16
by @mrsjmoon
"Muyi hak'uri dai Fanta kuka baya maganin damuwa sai ma k'ara wa, ki tuna abinda kika sanarmin yanzu, shin me yasa zaki maida hannun agogo baya?"
"Mama Deejah ce kwance kamar gawa? Jiya fa muna tare lafiya lau, shi ne abin da ya bijiromin na kasa daurewa."
"To ya zamuyi da k'addarar Allah? Sai hak'uri kawai tare da mik'a lamarin garesa domin samun d'aukinsa ba dan iyawarmu ba."
"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un."
Fanta ta ambata tare da sake k'amk'ame Mama, lamarin da yaso karyamata zuciya amma sai ta soma addu'a cikin fitar sauti a hankali.
"To zaki wuce gida kuwa in har kuka zakizo kina sanya mutane."
"Uncle na kasa daurewa ne."
"Ki cigaba da ambatar addu'ar da kika sanarwa da Mama har ta sami jarumta."
Motsa kai ta yi tare da janye jikinta ta koma gefen Deejah ta wurin kanta ta zauna bakinta na motsi alamun addu'ar ta ke yi hannunta na yawo saman sumar Deejah.
***
"Yaya ka kwatantamin gidansu sai inje na dubo maka ita."
"K'anwata kinfi kowa sanin tsaron Hajiya."
"Zance mata zani gidan Aunty Zainab ce."
"Tsakanin gidan su Deejah da gidan Zainab da tazara mai nisa kafin kije ki dawo na tabbata Hajiya zata kira taji idan kinje kuma in kika soma zuwa gidan Zainab kina fita zata kira Hajiya ta sanar mata da kin fito kinga kenan lamarin ba mai sauki ba ne."
"Yaya yanzu ya za'ayi?"
"Bari ruwan ya kare sai in lallab'a na tafi da kaina."
"Bazaka iya ba Yaya, jikinka bai warke ba, kallifa yarda kake magana kana hutawa."
"Buguwar da na yi a hakarkari na ne keyimin zafi amma banjin ciwon komi bayan shi."
"Ka dai samo wani dibaran domin kaima na tabbata Hajiya baza ta barka ka fita a haka ba."
"Bari in sake kiran K'awarta ko zanyi dacen ta d'auka tunda ita nata wayar a kashe ya ke."
"Ok jaraba mugani "
Cikin jan tsaki ya jefar da wayar gefe.
"Bata dauka ba ko?"
"Ina cikin damuwa wallahi, narasa wanda zan kira na sami labarin Khadija."
"Mijin Aunty Zainab mana tunda kace, ka ganinsu tare."
"Kuma hakan ya kamata, nagode k'anwata."
Kiran number ya yi aka d'auka bayan gaisuwa sai ya rasa abinda zaice masa.
"Ya dai Aliyu?"
"Yallab'ai dama zance ya wurin su d'iyarka?"
"Oh Khadija?"
"Eh."
"Wallahi yanzu Baba ke sanarmin Mamanta bata da lafiya tana Asibiti."
"Ya rabbi, shiya ban samun wayarta kenan?"
"Eh zaiyiwu hakan ne."
"Allah yabata lafiya."
"Amin."
"Wani Asibiti ne?"
"Ban sani ba dan nima yanzu zan tafi na d'auki Baba mu tafi amma in na isa zan kiraka."
"To nahode."
Ok bakomi."
Sauke wayar ya yi tare da lumshe ido.
"Itama bata da lafiya ne ?"
"Mamanta ne a ka kwantar."
"Ayya Allah ya sa kaffara ce."
"Amin."
"Amma Yaya kana son janyowa kanka ruwa fa."
"Kinga kada ki sake maganar sokuwar nan ya hadamu."
"To ai bance komi ba "
"Gara dai haka."
"Salma fito hakanan ki barsa ya huta."
"To Hajiya."
Gyad'a mata kai ya yi ta fice tana murmushi.
***
Habibu ya cika fam da takaicin Baba akan zagin dake da durawa Uncle duk kuwa da bai sanshi ba amma ji yake tamkar d'an uwansa ake zagi ga shi Baba Umaru na ji amma bai ce kanzil ba hasalima wani littafin addu'o'i ya bud'e yana bita. Zuwa can Habibu ya ce "Haba Malam Hadi kana Malami amma ake jin wannan ashariyar abakinka dan kawai makwafci ya nuna kulawa ga iyalinka abinda na yi imani kai bazaka iya yimusu ba."
"Kai Habibu ban son rashin ta ido kaji ko? Shin kasan muhinmancin iyali kuwa?"
"A'a sai ka koyar da ni irin yarda ka san naka."
"Akul Habibu, kada na kuma jin bakinka."
"To Baba."
"Baba wallahi mutumin nan ya rainani, dan Allah kayi masa iyaka da iyalina, kwata-kwata ban son su sake mu'amala da shi domin ina jin ana maganar arzikinsa bana halas ba ce wata kilama so ya ke ya shanyemin jininsu, ya kaini ya baro."
"A'uzubillahi! Me ya kawo wannan maganar kuma Hadi?"
"Baba wallahi lamarin ne ya kasa kwantamin dubi da yarda yake kashewa Uwani kud'i duba fa ka ga wayar dubbunnan kud'ad'e da ya mallaka mata tamkar bai san zafin nemansu ba."
Mik'a hannu Baba Umaru ya yi ya amsa wayar ya jefa a aljihu batare da ya duba ba.
Hararan gefen ido Baba ya maka masa domin yaso saida wayarce shi yasa ya d'auke amma azal ya sanyashi yin maganarta ta zamo haramiyarsa.
"Hadi duk yarda makwafci ya ce shi d'in d'an uwa ne saboda shaidansa kad'ai zai iya kaika gidan Aljanna, ina tunasar da kai abinda ka sani kake takewa shi ne ka kyautatawa makwafci zato tare da rufa masa asiri musanman ga wanda ya bada kula ga iyalinka."
"To Baba amma ai musulinci bai bashi damar shigamin gida lokacin da bana nan ba, ko dan gudun gudun zargin mutane."
"Abinda na ke tunasar da kai kenan cewa ka kyautata masa zato kuma zanyiwa tufka hanci akan irin haka bazai sake faruwa ba tunda ya wuce iyaka, shiga gida yana baligi."
"Yawwa Baba kaima dai kagani."
"Zan bincika lamarin tundaga farko kafin in yanke hukunci."
"Ai wallahi ko da ka ja masa kunni sai na makashi a kotu."
"Kotu!?"
Habibu ya amtaba batare da ya sani ba.
"Eh can zan kaishi kuma sai ya gane shayi ruwa ne, dani yake zancen."
"Wato in na fahinceka dama can kuna da jika'kkiya kenan?"
Baba Umaru ya furta cikin shakewar murya domin ya soma gajiya da rashin kangadon Baba.
"A'a kawai shiga lamarin iyalinsa da ya yi na ke son ayi masa iyaka da su."
"To ba amfanin sakani cikin lamarin da kayi kenan?"
"Da shi mana Baba, kawai rubdugu zanyi masa ya gane ba da wasa na ke yi ba."
"Hadi in kanayiwa Allah da mahaifanka ka janye maganar kai makwafcinka kotu."
"Baba ka...
"In har na isa da in sanya baki cikin lamarin to ka janye."
"Shi kenan amma wallahi sai ya fita harkan iyalina."
"Naji zai fita."
Daga haka shiru ya ziyarci motar, Habibu ya ja tsaki kad'an cikin zabgowa Baba harara ta mirror, dak'uwa Baba ya auno masa batare da ya bari Baba Umaru ya gani ba, wani hararan Habibu ta bunko masa tare da cije lips.
"Kayi koyin halin girma tamkar mahaifinka."
"Kafi kowa sanin hakinsa kaf na kafe saidai kayiwa kanka wa'azin kula da iyali."
"Baba yaushe Habibu ya koma mara kunya haka?"
"Habibu ban son na sake jin amonka."
"To Baba."
Ga masifa a bakin Baba amma Baba Umaru ya katange damar amayosu saboda bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne.
Koda suka isa Asibitin Uncle ya koma gida Baba ya yi ta hura hanci Baba domin bai so hakan ba, Baba Umaru dai na kallonsa cikin nazari ya yin da Habibu ke ta zabga masa harara cike da takaicin hanashi maganar da Baba ya yi da sai ya wanke Baba tas da ruwan kalamai.
Abin mamaki ko sannu da jiki Baba baiyiwa Mama ba da ya iso ya sameta cikin k'oshin lafiya sama da d'azun da ya barta cikin godiyan Allah, balle kuma ya yiwa Deejah da ke kwance tamkar gawa. Halin ko in kulan da ya nuna ya tab'a zuciyar Mama amma ganin su Baba Umaru sai ta kauda duk bacin ranta saboda matsayin su na da banne.
Addu'a Baba Umaru ya ke ta tofawa Deejah yana rik'e da hannunta na dama cike da tarin damuwa zuwa can ya juyo ya tambayi Mama yarda lamarin ya kasance.
Abinda Likitoci suka sanar mata ta fad'a masa ya jinjina kai ya sake tambayarta yarda ita kuma ciwonta ya sameta nanma abinda ta sani da wanda Uncle ya bata labari ta fad'a masa tare da taimakon Malamin nan duk ta sanar da shi sai dai bata tona tijarar da Baba ya yi ba.
"Alhamdulillah zanje gidan Malamin na yi masa godiya domin ya taimakeni wurin bawa amanata kariya, Allah ya biyashi da gidan Aljanna."
"Amin ya rabbi."
Habibu ya amsa da sauri yana aunawa Baba wani kallo.
K'ara hade rai Baba ya yi tamkar wanda aka aikowa da sak'on mutuwa.
Kallonsa Mama ta yi ta ce "Kaima Malam ka je ka gode masa domin ya taimakemu iya taimako."
"Zanje, ko ba Malam Isuhu mai gudun duniya ba?."
"Eh, haka fa sunarsa ya ke."
"Au a shema d'ana ne, kai masha Allah, ai ya yo gadon sanin lak'anin korar shed'anu wurin mahaifinsa Malam Hassan, madallah da d'an arziki irin albarka."
"Baba ka sanshi kenan?"
"Eh na sanshi Hurera, mahaifinsa mutumina ne kafin Allah ya yi masa rasuwa."
"Allah sarki gaskiya ya zamo Malami na gari."
Da sauri Baba ya kalleta ta sauke masa murmushi ya kauda kai yana tsinewa Uncle da Malam Isuhu cikin ransa.
Ni zan koma na aiko Habibu da sak'o wanda idan ta farka shi zata soma sha, insha Allah jikinta zai dawo dai-dai batare da firgicin komi ba balle kufcewar tunani."
"To Baba, nagode."
"Ke ma ki sha idan ya kawo sannan Hajiya zata zo bayan sallar magriba ta kwana da ku saboda kema ba lafiyar ce ta wadaceki ba."
"To Baba, Allah ya k'ara girma."
"Amin, Allah yasa kaffara ce."
"Amin."
"Hadi zamu barka a nan ne?"
"Eh Baba."
"To ayi ta hak'uri kada ka tada zancen nan a Asibiti saboda jama'a, idan sun dawo gida zanzo da kaina mu zauna kuma ka tabbatar ka bawa Malam Isuhu hadin kai anyiwa gidan nan addu'o'in da ya kamata dan na fahimce akwai damuwa cikinsa."
"To, za'ayi."
"Madallah, nabarku lafiya."
Suka fice da Habibu Baba ya rakasu da mugun kallo tamkar zai cinyesu da idanu.
"Malam uban nawa kake harara?"
"Kinga Hurera ki fita idona in rufe."
"Allah baka hak'uri amma ka sani ba zan tab'a hararan naka mahaifan ba."
Tana ambatar haka ta juya masa baya tana mai ambaton sunar Allah dan samun rinjaye akan zuciyarta domin kallon da ya raka Baba Umaru da shi ya sosa ranta.
"Ke! fice ki bamu wuri munafuka banza kawai, 'yar rahoto."
Da sauri Fanta ta fice tana sharan hawaye dan tana kwance gefen Deejah.
"Hurera kin san Allah na kara ganin Alhaji Muhseen a Asibitin nan sai ranki ya b'aci."
"Malam wai me kake nufi ne? Yanzu Uwata na kwance tamkar gawa amma ka kasa yi mata sannu da jiki balle addu'a amatsayinka na Malamin addini?"
"Uwanki kika ce ko uwata?"
"Tawa ce ba taka ba."
"To sai ki tsukemin bakinki mai kama da Asusu ki saurari kashedina wanda ke makwafin wajibi a bishi in ana son ganin dai-dai."
"Malam dan Allah ka tafi kaina ya somin ciwo."
"Yanzu kika soma ganin ciwon kai in dai bazaki bi abinda na ke so ba."
"Me kake nufi?"
"Abin da tunaninki ya baki."
"Kai ne sanadin ciwo na kenan?"
"Wannan kuma kanki akeji nidai na sanar miki kada Alhaji Muhseen ya sake shigamin lamarin iyali."
"Yanzu kuwa yasoma shiga saboda wata rana surukinka ne shi."
"Au Allah?"
"Insha Allah."
"Zamuga ni."
"Insha Allah khairan gamu gani."
"Shi kenan Hurera ki nunawa duniya ban isa da ke ba kinji?"
"Malam kayi nazari domin wallahi Alhaji Muhseen mutumin kirki ne, kai shaida ne domin kafin zuwar lokacin nan kasha sanarmin da cewa baka tab'a ganin mai kud'i mara girman kai da sanin darajan makwafci irin shi ba."
"Au saboda yana da arziki shi yasa kike son ya auri Uwani?"
Shiru Mama ta yi bata amsa ba.
"Shi ne irin mijin da kikeyi mata addu'ar samu kenan?"
Ya furta cikin cillowa Mama kallon banza.
"Eh."
Ta ambata kai tsaye.
"To ina tayata murna."
Kafin Mama ta san abin cewa ya buga babban rigarsa ya fice.
Dafe goshinta ta yi saboda jiri da ta soma gani. Ba dan Fanta ta shigo ba tabbas da fad'owa k'asa zatayi daga saman kujerar da ta ke zaune. Cikin sa'a Nurse ta shigo ita ta taimwa Fanta suka dorata gefen gadon Deejah, cikin gaggawa aka kawo wani dago d'akin aka maidata kansa, Likitoci biyu suka rufu kanta, cikin mintoci da basu gaza goma ba ta samu barci.
Fad'a Dr. jalal ke yi tamkar zai ari baki a k'arshe ya bada umurnin kada a sake barin Baba shigo masa Asibiti, har masu gadi ya sanarwa wannan kashedi.
***
Kamar yarda Malam Isuhu ya ambata bayan sallar la'asar ya iso gidan Uncle ya fito suka shiga cikin gidan su Deejah suka raba Qur'ani har da Uncle suka soma karatu da ya ke suna da yawa awa d'aya da rabi suka kammala suka soma jero addu'a d'aya bayan d'aya suna daf da kammalawa Baba ya fad'o gidan afujan-jan. Duk yarda yaso yin tijara kasawa ya yi darajar gamin Al-qur'ani sai ya sami kansa da zama aka shafa addu'ar da shi. Kallon da Malam Isuhu keyi masa ne ya yasa jikinsa k'ara yin sanyi.
Uncle ne ya mik'awa Malam hannu sukayi musabaha tare da mik'a godiya, ya dubi Baba ya russuna cikin ban girma ya gaisar da shi ganin karramashin da Uncle ya yi sai ya saki rai ya soma washe bakin dole.
Haka d'aliban suka soma gaisar junarsu ta hanyar musabaha daga k'arshe suka russunawa suka gaida Malaminsu da su Uncle, daga nan suka fice gidan ya rage saura su uku.
"Malam Yusuf ga mai gidan nan ni albarkacin makwaftaka ya sa na jagoranci lamarin."
"Malam Hadi kai ne maigidan Hajiya?"
"Eh, Hurera ba, ai bataje Hajji ba Malam."
"Inda rai da rabo Baba."
Uncle ya mabata cikin murmushi.
Tsaki Baba ya ja ya juya zai fice sai dai maganar Malam Isuhu ya dakatar da shi ya juyo a hanzarce.
"Me ka ce?"
"Cewa na yi na kudiri aniyar maidawa wanda ke son cutar da Hajiya aniyarsa."
"Haba Malam Isuhu kana masanin addini amma kana son saka sharri da sharri, ka da fa kamanta yin hakan d'aukan zunubi ne domin ba lallai ne ya sauka kan wanda ya aikata d'in ba."
"Idan na aikata tabbas sai ya sauka kan wanda ya yi tare da wanda ya yi sanadiin aiki."
"Kuma dai?"
"Eh, saboda rama mugunta ga macuci ba laifi ba ne."
"Kagane Malam Isuhu mubar maganar zanzo gida na sameka sai muyi maganar anatse mai cike da fahimtar juna."
Kallon k'urillah Malam Isuhu ya kafeshi da shi sai kuma ya murmusa tare da motsa kai ya kalli Uncle ya ce "Insha Allah sauka na k'arshe Malam Hadi zai jagoranta shi da d'alibansa."
"Malam da ka cikashe aikinka kawai."
"Alhaji ai tare dani za'a yi har da kai tamkar dai yarda mukayi wannan tare manufata shima Malam Hadi ya kamata ya taimaka da irin nasa baiwar tunda shi ne jigon gidan."
"Haka ne, to Allah ya kaimu lokacin."
"Amin."
Uncle ya amsa Baba kam kai ya wuya gefe zuciyarsa tamkar wuta saboda takaicin ya sa tijarar da ya zo da shi.
Sake yin musabaha da Baba Malam Isuhu ya yi Uncle ya rufa masa baya suka bar Baba tsaye tamkar an dasashi.
"Ya kamata in san inda kaina keyimin ciwo tun kafin gwad'o ya yi min k'afa."
Baba ya ambata cikin zare idanu, ganin Uncle ya dawo sai ya dai-daita natsuwarsa tare dajin wani kalan tak'ama ya ziyarce shi.
"Baba dan Allah kayi hak'uri akan laifin dana aikata maka na shiga lamarin iyalinka kai tsaye batare da na nemi izininka ba, hakan ya faru ne saboda halin dana ganta a ciki wanda tunanin nemanka ya b'acemin sai bayan na kaita Asibiti amma insha Allah hakan ba zai sake faruba, ka ya femin dan Allah."
Shiru ya yi yana kallon Uncle a d'age cikin hura hanci.
"Ni makwafci na gari ne ban aikata hakan don muzguna maka ba sai dan taimako irin ta makwafci na kwarai."
Ya sake ambatar haka a ladafce.
"Shi kenan ya wuce amma ka sani daga yau ban amince na sake ganin kafafunka a cikin gidan iyalina ba tunda ba gidan gala ba ne."
"Insha Allah zan kiyaye."
Tsaki ya ja, Uncle ya kalle shi da sauri domin tsaki nadaga cikin abinda ke fusatashi.
"Tunda kai kayi kid'an to kai zakayi rawar ba ruwan Hadi ciki."
"Ban fahinceka ba Baba?"
"Munufata tunda kai ka kaisu Asibiti ba zanyi asarar ko taro ba, kai da kaja ruwar kai zai duka."
Murmushi Uncle ya yi cikin jinjina halin Baba wanda samuwar lamarin yasa shi ganewa.
"Wannan ba komi ba ne Baba ai yiwa wani aka ce yiwa kai ne."
"To madallah, zaka iya ficemin a gida."
Wani murmushin Uncle ya kuma yi, ya karkace a ya tura hannu a aljihu ya ciro kud'i yan dari biyar biyar masu yawa ya russuna ya mik'awa Baba, wani kallon banza ya saukewa kudin amma a zahiri godiya ya ke gabga masa cikin ransa ya yi hakan ne dan kare marbata.
"Na me ye wannan?"
"Ihisanin dai dana saba yi maka ne na aiwatar amma ba dan wani manufa na daban ba."
"Nagode, Allah ya rubuce "
Ya furta cikin damk'e kud'in.
"Amin Baba."
Sukayi sallama cikin wal-wala lamarin da ya yi ta bawa Uncle dariya.
'Wato kudi masu sayo martaba da k'arfi da yaji.'
Cikin ransa ya ambata yana kuma murmusawa.
"Halayyan Baban Khadijatu nada ban mamaki, gashi dai masanin ilimin addini amma in ya kwab'a wani abin tamkar bai tab'a zuwa makaranta ba balle ace yana koyarwa."
Ya furta cikin ransa. Su Bintu ya gani suna shiga mota wanda ya tabbatar Asibiti zasu, ya k'arasa wurin cikin wal-wala amma ganin yarda fuskansu ya ke cikin rashin wal-wala sai ya tsare gira, duk suka fito suna gaisar da shi bai amsaba sai idanu da ya zubawa Nafisa wacce ke hakimce a gidan baya bata fito ba.
"Ina zaki je?"
Ya jefo mata tambayar.
"Asibiti."
"Kai waye ba lafiya?"
Ya maido da tambayarsa kan su Beebah da ke tsai-tsaye
"Mama da Deejah."
Safina ta amsa masa.
Ya juyo kan Nafisa kafin ya bud'e baki ta rigashi cewa "Makwafci ko me ya yi maka na aibu ya kamata ka saka masa da khairan dan koyi da halin Manzon Allah."
"Sallallahu Alaihi Wasallam."
Ya ambata tare da su Beebah.
"Abban Hafiz ina fatar daga yau fushin ya k'are?"
Ta ambata a hankali wanda da alama shi kad'ai ya jiyo saboda ya matso jikin motar ya bawa su Bintu baya.
"Allah ya kiyaye hanya."
Ya ambata tare da mik'a mata kudi "Ku saya musu kayan marmari."
"Ok."
Ta amsa tana kallon cikin idanunsa, murmushi ya sauke mata ta maida masa da martani. Yana tsaye suka fice inda Beebah ce ke jan motar.
"Allah yasa tuban gaskiya kikayi dan na san waye ke Nafisat idan kin so shirya tsiya."
"Alhaji gashi inji wani mutum ya ce abaka idan ka dawo."
Mai gadi ya ambata cikin miko masa Emblem.
Amsa yi ya ya nufi cikin gida yana kallon agogon da ke d'aure a tsin-tsiyar hannunsa na hagu.
*TALLA.*
*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*
Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)
*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in *** ko ***. Sai munjiku.*