ZANEN ZABUWA

Chapter 16

by @nanahaleema11

*ZANEN ZABUWA*


      ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1

*Page 16*




Murmushi yake har ya k'araso inda motar take ya bud'e ya shiga ya kalli Jannat da take kallon sa itama ya sake sakar mata murmushin masoya yace, "ya na ga kin canja? Lafiya dai ko?."


D'an yamutsa fuska tayi tace, "fad'uwar gaba nake ji sosai na rasa dalilin hakan, mu bar wajan nan dan Allah maybe ko kukan dabbobin nan ne yake sani." Kunna motar yayi tare da fad'in, "an gama ranki ya dad'e" ya fad'a yana jan motar suka bar cikin gidan gonar.


Tafiya sukeyi hankalin sa na kan titi ya d'an juyo kad'an ya kalle ta yace, "Jaana na tambaye ki wani abu?." Kallon sa itama tayi tace, "ina jinka."

"Yanzu a misali bikin mu ya kusa kamar saura sati biyu ko d'aya haka sai Yayan ki Imran ya bayyana ya zakiyi?."


Sai da ta runtse ido ta bud'e sabida fad'uwar gaba ta d'auke kanta daga kallon sa tace, "farin ciki zanyi da dawowar sa sosai zanji dad'i kuma ace dashi za'ayi biki na." Murmushi yayi kawai baice komai ba jin ya samu amsar da yake nema ya cigaba da tuk'in sa.


Har suka k'arasa gidan su Jannat hira suke sama-sama cikin nishad'i da shauk'in soyayya, a can nesa ya faka motar ya kalle ta yace, "bana so na k'arasa dake k'ofar gida Abba yayi fad'a nafi so na fara gabatar masa da kaina matsayin sirikin sa kafin ya kuma ganin mu tare." Cikin gamsuwa ta d'aga masa kai kawai dan haka kawai jikin ta yayi sanyi suka yi sallama ta fita ta k'arasa ya bita da kallo cikin so da qauna.


Cikin farin ciki Muhsin ya isa gida yayi parking ya shiga gida akayi sa'a Daddy da Mummy suna zaune Mufeedah na tsakiyar su da alama rarrashin da aka saba yi mata kullum suke yi.


Zama yayi a gefe guda yana murmushi Mummy ta kalle shi tace, "Muhsin any gist?." Murmushi ya sake yi ya gyara zama yace, "finally na samu matar aure." Kallon juna Daddy da Mummy sukayi Daddy yace, "Masha Allah, a ina take? Y'ar waye?."


Murmushi ya kuma yi tace, "ba y'ar kowa bace infact iyayen ta talakawa ne." Daddy ya had'e fuska yace, "ban gane ba me kake so kace min?."

"Abinda nace mana Daddy, daman ni bana ra'ayin auren mace from rich family nafi so na auri wacce na fita da komai yadda komai na bata zata karb'a tayi godiya."


Mummy tace, "Muhsin kana cikin hankalin ka kuwa? Ka manta Bilkisu y'ar governor garin nan she loves you so much ka tsallake kaje ka d'auko mana y'ar talakawa? Dame zamu k'aru da ita?." Tamke fuska yayi yace, "Mum ni bana son wannan yarinyar na fad'a miki tun ba yau ba, wacce na fad'a muku ita nake so kuma ita zan aura, abinda nake niyar yi ma ai shine zai k'arawa Daddy kima a idon talakawan gari har su sake zab'en sa nan gaba, zasu ga d'an sa na cikin sa ya d'auka ya aura masa y'ar talakawa waccce basu da komai kowa zaiyi ce yeah Daddy yana son talakawa tunda gashi ya aura masa ita ba k'yama balle hantara."


Daddy da yake sauraron sa ya tafa hannu yace, "I'm very lucky da Allah ya bani yaro mai mutuk'ar basira kamar ka Muhsin, abinda ka fad'a haka ne tabbas talakawa zasu ga ban k'yamaci irin su ba tunda har na aura maka ita kuma ko iyayen ta dalilin hakan dangin su da dama dey vote for me a zab'e me kamawa, good idea son."


Mufeedah da take jin su ta kalli Muhsin da mamaki tace, "U want to get marriage from poor family but ni kaca bazan auri talaka ba, tunda haka ne indai zaka aure ta nima dole a aura min shi da zarar Allah ya bayyana shi in ba haka ba kaima wallahi baza ka aure ta ba."


Muhsin ya d'ora k'afa kan d'aya yace, "Ni in in na aure ta zan inganta rayuwar ta cos nine mai kud'i ina da halin da zan bata rayuwa mai kyau but kefa,? Bashi da komai wata k'ila bashi da halin da zai ciyar dake kinga kuwa auren ku bashi da amfani."


"Exactly abinda ka fad'a haka yake son, but itama tunda tana son sa zan inganta rayuwar sa na bashi jari wanda zai iya rik'e min ita cikin farin ciki amma fa da sharadin ita kad'ai zai zauna da ita babu kishiya, bazan kai yarinya ta gidan kishiya indai yana son ta sai dai ya zauna da ita kawai in kuma yace a'a sai a barshi."


Farin ciki ya lullub'e Mufeedah ta rungume Daddy tace, "Thanks you Daddy." Abinda tace kenan ta mik'e kamar ba ita ba tayi sama a guje tana ihun murna.


Mummy ta bita da kallon har ta hau saman sannan ta kalli Daddy tana murmushi tace, "Mufeey tana son yaron nan sosai ka duba yadda take farin ciki fa, rabon da naga murmushi akan fuskar Mufeedah har na manta sai naji ina so yaron ya bayyana ta aure shi." Daddy shima yace, "haka nima ina so na ganta cikin nishad'i."


"Kai kuma yaushe zan tura uncles d'in ka suje a nema maka auren ta?." Muhsin ya mik'e tsaye yace, "gobe zanje na sami mahaifin ta daga nan sai a tura, nayi sama." Ya fad'a yana haye sama ya bar iyayen nasa a zaune suna tattaunawa akan lamarin.


Yana hawa saman Salim ya kira yace in yana da lokacin ya shigo da labari shi kuma yace gashi nan zuwa.


Ba jimawa yaji Salim ya shigo gidan ya haura sama wajan Muhsin d'in ya zauna yace, "ya dai na ganka cikin nishad'i haka?." Kallon sa Muhsin yayi yace, "finally nida Jannat mun kusa zama ma'aurata." Salim yace, "Ban gane ba?."

"Abinda nake nufi nida Jannat mun kusa yin aure dan yanzu soyayya tsakani na da ita tayi nisa."


Baki Salim ya bud'e yace, "yanzu sai da ka yaudari yarinyar nan ta fara son ka? Muhsin baka jin tsoron Allah ya kama ka akan hakkin ta?." Mushin ya kalle shi yace, "ni ba yaudarar ta nayi ba zuciyar tace ta kamu da soyayya ta ba forcing d'in ta nayi akan ta soni ba."

"Yanzu naji ita tana sonka kai kuma ba son ta kake ba ko?."

Jingina yayi da kujera yace, "Salim ina son ta son da ban tab'a yiwa wata d'iya mace ba, ban san lokacin da soyayyar ta ta kama ni haka ba sai tsintar kaina nayi a cikin ta a lokacin da tayi min mugun kamu, Salim ina ji kamar in na rabu da yarinyar nan bazan rayu ba wallahi."


Jinjina kai Salim yayi yace, "to tunda kana son ta da zuciya d'aya itama kuma tana son ka ai shine abinda ake fata, amma in ka saki Yayan nata daga hannun ka fa? Kasan dai shi yana son ta koda ita bata son sa."


Ajiyar zuciya ya sauke kana yace, "Zan sake shi ne a lokacin da bikin mu ya rage sati biyu kacal kafin lokacin na gama jiqa iyayen ta da kud'i yadda koda ya dawo ya nuna yana son ta sai dai a bashi hak'uri, kaga baban ta malami ne bazai bari ayi neman aure a kan aure ba, ya kuma riga ya bawa iyaye na auren ta bazai canja yace shi zai bawa ba dan kawai shine ya kula da ita tun tana k'arama, ina so yaga bikin mu da ita yadda zai fahimci ba'a ja dani a zauna lafiya, ina so na saka masa ciwon da bazai tab'a barin sa ba har abadah, ina so ya d'and'ana zafin rabuwar da abinda kake so, ina so yaji zafi fiye da yadda naji a kan fuska ta da zuciya ta lokacin da ya d'aga k'aramin hannun sa ya mare ni."


Salim yana jin sa yana jinina makirci irin na Mushin yace, "Muhsin inda a mace kazo da zan iya cewa kafi shaidan iya makirci, amma abubuwan baka ganin zasu yiwa shi Imran d'in yawa ba?." Murmushi yayi yace, "shi ya sani, ba shi mai zarra ba har ya d'aga hannu ya mare ni ai bai mari banza ba, ya mari fuska ta ni kuma na mari rayuwar sa."


Dariya sukayi suka tafa Salim yace, "to yanzu iyayen nata sun san da kai a k'asa?." Ya sake gyara zama yace, "Sai gobe nake da niyar zuwa na gabatar da kaina." 

"Meyasa sai gobe? Meye amfanin yau da daddare baza muje ba."

"Baiyi wuri ba Salim?."

"Wurin me yayi? Badai ita yarinyar tana son ka ba?."

"Tana so na mana."

"Kawai an jima ka shirya mu je ai da zafi-zafi ake dukan k'arfe."


Cikin gamsuwa yace, "Allah ya kaimu sai muje bayan magrib." Daga haka suka cigaba da tattauna yadda biki zai kasance.


Jannat kuwa tunda ta koma Gwaggo take kallon ta ganin dai murmushi take ita kad'ai komai tana yin sa cikin kazar-kazar kana ganin ta kaga wacce take cikin farin ciki.


Gwaggo bata tambaye ta dalilin farin ciki ba ta basar ta cigaba da abinda yake gaban ta ita ma kuma bata fad'a mata ba, lokacin da Jannat ta koma d'aki ta bud'e jakar ta ta makaranta nan ta tuna da batun kud'in da za'a biya ta ajjiye jakar ta fito falon ta zauna kusa da Gwaggo tace, "Gwaggo daman akwai kud'i da za'a biya na wannan semester da muka shiga a makaranta."


Gwaggo bata tambayi nawa bane tace, "toh ki jira Abban ki in ya dawo sai ki fad'a masa." Kai ta d'aga alamun toh jikin ta yayi bala'in sanyi Gwaggo ta kalle ta tace, "kin tuna Imran ko? Allah sarki bawan Allah yayi d'awainiya dake mai tarin yawa, yayi miki abinda ni da Malam bamu yi ba Jannat, tunda kika fara makaranta bamu san wani abu wai kud'in makaranta duk da hakkin hakan a kan mu yake amma yace mu huta shine zai biya, inda ta mu ne da yanzu ki daina wannan makarantar dan bamu da abinda zamu d'auki nauyin ki har ki gama, Imran yana son ki Jannat ba iya soyayyar y'an uwantaka yake miki ba akwai wani sirri a zuciyar sa wanda Allah kad'ai ne ya san meye shi, baki da masoyin sama dashi duk wanda zai soki a bayan sa yake domin kuwa shi tun kina zani yake son ki, ya amince yak'i ci indai ke zaki ci, ya amince yaki sha indai ke zaki sha, ya amince yak'i sakawa indai ke zaki saka, farin cikin ki shine nasa haka burin ki shine nasa, babu wanda zai biya imran akan hidimar da yayi dake sai Allah, shiyasa baza mu kai goshin mu k'asa mu d'ago ba ba tare da mun rok'i Allah ya bayyana shi ba, ina kuma ji a jiki na Allah ya kusa amsa addu'ar mu."


Jannat tayi shiru tana jin bayanan Gwaggo jikin ta yayi bala'in sanyi hawaye ya fara zuba a idon ta, tabbas tasan duk abinda Gwaggo ta fad'a gaskiya ne baza su iya biyan sa ba sai dai Allah ya biya shi, abu d'aya ne take tantama Anya da gaske akwai wani sirri a zuciyar Imran a kanta? In ma akwai meye shi?.


Mik'ewa tayi jiki babu k'wari tana kuka ta shige d'aki ta fad'a kan gado tare da lalubo hoton sa a wayar ta tana kalla tana kuka tana tuna abubuwa da dama da suka faru tana cigaba da zubar da hawaye.


Haka ta wuni har magarib kamar ba ita ba duk fuskar ta tasa sabida kuka ko magana bata yi sai kallo kawai.


Bayan sallar magariba Abba yana zaune kamar koda yaushe yana jiran lokacin i'sha Jannat da take zaune itama tmtace, "Abba akwai kud'i makaranta da za'a biya na fad'awa Gwaggo tace na fad'a maka." Abba da yake zaune akan sallaya yace, "Nawa ne kud'in?."

"Dubu arba'in ne."

Girgiza kai Abba yayi yace, "dubu arba'in! kuma yaushe ake son kud'in?."

"Daga yau zuwa kwana uku in ya wuce kwana uku kud'in zai k'aru."

"Fad'ar hidimar da Imran yayi dake b'ata baki ne, baki tab'a zuwa kin tambaye ni kud'i da za'a biya na makaranta ba koda kuwa na littafi ne komai shi yake miki, bana tunanin akwai wani wanda zai qaunace ki kamar yadda Imran yake qaunar ki, Allah ya bayyana shi da gaggawa."


Gwaggo tace, "Amin ya rabbi, abinda nima nake fad'a mata kenan d'azu, Imran kota ina shine a sama."


"Shikenan zuwa gobe in sha Allah zan bakin kud'in." Ya fad'a yana kallon ta.


"Allah ya amince." Ta amsa tana gyara zaman ta ya amsa da amin.


Sallama akayi yaro ya shigo yake sanar da Abba wasu samari biyu suna sallama dashi, baiyi musu ba ya d'auki hular sa ya saka ya fita.


Jannat kamar wacce aka yiwa duka haka take jin jikin ta gabad'aya kalaman Abba da Gwaggo sun d'aure ta da jijiyoyin jikin ta koya ta motsa sai sun fad'o mata a rai, A haka tayi sallar i'sha har lokacin Abba bai dawo ba tana niyar tafiya gidan Umma Abba ya shigo ya samu waje ya zauna yace, "Khadijah kema zauna."


Komawa tayi ta zauna Abba ya kalle ta yace, "Ina yaron da ya kawo ki a motar kwanaki?." Gaban ta ya fad'i ta kalli Abba tace, "yana nan." Abba yace, "Shine yazo yanzu yana neman a bashi izini ya fara zuwa wajan ki zance domin yana neman auren ki." Bata san dalili ba sai taji hankalin ta tashi ba d'ago ta kalli Abban nata yace, "daman can kuna soyayya dashi ne?."


Ai da sauri ta girgiza kai alamun a'a tace, "muna dai gaisawa dashi." 

"Yanzu dai ya same ni ya kuma nemi izinin zuwa wajan ki na bashi damar yazo gobe ku tattauna."


Shiru tayi bata amsa ba Abba ya kuma cewa, "Nayi mamaki da ya sanar dani ne d'ana ga Senator Al_Mustapha Bashir Bukar, mahaifin sa shine Senator kano ta tsakiya mai ci yanzu, a kwanakin baya nayi aiki a company mahaifin sa yana da kirki sosai bashi da wulaqanci ko kad'an amma abinda ya saka ni nake tantama shine, anya kuwa bada wata manufa yake son ki ba Jannat?."

Jannat dai tayi shiru bata ce komai ba kanta yana k'asa, Gwaggo tace, "wacce irin manufa kenan Malam?."


Abba ya sauke numfashi yace, "In kika duba a yanzu kaso casa'in cikin d'ari na yaran masu kud'in nan basa auren y'ay'an talakawa sai y'ay'an masu kud'i kamar su, abinda yake bani mamaki me yaja hankalin sa har ya fara son Jannat haka? Anya ba da wani abun yazo ba?." 


Gwaggo tace, "haka ne, amma ni sai nake ganin tunda har maganar tazo gare ka kamar bata wasa bace, ai duk namiji mai hankali in yana son yarinya kafin ya tunkare ta iyayen ta yake fara samu akai sai sun lamunce masa sai ya fara zuwa wajan ta, duk da bamu san mai Allah ya b'oye ba amma kuwa yafi k'arfin Jannat hausawa sunce dai-dai ruwa dai-dai tsaki."


Abba yace, "Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi shine abinda zamu ce kawai, kema kuma ki dinga addu'ar neman zab'in Allah kinji ko?." Ta d'aga kai alamun to yace, "Allah yayi miki albarka, tashi kije wajan Umman naki." Jiki a sanyaye ta mik'e tayi musu sallama ta fita.


Washe gari bata je makaranta ba tana zaune y'an kwalliya guda biyu suka zo hakan ya saka suka shiga gidan Gwaggo ita kuma Gwaggo ta shiga wajan Umma. 


Ta jima bata fito ba hakan ya saka Gwaggo ta dawo a lokacin sai da ta gama sannan ta koma wajan Umma, Bayan ta zauna kusa da Umman ta d'ora kanta a kan kafad'ar ta Umma take ce mata, "yanzu Gwaggo take fad'a min wanda yazo neman auren ki jiya, nayi miki murna sosai Jannat Allah ya daidaita ku, babu wanda baya son ya kai d'an sa inda zai ji dad'i, kowa yana son gidan hutu dan haka indai da alkhairi wallahi ina fatan Allah ya amince" Umma ta fad'a nishad'i a tare da ita.


Jannat ta kalli Umma tace, "au Umma murna kike?."

"Murna nake mana Jannat, meye baya so yaga nasa cikin jin dad'i?."

"Hmmmm." Shine kawai abinda tace ta mik'e ta shige d'aki Umma ta bita da kallo tana fatan Allah ya daidaita su.


Da magariba Muhsin yazo suka had'u da Abba a waje suka gaisa kafin ya shiga ciki ya turo masa Jannat d'in kamar yadda Abban yayi alqawari.


Batayi wata kwalliya ba domin hijjabi ne a jikin ta ta fito da sallaya ta shinfid'a masa a soron ya zauna yana kallon ta kamar ya cinye ta sabida qauna, ganin kallon nasa yayi yawa ya saka ta turo masa baki tace, "Ni ka daina kallo na."

"Kawai kice na makance kenan." Kallon sa tayi tace, "yeah indai har zan daina kallon ki dai-dai yake da na makance."


Murmushi tayi kafin su gaisa tace, "kai da mukayi da kai sai yau zaka zo wajan Abba me ya canja maka tunani kazo jiya?."

"Sonki mana Jaaana, shi ya canja min tunani na kasa kaiwa yau d'in sai da nazo na gabatar da kaina."


Murmushi tayi tace, "aikam naga alama."

"Sai naga kamar bakiyi farin ciki da zuwa na ba."

"Ko d'aya."

"To meyasa na ganki haka?."


"Muhsin kasancewar matsayin ka da nawa akwai banbanci mai tarin yawan gaske wanda ko waye yaji ance kana son aure na zaiyi tantama yaji kamar bada gaske bane, Dan Allah ka fad'a min gaskiyar abinda yake zuciyar ka shin da gaske ne kana sona da zuciya d'aya?."


Numfashi ya fesar cikin nutsuwa yace, "Na rantse miki da Allah Jannat da zuciya d'aya nake sonki kuma auren ki zanyi, wallahi bada wata manufa nake son ki ba Allah ne ya halicci soyayyar ki a zuciya ta dan haka ki kwantar da hankali ki bazan cutar dake ba domin Allah yasan abinda yake zuciya ta."


Ajiyar zuciya tayi cikin jin dad'i tace, "Naji dad'in hakan sosai."

"Nima haka Jaana." Daga nan suka cigaba da tattauwa kafin yayi mata sallama ya mik'e, itama mik'ewa tayi ya saka hannu aljihu ya d'auko rafar dubu hamsin ya mik'a mata yace, "ga kud'in zance."


Murmushi tayi tace, "ka barshi nagode." D'aure fuska yayi yace, "ank'i a barshi d'in, ki karb'a in ba so kike raina ya b'aci ba." Girgiza kai ta kuma yi tace, "Allah ka barshi nagode, in karb'a ma Abba fad'a zai min."

"Bazai miki fad'a ba ai kyauta nayi miki."

"Allah bazan karb'a ba kayi hak'uri." 

Da mamaki yace, "Jaana yanzu nine zan miki kyauta kice baza ki karb'a ba? A tsakanin mu daman akwai haka?."


Shiru tayi tana wasa da yatsun hannun ta bata amsa ba ba kuma ta karb'a ba, ajjiye mata yayi akan sallayar ya saka takalmin sa ya fice ta bishi da kallo dan tasan fushi yayi tayi murmushi tana kallon kud'in. 


Tana tsaye Abba ya shigo ya kalle ta ya wuce ciki dolen ta ta d'auki kud'in da sallayar itama ta shiga ciki.


Zama tayi a gefe Abba yace, "har ya tafi kenan?." D'aga kai tayi alamun eh kafin ta fito da kud'in tace, "Abba ya bani wannan, babu yadda banyi ba amma yace wallahi sai na karb'a k'arshe ma sai ya ajjiye ya fita." Abba ya kalli kud'in kana ya kalle ta yace, "an gode, amma kar ki zaqe wajan karb'ar kud'i a hannun sa domin hakan zai zubar miki da mutunci a wajan sa koda kuma kin aure shi zai dinga ganin kamar dan kud'in sa kika aure shi."


D'aga kai tayi ta mik'awa Abba kud'in yace, "naki ne ai Jannat rik'e a wajan ki." Girgiza kai tayi tace, "A'a Abba ka rik'e ni me zanyi dasu?."

Gwaggo tace, "ki ajjiye a wajan ki ko zaki amfani dasu."


Jannat tace, "sai dai ko na d'auki kud'in makarantar a ciki." Abba ya girgiza kai yace, "A'a biya miki kud'in makaranta a kaina yake ba kece zaki biya da kud'in ki ba, ki bawa Gwaggon ki ta ajjiye miki jn amfani dasu ya tashi kya karb'a. "


Ba musu ta mik'awa ta mik'awa Gwaggo kud'in ba tare da ta tab'a komai ba ta mik'e ta koma gidan Umma.


Dak'yar ta lallab'a Muhsin a daren ya daina fushi da ita bayan tayi masa alqawarin bazai sake yi mata kyauta tak'i karb'a ba.


Muhsin yayi zuwa na uku kafin Abba ya dakatar dashi yace zai neme shi, Jannat na gidan Umma Anty Surayya tazo suna cin abinci ita da Anty Surayya Umma take cewa, "Khadijah ya kike jin shi Muhsin d'in a ranki yanzu?."

D'an yatsine fuska tayi tace, "bana ce ba wallahi Umma."

Anty Surayya tace, "kinga Jannat ki yiwa kanki fad'a domin kuwa wani lokaci dama sau d'aya tak take zuwa a rayuwa in ta tafi bata dawowa, babu wanda baya fatan Allah ya kai nasa gidan hutu da jin dad'i ke kin samu meyasa kike k'okarin watsi dashi?."


Umma tace, "fad'an da nake ta yi mata kenan Surayya, indai har kina son sa ki aure shi in kuma bakya son sa sai a hak'ura ai baza'a so ki auri wanda bakya so ba, dana fara yi mata maganar sai kuka."


Ita dai Jannat tana jin su bata ce komai ba har suka gama yi mata fad'an da kuma yin addu'a da neman zab'in Allah. 


Daddare Jannat na zaune kusa da Umma ga Gwaggo a gefe Umma ta kalle ta tace, "Jannat Abban ki yace na tambaye ki kina son Muhsin ko bakya son sa? Yayi bincike akan yaron Alhamdulillah ba'a samu wani abu mara kyau a tare dashi ba ko dangin sa dan haka kina son sa ko A'a?."


Shiru Jannat tayi ta kasa bata amsa sai raba ido da take yi wata zuciyar na cewa tace eh wata zuciyar na cewa tace A'a, An d'auki tsahon mintina a haka kafin Umma ta katse shirun da fad'in, "ke muke saurare kina son sa ko bakya son sa?."


Ajiyar zuciya tayi cikin k'asa da murya kamar bata son yin magana tace...........