Chapter 14
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*14*
Jannat kuwa tana shiga gidan Gwaggo Umma da take zaune suka taso suna fad'in, "Alhamdulillah, Jannat ina kika tsaya haka yau?" Zama tayi ta d'an dafe kanta tare da fad'in, "kaina nayi min ciwo." Umma ta sake cewa, "Sannu, lafiya kike kuwa na ganki wani iri me ya same ki?."
Gwaggo waya ta d'auka ta kira Abba ta sanar dashi ta dawo sannan ta dawo da hankalin ta ga Jannat da take zaune hannun ta rik'e da kanta, "Umma cewa akayi mu zauna zamuyi presentation mu da muke maimaita aji, to shine mukai ta jira kowa yana tsoron kar ya tafi azo ayi babu shi ya fad'i amma babu malamin da muka gani, kin san wanda muke maimaita ajin nan wani lokacin muna shan wulaqanci kala-kala, muka k'araci zaman mu muka tawo, hanyar shiru babu kowa gashi babu haske ina ta sauri shine kawai wasu maza suka zo suka jani wani waje." Shiru tayi da takai nan tana d'aure fuska kamar wacce aka yiwa wani abun.
"Me suka yi miki?." A tare dukkan su suka tambaya cikin tashin hankali da jiran me zata ce, girgiza kai tayi tace, "Allah ne ya taimaka wani d'an makarantar yazo ganin sa shine suka gudu shi kuma ya kawo ni har nan yanzu." Ajiyar zuciya sukayi kafin Umma tace, "Alhamdulillah, Allah ya k'ara kiyaye gaba, kema kuma kar ki sake yin dare a makaranta yanzu in badan wanda ya taimake ki d'an albarka bane da shima cutar dake d'in zaiyi."
Ita dai Jannat shiru tayi kawai bata ce komai ba sai da aka gama jimamin sannan ta mik'e ta shiga band'aki tayi alwala ta tayar da sallar magariba bayan ta idar tayi i'sha kana taci abinci.
Da sallama Abba ya shigo suka amsa kafin yace, "Jannat d'auki mayafin ki kije soro bak'on da nace miki zakiyi yana jiran ki." Idon ta ya ciko da kwallah ta kalli Gwaggo taga ta kawar da kanta dole ta mik'e dan bata da ta cewa ta d'auki mayafin ta ta fita kamar yadda yace.
Bata wani jima da fita ba ta dawo ta zauna a inda ta tashi Abba yace, "har ya tafi?." D'agawa Abba tayi kanta a sunkuye yace, "ma sha Allah, Allah ya tabbatar da alkhairi, tashi kije gidan Umman naki kar dare yayi." Bata ce komai ba ta mik'e tayi musu sai da safe ta fita.
Gwaggo ta kalli Abba tace, "yarinyar nan bata son maganar aure sam gani take in tayi aure Imran baya nan kamar taci amanar sane duka hankalin ta ya tashi a kan hakan." Abba yayi murmushi yace, "muma dukkan mu baza muso tayi aure baya nan ba ai, amma lalube muke a cikin duhu Allah ya rubuta dukkan abinda zai faru, mu zubawa ikon sa ido muga abinda ya k'addaro mana, Allah ya sani ina ji a jiki na Imran shine mijin Jannat amma ta yaya? Yaushe? Duk shine ya sani."
"Haka ne, Allah ya zab'a mafi alkhairi." Ya amsa da amin.
Jannat kuwa da ta shiga gidan Umma tun kafin ta zauna tace, "Ya kukayi da wanda yazo wajan naki?." Turo baki tayi tace, "na fad'a masa ina da wanda nake so yayi hak'uri."
"Meyasa kika aikata hakan Jannat? Waye wanda kike so d'in?."
"Babu Umma, na fad'a ne dan ya k'yale ni kawai."
"Yanzu in Abban ki yaji fa?."
"Umma bazai ji bama, bazan iya aure Yaya baya nan ba Allah ya sani." Tana gama fad'ar hakan ta shige d'aki ta bar Umma baki bud'e tare da mamaki.
Washe gari ta kama alhamis Umma tayi niyar zuwa ziyara gidajen y'an uwan ta hakan ya saka ta shirya da wuri Jannat ta gama komai na gidan ta tafi ta bar mata gidan.
Itama tana gama shiryawa misalin k'arfe sha biyu da rabi ta d'auko jakar ta niyar duba littafai dan tana da exams k'arfe biyu na rana, neman duniya tayi amma bata ga littafin da take nema ba gashi duk wani jotting nata a ciki yake kuma jarabawar sa itace ta biyu.
Hankalin ta yayi bala'in tayi dan dai ta tabbatar ta fita dashi jiya gashi bata ganshi ba kuma yau, "Na shiga uku ina zanga littafin nan?." Ta fad'a tana cigaba da hartsiga jakar amma babu.
Dafe kai tayi tace, "kodai jiya na yar dashi ne a wajan da abin ya faru?." Mik'ewa tsaye tayi tare da fad'in, "tabbas a can na yadda dashi gwara na hanzarta naje na duba ko Allah zai saka na dace." Tana fad'ar hakan ta afka d'aki ta shirya sama-sama ta d'auki abinda tasan zata buk'ata na makaranta ta kulle gidan ta shiga gidan Gwaggo.
Mukullin ta baya Gwaggo ta karb'i kud'in mota ta fita a guje dan hankalin ta yana kan littafin, tsayuwa take a kan titi amma shiru babu abin hawa gashi har d'aya tayi tana neman wucewa, kamar tayi kuka haka take ji ga rana ta bud'e sosai tana dukan ta.
Mota ta gani ta faka a kusa da ita aka sauke glass d'in motar yayi mata murmushi tare da fad'in, "Jannat." Kallon sa tayi maimakon ta amsa sai ta tamke fuska tace, "sannu." Neman abin hawa ta cigaba dayi amma shiru babu ta dafe kai tana shirin yin kuka.
"Nasan kina neman wannan ko?." Ya fad'a yana d'ago mata littafin dake hannun sa. Kalla tayi taga littafin da take so bata san lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba tace, "Shine a ina ka ganshi? Dan Allah bani shi nake ta nema." Ganin murmushi ta ya saka shi jin dad'i sosai yace, "ki shigo mu tafi school din lokacin shiga exams d'in ki ya kusa gashi baki samu napep ba."
"A'a nagode ka bani littafin kawai."
"Zakiyi loosing first paper kizo muje na sauke ki."
Bata da yadda zatayi dole ta zaga ta bud'e ta shiga burin ta bai wuce ya bata littafin ba.
Tafiya suka fara ya mik'a mata littafin yace, "jiya kika yarda shi a inda abin nan ya faru d'azu na shiga school d'in naje wucewa ta wajan na ganshi ana shirin saka shi a dustbin shine na karb'a na duba naga sunan ki na tawo da niyar kawo miki gida." Murmushi ta sake yi tace, "nagode sosai ka taimake ni, da banga jotter d'in nan ba da na shiga uku, nagode sosai fa." Murmushi yayi mata yace, "kar ki damu an zama d'aya ai."
Bata sake cewa komai ba suka cigaba da tafiya har suka k'araso cikin makarantar, a kusa da hall d'in yayi parking yana kallon hall d'in yaga har masu tsoron jarabawar d'in har sun raba booklet hankalin ta yayi k'ok'oluwar tashi ta saddakar ta rasa wannan paper sai dai ta gyara next year.
Fitowa daga motar sukayi ya kalle ta yaga har idon ta har ya kawo ruwa duk sai yaji ya damu da hakan hankalin sa ya tashi yace, "kwantar da hankalin ki baza kiyi loosing paper ba." Girgiza masa kai tayi tace, "kana ganin wanda suke ciki kasan ai baza su bari na shiga ba, kalli yadda students suke waje an hana su shiga fa, nasan shikenan sai dai na gyara next year." Ta fad'a hawayen da take rik'ewa suna sakkowa daga idon ta.
Ganin hawaye na zuba a idon ta sai hankalin sa ya kuma tashi yace, "kar ki damu zaki shiga ina zuwa." Yana fad'ar hakan yayi hanyar shiga hall d'in itama kuma ta zauna tana share hawayen ta dan tasan babu ta yadda za'ayi su amince ta shiga.
Bai wani jima sosai ba ya dawo yace, "tashi kije." Mik'ewa tsaye tayi cikin mamaki tace, "sun amince na shiga?."
"Ba ke kad'ai ba duk wanda suka hana shiga ya shiga alfarmar ki, kiyi sauri kar su bada question paper." Ai bata sake cewa komai ba tayi ciki da sauri ko waiwaye bata yi.
Da kallo ya bita yana murmushi har ta shige ya lumshe idon sa ya bud'e, zama yayi inda ta tashi yana jin farin ciki da nishad'i ya cika zuciyar sa.
*☆☆☆*
Da wani irin ciwon ciki Imran ya wayi gari tun yana daurewa har ta kai ta kawo numfashin sa na fita dak'yar kamar wanda yake barazanar barin gangar jikin sa.
Yana kwance plat a k'asa cikin abincin dabbobi yana kallon sama idanun sa sun rune sun koma jajaye sosai sabida bak'ar azabar da yake ciki.
Bud'e k'ofar tare shigowa wajan bai saka ya motsa ba dan in ya motsa ba k'aramin ciwo yake ji ba, a kwance suka hango shi suka k'arasa ciki hannun su d'auke da kofi da kuma k'aramin plate, ajjiye masa sukayi a gefe d'aya daga cikin su yace, "gashi nan abin karin ka ne." Bai kalli abincin ba nema yake yace musu su taimaka masa da maganin ciwon ciki amma ya kasa sai bakin sa da yake rawa.
"Bawan Allah nan bashi da lafiya wallahi." D'aya ya fad'a yana kallon d'an uwan sa. Shima da yake kallon Imran cikin tausayi yace, "to ya zamuyi? A gaban ka na fad'a masa ya fara fad'a wai mu nemo masa magani."
"To haka zamu barshi ya mutu a hannun mu kenan?." Shiru shima yayi kafin yace, "Zauna dashi bari naje na nemo wani likitan yazo ya duba shi." Fita yayi ya bar d'ayan a tsaye a akan Imran yana kallon sa.
Numfashin sane ya fara sama da k'asa hankalin wanda yake tsaye ya tashi ya duk'a ya rik'e Imran d'in yana fad'in, "Sannu, Allah ya baka lafiya." Yana rik'e dashi har wanda ya fita ya dawo shida wani yaro a bayan sa.
"Zo maza ka duba shi dan Allah." Wanda akewa magana bai yi musu ba ya k'arasa inda Imran yake yana kallon yanayin sa, allura yayi masa guda biyu a take sannan ya ajjiye magani akayi dabarar da aka saka masa ruwa sannan ya kalle su yace, "jikin sa fa yayi zafi kamata yayi a kaishi asibiti gaskiya dan ko warin wajan nan dole ya saka masa ciwo."
Numfashi ya D'aya ya fesar sannan yace, "yanzu dai zai samu sauk'i ko?." Kallon Imran yayi da bacci ya d'auke shi yace, "zai samu sauk'i sosai amma in ciwon ya kuma tashi zai yi gaba ne ba baya ba, kaga ban san abinda yake damun sa ba tunda ba'a yi test ba na bashi pain reliever ne kawai." Girgiza kai sukayi cikin gamsuwa suka fita tare dashi gabad'aya aka bar Imran a kwance yana bacci.
Bayan tafiyar wanda ya buda shi suka zauna suna tattaunawa akana lamarin Imran, D'aya daga ciki yace, "nifa Allah sani na gaji da wannan abin, haka kawai an saka mu muna gadin bawan Allah ana cutar dashi kawai sabida kud'i, ka duba yanayin da yake ciki kowa ya ganshi sai ya tausaya masa." Shima d'ayan yace, "wallahi nima haka na gaji, kuma in mutumin ya mutu a hannun mu in maganar taje wajan hukuma wallahi sai an kama mu, Muhsin yana da damar da zaice bashi ne ya saka mu ba koda ya amsa shine mahaifin sa zai saka a fito dashi mu kuwa fa?."
Gigiza kai shima yayi yace, "gaskiya dole ne musan abin yi."
"Ya dai kamata gaskiya." Haka dai suka cigaba da tattauwa suna k'okarin nemowa kansu mafita.
*☆*
Jannat kuwa lokacin da ta fito daga first papper jotter d'in ta ta zauna ta koma gefe tana dubawa duk da hankalin ta ba'a kai yake ba, numfashi ta fesar ta lumshe idon ta fuskar Muhsin ta gilma mata a idon ta tayi saurin bud'e su ta zubawa rubutun dake jotter d'in ido.
"Ko ina zan gashi nayi masa godiya?." Ta fad'a tana d'an kalle-kalle amma bata ganshi ba.
Wasu y'an class d'in sune suka zo wucewa suka tsaya inda take suka ce, "gaskiya y'ar uwa mun gode in badan ke ba da yau bamu yi paper d'in nan ba, mun shiga alfarmar ki munyi jarawaba, Allah ya bar ku tare ya kaimu lokacin bikin ku." Murmushi Jannat tayi kawai tana jin wani banbakwai da suka ambaci lokacin biki.
Suna barin wajan ta cigaba da karatun ta amma zuciyar ta ta addabe ta da tunanin Muhsin maimakon tayi karatu sai ta dinga jiyo muryar sa a kunnen ta, rufe littafin tayi tace, "oh god." Ta fad'a tana dafe kanta kafin ta kuma bud'e jotter ta cigaba da dubawa.
Kiran sallar da akayi ya saka ta ta mik'e ta k'arasa inda wajan alwala yake tayi alwala ta yi hanyar masallaci, bayan ta idar ta sake samun waje kusa da hall d'in da zasuyi exmas d'in ta zauna tana cigaba da karatun ta har lokacin da zata sake shiga jarabawa ta mik'e ta shiga.
Sai bayan awa da rabi sannan Jannat ta fito daga d'akin jarabawar tana kallon agogon hannun ta, k'arfe biyar da rabi na yamma ta furzar da iska ta nufi hanyar da zata sada ta da gate d'in fita.
Gab zata fita daga cikin makarantar tana tafiya tsakanin motocin da suke ajjiye taji an furta, "Jannaty." Cak ta tsaya gaban ta yayi mummunan fad'uwa ta zaro ido waje jikin ta ya fara rawa lokaci d'aya, Da sauri ta juya ta kalli inda taji maganar idon ta bud'e cikin mamaki.
Sak ta tsaya tana kallon sa ta kasa rufe bakin ta haka idon ta a bud'e alamun mamaki da al'ajabi, hannu ya d'aga mata almun hiii amma yaga kamar hankalin ta baya jikin ta hakan ya saka shi tafa hannayen sa yace, "Hello Jannaty." Firgigit ta dawo hankalin ta da nutsuwar ta tayi k'okarin daidaita kanta ta sunkuyar da kanta k'asa tana raba ido.
"Are you okay?." Ya fad'a yana lek'a fuskar ta da ta sunkuyar, girgiza kai tayi alamun eh kana ta d'ago idanun ta ta kalle shi tace, "I'm okay, nagode da abinda kayi min d'azu Allah ya saka da alkhairi." Murmushi yayi mata mai kyau sannan tace, "Amin Jannaty, kar ki damu an zama d'aya ai dani dake, yamma tana yi zo muje na sauke ki a gida."
Girgiza kai tayi tace, "A'a ka barshi nagode zan samu abin hawa yanzu." Ta fad'a da niyar barin wajan, caraf ya rik'o hannun ta tayi saurin juyowa ta kalle shi bai saki hannun ba yace, "Yayan ki baya so ki dinga hawa napep meyasa baza ki bi maganar sa ba duk da baya nan.?"
Wani irin yarrrr taji a jikin ta tsigar jikin ta ta tashi, tunda take a duniya bayan Imran babu namijin da ya tab'a rik'e mata sai shi hakan ya saka taji wani iri a jikin ta, Da sauri ta juyo ta kalle shi tare da kallon hannun hakan ya saka shi saurin saki yace, "I'm sorry, amma please kizo muje na ajjiye ki." Ita mamaki ma yake bata tana tunanin ya akayi yasan da Yayan ta baya so ya ganta a napep? Ya akayi kuma yasan gidan su? Ya akayi kuma yasan suna Jannaty wanda Imran ne kad'ai yake fad'a mata shi.?
Ganin mamaki take ya saka shi yin murmushi yace, "kizo muje yamma na sake yi magariba na tawowa." Girgiza kai ta kuma yi tace, "ka barshi nagode."
"Dan Allah kizo muje." Zatayi magana yace, "Allah nace."
Ajiyar zuciya tayi yayi gaba tabi bayan sa suka isa inda motar take ya shiga itama ta shiga gaban motar ya kunna ya ja suka fita daga makarantar, "Jannaty!." Sai da ta firgita tayi saurin kallon sa kafin tayi magana ya riga ta yace, "yi hak'uri na tsorata ki."
"Dan Allah ka daina kira na da wannan sunan."
"Meyasa?."
"Sabida mutum d'aya ne yake fad'a min wannan sunan."
"Yayan ki ko?."
D'aga kai tayi alamun eh idon ta ya fara cikowa da kwallah.
"I'm sorry ki daina kuka ina so ne na maye miki gurbin Yayan naki da kika rasa." Kallon sa ta sake yi hawaye ya sakko daga idon ta tace, "ya akayi ka sani? Yama akayi kasan gidan mu? Sannan ka san Yaya na baya so na hau keke napep?." Murmushi yayi ya kalle ta kafin ya d'auke kai ya mayar kan titi yace, "wannan ba wani abu mai wahala bane ba ai Jannaty." Runtse idon ta tayi tace, "dan Allah ka bar kira na da wannan sunan dan Allah. "
"Shikenan na daina kiyi hak'uri." Hawayen idon ta ta share tace, "baka bani amsar tambaya ta ba."
"A lokacin baya na nemo bayanai a kanki ne keda yayan ki domin na d'auki fansar abinda Yayan ki yayi min dake kanki, a cikin wannan binciken ne na samu labarin b'atan sa da kuma tashin hankalin da kika shiga har ta kaiki ga fad'uwa a jarabawa kike maimaita ajin baya a halin yanzu, na tausaya miki sosai na jiki ki a jikina kamar y'ar uwa ta wacce miki ciki d'aya daga lokacin nake so na zama abokin ki ko nace yayan ki domin na d'ebe miki kewar da take damun ki, Jannat ban shiga rayuwar ki da wata manufa ba sai da alkhairi dan gani nayi in baki samu wanda zai d'auke miki kewa kamar yayan ki ba rayuwar ki da kuma karatun ki yana cikin had'ari, kinji dalilin da ya saka na sanki na da kuma gidan ku da duk abinda yayan ki yake so a kanki da wanda baya so."
Kafin ya gama maganar kuka yaci k'arfin ta sosai sai saurin sa da yake fita a hankali, gefen titi ya gangara yayi parking ya kalle ta cikin yanayin damuwa da tashin hankali yace, "dan Allah Jannat ki daina wannan kukan yana tab'a min zuciya, in laifi ne shiga rayuwar ki da nayi kiyi hak'uri banyi da wata manufa ba sai da niyar taimakon ki da kuma Yayan ki dan Allah ki daina kuka badan ni ba."
Bata daina ba sai dai ta rage sautin kukan ba kuma tace komai ba, tissue ya fara ya mik'a mata yace, "ki share hawayen ki dan Allah wallahi bana so naji kina wannan kukan zuciya ta zafi take min." D'ago jiqaqqun idanun ta tayi ta kalle shi ta d'an kulle su ta bud'e. Saurin d'auke idon sa yayi domin ji yayi wani abu yana sokar sa a jikin sa dalilin da ya sanya shi janye idon sa kenan.
Hannu ta mik'a ta karb'i tissue d'in ta goge idon ta bata ce komai ba yace, "Jannat dan Allah kiyi hak'uri da dukkan abinda ya faru a baya ki yafe min dan Allah." Bata ce komai ba sai ya girgiza kai yace, "Nasan abu mai wahala ne ki amince da ki yafe min domin nayi miki abubuwa da dama, ki rama marin da nayi miki a baya indai hakan zai saka ki yafe min." Ya fad'a cikin sigar tausayi kamar zaiyi kuka yana kallon ta.
Girgiza masa kai tayi tace, "ka daina wannan maganar ni komai ya wuce a waje na, kayi min taimako a jiya wanda in ba dan kazo ba da yanzu ba wannan maganar ake ba, sannan ka kuma taimako na har sau biyu wanda in badan kazo d'in ba da na shiga wata matsalar, dan haka komai ya wuce a waje na alfarmar taimakon ka a gare ni."
Murmushi yayi mai kyau yana kallon ta yace, "nagode sosai Jannat in sha Allah kuma zanyi k'okarin maye miki gurbin yayan ki da kika rasa kafin Allah ya bayyana shi, nayi miki alqawari zan zama kamar Yayan ki Imran zan kuma yi k'okari wajan ganin an ganshi kodan farin cikin ki."
Murmushi tayi kad'an tace, "nagode sosai, amma bana buk'atar kace zaka maye gurbin Yaya na domin kuwa a kaf duniyar nan babu wanda ya isa ya maye min gurbin sa har abada, zan d'auke ka kamar Yaya kamar yadda kace amma zancen maye gurbi babu shi dan bana tunanin Allah ya halicci wani a duniya da zai iya maye min gurbin yaya na, kayi hak'uri" ta Fad'a tana juyowa ta kalke shi.
"Babu komai Jannat indai zaki bani damar zama yayan ki ni yafi min komai a dad'i, nagode miki sosai kuma zanyi k'okarin wajan ganin na kokarta na baki farin cikin da kika rasa." Murmushi tayi masa kad'an tace, "nagode."
"Kin bani damar hakan?."
D'aga masa kai tayi alamun eh, jingina yayi a jiki kujera ya sauke ajiyar zuciya yace, "nagode sosai Jannaty, kuma nayi miki alqawarin samun dukkanin farin cikin da kike nema." Kallon sa tayi tace, "bana son kana kira na da sunan nan." Had'e hannayen sa yayi yace, "I'm sorry, murnar kin yadda ce ta saka ni na manta da komai, tsabar murna ji nake kamar na taka rawa."
Murmushi tayi bata ce komai ba ganin hakan ya saka shi yace, "na iya rawa sosai dan in na fara rawa sai ki d'auka jarumin india, sai da kiga ina rangwad'a kamar haka." Ya fad'a yana fara rawa da hannu yana kuma kad'a kansa kamar d'an india, Dariyar da ta jima batayi ba ta kama ta ai kuwa ta shiga darawa sosai kamar ba ita ba.
Tsayawa yayi cak yana kallon ta har tsagaita dariya ta kalle shi bata ce komai ba shima kuma ita yake kallo.
"Tsarki ya tabbata ga Allah subahanahu wata'ala da ya halicci wannan kyakykyawar sura, k'anwa ta hak'ika Allah ya halicci kyau a tare dake, dan Allah a dinga b'oye dariyar nan kar a yiwa wani dan zai iya zaucewa." Ya fad'a mata cikin murya mai taushi yana jifan ta da wani mislikin murmushi da ya kashe mata jiki.
Murmushi ta kuma yi tace, "ka bani dariya ne sosai rabon da nayi wannan dariyar har na manta, nagode sosai ka sani nishad'i a yau d'in nan." Murmushi yayi ya dafe k'irjin sa yace, "Allah nagode maka da ka bani ikon saka k'anwa ta nishad'i da farin ciki."
Bata ce komai ba amma har lokacin murmushi na kan fuskar ta kanta a sunkuye, bayan ta ya kalla daga keyar ta zuwa wuyan ta yaga kwantattun gashi k'ananu a kwance a wajan sun bi chocolate kalar ta, samun kansa yayi da jin wani irin yanayi wanda bai tab'a jin irin saba hakan ya saka shi d'auke idon sa ya dawo dashi ga fuskar ta yace, "Jaana ana tab'a fad'a miki kina da kyau kuwa?."
D'ago idon ta tayi ta d'an kifta su ta bud'e tace, "ba'a tab'a ba." Zaro idanu yayi yace, "kina so kice ko Yayan ki Imran bai tab'a cewa kina da kyau ba?."
Bata bashi amsa ba hakan ya saka cigaba da fad'in, "Jaanaa kina da kyau wanda ake kira kyau, kece kyau domin shi kansa kyau d'in ya ganki dole ya tsaya kallon kyau a tare dake, kyaun ki shine asalin kyau daga rabbil samawati, kyaun ki shine natural kyau ba mix, kyaun ki shine kyauwun da yake saka mutum ya zauce da zarar yayi tozali dake tabbas zai ga kyau, Jaana ki dinga godewa Allah ya gama miki komai na duniya sai dai fatan ki gama da duniyar lafiya."
Sak tayi tana sauraron sa har ya kai k'arshe ta lumshe ido tana jin dad'i a zuciyar sa da gangar jikin ta, tunda take a duniya ba'a tab'a yabon ta kamar yau ba, Yaya ta yana cewa tana da kyau amma ba kamar yadda Muhsin ya zayyane mata cikin kalamai masu dad'i ba, Samun kanta tayi da jin alfahari a kan hakan ta kalle shi tace, "nagode da yabon ka gare ni kum......." k'arar wayar ta ya hana ta k'arasawa ta d'auko ta a jaka ganin sunan Abba gaban ta ya fad'i ta kalli agogo taga har bakwai tayi a firgice ta kalle shi tace,
"Na shiga uku ashe dare yayi haka? Muje ka kaini gida dan Allah kaga har Abba ya fara kira na."
"Kwantar da hankalin ki Jaana babu abinda zai faru bara muje gidan."
Tafiya suke a hankali duk tsoro ya kamata har suka k'arasa k'ofar gidan su, suna shiga layin aka kawo wutar nefa ta hango Abba a zaune akan dakalin k'ofar gidan yana kallon duk wanda zai shigo layin.
Dafe k'irji tayi ta furta, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, na shiga uku." Kallon ta yayi ganin duk ta firgice yace, "menene?."
Da hannu ta nuna masa tace, "Abba."