Chapter 13
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*13*
Muhsin yana fitowa ya tofar da yawu yana sake yamutsa fuska dan bai daina jin warin ba har lokacin ya fara kalle-kallen gefe da gefen sa da alama wani abun yake nema. "Kuna ina!?." Ya fad'a cikin d'aga murya yana sake kallon gefen sa.
A guje mutum biyu suka tawo wajan ya kalle su up and down kana yace, "wannan wanne irin iskanci ne, kun san hatsarin tafiya ku bar wajan nan babu kowa kuwa? Yanzu in ya fito fa?."
Dukkan su kansu a k'asa yake har ya gama fad'an sannan d'aya yace, "kayi hak'uri Oga ganin mun kulle k'ofar ne ya saka muka zaga mu d'an ci abinci."
"Abincin banza, tsaron k'ofar baifi cin abincin naku ba?."
"Kayi hak'uri."
"Mtswww in kuka sake na sake dawowa wajan nan naga bakwa bakin k'ofar nan sai ranku yayi bala'in b'aci."
"Kayi hak'uri Oga baza'a sake ba insha Allahu."
Har ya d'aga k'afa zai tafi d'aga daga cikin su yace, "Oga." Juyowar da yayi ya kalle shi ya saka ya kasa furta komai har sai da Muhsin yace, "Meye?."
Sosa kai yayi kafin yace, "bawan Allah nan yana cikin wani hali kullum da ciwo yake kwana daga nan muna jiyo yadda numfashin sa yake fita kamar zai bar gangar jikin sa." Kama k'ugu yayi yace, "to sai me?."
"Wai ko za'a kaishi asibiti dan wallahi ko abinci baya ci."
"Kaje pharmacy ka karb'o masa magani amma batun zuwa asibiti babu shi kar ka sake yi min wannan banzar maganar." Yana gama fad'ar hakan ya bar wajan Salim ya bi bayan sa jikin sa duk a sanyaye.
Koda suka d'auki hanyar cikin gari Salim shiru yayi kamar babu shi a motar har sai da ya kalle shi yace, "kai wai qalau kake?." Kallon sa yayi kafin ya sauke numfashi yace, "Muhsin azabar da kake bawa Imran tayi yawa wallahi, cewa kayi fa kawai sati biyu zaiyi a hannun ka amma ka duba yanzu ya doshi wata shida a nan a cikin wannan wulaqantaccen wajan ga wari gashi babu abincin kirki ga rashin lafiya, please Muhsin ka saki mutumin nan ya koma gida ko hankalin iyayen sa da y'an uwan sa zai kwanta."
Girgiza kai Muhsin yake sannan yace, "Salim bazan saki shi ba har sai na auri k'anwar tasa in baza ka jure gani ba kar ka sake biyo ni." Salim yace, "haba Muhsin abin yayi yawa wallahi, ka kama shi ka kulle har tsahon watanni sannan kuma zaka aure masa k'anwa wacce yake fatan aura, yarinyar nan shine ya raine ta ya bata duk wata kulawa ya kuma bata ilimi da gumin sa, kamar ba musulmu ba."
Muhsin bai kula shi ba ya cigaba da tuk'in sa Salim yaja numfashi yana mai dana sanin kawo shawarar a d'auke Imran, duk da yasan haka zata faru da bai nemo komai akan imran ya fad'awa Muhsin ba, yanzu yake jin zafin bada goyan baya a kan kawo Imran wannan wajan.
Haka suke ta tafiya babu mai magana har suka isa gidan su Muhsin Salim tun a compound ya fita ya wuce gidan su dan haushin Muhsin d'in yake ji sosai shi kuma ya shiga gida domin ko a jikin sa.
Da Mufeedah ya fara karo a zaune kamar kullum tana abinda ta saba wato tunani har ya k'araso bata sani ba sai da ya zauna kusa da ita sannan ta d'ago kai ta kalle shi bata ce komai ba, "Mufeedah na fad'a miki ki daina wannan tunanin zan saka a nemo miki shi inbsha Allah."
Kallon sa tayi tace, "Yaya yaushe? Tun ina saka ran zuwan ranar na daina. Ina ji a jiki na yana can ana wahalar dashi, bazan tab'a yafewa wanda ya sace min miji ba ina kuma rok'on Allah ya tsinewa wanda ya d'auke min shi" kukan da yaci k'arfin ta ya hana ta k'arasawa ta kwantar da kanta a jikin sa tana kuka mai k'arfi.
Wani iri yake ji a jikin hakan ya saka shi lumshe ido ya bud'e yace, "ki kwantar da hankalin k'anwa ta mijin ki zai dawo Allah kuma zai tona asirin duk wanda ya sace shi, wannan yawan kukan naki ne ni bana so wallahi." Share idon ta tayi ta mik'e bata ce komai ba ta hau sama ya bita da kallo.
Tana barin wajan yaja dogon tsaki yana binta da kallo yace, "ke har kin isa ki d'auko jinin talaka ki kawo mana family? Talakan ma irin Imran wanda ya d'auki hannu ya mare ni tsabar tsaurin ido, ki gama kukan ki gama amma Imran yayi miki nisa yarinya."
Motsin ta da ya jiyo ya saka ya kalli wajan ya ganta da k'aton hijjabi da kuma key da mota ta nufi hanyar fita, ko bata fad'a ba yasan gidan su zata je dan yanzu bata da wajan zuwa sai gidan su Imran baice komai ba har ya fita shi kuma ya tashi ya hau sama.
Mufeedah kuwa k'ofar gidan su Imran tayi parking ta bud'e motar ta shiga gidan kamar yadda ta saba. A zaune ta tarar da Umma da Anty Surayya suna zaune suna hira tayi sallama ta shigo gidan kanta a k'asa.
Anty Surayya ta amsa tana fad'in, "Sannu da zuwa Mufeedah." Murmushi tayi ta d'urkusa har k'asa tace, "ina wuni Umma." Umma tace, "lafiya lau Mufeedah, ya mutanen gidan?." "Lafiya lau suke, ina kwana Anty." Anty Surayya tace, "lafiya lau Mufeedah, taso kizo ki zauna mana." Ba musu ta mik'e ta k'araso ta zauna a gefen ta tabarma kanta k'asa tayi shiru.
Anty Surayya ta mik'e tace, "bara na kawo miki ruwa." Da sauri Mufeedah tace, "A'a Anty basai kin wahala ba daga gida nake." Komawa tayi ta zauna tana fad'in, "to shikenan."
"Ba samu labarin saba ko?" Ta fad'a tana kanta a k'asa tana jiran amsar su.
"Shiru har yanzu Mufeedah muna nan dai muna ta addu'a" Anty Surayya ta bata muryar ta a sanyaye.
Shiru Mufeedah tayi bata sake cewa komai Umma bata sake magana ba sukayi shiru wajan, "Umma bara na koma gida" ta fad'a tana mik'ewa tsaye dan abinda ya kawo ta taji, Sallama sukayi ta tafi jiki a sanyaye kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
Bayan fitar ta Anty Surayya ta kalli Umma tace, "Umma yarinyar nan tana qaunar Imran sosai ki duba yadda take ta zarya a gidan nan tun daga lokacin bacewar sa." Girgiza kai Umma tayi tace, "nima naga alamun hakan Surayya, alamun ta sun nuna qaunar sa take bawai dan yana matsayin ma'aikacin ta take zarya a nan ba, daga farkon zuwa ta zuwa yanzu itama ta rame sosai."
"In Allah ya bayyana Imran ina shi ina auren yarinyar nan? Ai tafi k'arfin sa." Murmushi Umma tayi tace, "Allah ne kad'ai yasan abinda ya b'oye mu cigaba da addu'a kawai." Sallamar Jannat ta katse musu tunani ta shigo kamar koda yaushe fuska a cunkushe.
"Umma sannu da gida, Anty Surayya sannu da zuwa." Abinda tace kenan ta ajjiye jakar ta da mayafin ta ta juya ta koma soro ta bud'e d'akin da yake mallakin Imran ta shiga.
D'akin tass dan kullum sai ta shiga ta share ta gyara komai dan nan ne ya zama wajan zaman ta, k'arewa d'akin kallo take ta jingina da bango tana kallon hoton su lokacin tana da shekara biyar a duniya ya d'auke ta kanta na kafad'ar sa tana dariya shima haka. Dariyar tayi kafin hawaye ya maye gurbin dariyar ta zube a wajan tana kuka.
Anty Surayya ce ta shigo d'akin bata ce komai ya d'aga ta tare da rik'o kafad'ar ta suka fito tsakar gida ta zaunar da ita akan kujera ta zauna a gefen ta tace, "Haba Jannat wai har yanzu baza ki daina wannan koke-koken ba? Kukan nan da kike yi ba shine magani ba a yanzu, a duk inda yake addu'ar mu yake buk'ata ba wannan kukan naki ba, mun san dole ki kasa jure rashin sa amma hak'uri zakiyi ki daure ki kuma mik'awa Allah lamarin komai zai daidaita insha Allah."
Umma da take kallon ta cikin tausayi tayi ajiyar zuciya domin tasan in aka cire ta a wanda ya damu da b'atan Imran Jannat ce zata biyo baya itama kuma dan ta kasance uwa ne, amma da zata iya cewa Jannat tafi kowa shiga damuwa game da rashin sa, yadda ta shiga damuwa tasan ko y'an uwan sa basu shige ta ba sabida ita dashi ta saba fiye da kowa a duniya shiyasa take tausayawa mata.
"Kiyi hak'uri kinji Khadija, tashi kici abinci." Umma ta fad'a tana kallon ta. Bata yi musu ba ta share idon ta ta mik'e ta shiga kitchen.
Sai da akayo magariba sannan ta shiga gidan su Abba yana zaune yana lazumi Gwaggo na gefen sa ta shiga ta zauna tana jiran Abba ya idar dan yace daman tazo, sai da ya gama ya kalle ta yace, "Jannat jiya wani yaro d'an nan mak'otan mu yazo ya same ni akan yana son ki da aure." Gaban ta ya fad'i har bata san lokacin da ta dafe k'irji ba ta d'ago ta kalli Abban nata tace, "Aure kuma Abba?." D'aga mata kai yayi yace, "aure mana Jannat, ko haka zaki zauna bakiyi aure ba?."
Shiru tayi kanta a k'asa gaban ta yana fad'uwa ta kasa cewa komai, Abba ya d'ora da fad'in, "na bashi dama nace yazo ku tattauna gobe da yamma in Allah ya had'a shikenan in kuma ba shine mijin ba sai muyi fatan Allah ya kawo mijin naki." Shiru tayi bata ce komai ba ya sake cewa, "baki ji me nace miki bane?."
"Naji Abba, Allah ya kaimu goben." Ya amsa da amin ya mik'e ya fita sabida kiran sallar i'sha da yaji ana yi.
Yana fita ta fashe da kuka ta fad'a jikin Gwaggo, Gwaggo da take kallon ta da mamaki tace, "to Jannat meye na kukan? Kin san halin mahaifin ki tunda samari suka fara zuwa suna samun sa zance ya k'are, kiyi hak'uri kawai ki kwantar da hankalin ki ki kuma yi abinda yace."
"Gwaggo a wannan halin da nake ciki na rashin Yaya na ta yaya za'ayi min zancen aure? Nayi aure ma a wannan halin kamar naci amanar sane dan na tabbata in da nice ba'a gani ba Yaya bashi da nutsuwar da zaiyi aure har sai na dawo" ta fad'a cikin muryar kuka.
Shiru Gwaggo tayi bata ce mata komai ba dan bata san me zata ce mata ba hakan ya saka taja bakin ta tayi shiru. Sai da ta gaji da kukan dan kanta sannan ta mik'e tayi alwala tayi sallar i'sha ta d'auki mayafin ta ta koma gidan Umma.
Tun shigar ta Umma taga fuskar a cunkushe ta nemi waje ta zauna Umma ta kalle ta bayan ta zauna tace, "Khadijah me ya saka ki kuka naga idanun ki sunyi ja?." Maimakon ta bata amsa sai sabon kuka da ta sake fashewa dashi cikin kukan tace, "Ba Abba bane wai wani yazo ya same shi yana sona wai gobe zai zo mu gaisa." Murmushi Umma tayi cikin farin ciki tace, "Alhamdulillah a ina yaron yake?." Kallon fuskar Umma tayi tace, "Umma naga kina murmushi farin ciki kike?."
"To Jannat in banyi farin ciki ba me kike so nayi? Autar muce fa zatayi aure ba dole nayi murna ba." Takaici ya hana Jannat magana kawai ta zubawa Umma ido tana kallon ta tace, "Umma Yaya na baya nan ba'a san inda yake ba, ba kuma a san ranar da zai dawo ba amma shine ni zanyi aure,? Wannan abinda bazai yu bane Umma" Ta gama fad'a tana mik'ewa ta shiga d'akin Umma da gudu tana kuka.
Da kallo Umma ta bita kawai tana murmushi tare da tausaya mata domin tun ba yanzu ba ta fuskanci soyayyar tsakanin su bata shaquwa bace kad'ai, zuqatan su sunyi nisa cikin k'aunar junan su kawai dukkanin su basu fukanta bane, tasan dole Jannat zata sha mutuk'ar wahala in akace za'a aurar da ita amma dole tayi aure tunda shi Imran d'in ba'a san ranar da zai dawo ba wata k'ila ma ya mutu, Ajiyar zuciya tayi ta mik'e itama ta shiga ciki.
Yammacin washe gari Jannat ta fito daga exams tana zaune tana hutawa tare da duba littafi, daga can nesa taji an kwala mata kira ta juya ganin y'ar class d'in su ta saka ta mayar da hankalin ta kanta taji tana fad'in, "an ce kar wanda ya tafi za'ayi presentation." D'aga mata kai Jannat tayi bata ce komai ba ta cigaba da abinda take yi.
Tana nan zaune har biyar da rabi hakan ya saka ta mik'ewa ta nufi hall d'in da take tunanin a nan za'ayi presentation d'in, hall d'in a cike da y'an class d'in su ta shiga ta zauna itama ana jiran malami yazo amma shiru. Class captain ne ya mik'e ya fita dan ya tambayo malamin dan jiran yayi yawa sosai, bai jima ba ya dawo ya sanar dasu malamin yace repeaters ne zasu zauna su y'an fresh su tafi.
Duk ajin aka yoye ya zama kwata-kwata basu fi su sha biyar ba gashi magariba ta kawo kai, suna ta zaman jira har akayi magariba shiru kowa yana jin tsoron kar ya tafi malamin yazo, ganin magariba tayi ya saka dukkanin suka fito kowa yayi hanyar gida.
Duhu yayi Jannat sai sauri take dan da nisa daga hall d'in zuwa gate gashi wajan babu mutane da yawa, ga wajan shiru kamar daji, sauri take sosai tana waige dan tsoro take ji bata tab'a kaiwa haka a school ba sai yau.
Kamar daga sama taji an ja hannun ta da k'arfin gaske wanda hakan ya tilasta mata yin gaba tabi bayan su kamar zata kifa, cikin duhuwa suke janta tana ihu amma wajan babu jama'a har suka isa wajan ciyayi sannan suka sake ta, a jikin bango ta rakub'e jikin ta na rawa tace, "su waye ku? Me kuke so a waje na?."
Dukkan su fuskar su a kulle take da bak'in yadi hakan ya saka bata ganin kowa a cikin su ga wajan babu haske, "Ke muke so kuma kanki zamu bamu, mun jima muna jiran ranar da zamu same ki bata zo ba sai yau" wanda ya jawo hannun ta ya fad'a yana kallon ta. Jin abinda suka ce jikin ta ya tsananta wajan rawa ta d'urkushe a wajan tace, "dan Allah kuyi hak'uri kar kuyi min komai."
Da hanzari wani ya k'araso wajan ya fincike mayafin jikin ta hakan ya saka ta kwalla k'ara mai had'e da kuka. Haske su akayi da fitila mai shegen haske hakan ya saka su kallon wajan tare da barin wajan da gudun gaske ba tare da sun shirya ba, A gigice ta mik'e ganin su gudu tana kallon inda take ganin hasken kafin taga an kashe ana nufo inda take tsaye.
Muhsin ne ya k'araso wajan ya kalle ta baice komai ba ya d'auki mayafin ta ya bata ta karb'a, jikin ta har lokacin yana rawa ya sunkuya ya d'auki jakar ta da wayar ta yace, "muje." Ai ba musu tabi bayan sa suka fito daga wajan zuwa inda motar sa take har lokacin bata dawo nutsuwar ta ba ganin hakan ya saka shi yace, "ki nustu Jannat babu abinda zai cutar dake ina tare dake."
Sai a lokacin ta kalle shi ta fuskanci waye sannan tace, "nagode." Ta fad'a tana niyar barin wajan yace, "kizo na kaiki gida dare yayi kafin ki samu abin hawa zaki jima ga hanyar babu mutane."
D'an jim tayi bata motsa ba ba kuma tace komai ba ya saka cewa, "kizo muje bazan cutar dake ba." Bata da zab'in da ya wuce ta shiga shima ya shiga ya mik'a mata jakar ta da wayar ta yaja motar suka bar wajan.
Sai da suka fita daga makarantar yace, "Meyasa kika kai dare haka a school bayan kin san hanyar nan bata da kyau?." Bata bashi amsa ba sai kallon titi da take gaban ta na fad'uwa sosai ta kasa ce masa komai domin shima ba yadda tayi dashi ba.
Ganin hakan ya saka yace, "ki daina kaiwa haka a makaranta b'ata gari sunyi yawa a cikin ta yanzu in badan Allah ya kawo ni ba da yanzu ba labarin nan ake yi ba." Ajiyar zuciya tayi ta lumshe ido ta jingina da kujera bata ce masa komai ba har lokacin.
Fuskar ta ya kalla yaga ta kulle idon ta eyelashes d'in ta sun sakko k'asan idon ta sunyi zarara kamar wacce taje aka saka mata, wani abu yaji ya tsirga masa tun daga k'afar sa har cikin kasan hakan ya saka shi d'auke idon sa da sauri ya mayar kan titi zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri.
Sai da suka tsaya a k'ofar gidan su ta bud'e idon ta lokacin ana ta kiran sallar i'sha, kallon sa tayi tana mamakin ya akayi yasan gidan su har ya kawo ta? amma da yake bata son wata doguwar magana ta had'a su ya saka ta basar amma fad'uwar gaban ta ya k'aru ta rasa me yasa hakan.
Littafan ta ta d'auka da wayar ta ba tare da ta kalle shi ba tace, "Nagode." Tana gama fad'ar hakan ta bud'e motar ta fice ya bita da kallo, Murmushi yayi lokacin da yaga gidan da ta shiga ya kwantar da kansa a kan sitiyarin motar yana dariya kad'an-kad'an.
D'ago kansa yayi yana sake kallon gidan kafin yace, "plan 1 have done." D'auko littafin ta yayi wanda ya b'oye a motar kafin yace, "plan 2 is loading." Sake murmushi yayi ya ajjiye littafin ya ja motar sa ya bar k'ofar gidan yana jin wani irin shauk'i mai dad'i a zuciyar sa.
Wattpad@ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.