21
by @mrsjmoon
Page 21.
"Ke! Kuma me akayi miki kika b'are baki kamar faranti kina kukan iyashege, to maza ki rufe mana baki ko ingamu da ke ba ciwo ba ko mutuwa kikeyi zan iya taka gawarki na wuce ta kai ba ruwana."
Shiru na yi amma badan tsoron dukansa ba sai dan takaicin halinsa tare da tunanin yin kukana baida amfani.
"Dan an kira k'awayenki tik'a-tik'a shi ne abin yin kuka saboda Hurera ta gama sangartaki, ke yanzu dan Allah ko kunya bakiji kamarki kina kuka, inda a k'auye kike da yanzu kina da 'yay'ya bakwai zuwa goma amma dubeki zaune makar gar, to wallahi ki sani kwanaki kad'an ya rage in zar...
"Dan Allah Malam kayi shiru haka ban muji da abinda ya damemu tunda kai haka Allah ya yika baka gajiya da sababi mara ma'ana da ke janyo jin kunya."
"Hurera ni...
"Dan soyayyarka da mahaliccinmu ka daina fad'ar nan haka, haba dan Allah kai ko gajiya bakyayi da zance a gaban idanun kunya."
Tsuke baki ya yi yana aunawa Mama mugun kallo, kunya ce ta rufeni ganin yarda Uncle ya ke binsa da kallon banza, tabbas kallon ya haskomin karatun ruhinsa wato takaicin Baba mai jin tamkar a rufe rufeshi da duka.
"Uncle nagode da tarin d'awainiya Allah ya jik'an mahaifa ya kuma shirya maka zuri'a tare da gamawa lafiya cikin samuwar babban rabo ranar lahira."
Sai da ya yi gyaran murya sannan ya amsa lokacin har Mama ta amsa ya yin da Baba ya tsare giran sama da k'asa yana zabgomin harara.
"Bari inga Dr. Jalal."
Uncle ya furta batare da ya jira amsawarmu ba ya fice.
"Munafukin banza wai shi nan ya ji haushi na kori k'aninsa, to an koresun in zai iya ya rufeni da duka yaga inda tsiya ke zamaninta wallahi."
"Allah ya yi mana tsari da ganin tsiya."
"Amin."
Na amsa da sauri.
"Ya jikin naki?"
Baba ya ambata cikin taushin murya. Ban dauka da ni ta keyi ba shi yasa bance komi ba.
"Au dan kin samu na tambayi ciwon karyan da kikayi shi ne zaki maidani sokon banza?"
Kafin inyi magana Mama ta rigani da cewa "Gata nan ta warke ganin idanunka sai kuma me uban 'yan sababi."
"Hurera me yasa sam baki san darajar aure ba ne?"
"Sabon karatun sanin darajojin aure zamu koma makaranta muyo tare da kai domin kome ka kirani kaine malamina."
"Zan sab'a miki fa Hurera ba ruwana da Asibiti ne nan."
"Maza aikata abin yamad'i-d'i karo na biyu a safiyar nan a samu masu d'oraka a yanar gizo da bugawa a jaridu kaga ka zama dan wasan kwai-kwayo na zahiri kamar yarda sabon sunarka ya koma a unguwarka yanzu."
"Ni Malam Hadi kike kira da d'an drama?"
Banza Mama ta yi da shi, nikam tuni na juya baya tare da tura yatsuna cikim kunnuwana saboda na gaji da sauraren sababin Baba.
"Sai mun had'u a gida zan nuna miki nafi gaban iskancinki sannan kada kiga na d'aga darajarki a gaban abokan zamanki d'azun ki d'auka kin sameni ne a'a biyana zakiyi dan wallahi sai naci buhunar wake biyar domin na saka buri akan wanda sukayi satan sai reshe ya juye da mujiya dan haka sai ki shirya bi...
"Allah ya ganar da kai hanyar gaskiya."
Mama ta ambata tare da shigewa toilet ta barshi tsaye da baki bud'e, dariya ce ya zomin na kife fuska gudun kada ya jigoni na shiga uku
K'aran buga k'ofar ya sanarmin da Baba ya fice, numfashi na sauke ina auna lamuran Baba wanda na yanzu na ke d'orasu a mizanin rashin hankali.
"Astagafirullah."
Na ambata a hankali.
Shigowar Doctor, Uncle da su Beebah biye da su ya yi daidai da fitowar Mama daga toilet. Ya bani sallama tare da shawarwari agame da daina barin damuwa ko tunani na takuramu ni da Mama saboda su ne babban matsalolinmu.
Sosai Mama ta yi masa godiya, su Fanta suka tattara mana kaya muka fito. Ni da Mama tare da Bintu motar Uncle muka shiga ya yin da su Fiddausi suka shiga wanda suka zo a ciki Beebah ta ja, ta yi gaba Uncle ya rufa mata baya, akan hanya ya kira Hajiya Inna ya sanar mata da an sallamemu.
"Yawwa Alhaji sanar da Malam kada ya zama abin laifi duk da yasan za'ayi sallaman."
"To Mama."
Ni ya mik'owa wayar batare da ya furta kalma ba.
Sunar da naga an sanya Baban Nana na kira har ta tsinke ba'a d'auka ba, haka na yi ta kira sau ba adadi a k'arshe sai aka kashe wayar.
Mik'awa Uncle wayarsa na yi ya amsa batare da ya cemin uffan ba haka nima ban tofa ba.
"Mama dan girman Allah kiyi ta hak'uri da Baba insha Allah hakurinki babban riba ne saboda halinsa ba ke kad'ai yake yimawa ba, na fahimci haka Allah ya yo shi mafad'aci ga saurin hasala akan abin da bai kai ya kawo ba."
"To Alhaji Allah ya k'ara mana hak'urin baki d'aya."
"Amin."
Muka amsa.
Wayar Bintu na amsa na turawa Aliyu sak'o. Ina kallon Uncle na hararan hannuna ta gefen ido sai lamarin yabani dariya na murmusa har sautin na fitowa ya kalleni ido cikin ido na lumshe nawa.
"Ina wayarki?"
Ya furta cikin rad'a.
"An sace wayar."
"Inji wa?"
Wannan karan ya bud'e murya.
"To Uncle nazo da ita Asibiti ba'a ganta ba."
"Ok za'a siya wani."
"A'a kada a siya tana wurin Baba Umaru, Habibu ya sanarmin da sun dawo daga tafiya za'a kawo mata."
"To Mama."
Ya amsa cikin girmamawa.
Wayar hannuna ta yi k'ara number Aliyu ya baiyana sai na maida silent tare da maidawa gefe na ajiye, ina kallo kira ya yi ta shigowa ban d'auka ba saboda idanun Uncle wanda yanzu k'imarsa ya kuma ninkuwa a gare ni ainun.
"Ki d'auka wulak'anci bai da kyau Khadijatu."
Cikin rad'a ya ambatamin haka, kallonsa na yi ya jinjinamin kai maida kai gefe na yi batare da na bi umurninsa ba.
Muna isa gida su Beebah suka gyaramin d'akina dana Mama cikin a binda baifi awa d'aya da dawowarmu ba gidan ya koma fes har girki sun d'ora, wanka na yi muka zauna a baranda saman babban tabarma Fanta na yi min fifita sakamakon zafin da na ce yana damuna, shi yasa na sanya riga mai yankakken hannu da siket mara nauyi sai na sanya k'aramin hijab wanda ya tsayamin iya wuya.
Aunty Nafisa ce tare da yaranta suka shigo mun gaisa cikin mutunci Mama ta sake yi mata godiya akan d'awainiyar da Uncle ke kanyi mana. Muna tare da ita har dare sannan tsawon lokacin ban hango tijara a idanunta ba domin duk had'a idanun da zamuyi bata yimin mugun kallon da ta ke bina da shi a tun sanina da ita. Sai bayan isha'i ta wuce tare da su Bintu, su kabar Beebah da Fanta.
Ina sallah na jiyo shigowar Baba Umaru Ina idarwa na tafi muka gaisa sai tsokanata ya keyi da gawa tak'i rami, Kawu Habibu na taremin. Shigowar Baba yasa na bar wurin da sauri ina jin Kawu Habibu na k'orafin sababin Baba dan ganin yarda na tsorata da shigowarsa. Ba jimawa na jiyo muryan Uncle inda na fahimci masalaha akazo samu bisa jagorancin Baba Umaru.
"Aliyu ya na k'ofar gida fa."
Idanu na zubawa Beebah, ta gyadamin kai "Tun kina wanka ya zo kuma ya kamata ki fita."
"A gaban su Baba Umaru zan fita zance?"
"To me ye? Kinga ba sai Baba ya gane muna da masun-sunar da ya yi mana gorinsu ba."
Sunkuyar da kai na yi saboda yarda ta yi maganar na gano zagin da Baba ya yi musu d'azun ya b'ata ranta.
"Uhm wallahi badan mahaifinki ba ne Deejah na rantse da d'azun bansan kalan maganar da zanyi masa ba dan har zagi zai iya masa amma sai ya zamo ya haifeki 'yar albarka."
"Aunty Beebah ba Uncle ya ce maganar ta wuce ba."
"Ya wuce Fanta kawai dai har yanzu haushi lamarin ya ke bani barinma dana jiyo muryansa yanzu."
"Kiyi hak'uri nima d'iyarsa bai bari ba, kin dai gani da idanunki."
"Ya wuce yanzu tashi ki tafi wurin masoyinki."
"Dan Allah ku fita ku wakilceni domin bazan iya tsallake taron can ba."
"Fanta tafi ki sanarmasa tasha magani jiri ta ke gani ya shigo su gaisa."
"A'a kada ya shigo."
"Me kike nufi?"
"Ya tafi sai da safe ya dawo."
"To baki isa ba sai ya shigo tunda dubiya yazo ba soyayya ba."
Tab'e baki na yi jin abinda ta ce idanu ta zaro na zabga mata harara tare da hayewa saman doguwar kujera na kwanta. Fita sukayi tare da Fanta zuwa can na jiyo sallamar Aliyu da sauri na tashi na jira hijab na cure wuri d'aya. Duk Ina jin sadda ya gama gaida kowa su Beebah suka yi masa jagora zuwa d'akina na sha mamaki da banji Baba ya yi sababi ba amma tuno da Baba Umaru a wurin sai na barshi saboda ganinsa sa ne ya tsuke baki.
Tashi zaune na yi muka gaisa daga nan shiru ya biyo baya, su Beebah dai na zaune saman gado kowacce na latsa wayarta basu da niyya bamu wuri sai hakan ya yimin dad'i saboda har cikin raina banda kalman furta masa..
"Allah ya k'ara lafiya."
"Amin, nagode."
"Bakomi ke matar Ali ce insha Allah."
Da sauri na kalleshi ya dokamin murmushi sunkuyar da kai na yi.
"In Allah ya kaimu gobe Hajiyana tare da Salma zasu zo dubaki."
"Ok Allah ya kaimu."
"Amin."
Ya mik'e ya fice Fanta ta rufa masa baya.
"Ke matar Muhammad Muhseen ne ba Ali ba."
"Uhm Beebah hoo naga dai ke ce duk kikayi kid'a da rawar nan fa."
"Shi yasa na ke son goge zunubina."
Dariya ta bani sosai na dara tana tayani.
"Allah Deejah kafin in bar garin nan sai kin rabu da Aliyu."
"Saboda me?"
"Haka nan naga yanzu baku dace da juna ba, farar mace sai farin namiji kamar Uncle zubin labarawa."
"Kinyi kuskuren fad'ar karin.maganar Malama cewa akayi farar mace sai bakin namiji, farin namiji kuwa sai farar mace tamkar yarda Uncle suke da Aunty Nafisa ita chocolate shi fari, my Ali baki ni 'yar fara kad'an."
"Ko ba 'yar fara kad'an ba."
Ta furta cikin kawomin duka na gofce tare da komawa serious na ce "Bazan auri Aliyu ba saboda da wasu manyan dalilai wanda zan sanar da ke kafin ku tafi."
"Zanso jinsu yanzu saboda tafiyarmu zai iya yiwuwa gobe ne."
"Gobe kuma?"
"Eh saboda Aunty Nafisa ta had'a mana gurmi wurin tsoho mai ran k'arfe ya kira Uncle lallai mu taho gobe ko ya iso garin Kaduna da kansa ya d'aukemu musanman ni da ke aikin taimakon al'umma."
"Wayyo zansha kewa."
"Muma haka amma tafiyar banda Fanta saboda muna da biki watan gobe zasuzo da fatan zakiyi mana kara kizo?"
"Insha Allah zanzo duk da muma zamuyi tafiya amma nasan kafin bikin mundawo."
"Dan Allah kizo."
"Insha Allah."
"Ok."
"Bikin na miji ko mace?"
"Babban yayarmu baki d'aya shi ne zaiyi aure."
"Masha Allah."
"K'aton tazuru ne fa duk k'anninsa sunyi aure da 'ya'yanzu shi kuwa ya tsaya bautawa boko, da kiranye ya dawo Nigeria, baki gansa ba tamkar bature."
"Ikon Allah, lokacin auren nasa ne baiyi ba sai yanzu."
K'asa ta yi da murya sannan ta ce "Ina son shi fa insha Allah zanzo a ta biyu shi yasa na yakice Yaya Abdul da k'arfi da ya ji."
"To wata sabuwa inji 'yan ca-ca."
"Ki bari kawai dear ni kad'ai na ke kidana da rawana sannan in banda ke ba wanda ya sani."
"To ta ya za'a yi auren kenan?"
"Ta yarda akeyi."
"Zanso ganin wannan soyayya wacce ta ke ma kauniya."
"Ki bari kawai Deejah ni kaina na bata wannan sunar amma ina fatar ta sami ido bada jimawa ba domin ba zan iya bawa kowa ruhina ba sai Yaya Mubajjal."
"Wow suna mai dad'i ga tarin ma'ana."
"Duk mai sunar ya tarasu wallahi ya san kansa baruwansa kowa na sa ne, kinga tunda ya dawo duk jikokin gidan shi ke d'awainiyar karatunsu hatta da mu da muke jikokin d'iyoyi mata ya d'auki nauyi sai d'an abin da ba'arasa ba iyayenmu keyi mana, kud'i ya ke samu tamkar yana hak'osu a k'asa saboda a can turai ya ginu har kamfanoni ya ke da su tare da turawa."
"Masha Allah, matarsa ta yi dacen miji mai son zumunci."
"Wallahi fa ta yi dace kuma ta tsinci dami akala domin d'iyar kawunsa zai aura itama yar boko ce lecturer ce sai dai yafita kyau da aji nesa ba kusa ba."
"To ke Beebah ba sai ki cire kanki a lamarinsa ba ki fidda masu sonki tunda shi ya sami mata."
"Bazaki gane wani kalan so na keyi masa ba wallahi ba dan kudi da kyawunsa ba ne na kamu da k'aunarsa, tun ranar da nagansa naji fad'uwar gaba kuma tundaga ranar duk in mun had'u sai na shiga yanayin daburcewa, tun ban gano dalilin ba har nagano sonsa na ke yi."
"Ikon Allah sai ji da gani."
"Kin nan me?"
"Sai kin fad'a."
"Duk cikinmu yafi yimin magana ko yanzu mafi yawancin shirye-shiryen bikin shi Momynmu zatayi wanda ni ya d'ora a kai na nemi shawararta ta ce in bar mata komi a hannunta daga nan fa ya maida gidanmu wurin zuwarsa ni kuma anan na kuma kamuwa da kaunarsa matsananci saboda yarda ya ke shigemin ko nak'i fitowa idan ya zo sai yanemi izinin momy ya biyoni d'akina shi yasa na daina gudu duk in ya zo sannan gashi ya iya tsokana irin ta abokannan wasa sai dai in yana yimin daburcewa na keyi sam ban iya maida masa da martani inda zai ta kirana da 'yar k'auye mai kunyar maza, wani zubin Momy ce zatayi ta taremin."
"To shima yana sonki kenan?"
"Ko d'aya, haka yakeyiwa dukkanmu sai dai kafin ya kirasu ne ya kirani sau ba adadi."
"Amma naga ko sau d'aya banga kunyi wayata ba."
Nunomin wayarta ta yi naga Miss call barkatai.
"Kullum sai ya kirani wani in amsa wani in share saboda haushin auren da zaiyi."
Dariya na kyale-kyale da shi ta tale baki tamkar zata fashe da kuka.
"Sorry dear in baki shawara?"
"Eh."
"Ki rik'a amsa kiransa inda hali ke ce zaki soma kiransa sannan ki b'oye kishin nan ta gaibu domin wanda kikeyi bai sani ba, ki nemi zab'in Allah ba son zuciyarki ba, in har mijinki ne da kansa zai furta miki k'auna."
"Nagode da shawara amma da kamar wuya hakan ya faru kawai ni ce zan ambatawa Kaka ina son shi na tabbata aurenmu zai k'ullu cikin ruwan sanyi "
"Ban amince kiyi haka ba saboda naji masu iya magana sunce matar shige bata daraja, gara ya furta da kansa."
"D'an boko ne da makar wuya ya zauna da mata biyu."
"To ki hak'ura da shi mana ki rik'e Yaya Abdul."
"Wannan kam ko mu biyu muka rage a duniya ba zan tab'a aurensa ba, nayiwa kaina wannan alk'awarin."
"Tsana in ya yi yawa mafi lokuta k'auna ke komawa, to dan Allah ki barwa Allah lamarin sai ya zab'a miki mari alkhairan."
"Insha Allah zan mik'a lamarin ga mai zab'awa bayi duk abinda yafi zama alkhairi a garesu."
"Da kyau tawan."
Murmushi mukayi tare da tafawa. Gyaran murya Fanta ta yi muka kalleta tsaye bakin k'ofa ta kafe Beebah da ido.
"Me ye?"
"Kin tsargu ne? To babu komi sai dai ni ce ta uku wacce ta san makauniyar soyayyar nan."
Dak'uwa ta yo mata muka fashe da dariya.
"Wallahi Aunty Beebah da a ce Yaya Mubajjal zai aureki da zance kunfi dacewa akan Aunty Hajara nan mai k'aton goshi da uban salo wai ita 'yar boko."
"To sannu 'yar son kai."
"Serious aunty Beebah, kun dace da juna kuma zan tayaki addu'ar Allah ya baki shi a matsayin miji."
"Amin 'yar uwa nagode."
"Sai dai wani hanzari ba gudu ba maganar fidda miji da Dady ya yi miki yana nan fa ba d'aga k'afa, shin ya zakiyi?."
"Ki bari kawai 'yar uwa babban DAMUWATA yanzu wannan maganar ce ga Momy ta goya masa baya shi yasa na ke jin tamkar kada in koma."
"Ga shawara ki kira Yaya Mubajjal ki sanar masa tare da neman shawararsa ko ki nuna masa ya nema miki alfarma wurin Dady da ya k'ara miki lokaci tunda kuna d'asawa ba zai juya miki baya ba."
"Good idea Aminiyata."
Na ambata cikin jinjinawa Fanta.
"Kuna ganin in aikata hakan?"
"Eh amma shawarar k'arshe na ya nema miki alfarma Dady ya k'ara miki lokaci kawai zakiyi masa. "
"Tam shi kenan, anjima zan sanar masa naji abin da zaice."
"Allah ya sa ya ce zaki aureni Habibatu."
Rungumeni ta yi cikin cewa "Da na kwana yi miki addu'ar gamawa lafiya da barin miki kyautar Umrar da Uncle ya yi min."
"Oh Aunty Beebah ba kunya."
"Amsa naki Fanta."
Ta watso mata d'ak'uwa cikin tsare gira.
Dariya muka sanya cike da nishad'i.
***
Washe gari tunda subahi kiran Uncle ya tashemu inda ya sanar da Beebah ta shirya shi zai kaisu. Ina azkar duk jikina a sanyaye na jin zasu tafi.
Sabo akace turken wawa to hakan ya faru gareni domin yinin ranar ko murmushi banjin na yi ba tun Mama da d'aukan abin da wasa har ta ga da gaske na ke sai ta koma bani baki amma duk da hakan ban dawo wal-walata ba na dai rage tsare gira. Fanta dama tunda taga ina hawaye ta fice ban sake sanyata a ido ba.
Misalin k'arfe uku na rana muna zaune saman tabarma Mama na damamin furar Tamba wanda Hajiya Inna ta aikomin da shi, muka tsinkayi sallama atare muka amsa wata Mata mai jiki tana da haske dai-dai misali ta shigo tare da matashiyar budurwa wacce kallo d'aya na yi mata na gano k'anwar Aliyu ce saboda kamarsu da juna har ya b'aci duk kuwa da tana fara shi kuwa bak'i.
Cikin girmamawa Mama ta basu wurin zama yarinyar ta zauna ta gaisar da Mama tare da yimin ya jiki na amsa cikin murmushi saboda naji dad'in ganinsu.
Matar kam tsaye ta yi k'erere tana jifana da wani kallo wanda ya saukemin kasala tare da bugun k'irji, gaisuwar da na ke nufin yi mata nakasa aiwatarwa, alokaci d'aya na nemi farin cikin ganinsu na rasa.
Mama da bata lura da kallon ba ta tafi d'auko musu abin motsa baki.
"Ina yini?"
Na furta cikin jajircewa.
"Mahaifiyar Aliyu ce dafatar ya sanar miki zuwana?"
Ta maidomin da amsar gaisuwar ta bayyanamin kanta.
"Eh, kunzo lafiya?"
"Ba damuwarki ba ne wannann."
Da sauri na kalleta ta zaromin manyan idanunta kauda kai gefe na yi ina jan addu'ar duk da yazo bakina.
"Na zo yi miki kashedi ne a kansa, ki rabumin da d'a ba zai aureki ba na zab'a masa wacce ta dace da shi domin auren zumunci zaiyi da d'iyoyin ar...
"Akul! kika nemi aibatamin d'iya akan idona Hajiya Asiya, tunda dai kin fad'i abin da ya kawoki to fice min a muhalli tun ranki baifi nawa b'aci ba."
Cikin fushi Mama ke maganar wanda na hango mamaki a idanun wacce ta kira kanta da mahaifiyar Aliyu jin kalamin Mama
"Ni kike kora a gidanki?"
"Ya wuce kokwanto, maza ficemin ko in sanya afitar da ke kuma idan kin isa da d'anki kada na sake ganinsa a k'ofar gidana balle ya shigomin muhalli."
"Haka kika ce?"
"Eh."
"Kin tabbata d'iyarki ta rabumin d'a kenan na har abada?"
"Ko a lahira bana fatar Uwata ta had'u da d'anki."
"Masha Allah, abu yazo cikin sauk'i, nabarki lafiya."
Banza Mama ta yi da ita illa nuna mata hanyar ficewa da ta yi.
"Hajiya ba haka kukayi da Yaya ba dan Allah ki ba su hak'uri dan d'anki zaifi cutuwa."
"Zaki tashi mu tafi ko sai na sab'a miki?"
Da sauri Salma ta mik'e suka fice na kalli Mama ta watsomin harara sai na tashi da sauri na shige d'akina ina jin zuciyata tamkar zata fad'o k'asa.