DAMUWATA

11

by @mrsjmoon


Page 11.


"Kiyi hak'uri Deejah amma mahaifinki ya cika fad'a, wallahi tsoro ya bani ganin yarda ya shigo a fusace sannan d'azun da safe na sunkuya ina gaisheshi amma ko kallo ban isheshi ba, na yarda wannan halayyan nashi ya sanya baku jituwa."


"Sister Beebah halayyan Baba halitta ce dan koni ada tsoronsa na ke ji amma tunda na fahimci haka Allah yayoshi sai na saba kamar yarda Aminiyata ya bi jikinta."


"Uhm ku mumaida hankali a kan aikinmu kunsan kowa abin da tafi so za'a dafa mata." 


Na datse zancen saboda yarda na ke jin b'acin rai kuma ban son su gano hakan.


"Hakan ba zai yiwuba kawai muyi musu girki d'aya wanda zasuci baki d'ayansu."


"Nima hakan naga yafi Sister."


"Ki tafi ku huta insha Allah kafin su iso na kammala komi." 


Na kuma ambata cikin tsare gira.


"Baza'ayi haka ba Fanta tafi ki d'ebo komi a gida kizo ayi amfani da shi."


"Idan ta d'ebo kada tazo dashi gidan nan, insha Allah bazamu rasa abin yin amfani ba duk da muna talakawa."


"Ya Salam, please Deejah ki fahimce ni mana."


"Beebah dan Allah kiyi shiru muyi abinda ya kamata dan banjin ina da natsuwar fahintarki ba."


"Tam na yi shiru Aunty."


"Ko ba Aunty ba."


Dariya suka kyalkyale da shi ganin yarda na tsuke fuska.


"Fushin baiyi miki kyau ba Aminiyata."


Murmusawa na yi.


"Yawwa ko ke fa sai annuri na kuma cika kyak-kyawar fuskanki."


"Ban da zagi fa Aminiyata."


"Allah ba zancen zagi domin ke kanki kinsan mai kyauce tamkar tauraruwa cikin dubbab taurari."


"Kinyi na kud'in ki wallahi."


"Ai gaskiya Fanta ke fad'a ke d'in tubarkallah masha Allah, tamkar 'yar buzaye ko Shuwa Arab."


"Eh wallahi Sister Beebah."


"Dan Allah ku barmin kunnuwa su huta."


"Ank'i sai kin sanar da mu nasabanki daga wani yare kika fito."


"Yaren Baba mana Hausa Fulani."


"Amma kinsan Allah ko a farce baki kama da Baba haka 'yan uwanki duk kinfisu kyau duk da suma da farare cikinsu amma naki hasken na dabanne."


"To ni bakuga yarda Mama ke da haske ba, ita na d'auko."


"Eh gaskiya hasken Mama kikayo aminiyata amma duk da haka kinfita fari."


"Eh nafita kam amma ai munyi kama."


Karkacewa Fanta ta yi tana k'aremin kallo na kai mata duka ta ja baya cikin cewa "Kuna kama a halittan idanunku da kyawun diri amma in banda nan ban hango ta inda kukayi kama ba."


"Kai Fanta ki duba dai da kyau hatta madai-daicin bak'insu iri d'aya ne."


"Kai Beebah a she haka kika k'arewa Mama kallo?"


"No a photonku na tantance."


Banza na yi da su ganin in na biye musu ba zamuyi abinda ke gabanmu ba.


Bintu Alale, Firdausi jelop d'in macaroni jelop sai Safina shinkafa da miya. Komi dai-dai mukayi yarda bazai zamo anyi albazaranci ba. Mun jere abincin a d'akina muka zauna muna hira Fanta ta kalli Beebah ta langab'e kai.


"Me ye malama?"


"Dan Allah Sister idan ya iso ki kulashi kinga domin ke zaizo"


"Wai Yaya Abdallah zai kawo su?"


"Eh."


Dogon tsaki Beebah ta ja tare da mik'ewa zata fice.


"Kada ki yi haka sabida ance bak'onka Annabinka."


"Fanta wallahi inda na san munafuncin da kuka k'ulla kenan tabbas da bazan jirasu ba zan wuce amma ko yanzu ba zaku sami abinda kuke so ba na rantse."


"Eh mun yarda amma dan Allah ki kulashi cikin walwala in ya wuce sai kiyi mana duk masifar da kika so."


Shiru ta yi, Fanta ta janyo hannunta ta zaunar gefen katifa tana yi mata magana a kunni, tagumi ta zabga na yi gyaran murya ta kalleni na girgiza mata kai, murmushi ta saukemin wanda a fili na dole ne saboda hakan ya bayya a saman fuskanta.


"Me ke faruwa, kuke 'yan b'oye-b'oye?"


Na cillowa Fanta tambayar duk da shiga lamarin rayuwar mutane ba halina ba ne.


"Gata nan kiyi mata nasiha ta daina wulak'anta mana Yaya, saboda shi tak'i bin su Bintu sada zumunta shi ne ya biyosu domin ya ganta dan ta yanke alak'a dashi tsawon wasu watanni, ta daina d'aukan wayarsa tayi blocking nasa a k'arshema ta saka shi a black list, in kuma ya kirata da wayar Mamansa ko k'anninsa tana jin muryansa zata kashe wayarta baki d'aya."


"Innalillahi, me ya yi zafi haka?"


"Wai bazata auri mai mata ba saboda tana tsoron jarabar matarsa mai hali irin na Aunty Nafisa sak."


Wani zabura Beebah ta yi tayo kan Fanta, ita kam ta kwasa da gudu ta fice zata rufa mata baya na rik'eta cikin tsare gira na ce "Ke kin gujewa auren tashin hankali amma ni kin dage sai na yi?"


Numfashi ta yi ta saukewa cikin alamun fushi, zuwa can ta yi gyaran murya sai lokacin na saki hannunta dana kama. Ruwa ta d'auka ta sha sosai sannan ta k'ara yin gyaran murya ta soma magana cikin natsuwa.


"Duk abinda Fanta ta sanar miki gaskiya ne illa abu d'aya shi ne da ta ce halin Mas'uda d'aya da na Aunty Nafisa, sam halinsu ya sha bamban saboda Aunty Nafisa bata tsafi haka tana shakkar Uncle Muhseen sakamakon da ita Mas'uda mijinta bai isa da ita ba hatta da mahaifiyarsa sai taso yake zuwa gaisar da ita, k'anninsa kuwa ta haramta musu zuwa gidanta, tun abin na damunsu har yanzu ya daina. Shin ta ya ina kallon wannan lamari zan amince na zama matar shige wacce bata tab'a yin daraja."


"A gaskiya Mas'uda bata da hali amma duk da haka ina ganin aurensa zai baki damar kwatosa daga halaka, domin zaki nusar da shi hakkin uwa kan d'iyoyinta, kiga kenan tamkar kinyi jihadi ne."


"Ada naji zan iya yin hakan amma tunda na had'u da burin zuciyata duk da shima tamkar son maso wani na keyi masa wanda masu iya magana kan kirasa da k'oshin wahala, naji gara in hak'ura da shi na kama na gasken a haka nan."


"Son maso wani bana gaske ba ne Sister, kidai yi hak'uri ki kama Yaya Abdallah please."


"Ko mu biyu muka rage a duniya ba zan aureshi ba."


"Me ya yi zafi?"


Banza ta yi da ni na rik'o hannunta "Beebah walalhi Abdallah ya bani tausayi yana cikin matsalar rayuwa gashi kin kasa fahimtarsa."


"Shi kuma baisan da yana cikinta ba domin duk wanda ya nusar da shi illar rayuwar da a keyi a gidansa sai ya k'ulla gaba da shi nima dan na nuna masa illar watsi da goggo da ya keyi shi ne ya soma zagina tamkar ya sami d'iyarsa har da cewa bashi bani shi ne na nuna masa nid'in 'yar halas ce na datse dik wani hanya da zai sadani da shi domin na fahimci gani yake bazan iya rabuwa da shi ba saboda kud'insa tare da kyawun da Allah ya bashi sai dai ya makaro domin ni una sonshi ne domin Allah badan wani abu nasa da Allah ya yi masa baiwar samu ba kuma kinji na rantse wallahi har ya koma ba zaiga dariyana ba, zai san ya zageni, zai san ya kirani da wawiya, banza, wofi mara tunani."


Innalillahi wa Inna ilaihin, a gaskiya Yaya Abdallah bai kyauta ba, zagi na zubda mutunci duk kuwa yarda kake d'aukan mutum."


"Ai kam ya zubar masa a idanuna, zubewa na har abada."


"Please Beebah ki sassauta hukuncin da kikayi masa, ki tarbesa in yaso da ya tafi ki watsar da shi."


"Ai na rantse kuma bazanyi kaffara ba, walalhi zai san ni 'yar hakas ce gaba da bayana."


"To Allah ya kyauta, abin ya girmama."


"Amin."


Shiru mukayi zuwa can na ce "Tashi kiyi wanka tunda kin koramin Aminiya, idan kin fito sai inyi."


"Na fasa."


"Duk saboda jin Ab...


"Deejah dan girman Allah kibar zuciyata ta sami natsuwa da kiramin sunar mara hankalin nan."


"Na shiga uku ni Nana Khadijatu."


"Ki tafi kiyi wankanki."


"Ok bari na fita na samo musu drinks saboda ba abasu Zobo da kunun Aya kawai ba tunda gasu tafe da babban bak'o."


Harara ta zabgomin na murmusa tare da ficewa.


"Walalhi sai na ciwa su Safina mutunci musanman Bintu dan nasan itace uwar kaud'in ingizashi ya zo."


"Ba ita bace sister Beebah, goggo ce da kanta ta ce ya dawo dasu kuma shi ba danke zaizo ba ni ce na ambaci hakan amma dan Allah kiyi hak'uri bansan haka ranki zai b'aci ba."


"Bakomi Fanta ya wuce." 


Ta ambata cikin sakin fuska tamkar ba ita ce ta murtukesa ba.


Murmushi suka sakarwa juna. Tafi na soma daga bakin k'ofa sannan na shigo muka had'a ido da Fanta na kanne mata ido d'aya ta yomin jinjina da babban yatsarta amma a wayance gudun kada Beebah ta harbo jirgin domin plan muka had'a dan ta sakewa Abdallah fuska. 


"Kin san Allah Deejah sister Beebah tana da gaskiya dan Yaya Abdallah mijin ta ce ne na gaske, hatta da unguwa in zaije idan matarsa bata gamsu ba fasawa yakeyi wai baya son barinta cikin tunanin inda ya je."


"Ikon Allah amma kam ta sami miji mai gaskiya."


"Uhm na banza da wofi ba tunda na b'atawa mahaifiyarsa raina akanta."


"Kuyi masa addu'a wata rana sai labari."


"Idan sister Beebah ta amincewa aurensa ba."


"Ba sai Beebah ce zata saitashi ba ko matarsa zata iya nusar da shi illar b'atawa iyaye rai."


"Banjin hakan zai faru ba tunda akanta komi ke faruwa, ita ce silar faruwar komi dan ance tunda ya soma neman aurenta halayyansa na kirki suka sanja zuwa na tsiya."


"To Allah ya shiryata."


"Amin, shi yasa na ke ya bawa Uncle wallahi domin shi jajirtacce ne domin duk son da ya keyiwa Aunty Nafisa tana sab'awa umurninsa zai hukuntata musanman da yanzu sister Beebah ta kuma d'orashi akan hanyar saita mata tunani wanda muke fatar halin rashin kirkinta ya zamo tarihi."


"Ku ne kuka ambata masa ya nemi aurena kenan? Shin kuna tunanin tahanyar yi mata kishiya ce zai dawo da ita hanyar gaskiya?"


"A'a shi da kansa ya ambata yana sonki wanda najima da fahimtar d'abi'unki na burgesa bai furta miki kalman k'auna ba ce sai yanzu, kinsan komi lokaci ne. Sannan Aunty Nafisa kuwa muna fatar ta dalilin zama dake ya saka ta yi koyi da halinki nagari ta dawo mai kyakkyawar mu'amala da kowa musanman mu jininta."


Shiru na yi na kasa sake cewa komi saboda yarda nake jin fad'uwar gaba.


Gyaran muryan Beebah ya sanya muka gane ta fito wanka, da sauri Fanta ta shige toilet dan gabatar da wankan itama.


"Insha Allah tsoron da ke ranki zai zamo tarihi sabida muna kanyi miki addu'ar samun rayuwa mai inganci a gidan Uncle."


"Ke da su wa?"


"Mama da Sisters d'ina."


"Shin da gaske su Bintu sun san da maganar nan?"


"Eh dan aminiyarki ta fesa musu kuma sunyi na'am da lamarin saboda zamansu da ke na kwanaki biyu sun fahimci bakya da matsala zaki iya hak'uri da halayyan 'yar uwanmu."


"Uhm har yanzu kuna kan bani mamaki wai ace kuna 'yan uwar Aunty Nafisa na jini amma kuna murnan da ayi mata kishiya."


"Ke ba kishiya ba ce Deejah, abokiyar zamace tagari mai tarin nagarta wanda muka tabbatar bazata iya bin hanyar banza ba dan ta cutar da 'yar uwanmu sabida kina aiki da iliminki kuma kin gama samun tarbiyya daga uwa ta gari wato Mama."


"Nagode da wannan yabawan, insha Allah zan nemi zab'in Allah cikin shi da Aliyu, duk wanda ya zab'amin zan amshesa da hannu biyu tare da mik'a godiya gareshi."


"Uwata neman zab'inki ya kasance na kan kowa da kowa ne ma'ana ki nemi zab'in Allah akan duk inda mijinki yake yazo gareki bisa amincinsa idan kuma yazo to ki amshesa da hannu biyun da kika ambata domin yanzu bana goyon bayan Alhaji Muhseen ko Aliyu saboda zab'in Allah shine sama da komi haka yardansa babban alkhairi ne ga rayuwar bayinsa dan haka ked'in alluran cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka, ina fatar managarci, jajirtacce, mai tsoron Allah S.W.A da son Manzon Allah S.A.W zai d'aukeki ku rayu cikin inuwar aure na har abada."


"Amin ya rabbi Mama." 


Beebah ta ambata cikin rawar murya saboda kalaman Mama sun shigeta ainun, ita dai zuwarta garin Kaduna tana ta samun natsuwar ruhi ta kalaman Mama masu cike da fikra.


Ni kam zubewa na yi gaban k'afafun Mama ina jan numfashi. Kamo ni ta yi ta rungume tana bubbuga bayana.


"Habibatu aramin ita muje unguwa, inaga sai bayan isha'i zamu dawo sai ku kula da gidan."


"Tam Mama kudawo lafiya."


"Allah ya so hakan."


"Amin."


Daga haka muka fice Mama na rungume da ni, a d'akinta na yi wanka na shirya.


"Uwata gidan Baba Umaru zamu saboda lamarin Malam yasoma bani tsoro kada wata rana ya kasheni ya maidake marainiya ya mallake dukiyar da ke zalama akan shi."


"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, Mama me ya kawo wannan magan-ganun? Dan Allah kidaina ambatarsu dan suna sanyamin shakku."


"Shakkun me ne Uwata?"


Shiru na yi ganin haka sai ta ja kunnina da k'arfi na sanya k'ara ta kuma mud'ewa rik'e hannunta na yi cikin cewa "Shakkun ganin kamar ni ba d'iyar Ba...


"Nana Khadijatu!!."


Kiran sunana da Mama ta yi da k'arfi ya sanya ni yin dif da maganar ina girgiza kai.


"Wuce muje kuma kada na sake jin wannan banzan kalamin ya kuna fitowa a bakinki.'


"Kiyi hak'uri Mamana."


"Na yi, wuce muje magriba na kawo jiki."


Tafe muke a cikin Napep ina nazarin yanayin Mama, na hango tana tare da damuwa amma tana k'ok'arin b'oyemin sai na samu kaina da jin b'acin rai abinda na ke korerarsa kullum yana neman samun muhallin zama a ruhina wato tsanar Baba domin na tabbata shi ne silar faruwar b'acin ran Mama ta dalilin shigowarsa d'azun. Sadda muka isa gidan Baba Umaru suna gabatar da sallar magrib muma alwalla mukayi muka gabatar inda bamu tashi ba muka cigaba da azkar zuwa lokacin sallar isha'i domin tarbiyyan zuri'ar Baba Umaru idan anyi sallar magrib ba'a tashi sai an sallaci isha'i sai bisa babban dalili, hatta da yara k'anana 'yan shekaru Tara zuwa sama sun san da d'abi'an, 'yan k'asa da sune kawai zakaji karad'insu suma da zarar Baba Umaru ya shigo zasu natsu saboda baison hayaniya sam amma fa ya iya jan jikokinsa da sawa kamar yarda yakeyimin.


"Jikalle kuma takwarata kin b'uya ko kuma ince Hurera ta b'oyeki, sam bata bari kiyi zumunci da mu."


"Ayi hak'uri Hajiya Inna, ai gani yau nazo a gadonkima zan kwana."


"Kamar gaske."


Murmushi na saki ina kallo idanun Mama da itama ke doka murmushin.


Surikan gidan ne sukayi ta shigowa d'akin Hajiya Inna suna gaisar da Mama ni kuma ina gaisar dasu cike da kunya saboda yarda suke ta k'orafin na daina zuwa gaishesu.


"Zata rik'a zuwa duk ranar Juma'a insha Allah." 


Mama ta ambata cikin 'yar dariya.


"To Allah ya nufa hakan." 


Hajiya Inna ta amsa.


"Amin." 


Suka amsa tare da ficewa.


"Taho muje mu gaisa da Baba naji shigowarsa."


Mama ta ambata cikin tashi tsaye.


"To."


"Hurera abi komi a hankali banda gareje kinji?"


"To Inna."


"Alhaji ya soma sanarmin da lamarin, ina ta yaki addu'ar Allah ya rayaki ku jima da Nana Khadijatu."


"Amin ya rabbi Inna."


"Sannan kiyi tunani akan zuwa wurin danginki domin shekara ashirin da d'aya ba kwanaki ashirin da d'aya ba ce."


"Insha Allah Inna zanje domin har da maganar nazo sanarwa Baba amma sai na soma zuwa Kwara naga zuri'ar Baba Abdul Ganiyu."


"Masha Allah Allah ya ida nufi."


"Amin."


Ina tsaye ina saurarensu farin ciki ya gama cikani jin zamuje wurin dangin Mamana abin da najima ina mafarkin zuwan lokacin.


"Uhm inda rai da rabo."


"Tabbas haka nr Uwata." 


Kallon Mama na yi a she zancen zuccin da na yi ya fito fili.


"Idan kin gaisar da Baba ki fita in mungama zan kiraki."


Ta sanarmin daf da zamu shiga falon Baba Umaru.


"To Mama."


Da sallama muka shiga falon dattijon ya amsa mana tare da cillomin tsokana irin ta jika da Kaka.


"Matar b'oye yau ta bayyana to ki koma bana yi dan ban rasa mai neman ladar ba, gasunan buhu-buhu sai wanda naga damar ansawa gaisuwa tare da sakawa aiki."


Dariya na sanya saboda yarda yake maganar cikin zare idanu cike da barkwanci.


"Alhamdulillah yau na saka mai fuskan shanu dariya."


Nan ma wani dariya na kuma sanyawa cikin kulle bakina, hatta da Mama dariyar ta ke yi. Bayan mun gaisheshi na fito na bar Mama zaune gabansa cike da ladabi.


D'akin Hajiya Inna na dawo muka soma hira cikin maida zancen halayyan Baba wanda na fahimci na b'ata mata rai ainun. K'aran wayata ya katse mana hiran ganin Aliyu ne sai na kalleta ta sakarmin murmushi tare da mik'ewa ta fice tana cewa "Takwarata ba dai kunya ba to na bar miki d'akin, a ci soyayya lafiya."


sunkuyar da kai na yi, ina jin ta fice na gyara zama tare da d'aukan wayar wanda kiransa na biyu kenan, yi masa sallama na yi cikin laushin murya fiye da wanda Allah ya horemin.


*Affuwan 'yan uwa l ina cikin uziri ne shi yasa jiya kuka jini shiru.*


*TALLA.*


*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*


Sabulu (molato and black soap)

Scrub

Face cream

Oil

Body lotion

Shower gel

Kulachan

Humra (White and black)

Turaren tsugunon

Turaren kaya

Turaren wuta na d'aki

Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)


*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in *** ko ***. Sai munjiku.*