20
by @mrsjmoon
Page 20.
Tsam na yi ina nazarin zantukansu tare da son gano abinda Mama ke b'oyemin amma iya hangena na kasa gano abin, lamarin da ya sanya sanjawan bugun numfashina ya soma fita da sauri batare da na san dalilin faruwarsa ba, na yi hanzarin kulle bakina gudun kada sautinsa ya bayyana su gano na farko har na jiyo hirarsu tunda na gano basa so inji.
Hakan danayi ya sanya na sark'e cikin fitar da tari mai k'arfi. A tare suka iso gareni, Mama ta soma shafamin baya cikin jeramin sannu Hajiya Inna kuwa ta kafamin kofin ruwa a baki, bayan tarin ya tsaya sai na tsirawa Mama ido ta ware nata na lumshe nawa tare da motsa leb'b'ana.
"Me kike son sanarmin Uwata?"
"Godiya na ke son yi muku."
Na furta duk da ba shi ne a raina ba.
"Da akayi me?"
"Kula da ni batare da gajiyawa ba."
"Wannan hakkin mu ne Uwata dan haka babu godiya a tsakaninmu, kinji ko?"
Motsa kai na yi ina saukewa Hajiya Inna murmushi wacce ke binmu da kallo cikin sigan tausayi.
'Da magana a bakinki Hajiya Inna kuma zan jiyo shi da yardan Allah.'
Na ambaci hakan a raina tare da zamewa dan in kwanta saidai Mama ta hanani hakan inda ta umurceni da in sauka in d'auro alwalla inyi Sallar Subahi. Na sakko ina cije baki saboda jirin da baigama sakina ba. Ita ta taimakamin na shiga toilet, tana tsaye na yi tsarki tare da d'auro alwalla muka fito saboda ta san halina da son wanka ina iya k'ara sanyawa jikina ruwan sanyi da zarar ta bani wuri.
A Zaune na gabatar da sallah a cikin sujata na k'arshe na rok'i Allah da ya bayyanamin abinda Mama ke b'oyemin ko da jinsa ko ganinsa zai zamo ajalina ne.
Na yi wannan addu'ar ne saboda yarda na ke son sanin lamarin.
Haka nan kawai naji b'acin rai ya kanai-naye ruhina cikin sekonni bayan na d'ago daga sujjadar, koda na sallame sallar sai na koma saman gado na kwantar tare da juyawa su baya.
"Uwata jikin ne?"
"A'a."
Na amsa a tak'aici abinda ban tab'a yi mata ba kenan bata amsa cikin rashin girmamawa.
"To tashi kisha tea kafin Likita ya shigo."
"Barci na ke ji Mama."
Wannan karan cikin rawar murya na amsa mata.
Hannunta na ji cikin sumata sai na sake lafewa batare da na juyo ba.
"Uwata na san kina tare da damuwa b'oyenmin kike yi."
Tashi zaune na yi cikin son dai-daita fuskata zuwa wal-wala.
"Kada ki wahalar da kanki Uwata wurin layancewa domin na jiyo dirin damuwarki a k'irjina, oya maza sanarmin da shi tun ban sab'a miki ba."
Dariyar dole na sanya duk dan in nuna mata ban tare da damuwar komi na d'aga yatsa na nuna Hajiya Inna wacce ta bud'e baki tare da zaro idanu jin abinda Mama ta ambata ina cewa "Kalli Hajiyarki k'uda na shirin fad'awa bakinta."
Harara ta zabgamin na kamo hannayenta na rungume a k'irjina ina doka murmushi.
"Harbawan me zuciyarki ta ke yi haka da sauri?"
"Wai tana neman ki aminta da kalaman d'iyarki ce na bata tare da damuwan komi."
"Na amince Uwata bata cikin damuwa tunda muna tare da ita a ko da yaushe kuma zamu cigaba da kasancewa da ita har zuwa sadda k'asa zai rufe idanunmu tare da burin had'uwa da juna a gidan Aljanna."
"Allahumma Amin Mamana."
"Wannan k'auna taku Hurera na bani tsoro anya lamarin nan kuwa mai b'ullewa ce?"
"Inna bakomi sai khairan, wannan shi ne ni'imar da Allah ya dasa a cikin shayar da 'ya'ya nono ko da ba...
Sai kuma ta yi shiru tare da mik'ewa ta nufi hanyar toilet.
"To Allah ya tabbatar da khairan mara iyaka Hurera."
"Amin tsohuwar su Mama."
Na amsa cikin tsokana.
"Fad'i ki k'ara da ihu tsohuwar su ce ko wani ya ce taki ce?"
"Eh kince dole sai na kiraki da Inna kinga kenan kin saka dole kin zama tsohuwata."
"Takwara ciwon nan naki yazo miki da son surutu."
Lumshe ido na yi bance komi ba itama daga haka bata sake magana ba.
Ganin Mama ta ji bata fito ba sai Hajiya Inna ta hadamin tea mai kauari ta tsareni saida na shanye. Lokacin dMama ta fito kanta k'asa dan tak'i kallona saina nuna tamkar ban lura da b'oyemin fuskanta da ta ke yi ba na d'auko apple na soma gutsira cikin zantukan zucci masu yawa a game da bak'on lamarin da na kasa gano kansa balle tushensa.
"Kunga tafiyata na koma gida na huta tunda duk kun warke."
Hajiya Inna ta ambata cikin kallon Mama wacce da alama ta yi nisa cikin tunani bata jiyo maganar ba.
"Ayya Hajiya Inna ki jira mu tafi tare tunda zamu sami sallama yau insha Allah."
"Takwarata su Malam na kan hanya dawowa to ina son zan sama musu wani abu kafin su iso."
"To tafi na baki izini tafi."
"Ja'ira kin samu lafiya fa bakin ya bud'e da tsokana kala-kala."
"Eh dai tafi sai nazo kwance jikka."
"To amma dai ki tabbatar kin maida jikinki saboda Malam bai sakewa ramamman mace fuska dan na tabbata wannan manya idanun naki da suka sake fitowa zasu firgitamin miji tsaf."
Kafin in bata amsa ta fice da sauri tana dariya Mama na tayata domin ta maido da hankalinta kanmu.
"Hajiya Inna kenan ta san kan iya tsokana."
"Uwata ke ce Inna ke sakewa irin haka duk cikin jikokinta saboda bata yarda da wasan jika da Kaka ba gudun rashin kunya irin na wasu jikokin sannan wasan kansa wasu Malaman sunce baya cikin musulinci."
"To Mama me yasa ni kad'ai takeyiwa?"
"Ita zata amsa miki wannan tambayar kam."
"Mama wai me...
Dawowar Hajiya Inna yasa ban furta abin da na yi niyya ba, muka zuba mata ido ta iso ta ja hannun Mama suka fice zuwa can ta dawo ita d'aya tare da d'aukarwa Mama hijab shima bata jima ba ta dawo ta zauna saman kujerar roba a gabana muka zubawa juna ido, numfashi ta ja ta soma magana "Nana Khadijatu Allah ya jarabceku da rayuwa k'ark'ashin baudd'en mutum sam Malam Hadi bai aiki da saninshi a matsayinsa na babban Malamin da ake ji da shi."
"Me ya faru kuma?"
"Ina fita na had'u da Alhaji Muhseen yazo tafiya da Mamanki wai ya tsayar da matarsa a waje sai sun nemi gafarar Hurera kafin kafafunsu ya shiga masa zauren gida sannan ya tara mutanen unguwa nata fesa musu lamarin da bai kamata ba domin ance duk wanda ya rufawa wani asiri to Allah zai rufa masa."
"Duk me ya janyo hakan Inna?"
Tsit na yi jin bak'in labarin abin kunyar da matar Baba tare da 'ya'yansa suka tafka.
"Dan rashin kyautawa kam sunyisa Takwarata amma ai fad'ar cikin gida ne bai kamata ya bari na waje su ji ba ko dan mumbarin da ya ke hawa bada sallah."
"Abin kunyar ce kam hakan Inna kuma ina tabbatar miki da wata manufa nasa yasa shi kiran Mama."
"Abinda itama ta ke sanarmin kenan dan ta nuna bazata je ba na bata kwarin guiwa."
"Ko me ye dai Allah na tare da masu neman taimakonsa."
"Wannan haka ya ke Khadijatu, masu neman taimakon Allah cikin lamarinsu basa tab'a ganin bak'in cikin ratuwa."
"La shakka babu Inna."
Munyi shiru zuwa can Hajiya Inna ta soma yimin hira inda yawancinsa akan yarda rayuwa ta ke juyawa al'umma ce musanman wad'anda suka d'auki duniya da fad'i. Knocking a kayi Inna ta amsa da a shigo matar Kawu Habibu ne tare da Aliyu Muktar, ware ido na yi shi kuwa ya tsaya a k'ofa yana jefomin murmushin k'auna, sunkuyar da kai na yi jin Zainab na tsokanarsa, bai kulata ba ya iso gaban Hajiya Inna ya sunkuyar har k'asa ya gaisar da ita ta amsa cikin tambayar sa mahaifiyarsa.
"Hajiya ya mai jikin?"
"Gatanan ta warke tunda bakiyi tunanin zuwa cikin lokaci ba sai da kikaji mijinki zai dawo gudun kada ya saukemiki halin nasa yasa kika zo to angode amma ki sani shi kyautatawa abune mai kyau kuma lalura na kan kowa dan Khadijatu bata zo miki barka ba bai zama hujjar da zaki riketa ba domin kinfi kowa sanin halinta na rashin son jama'a."
"To Hajiya ai duk rashin son jama'arta sai ayi mata fad'ar rik'o da zumunci tunda duk abu d'aya muka aikata har gara ni da ita."
Shiru Hajiya Inna ta yi cike da takaicin domin abinda ta tsana kenan ta nunawa mutun kurensa ya k'i amsa.
"Hajiya Inna a yi hak'uri idan na k'ara samun sauk'i zanzo ganin Baby musanman tabbas na san ban kyautaba, Ina neman affuwan Matar babban mutum mai halin girma."
"Allah ya yi miki albarka Takwarata."
"Amin."
Muka amsa tare da Aliyu wanda ya koma gefe yana saurarenmu tunda ya gama gaisar da Inna.
"Bari in lek'a gida Takwara."
"To Inna sai kin dawo."
"Aha, ke kuma idan kinga dama ki zauna da ita kafin wani cikin ni da Hurera ya dawo."
"Agaskiya ba zan zauna ba saboda jego na keyi nadai zo dubata kada ya zamemin abin magana wanda duk da hakan gashinan ban tsira ba saida akayimin luguden labba."
"Matar Kawu ki iya bakinki fa, Inna ba sa'ar yinki ba ce dan haka ki tauna kalaminki kafin ki furta in har kina son gamawa lafiya."
"Idan ank'i yin hakan fa?"
Bud'e baki na yi zan bata amsa Inna ta d'agamin hannu tare da komawa ta zauna.
"Zaki iya tafiya tunda kin gaisar da itan."
"Ok na barku lafiya, Allah ya k'ara affuwa."
Banza mukayi da ita ta fice abinta ba damuwar komi.
"Hajiya dan girman Allah kiyi hak'uri, halin Zainab sai ita sam bata san ya kamata ba ko a family haka ake fama da ita bata da kunyar gayawa babba duk kalamin da ya fito bakinta."
"Kada ka damu Aliyu, wannan ba sabon abu ba ne, Allah dai ya ganar da ita."
"Amin."
Ya matso daf da gadon ya ce min "Na yi kewarki, Allah yasa kaffara ce."
"Amin."
Kud'i mai yawa ya ciro yan dari bibiyu sabbi fil ya ajimin saman cinya sannan ya fice bayan ya sake bawa Hajiya Inna hak'uri.
"Me ke tsakaninku da shi Takwarata?"
Shiru na yi tare da kulle fuska da tafukan hannayena.
"Oh na fahimta, to ba damuwa za'a kuma yayibo irin rashin d'a'a ba."
"Hajiya Inna me ya yi?"
"Jinin Zainab basu k'ara shigomin ahali da yardan Allah dan haka tun kafin ki haukace a shiriritan so dinan ki koreshi."
Idanu na zare ta zabgomin harara.
"Inna wai ya suke da matar Kawu?"
"Abokik wasanta ne domin da babanshi da Mamanta uwarsu d'aya ubansu d'aya kuma yayarshi wanda suke uba d'aya abokin Habibu ne, agidansu Habibu ya had'u da ita dan Mamanshi ita ta rik'eta har zuwa aurenta."
"Ikon Allah amma duk shekarun da muka kwashe da Aliyu ban tab'a sanin hakan ba."
"To ina kike zuwa balle ki had'u da 'yan uwansa sannan shima Aliyun bai zuwa gidan Habibu sai hab'o."
Shiru na yi ina nazarin wannan lamari, ta ke naji duk damuwar da na ke ciki ya koma ba komi ba saboda tuno mugun halin Zainab da tasha gwadamin wanda nashajin Hajiya Inna na cewa d'aukosa ta yi wurin uwar goyonta.
'Wato mahaifiyar Aliyu bata da kirki kenan? Aikam na hak'ura da kai domin ina burin aure na ke inda Zan sami kwanciyar hankali ba kishiyarta ba.'
"Ban son shiga dogon tunani saboda lalurarki."
Na tsinkayi muryan Hajiya Inna daf da ni. Kallonta na yi har lokacin bata cikin walwala.
"Kiyi hak'uri Inna."
"Ya zamamin dole Khadijatu sai dai DAMUWATA shi ne na yarda surikata gudan jinina d'aya tilo zata zamemin abokiyar gaba."
"Ban gane ba Inna? Kina nufin su Mama Indo ba surukanki ba ne?"
"Surukaina ne amma duk kan mazajensu 'ya'yan uwar gidan Alhaji ce wacce ta rasu ta barmin su duk suna k'ananu, Habibu shi ne yarona na shida kuma shi ne ya rayu har naga aurensa domin yayunsa da k'anninsa daga sun taso suke mutuwa domin babban yayarsa na daf da yin aure ya sami hatsarin mota ya mutu nasan kin tuna lokacin."
Eh na tuna da kawu Hamza, Allah ya ji kansu da Rahma "
"Amin.
"To yau kinji yarda na ke da su Balarabe."
"Allahu albar, sannu Inna, lallai ke ta daban ce, Allah ya biyaki da khairan."
"Amin ya rabbi."
"A gaskiya su Mama Indo nada ladabi sama da Zainab sam ba wanda zaice ba ke ce kika haifi mazajensu ba."
"D'iyoyin tarbiyya kenan, sannan sun samu mazaje tsayayyu masu jajircewa akan abin da suke so dole abi ba irin Habibu ba da gata ya yiwa yawo ya ke ganin matarsa ba komi ta ke yimin ba saima ganin ni ce nacika fad'a da saka ido."
"Shi Kawun ke kallonki da hakan?"
"Ya wuce kokwanto Khadijatu domin yanzu indan da gabansa hakan ya faru wallahi tsaf bayar matarsa zaibi ya yi ta k'unci na tozarta masa iyali gaban mutane."
"In haka ne kam da sake wallahi, ai lamarin uwa sama da komi ya ke, gashi wayayye da ilimi amma bai aiki da shi."
"Ki bari kawai Khadijatu, shi yasa na kance da shi halinsa d'aya da Hadi."
Kulle baki na yi idanu waje na ke girgiza mata kai murmushi ta yi kad'an ta ce "Na tabbata ko halinsu bai zo d'aya ba a wani abin zaizo domin ya yi nisa akan lamarin figaggiyar matarsa mai zubin zabbin daji da kanta kamar k'ullin maganin sanyi."
Dariya na kyale-kyale da shi tana tayani. Daga haka muka saki zancen domin nagano ta sanyo mana raha ne saboda bata son acigaba da zancen.
***
Ina cin abincin rana faten Irish ne ya ji hanta da ganyen ugun wanda su Fanta suka kawomin, sai hira mukeyi hankali kwance domin Hajiya Inna ta sami wucewa gida tunda ta ga isowarsu.
Mama ce ta shigo Uncle na biye da ita tare da Baba a bayansu. K'irjina ne ya harba ganin Baba domin na tabbata sai ya b'atamin rai kafin ya tafi.
"Kai dalla! Ku fice ku bata wuri ta sha iska, kunzo kun nanuk'eta da tik'a-tik'an jikinku ba mijin kwasa ko da ya ke duk jirgi d'aya ya kwasoku da ita ga kyau da wayewa ba mashin-shini, kai tir muku!."
Tashi su Fanta sukayi duk suka fice jikinsu a sanyaye, na kalli Uncle wanda na hango b'acin rai a idanunsa kwance sai kawai na fashe da kuka mai sauti ina kaiwa k'arfe gadon duka wanda ke nuni da takaicin da na ke ciki.
*TALLA.*
*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*
Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)
*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in *** ko ***. Sai munjiku.*