D'A NA KOWA NE

33_34

by @mamanamatullah

ƊA NA KOWA NE

   [RAYUWAR SAMHA]

          

MALLAKAR..

 Mmn Amatullah(Sarauniyar Jarumai)



JARUMAI WRITERS ASSOCIATION💪🏻📚


33_34



🔚🔚🔚🔚


 

''Ki ce abu ya yi daidai,gara da Allah yasa nazo kenan," "Au haka kace,to ai sai kayi sauri katashi don nasan yanzu gab take da dawowa" Duban ta yaƙarayi tare da cewa "To ko dai tadawo yanzu ai dai buƙata tabiya" Nasan da haka amma ni banaso tazo ta sameka,don ni za ka bari da kunya don nasan ko ajikinka kai" Dariya sosai Faruq, ya yi tare da cewa "Ke dai matso raciya ce" "Aa fa babu maganar tsoro sai gaskiya" "To naji,bari na tashi,za'abarni nayi wanka kokuwa,shima sai naje gida? Ya tambaya cike fa zolaya "Wanne wanka kuma ai inkaje gida kayi,salonkana cikin toilet tadawo" Ido yazaro tare da faɗin "Kai my lovely yanzu haka zan tafi? Ganin son zancen ya keyi,yasa tafara kuka cike da shagwaɓa har da shure shure,kai kace karamar yarinya ce mai makon ya tashi yatafi sai ma ƙayatar da shi da abin ya yi,ji ya yi kamar ma ya koma su dauwama a haka, rungumota ya yi sosai a jikinsa tare da cewa "I love you, I need you my lovely" Ido ta dan zaro tare da lallabawa ta zare jikinta...


 Dakyar tasamu ta lallaɓasa ya fice,itakuma ta faɗa toilet..


Washe gari,


Misalin karfe,,9am suka ɗauki hanya,zuwa Adamawa,da yake jirgi,sukabi,daga gombe zuwa Adamawa,basu wani jimah ba suka isha,shatar mota suka dauka in da zata kaisu,har rugar su samha..


 Sam bakin samha yaƙi rufuwa don farinciki yau zataga baba da sauran dangi...


Tun da suka shigo unguwarsu take ganin sauye sauye,bata gama tsinkewa da lamarin ba sai da taji Faruq, yana cewa,da direba nan ne,gaban wani gida suka tsaya ginin zamani,tun daga ƙofa zaka tabbatar da yana da kyau,cike da mamaki take,kallon gidan, don tabbas nan gidansune dan ga sauran makotansu nan,to amma waya mai danshi haka,ta tambayi kanta,sai dai babu mai bata wannan amasar...


Faruq ne yakatse,mata tunani tahanyar cewa kifito mana, fitowatayi tana ƙara ƙarewa gidan kallo,cike da mamaki,fitowar ta tayi daidai dafitowar baba daga cikin gida cike da mamaki baba yanke kallonsu,ɗon betaɓa tsammanin ganin,suba cike da farinciki,samha taruga ta rungume babanta,shima Sam farincikin sa ya kasa ɓoyuwa,cike da zumuɗi tace "Babana nayi kewarka ba kaɗan ba" "Nima "yar baba" ,Rabata ya yi da jikinsa,cike da fara'a yace dasu Abba bismilla kushigo daga ciki maraba lale,nan fa samha tasaki baki tana kallon yan da gidansu yakoma wani babban falo,ya kaisu wan da ya ji manyan kushin,masu kyau,zama sukayi shi da kansa yanufi firij yakawo musu,ruwa, da damun fura mai kauri tasha nono,da hanzari ya futa ya samo musu tsire me zafi.Ya dawo ya zauna aka gaggaisa,tare da tambayar bayan saduwa..


Ebtihal Faruq, yamiƙawa baba tare da cewa "Baba gata asaka mata Albarka" Cike da farinciki marar misaltuwa baba ya karɓeta,tare da cewa "ma shaa Allah gata nan kuwa kamar an tsaga kara kai da ita,to Allah ya rayata yakuma Albarkaci rayuwa,yasunan ta ne? "Ai baba sunan innar samha ne da ita" "Kai ma shaa Allah wannan Abu ya yi,kyau ai wannan nikukayiwa kara" Ya faɗa cike da matsanancin farin ciki..


Sosai baba ya yi wa su Abba godiya abi sa amanar da suka riƙe masa tare da cewa " ƴar baba kitayani godiya gurin mijinki kinga yan da ya mai da gidan nan ko? Faruƙ ya tari numfashin sa ta hanyar faɗin Kai haba baba ai ba sai kunyi haka ba nima ai gidan mu ne"..



Sabida mamakin yaushe yadawo garin,be taɓa sanar,da itaba samha kasa magana tayi..


Abba ne ya ce Ai haryanzu mune da godiya ba kai,ba don kabamu farinciki fiye da wan da mike ciki a baya a cikin gidan mu mugode Allah yabar zuminci" "Amin,wannan haka ya ke Alhaji mun gode,Allah ya saka da mafificin Alkairi" "Ai samha ƴace wacce kowacce mace zataso tasamu suruka irinta,kokuma a matsayin ƴa don haka muke da godiya"...


Tun da tashigo ita ba taji motsin inna mari ba balle su maryam,gashi,har sunkusah awa ɗaya da zuwa,baba ta duba tare da cewa "Baba wai ni ina inna mari dasu maryam tun da mukazo ban jisuba? Hmmm,nisawa baba ya yi tare da cewa, "maryam ta yi aure tana gidanta yaranta,2 sadi kumah yana yawonsa sabi uwarsa ta ɓatashi,mari,kuma tana ɗaki babu lpia, tsahon wata 3 kenan tana fama da matsanancin ciwon ƙafa,anyi maganin anyi amma har yanzu ba'a daceba"..


Subahanallah! Abba yace tare,da cewa "Allah ya bata lafiya, zamu iya zuwa mu duba ta" Amin Baba ya amsah tare da cewa kuzo muje mana me ze hana"


Gaba ɗaya suka nufi ɗakinta, tun daga bakin ƙofa zakafara jiyo ihunta,tana kiran sunan samha,sabi da tana cikin tsananin ciwo,kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da haka,cike da tausayawa duk suke kallonta,musamman samha,oga Faruq kuwa ko ajikinsa musamman idan ya Tuna da irin muguntar da tayiwa Abar kaunarsa...


Kungantanan,kullum haka take yini babu dare babu rana tana kiran sunan samha,, akan ta yafe mata"..


Ai dagudu samha tabar ɗakin tana kuka don bazata iya cigaba da ganin ta acikin wannan halinba,Faruq ne ya rufa mata baya,da kyar ya samu ya rarrasheta,tayi shiru..


 Misalin karfe,3pm Su Faruq, suka tafi,in da sukabar samha sai tayi 2 weeks ze dawo ya ɗaukesu..



Gaba ɗaya yinin ranar HK samha ta yishi zuciyarta fall datausayin inna mari...


Washe gari 


Maryam,tazo gida dan taji labarin zuwan samha,kuka sosai maryam ta dingayi tare da Neman yafiyar samha, idan kukaga maryam za ku yi,tsammanin Babar samha ce sabida yanda ta tsofe,abin babu daɗin gani,sosai samha ta tausaya mata take ta yafe mata..



Zaune samha take ita da baba suna firar yaushe gamo,,in da samha take tambayar baba abin da yafaru bayan tafiyar ta..


"Ai ƴar baba bayan tafiyarki abubuwa dadama sunfaru,naga abubuwa iri-iri a gurin mari, don haka ta sakoni gaba da habaici, wai na ɗaukeki na bayar gawan da ban saniba,fata kuwa babu wan da batayi mikiba lokacin da kuka shekara da tafiya anan abin yafi kowanne lokaci tsanani. don akullum tabuɗe baki bazata faɗi Alkairi a ka kiba,daga tace kina chan cikina cin bakar wahalah sai tace in sha Allah kina hannu marar kyau,abin duk yabi ya dameni,gashi bansan in da zanga Faruq ba balle ke,sai alokacin na dingajin kamar nayi wauta,kullum cikin tuna nin ki nake da irin halin da ki ka shiga,lokacin da kuka shekara,2 ne wata rana,INA zaune abin duniya duk yabi,ya isheni,kamar daga sama sai ga Faruq a wannan rana nayi matukar farinciki marar musaltuwa,jinayi duk kun,cina ya ya ye,in da bangaran mari bataji ,daɗin haka,ba..


Zuwan furuq ne yasa n samu nutsuwa dan na tabbata kina lafiya. Zuwan San kusan 4 bayan tafiyar Ku,sannan yasa aka gyara mana gidan nan tsahon shekara guda kenan


Fatan da mari take yimiki kumahsai ya fadah kan maryam in da ta hadu da mugun miji,wanda ya ke wahalar da ita haka sadi sam ya bajin maga a ya zama fitinan ne, dan wani lokacin Sam baya kwana a gida munan dai ,munata addu'a,Allah ya shiryashi ita kuma mari haka kurum takamu da mummunan ciwon ,ƙafa wanda aka kasa gane kansa,anyi magani amma kamar ma ƙara ,tura ciwon akeyi,tsahon wata 3 kenan,to kinji abin da yafaru, sosai samha ta tausaya musu Dan har da hawaye ta zubar...


Baba taduba tare da cewa, ai yakamata baba a kaita. Asibiti sucan ƙila su gano abinda ya ke damunta" "Eh to haka ne banƙi ta ta kiba sai dai bansan kuɗin da zasu nemaba" "Aa baba karka damu da mawa zasu nema ni zan ɗauki nauyinta gabaki ɗaya" "yanzu duk abinda baiwar Allah nan tayi miki a RAYUWA amma duk kin manta har za ki sakamata da wannan?..


"Ai baba babu komai karma damu da wannan, ai ita RAYUWA ba haka takeba idan mutin ya yi maka mugunta kamata ya yi kamayar masa da Alkairi,shine shedar kafishi,amma idan kamayar masa da sharri to ai kunzama ɗaya kai da shi don haka babu komai duk abin da tayimin ni bani tayiwaba kanta tayiwa,kumahɗ na yafe mata duniya da lahira,Allah ya yafemu baki ɗaya"..


"To ai shikenan Allah ya saka da Alkairi,dama haka akeson mutum na gari yakasan ce,mai mayar da Alkairi ga sharri,don haka babu ,abinda zance miki sai Allah ya albarkaci rayuwa" "Amin,baba.



Kamar kowacce safiya takan,je ɗakin mari tadubata haka zatayi ta kuka tana Neman yafiyarta "Babu komai inna nayafe. Miki duniya da lahira Allah yayafe mana baki ɗya kuma in sha Allah zan kai ki asibiti a dubaki in in sha Allah za ki samu sauki" Godiya sosai mari ta dingayi tana mai ƙara da ta Sanin abinda tayiwa samha a rayuwa..



Duk kan dangi samha ta ziyarcesu,tare da goma ta arziki...


Satin samha ɗaya ta ɗauki inna suka kaita asubiti in da likitoci sukayi ikar kokarinsu amman yazama dole a yanke ƙafar mari,babu yanda su samha suka iya dan wannan ita kaɗai ce mafita...


Mari tanaji tana gani aka yanke mata ƙafa ɗaya,amma ita hakan yafi mata dan ita kaɗai tasan irin azabar da take ciki,bayan tadawo hayyacinta godiya ta dingayiwa samha tare da ƙara fashewa da kuka na dama...


Kwanan ta 4 akasallamesu,suka dawo gida,ta cigaba da shan magani...


Yau ne su samha suka cika sati 2 yau zasu koma gida tun safe take tashiri, misalin karfe, 11 Faruq, ya isho ɗaukansu in da yazo ya tarar da abin da samha tayi sosai ya jinjina wacce,irin zuciya samha,take da ita ya ji dadi sosai tare dayiwa inna fatan samun lafiya



Misalin karfe 1 sukatafi...



Agurguje,

Bayan shekara,1 abubuwa da dama sun faru,ciki har da kammala karatun samha,in da tafitar da sakamako mai kyau...

.



Zaune take a parlour, ƙauke da katon cikinta,wan da haihuwa koyau ko gobe,gefe guda kuma Enbtihal ce zaune an cikamata gabanta da kayanwasa saifaman gwaranci takeyi dan bata ,iya maganaba,sai dai akwai kafa gakuma lafiyar gwaranci, dan yan zune take cika shekara 1 da haihuwa,,



Wata ranar asabar ce samha ta tashi da matsanancin ciwon baya,cike da rudu Faruq ya ɗauketa suka nufi hospital, tasha wahala sosai kafin ta haifi twice ɗin ta duk maza ma sha Allah...


Karkuso kuga farinciki agurin Faruq, da su mama kwanansu 2 aka basu sallama


Nanfa ƴan uwa da dangi akayita kai komo wajan barka


Ranar suna,yara sukaci sunan Abba da baba ana kiransu da mubeen da waleed


Har su baba da inna dasu, maryam sun halarci taron sunan sosai bakadan ba samha,taji daɗin ganinsu


Alhmdllh taro yatashi lafiya..



Bayan shekara 5 


Sosai arzikin Faruq, yafi nada ,in da yasake musu,wani katon gida sun koma,in da suke gudanar da rayuwarsu cikin so dakuma ƙaunar junansu rayuwar gidan mai cike da birge duk wan da ya gani..



*ALHMDULLAH*


*Anan nakawo karshen wannan littafi nawa mai taken ,ƊA NA KOWA NE,, da fatan za ku ɗauki tarin darasin da ke ciki mai kyau kuzubar da marar kyau*


Godiya

*Duk kanyabo da godiya sun tabbata ga Allah ,wanda da ikonsa ne na fara lafiya a yau kuma na gama lafiya*


*Ina godewa ɗaukacin masoya wannan book, tare da fatan Alkairi tare da kwarin guiwar kune,har nakawo,karshen,wannan book,ina godiya over one love guys*,🥰




Ina yiwa ɗaukacin masoya book ɗina fatan Alkairi aduk in da ku ke


Sai mun haɗu a Sabon novel ɗina mai taken........🤪





Sarauniyar jarumai ce😘