DAMUWATA

22

by @mrsjmoon


Page 22.


"Dan Allah ki fito waje zuciyata na koma ga mahallicina ko na huta da wannan rayuwa mai cike da damuwa kala-kala, shin wai meye dalilin zamowata mara sa'ar rayuwa ce? Ina burin gabatar da rayuwa mai cike da kwanciyar hankali tamkar sauran mutane? Wayyo ni Nana Khadijatu ina zan saka kaina? Mahaifina bai bar ruhina ya sami natsuwa daga wasi-wasin shi d'in uba na ne ko zaman agolanci na ke yi a k'ark'ashinsa ba sannan ga saurayin da na sama bayan tsawon lokacin dana kwashe ina geben samun abokin rayuwa Mahaifiyarsa ta jagoranci rabuwarmu duk da na soma fidda shi a raina amma banso rabuwarmu ya zo ta wannan sigan ba. Ina da tulin tambayoyi a gareki Mama dan Allah ki amsamin su ko natsuwar da na ke nema ya rab'eni. Ya Salam, ya rabbi ka kawomin d'auki badan halina ba. K'alu Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, Allahumma ajirni fi masibati wa khalifni khairan minha."


Sune kalman dana rik'a ambata cikin matsanancin kuka hannayena duka biyun dafe da k'irjina wanda na tabbatar bana rabuwa da Aliyu ba ne domin ina jin wani sabon lamari na daban zai sameni wanda zanyi kukan shi yasa na bud'e baki ina yinsa tamkar wacce aka aikowa da sak'on mutuwar Mama. A k'arshe zamewa na yi na kwanta saman sallaya ina cigaba da kuka amma mara sauti saboda yin mai sautin zai janyo hankalin Mama saidai duk da rage sautin bai hanata jiyowa ba.


Ina jin shigowarta nak'i motsawa tana d'ora hannunta a gadon bayana sabon kuka ya kubcemin na fashe da mai k'arfi sosai cikin jijjiga. Hannunta ta soma yawo da shi a bayana a hankali ba tare da ta yi magana ba, ina ji a jikina itama kukan ta keyi mara sauti, d'if na d'auke nawa tare da tashi zaune da hanzari na fad'a jikinta ina cewa "Natuba Mama dan Allah ki yafemin ba burina kenan ba na sakaki kuka lamarin ne ya dameni dole saina zubda jirwaye zan sami natsuwar jiki da ruhi, dan Allah kada kiyi fushi da ni, natuba Mamana, kiyi shiru dan girman Allah, zubar hawayenki dafi ne a gareni dan Allah kibari kada wani abu mara kyau ya sameni sanadin kukan nan."


"Banyi fushi dake ba Uwata kuma ba kuka na ke yi ba fatana ki sanya salama cikin ranki dan samuwar lafiyarki sannan kada kiyi zargin na jagoranci rabaki da mosayinki ne saboda da wata manufa tawa a'a sam ba haka ba ne ina dai burin kiyi rayuwa ce mai cike da 'yanci wanda zaki sakata ki wala a gidan aurenki ba wanda zaki dawwama cikin k'unci ba bisa takurawar uwarmiji wannan dalilin yasa na datse alak'arki da Aliyu kuma idan har na isa na fad'a ki ji to daga yau babu ke babu Aliyu har abada sunarsama bana son ki sake ambata koda a cikin zuciyarki ne, burina ki kasance tamkar baki tab'a sanin shi ba balle ki tuna kun tab'a musayan kalaman k'auna."


"Mama...


"Uwata hakan na ke buk'ata da ke, hatta da makaranta da kuke had'uwa kin daina zuwarsa kenan domin na tsani mahaifiyarsa da shi kansa tunda ta sanya Uwata zubda hawaye a kan idona sannan ta nemi aibatamin ke da kalma mafi muni da natsani jinsa."


"Mama na hak'ura da shi tun kafin zuwar wannan lokaci kuma insha Allah zan ciresa a babin rayuwata sai dai ina rok'on da ki janye kalman tsana ga Aliyu saboda baiyi komi ba ko ba komi ya so Nana Khadijatunki da zuciya d'aya, ya karya bak'in tarihin nan na tana da bak'in jini ta rasa mai furta mata kalman so."


"To Uwata na jenye harma da Mahaifiyar masa duk na yi hak'uri irin wanda Allah da Manzonsa duke son mumunai nagari sunayi wato hak'uri mai kyau."


Sunkuyar da kai na yi ganin tana kallona cikin murmushi ga hawayenan cikin kwarmin idanunta suna daf da zubowa. Ban d'agoba na mik'a hannu na share mata hawayen, ta rik'e hannuna gam na d'ago da sauri ta motsa kai, matsowa jikinta na yi ta saki hannuna na samu damar shigewa na lafe, bubbugamin baya ta soma tamkar uwa na rarrashin 'yar yaye.


"Mama tun jiya na soma cire Aliyu a ruhina saboda... Na sanar da ita duk abin da ya faru zuwar matar Kawu Habibu dubani da zantukan da mukayi da Hajiya Inna.


"Alhamdulillah, Allah ya zab'a miki mafi alkhairi."


"Amin Mama." 


Na amsa a hankali cike da kunya ta shafi sumar kaina cikin cewa "Taho muje ki tayani aiki domin zama wuri d'aya na janyo tunani mara tushe da fatan ban takura Uwata ba?"


"Mama kekoh."


Na ambata a shagwab'e.


Hanncina ta ja na d'auke numfashi cikin sigan wasa ta saki da sauri na fashe da dariya tana tayani.


"Allah ya cigaba da albarkatan rayuwarki Khadijatu."


"Amin Mamana."


Fitowa mukayi Mama ta yi ta yimin hira mai sanya mantawa da duk kan damuwa.


"Uwata yau Litini insha Allah jibi laraba zamu tafi Kwara dubo jikin Babana."


"Allah ya kaimu Mama."


"Amin."


"Gobe zamuje yi masu tsaraba da fatan zaki iya shiga kasuwa?"


"Zan iya Mama."


"Madallah, anjima Habibu zaizo muje shagunana domin ina son saidaasu na had'esu ya zama babba guda d'aya kamar super market."


"Masha Allah, Allah ya taimaka."


"Amin, zan dank'a a hannunsa dan hakan zai fi akan yawo da hankalin da masu hayan keyimin ko ba komi shi nawane, da wasu su cinyemin gara shi ya ci ya more."


"Hakan ya yi Mama, Allah ya yiwa nema albarka ya taya Kawu Habibu rik'o."


"Amin."


"Jiya an sami masalaha tsakanin Alhaji Muhseen da Malam ina fatar nadamar da na hango a idanun Malam ya zamo na gaskiya ne."


"Amin ya rabbi."


Shiru ya ratsa wurin na dubeta kad'an ta motsa kai alamun tana saurarona.


"To Mama kin hak'ura da zancen dukiyanki na wurin Baba ko?"


"A'a bazan hak'ura ba dan zaman jiya har da shi aka tsaida maganar ina dawowa daga Kwara zai dank'amin kayana domin lokacin yin amfani da su ya yi dama an bashi ne ya ajiye amatsayinsa da shugabana sai ya nemi a bashi damar ya juya zuwa sadda za'a nema to lokacin neman ya yi."


"To Mama idan baya da shi fa?"


"Na sanar miki yana da gidan gona wanda da kud'ina ya mallaka haka ya siya gonaki duk da kud'in yanzu haka takardun gonakin jiya Baba Umaru ya amsa daga hannunsa gidan gonar kuma zaiyi masa kud'i Habibu zai siya sai a had'a da gonakin a lissafa in sun kai adadin kud'ina in kuma sun wuce sai abashi ragowar hakk'insa."


"Kuma duk Baba ya amince cikin ruwan sanyi?"


"Eh saboda Baba Umaru ba sa'ar wasanshi ba ne sannan komi da akayi anyisa ne a rubuce tare da shaidu. Idan komi ya kammala filin da ke kan layin su Baba Umaru za'a siya a gina babban Mall wanda zai kasance babu ce kawai ba'a siyarwa."


Dariya na sanya cike da jin dad'i na ce "Da sai in zama shuga mai bada umurni."


"Allah dai ya cika mana burinmu Uwata domin komi da kikaga inayi to dan ingantuwar rayuwarki ne, kada k'asa ya rufe idona Malam ya handame komi ya koramin."


"Godiya na ke Mamana amma dan Allah ki kyautatawa Baba zato."


"To naji amma ki sani ba godiya a tsakanin Uwa da 'ya sai addu'ar samun babban rabo ranar lahira."


"Allah ya biyaki da gidan aljannatul firdausi."


"Amin ya rabbi."


"Yawwa Mama wai ya muke da Baba Abdul Ganiyu nan?"


Shiru ta yi har na cire rai da jin amsar tambayar sai kawai na kamo hannunta na langab'e kai cikin sanyin murya na ce "Kiyi hak'uri Mama idan sanarmin zai takuraki wallahi na fasa jin nasabanmu da shi."


"Zan sanar da ke amma a takaice domin zuwa yanzu ya kamata ki soma sanin ya ni ke da duk wanda kika ganmu tare."


"To Mama Ina saurarenki."


"Kinga Baba Abdul Ganiyu abokin mahaifina ne na k'ud da k'ud amma shi bayarbene ya yin da Mahaifina Abdullahi ya zamo Hausa Fulani d'an asalin garin sokoto. Sadda Allah ya nufa zan zo garin Kaduna da zama Baba Abdul Ganiyu ne ya had'ani da Baba Umaru wanda shi kuma ya zamo abokin kasuwancinsa daga arewa zuwa kudu. Baba Umaru ya rik'e ni tamkar shi ya haifeni dan haka wad'an nan mutanen biyu bani da kamarsu in kika cire mahaifana, Abdaullahi da Hadiza da kuma ke 'ya ta."


"Allah ya kai haske k'abarinsu."


"Amin."


"To Mama ina danginmu na Sokoto?"


"Suna nan."


"Me yasa ba...


"Uwata kada ki tsananta bincike domin na yi miki alk'awarin sanar da ke komi idan lokacin ki sani ya yi."


"To Mama na kame bakina."


"Da kyau, idan zaki sha furanki tana cikin fridge."


Murmushi na yi jin ta sauya akalan zancen.


"Ko sai zuwa dare zaki sha?"


"A'a zan sha yanzu, bari in d'ibo kad'an."


"Aha, sai ki zuba zuma zaifi dad'in d'and'ano akan saka siga."


"To Mamana."


Ina shan furar na dubi Mama wacce ke gyara zogale zata dafa mana wanda Hajiya Inna ta aikomin da shi domin na ce kwad'onsa na ke son ci da dare.


"Ya dai Uwata?"


Lashe lips na yi na amsa da "Ina burin na ganni cikin danginmu duk da bana son hayaniyar jama'a amma son ganina tsakanin kakanni, iyaye da abokanan wasa maza da mata wannan babban buri ne da ya jima a ruhina sai dai idan na nutsa cikin tunani sai wani lamari da na rasa gane kansa ya zo ya shafe burin ta hanyar jefani cikin fargaba har sai na ji ban son ganina cikin dangin baki d'aya sai na rik'a jin dama banzo duniyar ba."


Banza Mama ta yi da ni domin tunda na fara maganar bata nuna zata furta kalma ba. Na matso jikinta na jingina ina sauke numfashi, still bata kulani ba sai na gyara zama a gabanta na ce "Zanso idan mun dawo Kwara mu tsaya a Sokoto inda halima ki barni a can na zaga dangi na birni da karkara dan samun ladar zumunci."


"Allah ya kaimu lokacin amma zuwa Sokoto ba yanzu ba saboda ko wani tafiya nasa daban na ke son yi."


Jinjina kai na yi ina wasa da ganyen zogalen da ta tsinke.


"Uwata da magana a bakinki ko?"


Kallonta na yi ta waremin idanu cikin jiran abinda zan fura sai na girgiza kai tare da tashi na shige d'akina ina murmushi.


"Nana Khadijatu kenan, Uwata ta kaina, nasan damuwarki bai wuce zantukan da kika gamayi na yi banza da ke, affuwan Uwata bana da jarumtar biye miki ne."


Mama ta furta tare da mik'ewa ta shige madafi.


***

*Asabe da Hinde.*


Asabe ce zaune a k'ofarta ta tsefin kai wanda da kyar ta ke kamo bindin korar saboda tsabar tsufar da ya yi gami da datti, Hinde kuwa tana nesa da ita tana gyaran gyad'an miya.


"Hinde wallahi duk tijarar da na gani gami da iziya a hannun masu babbak'un kaya ban saduda ba ko misk'ala zarratin domin sai naga bayan Hurera kafin k'asa ya rufe idanu zanji dad'in a raina."


"Yaya tamkar kin shiga zuciyata, tunanin da na keyi kenan yanzu, wallahi da abin na ke kwana na ke tashi musanman mijin da Uwani zata aura, gashi mutumin kirki sam abinsa bai rufe masa idanu ba da ganinsa ya san abinda yakeyi, hak'ik'a zataji dad'in zama da shi, Hurera zata huta fiye da zatona, zata tabbata cikin jin dad'i mu kuma 'yan maula domin ko Malam sai yarda ta yi da shi dama ya lafiyar giwa balle ta yi hauka."


"Hinde kin sosamin inda keyimin k'aik'ayi, billahil azim ji na ke tamkar in wayi gari acemin Alhaji Muhseen ya mutu na rantse da sai na yi rawa da juyi dan Hurera taga samu taga rashi kenan a lokaci d'aya."


"Ai idan zaki bani had'in kai na rantse sai dai ya auri wata amma ba Uwani ba, domin nafi jin takaicin ni'imar da zata shiga muna kallo tamkar tumakai."


"Ina tare da ke 'yar uwa, tunda mun samu ya yi mana yayyafin naira muyi jari to mu had'esa kaf mu fantsama neman sa'ar datse wannan bak'ar alak'ar domin ba zan kirashi da fari ba."


Wata dariya Hinde ta b'arke da shi wanda ya bawa Asabe tsoro ta shige d'akinta da gudu biyo bayanta Hinde ta yi tana cigaba da dariyar tamkar ta sami tab'in hankali nanko ras ta ke tsabar jin dad'in kalaman Asabe ce.


***

"Yaya Aliyu kabi umurnin Hajiya domin ta yi rantsuwa ba zaka auri kowa ba sai Amira."


Numfashi ya sauke ya kafe Salma da ido "Me Hajiya ta aikata a gidan su Khadija wanda ya janyo ta sakani a black list ko na kirata bai shiga na ganta a online na yi mata magana ta yi blocking d'ina na sanja layi na kirata tana jin muryana ta kashe na tura sak'o ta wayar K'awarta Fanta ta k'i dawomin da amsa, maza sanarmin da abinda Hajiya ta aikata musu da ya janyo na fuskanci wannan lamarin.


"Kayi hak'uri Yaya ba zan iya sanar maka ba saboda nayiwa Hajiya alk'awarin kame bakina."


"Zanje gidan yau da kaina in yaso zanji komeye a bakinta."


"Kada kaje saboda Mamanta ta fusata zuwanka zai zamo zubewar mutuncin Hajiya ce domin ta ce idan ta isa da kai ta hanaka zuwa gidan, kenan zuwanka tamkar Hajiya bata isa da kai ba ne."


"Duk me ya kawo wannan zantukan daga zuwa dubiya?"


"Wanna tambayoyin Hajiya ke da amsoshinsu kuma ya kamata ta amsa maka domin ina zargin da abinda ta ke b'oye mana wanda ya shafi Khadija domin da kunnuwana na ji aunty Zainab na yi mata rantsuwa akan wani abu na so jin abin amma Hajiya ta sauya zancen tare da rufeni da fad'a dan na nemi k'arin bayani."


"Zainab zan sama naji munafuncin da ta k'ulla domin tunda ta gano Khadija ce wacce na ke so na hango tsanar lamarin a idanunta, kuma wallahi idan ta yi sanadin rabani da wacce na ke so rayukanmu zasu b'aci matuk'ar b'aci."


"Kabi komi a sannu Yaya amma ina ji a jikina Deejah ba matarka ba ce."


"B'acemin da gani ko in nad'a miki duka! Wawiya kawai wacce ba'ajin alkhairi abakinta sai sharri."


"Ni d'in Yaya?"


"Zaki fice ko sai na zubda miki da hak'ora?"


Cikin fushi Salma ta bar d'akin tamkar zata saka kuka.


"Ina cikin tsaka mai wuya ni Aliyu."


Ya furta tare da sake dialing number Fanta haka ya gama ringing ba'a d'aga ba, kwanciya ya yi na cigaba da kiran wayar amma baiyi dacen an d'auka ba balle ya rok'eta ta had'ashi da Deejah.


"Why Hajiya? Kin san yarda na ke jinta a ruhina kuwa? Wallahi ba zan auri wacce kike muradi ba domin ban tab'a kallonta a matar da zan aura ba sai k'anwa."


"Zakata tabbata ba aure kenan in har baka auri d'iyar d'an uwana ba wallahi ba zanyi kaffara ba kai da aure sai in anayi a lahira sai dai kuma in zakayi ba da sa albarkana ba wannan kam sai ince na barwa duniya kai babu ni babu kai har abada."


"Hajiya me yasa kika sanja daga mai k'aunar farin cikin 'ya'yanki zuwa kishiyarsa?"


"Son k'ulla zumunci ya sanjani kuma ba zan tab'a dawowa ba dan haka zab'i ya rage ga mai shiga rijiya, walau kayimin biyayya ka auri jininka Amira ko ka band'aremin na barwa duniya kai tare da yima tofin jeka ka gani."


"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un! Hajiya wai me ye haka kikeyi?"


"Idan ka gama yanke shawara ka sanarmin wallahi ba zan matsa maka sai ka so cikar burina ba amma dai ka tuna zab'i biyu na baka kuma duk wacce ka d'auka zan amsa da hannu biyu."


Tana fad'ar haka ta fice daga d'akin.


Kuka ya fashe da shi mai sauti baya ko jin kunyar k'anninsa su jiyo shi.


"Zainab!." 


Ya ambata cikin kaushin murya. Wayarsa ya laliba ya doka mata kira bugu d'aya ta d'auka cikin karad'in cewa "Angon Takwara my in-law kana lafiya?"


"Abinda kikayimin Allah ya yi miki fiye da shi, Allah ya sanyo k'unci a ruhinki sama da wanda kika jagoranci dasamin, Allah ya kawo sanadin da mijinki zai gano b'oyayyen halinki na raina masa Mahaifiya, Allah ya karya k'adarinki ki gamu da gamonki ta hanyar da bakiyi zato ba."


"Me ke damunka Aliyu?"


"Allah ya isa tsakanina da ke kuma k'anwarki ba dai taji dad'in zama da ni ba, wawiya kawai bulutu mai saka khairan da sharran."


Kafin ta sake furta kalma ya datse kiran.


Sai numfashi ya ke saukewa cikin furzar da huci, key d'in mashin nasa ya d'auka ya fice tamkar zai kifa.


Zainab kam kuka ta fashe da shi cikin durawa Aliyu zagi tamkar ba yayata ba, ganin hakan baiyi mata ba ta kira Hajiya ta rattafa mata k'arya da gaskiya.


Shiru Hajiya ta yi bata da niyyar cewa komi saboda yarda ranta ya b'aci.


"Hajiya wallahi in wani abu mara kyau ya sameni bakin Aliyu ne."


"Zaizo har gida ya baki hak'uri d'iyata, ki daina kuka insha Allah ba abinda zai sameki sai alkhairi."


"To Hajiya nagode."


"Na ce ki daina kukan nan."


"Na bari."


"Da kyau, ki shafamin kan jikalleta."


Bata amsa ba Hajiya ta kashe wayar tare da neman Aliyu aka sanar mata wayar a kashe ne. Tsaki ta ja ta cije leb'en k'asa cike da takaicin rashin samunsa.


Aliyu kam na fita gidan su Deejah ya nufa sai dai ya aika yara har uku ana dawo masa da amsar bata nan alhalin duk in ya tambayi yaran sun ganta suna amsa masa da ita ce ta ce a ce masa bata nan. Garin yaji na juya masa ya samu dakali ya zauna ya tsirawa bishiyar ced'iya da ke nesa da k'ofar gidan ido tamkar mai irga rassanta nan kuwa lulawa ya yi cikin tunani.


"Kai! Me kakeyi a nan?"


Muryan Baba ya katse masa tunani.


Firgigit ya yi tare da zubewa yana gaisheshi.


"Lafiya, daga ina?"


"Abokin karatun Khadija ne."


Ya sami kansa da furta hakan.


"Oh bari aturo maka ita dan nasan kazo gaisheta sa jiki ne ko?"


"Eh, Baba."


"To jirata."


Da idanu ya raka Baba yana zabga masa albarka a cikin ransa. Yana tsaye na fito fuska a had'e. Wawan ajiyar zuciya ya sauke ya taho da hanzari tamkar zai rungumeni na koma da baya cikin zaure da sauri ya rufa min baya, ganin zan koma cikin gida sai ya rik'o hijabina na juyo idanuna na zubar hawaye na had'e hannayena alamun rok'o na ce "Dan soyayyarka da fiyayyen halitta Aliyu ka rabu da ni rabuwa ta har abada."


"A'a Khadija, kada kiyimin haka, ruhunanmu bazasu d'auka ba dan Allah ki saurareni."


"Aliyu lamarin mahaifiya dabanne da na kowa dan haka na ke baka shawara da kayi mata biyayya tamkar yarda na yiwa tawa Mahaifiyar na tabbata zamuga haske cikin rayuwarmu."


"Khadija kin amince zaki iya rabuwa da ni?"


Shiru na yi masa saboda bakina ya yi nauyin amsawa Amma ba wai dan bazan iya amsawa da a'a ba ne sai dan ina ganin cin kuska ne na amsa masa kai tsaye.


"To ni bazan iya hak'ura da ke ba ki rubuta da k'aunarki zan koma ga mahaliccinsa."


Kuka ne ya kufcemin ganin yarda ya ke furta kalamin da iya kacin gaskiyarsa.


"Koma ciki kai kuma tafi kayiwa mahaifiyarka biyayya dama Uwani ba sa'ar aurenka ba ne Allah ne ya baka ita har ta soma kulaka sai kuma somuwar Uwarka ta yi sanadin b'ata komi saboda son zuciya."


Tsit mukayi muna kallon Baba da ya shiga tsakiyarmu ya raba tsakaninmu yana mazurai.


Hannun na d'aga masa alamun bye na shige gida da gudu shi kam zubewa gaban Baba ya yi ya ce "Baba kayi wani abu akai wallahi jna sonta, itama tana sona."


Mik'a masa hannu Baba ya yi Aliyu ya zaro idanu kai Baba ya gyad'a.


"Ban fito da kud'i ba Baba kayi hak'uri zan kawo maka."


"Zaka iya tafiya kuma wannan shi ne rana ta k'arshe da zaka sake zuwamin k'ofar gida tunda matsiyaci ne kai."


"Baba kayi hak'u...


"Kaci Uban Uwarka mataccen nan na ce kaji ko?"


Baba ya gabgowa Aliyu zagi cikin nad'e hannun riga, alamun zai bugeshi.


Da gudu Aliyu ya fito zauren ya kunna mashin d'insa ya bar unguwar amma yana jin aransa ba zai iya rabuwa da Deejah ba.