida ciwo ta shigo cikin falon da suke zaune, da kallo suka bita Yaya Binta tace, "Jannat ciwon kan ne?." Kai kawai ta iya d'aga mata dan bata tunanin zata iya cewa wani abu. "To bakya jin abinci Jannat ba dole kiyi ciwo ba dubi yadda kika rame kamar bake ba."


Bata iya cewa komai ba ta shige cikin d'akin Umma, Anty Surayya tace, "Halin da Jannat take ciki shine yake sake karya min zuciya ku duba yadda ta koma kamar wacce tayi ciwon shekara guda." Duk da Yaya Binta ba wani shiri suke da Jannat ba amma ita kanta in ta kalle ta tausaya mata take yi domin duk wanda yasan Imran yasan Jannat haka duk wanda yasan Jannat yasan Imran dole ta shiga tashin hankali rasa shi a lokaci d'aya. 


Umma tace, "Addu'a zamu dinga yi mata itama Allah ya sassauta mata abinda take ji, dan yarinyar tana cikin damuwa sosai ko baccin kirki bata samu in muka kwanta taita firgita kenan ko kaji tana ta ambatar sunan Imran a cikin bacci." Basu sake cewa komai ba kowa da abinda yake ransa babban fatan su bai wuce ace yau an samu inda Imran yake ba.


Da yamma Nafisa tazo ganin gidan su Jannat d'in a kulle ya saka ta shiga gidan su Imran, tana shiga ta ganta a zaune da abinci a gaban ta sai jagula shi take Umma na gefen ta tana aikin rarrashin ta taci amma ta kasa ci. Da sallama Nafisa ta shigo suka gaisa da Umma tayi mata jaje kafin ta kalli Jannat tace, "Sannu Jannat, ya jikin naki?." 

"Ba sauk'i Nafisa indai ba ganin Yaya na akayi bazan tab'a samun sauk'i ba."

"Kiyi hak'uri Allah zai bayyana shi da gaggawa in sha Allah."

Umma tace, "abinda ake nuna mata kenan amma ta kasa fahimta."


Shiru ne ya biyo baya kafin Umma tace, "Nafisa ya makaranta? Ana ta karatu yana wuce Khadijah ko?." Nafisa tace, "wallahi kuwa Umma ana ta karatu sosai dan har mun tafi sabon aji." Jannat ta kalle ta tace, "au har an fitar da result?."

"Eh mana an fitar dan bakya hawa WhatsApp ne yanzu da kin gani." Tab'e baki tayi kafin tace, "an kore ni ko?." Nafisa ta kalle ta tace, "ba'a kore ki ba amma dai kin samu repeat sai kin sake maimaita level 200."


Umma tace, "Subahanallahi, Khadijah kin gani ko yanzu da kin koma makarantar ki ai da ba haka ba, zaman ki a gida bazai dawo da Imran ba." 


Jannat da bata damu ba ko kad'an tace, "ni wallahi Umma naso ma kora ta sukayi dan na tsani karatun gabad'aya bana tunanin zan iya yin sa a halin da nake ciki, karatu sai da nutsuwa kuma ni bana tare da ita a halin yanzu shiyasa na yanke shawarar daina zuwa kawai."

Anty Surayya da ta fito daga d'aki tace, "Haba Jannat in kika yi haka kuwa baki kyautawa Yayan ki ba kin manta yadda yake mutuk'ar son kiyi karatun nan ne,? In kika fasa ai baki cika masa burin da ya jima dashi a ran sa ba." Kallon Anty Surayya d'in tayi tace, "Anty ya zanyi bazan iya karatu yanzu ba gabad'aya bana sha'awar yin sa." Ta fad'a tana fashewa da kuka.


Umma tace, "hak'uri zakiyi ki daure ki kuma mik'awa Allah lamuran gabad'aya." Bata ce komai ba suka cigaba da hira sama-sama amma dukkan su ran su babu dad'i.


Ranaku suna ta tafiya kamar wasa babu Imran babu labarin sa, dak'yar aka tursasa Jannat ta koma makaranta badan tana so ba sai dan babu yadda zatayi gashi yanzu ba dad'in makarantar take yi ba sabida yanzu Nafisa ta fita aji.


Gabad'aya lamarun an mik'awa Allah ana ta addu'a da saukar alkur'ani ana fatan Allah ya bayyana shi cikin k'oshin lafiya in kuma ya bar duniya Allah ya jikan sa. Duk wanda yasan Jannat a dah ya ganta a yanzu sai ya tambaya rashin lafiya tayi sabida bala'in ramar da tayi, ta kuma rage walwala da fara'a ko a makaranta keb'e kanta take yi.


B'angaren Mufeedah ma hakan take koda yaushe cikin tunani take ta ajjiye aikin gabad'aya ta daina zuwa duk sati sai anzo an auna bp ta sabida jinin ta yayi mugun hawa a kwanakin baya, su Mummy duk sun zubar da makan yak'in su suna rarrashin Mufeedah dan ba k'aramin rama da azabtuwa take yi ba. Kullum tana hanyar zuwa gidan su Jannat bata kwana uku bata je ba kowa ya santa sai dai har lokacin basu tab'a had'uwa da Jannat ba sai dai su samu sab'ani.


Yau ta kama ranar litinin da misalin k'arfe sha d'aya na safe Jannat tana zaune a harabar makaranta tana duba littafi tana jiran lokacin shiga aji yayi su shiga. "Assalamu alaiki." Taji an fad'a daga gefen ta juya dan ganin waye idon su ya had'u dana Muhsin da yake tsaye yana aika mata da murmushi. Sanin mahimmacin sallama ya saka tace, "wa'alaika salam." 


K'asa ta mayar da kanta ta cigaba da karatun ta hankalin ta a kwance dan ko kallo bai ishe ta ba, "Zan iya zama?." Muhsin ya fad'a yana kallon ta da murmushi mai kyau a fuskar sa. 


Bata d'ago ta kalle shi bama balle ya saka ran zata amsa masa karatun ta kawai take yi. Ganin hakan ya saka shi sake cewa, "Hajiya ina ta magana fa ya kamata a duba ni kafin na bushe." Kamar bada ita yake ba ko motsi batayi ba balle ya saka ran zata amsa masa.


Zai kuma magana kenan ta mik'e ta d'auki jakar ta ta bar wajan cikin nutsuwa tana tafiya tana duba agogon hannun ta. Da kallo ya bita yana sakin murmushi mai kyau cikin tsantsar nishad'i da farin cikin da bai san dashi ba yana kallon ta har ta shiga hall d'in da yake da kusa ita.


"Muhsin wannan fa ba ajin ka bane, ya zaka zo kana kula yarinya a gaban y'an makaranta tana wulaqanta ka? Gaskiya yawa ne wallahi" Salim ya fad'a yana kallon sa.


Muhsin ya jiyo ya kalle shi har lokacin fuskar sa da murmushi yace, "ni farin ciki ma nake ji da ta wulaqanta ni d'in."

"Kamar yaya kenan? Ban gane ba?."

"Cikin kwanakin nan tana burge ni sosai ina kuma so nayi mata magana."

"What! Ban gane ba?."

"Bana so ka gane daman but firstly ina so na samu kusanci da ita, i mean abota nake so mu qulla."

"Muhsin are you?." Ya fad'a da mamaki yana kallon sa.


Tsaki yaja kafin yace, "yeah it's me, kuma it's not a plan har cikin raina nake fad'a maka so ka samo mana solution." Girgiza kai Salim yayi kafin ya sake cewa, "gaskiya I'm surprised." Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe ido ya bud'e sannan yace, "Ka daina mamaki Salim kayi abinda nace kawai." Yana gama fad'ar hakan ya wuce ya bar Salim da baki a bud'e yana kallon sa cikin mamaki da al'ajabi, Ganin ya shiga mota ya saka Salim girgiza kai ya bi bayan sa da sauri suka shiga mota suka bar school d'in. 


Tafiya suke yi sosai Muhsin yana kwarara gudu kamar zasu bar gari babu wanda yake magana sai waqar rema mai suna calm down da take tashi a motar kad'an-kad'an. Sosai suke tafiya har suka bar cikin gari suka shiga unguwar da babu mutane sosai sai gida tsili-tsili sannan ya karya kwana suka shiga wani k'aton Estate wanda sai ka irga gidajen da suke cikin Estate.


A bakin wani gate babba ya danna horn jimm kad'an mai gadin ya lek'o yaga waye ya koma ya bud'e gate d'in suka shiga.


K'aton gidan gona ne mai d'auke da nau'in abubuwan kiwo da dama a wajan, tun daga kan Dokuna, d'awisu, kaji, zabi, tattabaru, shanu da sauran su ko wanne da mahallin sa.


Ciki suke shiga har suka isa wajan wata k'ofa k'arama wacce tun a bakin ta zaka dinga jiyo kukan kaji daga cikin d'akin, kallon Salim Muhsin yayi ya tab'e baki yana toshe hanci ya hannu ya tura k'ofar suka shiga ciki, karo suke da kaji Mushin sai rab'ewa yake dan baya so su tab'a shi a haka har suka k'arasa can k'arshen d'akin suka isa wata k'ofa da duk tayi kura har da yana a jikin ta, Salim ya bud'e k'ofar suka tura suka shiga.


Damin abincin dabbobi ne a ciki sunyi tsiri kamar zasu zobo babu wani space sosai a d'akin da inda mutum d'aya zai kwanta ma babu duk da girman sa, banda warin abincin babu abinda d'akin yake kasancewar babu babbar taga sai k'arama da take can sama dan in kana d'akin baza ka banbance dare da rana ba sabida rashin hasken da yake d'akin. 


Zaga d'akin suke hancin Muhsin a toshe har suka k'arasa wani waje dashi babu yawan kayan sosai a wajan suka ja burki suna kallon wajan.


A zaune yake kansa a k'asa k'afar sa a mike kayan jikin sa sunyi kaca-kaca, da farko in ka ga wanda yake zaune zaka dauka almajiri ne ko mahaukaci duba da yadda kasan ya cika da gashi haka ma fuskar sa amma in ka lura zaka fahimci tsantsar wahala ce ta mayar dashi haka.


Muhsin ya kalle shi ya bud'e hancin sa cikin dauriya yace, "Malam Imran ya akaji da zaman kad'aici?." Imran da kansa yake a duk'e ya d'ago kansa ya kalli Mushin da idanun sa da suka kankance suka koma k'ananu sabida wahala har baya iya bud'e su sosai, baice komai ba ya sake mayar da kansa k'asa ya mayar da idon sa ya lumshe.


"Kamar yadda na saba kawo maka labari koda yaushe a kan k'anwar ka ko nace matar ka kamar yadda kake fad'a a cikin tatsuniyar ka, ina so ka sani daga yau zamu k'ulla abota dani da k'anwar ka." Muhsin ya fad'a yana zama akan rabin buhun abicin kajin yana kallon Imran cikin murmushin mugunta.


"K'arya kake kome zaka yiwa Jannat baza ta tab'a sauraren ka ba ina da wannan tabbacin." Imran ya fad'a cikin muryar sa da tayi bala'in dashewa dan in baka saurara sosai ba baza ka fahimci abinda yake cewa ba.


Dariya Muhsin yayi ya kalli Salim da yake tsaye yace, "Salim wannan confidence d'in nasa yana burge ni sosai amma san bashi mamaki" dawo da kallon sa yayi ga Imran d'in sannan ya cigaba da cewa, "Kaine kake ganin baza ta saurare ni ba amma ni nasan zata saurare ni domin ba iya abota zamu qulla da ita ba har soyayya zamu qulla mai k'arfin gaske wacce zata kaimu ga aure ni da ita."


A fusace Imran ya d'ago ya kalle shi suka had'a ido Muhsin ya d'age masa gira guda d'aya yace, "ya naga ka fusata haka? Kwantar da hankalin ka bamu kai ga qulla soyayyar bafa ina dai fad'a maka ne ka shirya shiga bak'in ciki da kunci a duk ranar da kaji na aure ta."


Girgiza mai Imran yayi yace, "Abinda bazai tab'a faruwa ba kenan har abadah ko me zaka yiwa Jannat baza ta kalle ka ba balle kayi nasarar had'a abota da ita balle kuma aje ga soyayya." Numfashi yake saukewa sabida ciwon da cikin sa yake masa kana ya cigaba da cewa, "kud'in ka baya gaban Jannat ina da tabbacin baka da abinda zaka d'auki hankalin Jannat dashi balle ta saurare ka."


Dariya Muhsin ya kuma yi ya d'an yatsine fuska dan warin wajan na damun sa sannan yace, "Imran kenan, naga alama ka yadda da k'anwar taka sosai tunda gashi har kana bani tabbaci a kanta haka." 

"Ba tabbaci nake dashi a kanta ba amincewa nake dashi a kanta ka daina cewa tabbatarwa kad'ai, ka daina tunanin dan ka d'auke ni ka kawo ni nan tsahon watanni zai saka Jannat ta manta dani har kayi galaba a kanta, in ma wannan tunanin kake ka daina, domin kuwa babu wani d'a namiji da Jannaty zata so sama dani nasan kuma zata jira ni har na fito muyi aure, kar ka sake magana akan zaka qulla wata alaqa da Jannat domin hakan bazai tab'a yuwa ba, wahalar da kanka kawai zakayi gwara tun kafin lokaci ya qure maka kasan abin yi."


Girgiza kai Muhsin yayi yace, "ni kuma ina so na shaida maka sai na auri Jannat badan wai dan na d'auki fansa akan ka ba sai dan ina son ta." Kallon sa Imran yayi da mamaki Mushin ya bud'e ido yace, "eh ina son ta so ba d'an k'adan ba."

"Zaka iya son ta amma ita baza ta tab'a son ka ba."

"Haka kake gani?."

"Hakan ne ma ai ba gani nake ba."

"Wow! Ni kuma ina so na tabbatar maka da Jannat zata so ni za kuma ta qaunace ni sama da yadda kake cewa ta qauna ce ka."

"Sai dai in asiri zaka yi mata."

"Hhhhhhh Imran kenan."

"Kayi dariya mana."

"Tausayi kake bani ne ina hasashen halin da zaka shiga a duk lokacin da ka samu labarin na auri Jannat."


Shima murmushin k'arfin hali yayi yace, "kaine kake bani tausayi domin ka fad'a tarkon son maso wani, soyayya ta a zuciyar Jannat ZANEN ZABUWA ne a haka Allah ya halicce shi babu wani nau'in abu da ya isa ya goge shi haka nake a zuciyar Jannat, ka kama kanka tun kafin lokaci ya k'ure maka." 


Muhsin yace, "A ganin ka kenan Imran, amma ni zan tabbatar maka da hakan dan bazan sallame ka daga nan ba har sai Jannat ta haihu in na namiji ne zan amince a saka masa sunan ka." Tsaki Imran yayi ya kawar da kai yana jin wani irin zafi na taso masa daga zuciyar sa dan sosai yake jin kishin kalaman Mushin a kan Jannat, da ace yana da k'arfi da lafiya babu abinda zai hana bai buge masa baki ba.


"Imran ina tabbatar maka da sai na auri Jannat in kuma ban aure ta ba ka kira ni duk abinda kaga dama haka zalika ka saka ayi min ko wanne hukuncin da yayi maka." Ya fad'a cikin k'arfin guiwa da kuma alwashi.


Imran ya dawo da kallon sa gare shi yace, "ni kuma ina tabbatar maka da Jannat baza ta saurare ka ba balle har ta kai ku ga maganar aure, in kuma Jannat ta saurare ka na yadda ka barni a nan har k'arshen rayuwa ta ka kuma yi min tsattsauran hukuncin da duk kaga dama, in kaso zaka iya sakawa a yanki naman jiki na duka na amince da wannan."


Muhsin ya mik'e tsye ya kalli Salim yace, "kaine shaida duk a gaban ka akayi komai in lokacin hukunci yayi kaine zaka bada shaidar wanda za'a hukunta." Salim ya girgiza kai kawai domin shi gabad'aya ba wannan ne a gaban sa ba abinda yake ran sa badan.


Kallon Imran Muhsin yayi sannan yace, "ina tabbatar maka da bazan dawo nan ba sai soyayya ta da Jannat tayi nisa." Yana gama fad'ar hakan ya d'aga k'afar sa da niyar barin wajan Imran yace, "Ina tabbatar maka da wannan ranar baza ta tab'a zuwa ba har Allah ya tashi duniya, domin Jannat baza ta so ka ka da abota bama balle soyayya, ka rubuta wannan ka ajjiye." Murmushi Mushin yayi baice komai ya d'an tafa hannun sa ya yiwa Imran alamun jinjinasuka fita daga d'akin tare da jan k'ofar suka kulle.




_Oh ready an fara payment na ZANEN ZABUWA book2 naira 300 ne har yanzu, in kin shirya tuntub'i wannan number 2347045242700 but only WhatsApp._



Wattpad@ Nana_haleema 

Arewabooks@ nanahaleema11.