FANSAR FATALWA

FANSAR FATALWA 012

by @shamsiyyamanga

*FANSAR FATALWA*

( _Horror Story_ 💀☠️).


_Tsarawa/Rubutawa_


*©* *SHAMSIYYA MANGA*


*SADAUKARWA* : _Wannan book ɗin gaba ɗayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._


*Free book*


-------------------------------------------

*Bissimillahir rahmani rahim*


*012*

____________________________


Lokacin da su Amrah suka koma gida Malam Kabiru bayannan sakamakon wata tafiya ta gaggawa da ta ta so mishi ya tafi cikin Kaduna.


A tsakar gida suka zauna inda suka shiga fito da kayayyakin da suka zo da su ɗin, ido waje gwaggo Sa'adatu ta shiga bin su da kallo tana mamakin yawan kayan, sannan ta buɗi baki ta dubi Umar tace.


"Umar wannan kayan fa haka,ko dai ido na ne?".


Murmushi Umar ya yi sannan yace.


"Gwaggo ba idon ki ba ne wannan kayan duka na Amrah ne,na tafiya makarantar ta".


Kayan Gwaggo Sa'adatu ta shiga ɗagawa ɗaya bayan ɗaya baki buɗe.


"Kai Umar a ina ku ka samu kuɗin siyo waɗannan kayan haka?".


"Wallahi Gwaggo Anwar ne ya yi duk waɗannan siyayyar kuɗin da muka tafi da su ma ga su nan ko taɓa su bamu yi ba mun dawo da su".


Umar ya faɗa yana ciro kuɗin a aljihun shi yana nuna wa Gwaggo Sa'adatu.


Shiru Gwaggo Sa'adatu ta yi kamar mai nazarin wani abu kafin can ta ɗago tace


"Amma Umar kana ganin hakan ba kuskure ba ne ba kuwa?".


"Gwaggo kuskuren mai Kennan?".


"Kafi kowa sanin halin mahaifin ku, kasan sarai idan har ya ga waɗannan kayyayyakin ran mu ne gaba ɗaya zai ɓaci".


Caraf Amrah ta amshe zancen wadda tun da suka dawo sai yanzu ta yi magana.


"Wallahi nima Gwaggo tun da muka taho abun da yake ta mun yawo Kennan a rai,gashi ba halin mutum ya maka kyauta kuma kace ba zaka karɓa ba, amma ni nasan matuƙar Abba yaga kayan nan sai ya sa an mayar wa da Anwar su,kuma ma Gwaggo kin ga Abba bai san alaƙar da take tsakanin mu da Anwar ɗin ba, nikuma gaskiya da ran shi ya ɓaci gwanda kawai tun kafin ma yazo ya ga kayan kawai a ƙira Anwar ya zo ya ɗauki kayan shi".


Amrah ta faɗa fuska da damuwa.


"Hakane Amrah kema kin ce wani abu,amma in sha Allah zan yi ƙoƙari na fahimtar da Abba har ya fahimta, kuma zan sanar dashi ƙudurin Anwar ɗin a kan ki".


Umar ya faɗa yana kallon su duka su biyun.


"To Shikennan Umar Allah ya maka Albarka, sai ya dawo ɗin muji abun da zai ce".


Gwaggo Sa'adatu ta faɗa tana miƙewa tare da mayar da kayan gefe.


Tashi Amrah ta yi tace


"Gwaggo bari na je gidan Anty Naja (matar Hisham) na dawo jiya tace naje na mata kitso".


"To a dawo lafiya ki gaida ta".


Sai yamma liƙis Malam Kabiru ya dawo, Gwaggo Sa'adatu kaɗai ya tarar a gidan, da fara'a ta tare shi tana mishi sannu da dawowa,sannan ta shimfiɗa mishi tabarma a tsakar gida kasancewar lokacin zafi ne.


Abinci da ruwa ta kawo mishi sai da yaci ya tashi ya shiga wanka bayan ya gama komai ya zo ya zauna, kafin Gwaggo Sa'adatu ta shiga bashi labarin siyayyar da Anwar ɗin yayiwa Amrah ɗin, har Gwaggo Sa'adatu ta gama zancen da take ɗin Malam Kabiru bai cai uffan ba.


Tun daga irin kallon da Gwaggo Sa'adatu ta ga Malam Kabiru ɗin yana mata ta sha jinin jikin ta.


Tashi ta yi ta shiga ɗaki sannan ta shiga fitowa da kayan da Anwar ɗin ya saiwa Amrah ɗin.


Ai tun kafin ta gama fito da kayan gaba ɗaya taji ya ƙira sunan ta da kakkausar murya har sai da hanjin cikin ta ya kaɗai.


"Sa'adatu mai nake gani haka?".


Cikin inda-inda Gwaggo Sa'adatu ta fara magana.


"Malam su ne kayan da nake faɗa ma yaron can Anwar abokin Umar ya saiwa Amrah wallahi yaron akwai kirki ga.......".


Saurin dakatar da ita Malam Kabiru yayi sannan yace.


"Sa'adatu yaushe hankalin ki da tunanin ki suka fara gushewa ban sani ba?, Eyeee nace yaushe hankalin ki da tunanin ki suka fara gushewa ban sani ba,idan su su Amrah da Umar ɗin basu da hankali ƙuruciya tana ɗawainiya da su ai ke babba ce kuma kin fi su hankali".


Ya faɗa yana duban Gwaggo Sa'adatu ɗin fuska a haɗe.


"Mala.......".


Saurin dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu sannan ya cigaba da magana


"To tun wuri ma kiyi gaggawar ƙiran Umar ɗin a zo a ƙiran yaron ya zo ya ɗauke kayan shi, kamar yadda na yi alƙawarin zan sanya Amrah a makaranta zan kai ta,idan ina da shi idan bani da shi babu wani ɗan Adam da zan nemi taimako a wajen shi,dan haka ni talaka ne zan yi iya abun da zan iya akan Amrah sauran ta yi haƙuri a hankali idan Allah ya hore mun sai na mata amma a yanzu, a zo a mayar da kayan nan tun kafin ran kowa ya ɓaci,wannan ai salon ku sanya a zage ni ne, to ba zai yiwu ba".


Tun daga ƙofar gida Amrah ta fara jiyo maganganun mahaifin nata, idan ta shiga cikin gidan bakin ta ɗauke da sallama sannan ta ƙarasa wajen da iyayen nata su ke tsaye.


Durƙushewa ta yi a ƙasa tare da fara magana cikin rawar murya.


"Abba dan Allah ka yi haƙuri,in sha Allah ba za'a yi abun da zai sanya ka a cikin ɓacin rai ba, Abba daman ni wallahi ba'a son rai na aka karɓo kayan ba, dan haka ka yi haƙuri wallahi za'a mayar mishi, amma Abba dan Allah kar ka sanadiyar haka ran ka ya ɓaci".


Amrah ta faɗa tana ƙarashe sakin kukan da take riƙewa ɗin.


Tausayin Amrah ɗin ne ya kama Malam Kabiru ɗin da Gwaggo Sa'adatu, a hankali Malam Kabiru ya dube ta ya fara magana.


"Amrah ko kaɗan rai na bai ɓaci ba, kuma bana fatan Allah ya kawo ranar da zaki zamo sanadiyyar ɓacin rai na,ke ɗin yarinya ce mai biyayya, dan haka ina son ki ɗauki wannan abun da nake shirin yi a matsayin shine dai-dai".


Share hawayen ta Amrah ta yi sannan tace.


"Abba komai ka aikata a garemu shine dai-dai bamu taɓa ɗaukar wani hukunci da ka zartar a cikin gidannan a matsayin ba dai-dai ba,dan haka komai ka zartar zamu karɓe shi ko da bai mana daɗi ba".


Sosai Gwaggo Sa'adatu da Malam Kabiru suka ji daɗin maganganun Amrah ɗin,inda suka shiga sanya mata albarka.


A daren ranar Malam Kabiru ya ƙira Umar ya sanar da shi a kan hukuncin da ya yanke ɗin,yace kuma maza-maza ya sanar da Anwar ya zo ya ɗebi kayan shi


Duk yadda Umar ya so ya fahimtar da mahaifin na shi akan Anwar yayi hakan ne dan Allah amma ina Malam Kabiru ya ƙeƙashe ƙasa kasancewar shi mutum mai magana ɗaya.


Haka Umar ba dan ya so ba ya ƙira Anwar ya mishi bayanin komai,kuma Alhamdulillahi Anwar ya fahimta inda ya zo ya ɗauki kayan.


Sai dai fa Anwar yana komawa gida ya sanar da mahaifin shi cewar yana so a zo a tambayar mishi izini a wajen mahaifina.


Hakan kuwa aka yi ana saura sati ɗaya na tafi makaranta iyayen Anwar suka zo suka nemi izini a wajen Mahaifina, kuma cikin ikon Allah mahaifina yace a bashi kwana biyu.


Kamar yadda mahaifin Amrah ya faɗa hakan kuwa ta kasance a cikin kwanaki biyun da ya faɗa ya ƙira Amrah ya tambaya ta shin ko ina son Anwar,shirun da na yi shi ya bashi damar fahimtar komai inda yace ta tashi ta tafi.


Amrah bata tashi tafiya makaranta ba sai da aka tabbatar da angama komai na maganar auren su da Anwar kawai rana ce ba'a sanya ba,amma dai an bashi ita an gama komai maganar auren akwai ta akan Amrah.


Cikin kwanaki ƙalilan ɗin da suka ragewa Amrah na tafiya makaranta, Malam Kabiru mahaifin Amrah ya yi duk yadda zai yi yayi bakin ƙoƙarin shi inda ya mata siyayyar duk wani kayan buƙata dai-dai ƙarfin talaka.


Gwaggo Sa'adatu ma ta yi iya bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta haɗa mun ɗan abubuwan da ba'a rasa ba, irin su kayan yaji, niƙaƙƙen kayan miya,mai, manja,daddawa,taliya ƴar mirji,yajin borkono,da yajin ƙuli-ƙuli da sauran su dai duk sai da ta tabbatar ta haɗawa Amrah.


Su yaya Hisham ma sun yi iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun taimakawa Abba an mun siyayya dai-dai ƙarfin talaka ba abun da aka rageni dashi.


Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, yau ta kama ranar da Amrah zata tafi makaranta.


Tun asubah da ta tashi ta yi salla bata koma bacci ba ta shiga shiryawa, sai da ta sa kaya sun kai wajen biyar tana cirewa ita a dole bata yi kyau,da ƙyar dai Gwaggo Sa'adatu ta nemo mata wata atamfa mai ruwan ganye da hijab har ƙasa, daman Amrah bata sa mayafi.


Ƙarfe Bakwai dai-dai yaya Hisham suka zo shida Umar dan tafiya raka Amrah makarantar inda zata fara karatu a AHMADU BELLO UNIVERSITY ZARIA Fannin Medicine.


Malam Kabiru ne ya aiko ƙiran ta inda ta je ta same shi a cikin ɗakin shi.


Zama ta yi a gefen shi inda Gwaggo Sa'adatu take zaune daga ɗayan gefen.


"Amrah".


Malam Kabiru ya ƙira sunan Amrah ɗin cikin wata iriyar murya da bata taɓa jin shi da ita ba.


Saurin ɗago idon ta Amrah ɗin ta yi sannan tace.


"Na'am Abba"


Jikin ta duk ya yi sanyi.


"Amrah yau dai gashi Allah yayi zaki tafi makaranta,nayi iya duk ƙoƙarin da zan yi naga na miki duk abun da ya kamata dan haka duk abun da ki ka gani kawai kiyi haƙuri dashi, sannan abu na gaba Amrah dan Allah ƙawaye ki san irin ƙawayen da zaki yi mu'amala da su saboda a wannan zamanin ƙawaye sai an tona ake samun na kirki, Amrah duk abun da zaki yi kar ki manta da ga gidan da ki ka fito,kar kuma ki manta da ke wacece da kuma matsayin mahaifin ki,mutunci, Amrah ki riƙe mutuncin ki sannan kar ki ringa hangen rayuwar wasu. Kiyi haƙuri da abun da ki ka je da shi kar kice dan wance tana da abu kaza kice kema sai kinyi. Na sani Allah ya sani ga ƴanuwan ki nan shaida ne tarbiya dai-dai gwargwado na baki ita Amrah idan har ki yi watsi da tarbiyyar da na baki Amrah baki mun adalci ba,sannan kin cuci kan ki bani kika cuta ba, dan haka zan ƙara maimaita miki ƙawaye ki kula da su bance kar ki kula ƙawa ba amma dan Allah ki san irin ƙawyen da zaki yi mu'amala da su,Allah Ubangiji ya kare ki,ya baki abun da ki ka je nema ya kuma dafa miki a harkar karatun ki".


Tun da mahaifin Amrah ya fara magana jikin Amrah ya yi wani irin sanyi kamar ruwan fridge,wasu hawaye ne suka shiga biyowa ta kuncin ta ita kam ji ta yi lokaci guda karatun ya sare mata a rai har taji kamar tace ta fasa, a hankali ta sanya hannu ta goge hawayen fuskarta ta sannan ta buɗi baki ta fara magana.


"Abba in sha Allah karma yadda ka yarda cewa ka bani tarbiya dai-dai gwargwado Abba na maka alƙawarin ba zan taɓa watsa maka ƙasa a ido ba, Abba in sha Allah zan yi karatu kuma zan zo maka da kyakkyawan sakamako wanda zaka yi alfahari dani, Abba fatana shine kawai ka tayani da addu'a kamar yadda ka ke mun kullum,ba zan taɓa fatali da irin tarbiyyar da ka bani ba Abba wannan alƙawari ne na ɗaukar wa kai na".


Kuka sosai Amrah ta shiga yi kamar an aiko ta.


Rungumeta Gwaggo Sa'adatu ta yi sannan ta shiga bubbuga mata bayan ta alamar rarrashi.


Sai da ta rarrashe ta kafin ta tashi inda suka fice a gidan dan mata rakiya zuwa tasha su hau mota.


Sai dai suna fita suka tarar da Anwar a tsaye a ƙofar gidan a jikin motar shi.


Ba yadda suka iya haka Gwaggo Sa'adatu da Hisham da Umar suka shiga motar bayan an sanya kayan Amrah a bayan motar suka kama hanyar Zaria ɗin daga garin Giwa.


Amrah sosai take kuka ga wani irin matsanancin faɗuwar gaba da take ji tun da suka kama hanyar zuwa garin Zaria ɗin wanda ta rasa gane kan shi.


Allah sarki ashe mafarin tarwatser duk wani farin cikin ki ne Amrah.🥺😫


*MANGA* ✍️

_Comment_

_Share_