Chapter 17
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 17*
"Umma indai yayi muku kamar yadda Abba yace shikenan." Umma ta kalli Gwaggo itama ta kalle ta kafin Umma tace, "kamar yaya in dai yayi mana mune zamu zauna dashi ko ke? Kece zaki zauna dashi ba mu ba ki fad'i abinda yake ranki in yayi miki shikenan."
Ajiyar zuciya tayi ta rasa meyasa bakin ta yayi mata nauyi ba dak'yar ta bud'e baki tace, "Yayi." Abinda tace kenan ta mik'e a guje tayi d'aki.
Hannu Umma ta d'aga sama tace, "Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, Allah ya tabbatar mana da alkhairi yasa ayi damu." Ta fad'a cikin nuna tsantsar farin cikin da take ciki. Gwaggo ma murmushi tayi kawai bata ce komai Umma ce take ta murna abin ta.
A lokacin Abba ya shigo Umma take shaida masa yadda sukayi da Jannat ya saka albarka yace zai yi magana da yaron.
Har Umma ta koma gida Jannat ta kasa fitowa daga d'aki sai raba ido take a kan katifa har Gwaggo ta shigo ta kalle ta tayi murmushi tace, "Sai ki tashi ki koma gidan naku dare yana yi." Kamar munafuka ta mik'e ta d'auki mayafi ta fita a guje. Daren ranar Jannat da Muhsin sun yishi cikin soyayya da nunawa kansu qauna a waya har bacci ya d'auke ta.
Washe gari kamar yadda Abba ya fad'awa Muhsin yazo ya same shi lokacin da ya bashi lokacin a lokacin yazo cikin manyan kasa da suka yi masa matuk'ar kyau Abba yayi masa iso har d'akin sa da yake soro ya zauna suka gaisa cikin girmamawa kafin Abba yace, "Abinda yasa nace kazo kamar yadda na sanar dakai a waya yarinya tace kai take so kai zata aura, abinda nake so dakai kafin a kai ga iyaye sun shiga maganar ina so kai da ita kuje kuyi gwajin jini a kawo min sakamakon na gani kafin magana tayi nisa."
Cikin gamsuwa Muhsin ya d'aga kai kansa a k'asa yace, "Haka ne Abba, za'ayi kamar yadda kace in sha Allah, yaushe kake so muje d'in?."
Abba yace, "duk lokacin da kuka shirya amma akwai abokin Imran Nura tare dashi zaku je ayi komai a gaban sa." Muhsin ya sake cewa, "to Abba ko yanzu in yana nan sai muje in babu damuwa."
"To shikenan zan nemi Nuran a waya in yana kusa sai yazo kuje in baya nan lokacin da yake da lokaci sai kuje." Muhsin ya gyad'a kai yace, "to Abba abinda kace."
Waya Abba ya d'auko ya kira wayar Nura akayi sa'a ya d'auka yace masa in yana kusa yazo akayi sa'a yana nan yace gashi nan zuwa.
Ba jimawa Nura ya shigo d'akin da sallama suka gaisa da Abba kafin ya mik'awa Muhsin hannu su gaisa Abba yace, "Nura akwai inda zaka je yanzu?." Girgiza kai yayi alamun a'a kafin yace, "babu inda zanje Abba, akwai aiken da za'a yi maka ne?."
"Shine wanda zai auri k'anwar ku har magana tayi nisa ma, kaine wakilin Imran shiyasa na kira ka kuje asibiti ayi musu gwaje-gwajen na jini sai ku kawo min sakamakon."
Kallon Muhsin Nura yayi suka had'a ido kafin ya d'auke kansa ya dawo da kallon sa ga Abba yace, "toh Abba yanzu zamu je?."
"Eh yanzu zaku mana ku jira na kira Jannat d'in."
Cikin girmamawa suka mik'e suka fita zuwa inda motar take Abba kuma ya shiga gida, Jannat na zaune kusa da Gwaggo Abba yace, "Jannat maza tashi ki saka mayafi kije ga Muhsin da Nura can a waje suna jiran ki zaku je asibiti ayi muku gwaje-gwaje na jini." Gwaggo ta kalli Abba tace, "Gwaje-gwajen me kuma Malam?." Abba yace, "Na jini mana yadda cututtukan nan sukayi yawa gwara kowa yasan matsayin sa kafin magana tayi nisa." Gwaggo ta girgiza kai tace, "haka ne."
A lokacin Jannat ta fito cikin dogon hijjabi har k'asa ya kalle ta yace, "suna waje suna jiran ki shida Nura." Da to ta amsa ta nufi hanyar fita cikin nutsuwa.
A kusa da mota ta hango su a tsaye ta k'arasa inda suke da murmushi ta kalli Nura tace, "ina wuni Yaya Nura." Fuskar sa babu walwala ya amsa yana kawar da kansa gefe duk sai taji babu dad'i kasancewar ba haka suka saba gaisawa ba, had'a ido sukayi da Muhsin yayi mata murmushin da ya wanke mata zuciya tasss ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi itama.
Da kansa ya bud'e mata bayan motar ta shiga shima ya shiga Nura ya shiga gaba suka bar cikin unguwar.
Kallon Nura yayi da yake aikin danna wayar sa yace, "Akwai wani likita da na sani a wani private hospital dake nan kusa sai muje." Nura da zuciyar sa take a cushe ya d'ago yace, "A'a gwara muje murtala akwai abokina da yake aiki a lab d'in." Yatsine fuska Muhsin yayi yace, "gaskiya bazan iya zuwa wannan asibitin ba mutane sunyi yawa bana son cunkoso."
Kamar ya make shi haka Nura yake ji a dak'ile yace, "Sai muje nasarawa."
"No gwara muje Akth." Tab'e baki Nura yayi baice komai ba dan ba k'aramin zafi yake ji a ransa ba in ya tuna matar da abokin sa yake mutuwar qauna zatayi aure shiyasa suke bashi haushi dukkan su.
Babu wanda yake magana har suka k'arasa asibitin yayi parking kafin ya d'auko waya yayi kira kafin su fita daga motar. Direct lab suka nufa wanda ya yiwa waya wajan sa suka je aka fad'a masa medical check up za'a yi musu na jini babu b'ata lokaci aka d'auki jinin su duka biyun aka shiga aunawa.
Sun jima a wajan kafin a kawo results d'in Mushin bai karb'a ba aka bawa Nura ya bud'e yana gani, na ko wanne ciwo da aka yi musu gwajin duka babu genotype kuma dukkan su AA ne. Ninkewa yayi ya saka a aljihu kafin su d'auki hanyar dawowa gida duka babu mai magana har lokacin.
Da suka isa yayi parking Nura yayi musu sallama ya fita ya bar su a motar, Juyowa Mushin yayi yana kallon idon ta yayi murmushi yace, "Hijjab yana yi miki kyau sosai." Murmushi itama tayi tace, "Kaima saka manyan kaya da hula suna yi maka kyau sosai." Y'ar dariya yayi yace, "Shi wannan d'in waye?."
Ta gane Nura yake nufi hakan ya daka ta tace, "Sunan sa Nura shine kad'ai abokin Yaya na." Jinjina kai yayi kamar Abba bai fad'a masa ba yace, "Amma sai naga kamar baya son aure na dake." D'an zaro ido tayi tace, "Haba dai me zai saka yak'i so? Kawai dai yana kewar Yaya na ne."
"Haka ne kuma, yanzu kinga munyi yawo mun gaji nasan kuma Abba baya nan anjima zan dawo nasan zuwa lokacin results d'in yaje hannun sa sai naji me zaice ko?." D'aga kai tayi tace, "toh Allah ya kaimu anjiman." Ya amsa da amin sukayi sallama ta fita daga motar ta shiga gida.
Kamar yadda yace kuwa bayan sallar i'sha ya dawo zuwa lokacin Nura ya kawowa Abba sakamakon ya kuma tabbatarwa da Abba babu mai matsala a cikin su dukkan su lafiya suke. Koda Abba suka had'u da Mushin d'in cewa yayi ya turo magabantan sa.
Farin ciki wajan Muhsin kamar an tsoma shi a aljanna haka yake ji ya dinga yiwa Abba godiya har abin ya bawa Abba mamaki ko Jannat bai tsaya ya nema ba ya yiwa Abba sallama ya tafi burin sa yaje gida ya sanar da iyayen sa.
Gwaggo da Abba suna zaune a tsakar gida kamar koda yaushe Jannat ta shiga wajan Umma Abba ya kalli Gwaggo yace, "Yaron nan fa na sanar dashi ya turo magabatan sa anyi gwaji komai lafiya." Gwaggo ta kalli Abba kafin tace, "toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, amma wani lokacin nakan ji babu dad'i in na tuna da Imran sai naga kamar ba'a yi masa adalci ba."
Ajiyar zuciya Abba yayi yace, "Nima ina yin wannan tunanin abinda yake dakatar dani akan sa shine in na tuna shifa yace bada aure yake son Jannat ba, kuma abinda yake kuma d'aure min kai duk lokacin da nayi istihara akan auren Jannat fuskar Imran Allah yake nuna min a mafarki, kar kuma ki d'auka sau d'aya nayi hakan har sau uku ina ganin fuskar sa amma ya rame kamar bashi ba, kwanaki nayi wani mafarki a mafarkin sai Allah yake nuna min kamar silar bayyanar Imran yana tattare da auren Jannat ne to amma na rasa ta yaya hakan zata kasance, Allah kad'ai shine yasan abinda ya b'oye mu jira muke kawai muga ikon sa."
Ajiyaf zuciya Gwaggo tayi tace, "Toh Allah yasa muga alkhairi. " ya amsa da amin suka cigaba da hira.
*☆☆*
"Mummy! Daddy! Mufeey, kuna ina?." Da haka ya shiga falon gidan yana kalle-kalle. Dukkan su suna falon sama daga saman Mufeey tace, "gamu nan Yaya." Bai jira komai ba ya hau saman a guje cikin farin ciki.
Zama yayi a kan kujera ya kalli family d'in nasa yana murmushi mai nuna yana cikin yanayi mai dad'in gaske, "to lafiya kake kuwa? Kazo ka samu a gaba kana murmushi me ya faru?." Mummy ta fad'a tana kallon sa itama da murmushin a fuskar ta.
"Daddy iyayen Jannat sunce na tura magabata na ayi maganar aure." Ya fad'a cikin zumud'i har gyara zama yake akan kujerar. Tsaki Mummy tayi tace, "yanzu akan wannan kazo kana kwala mana kira? Ni wallahi na d'auka wani babban lamari ne ya saka ka farin ciki haka."
Kallon mahaifiyar tasa yayi yace, "Mummy wannan ba abin farin ciki bane ba kenan? Cewa fa akayi na turo ayi maganar aure na da ita me zanyi in ba farin ciki ba?."
"To daman ai dole suce ka turo kaf dangin su babu wacce ta samu kwatankwacin ka ya za'ayi su bari ka sub'uce musu?."
D'aure fuska yayi yace, "Mummy iyayen matata ne pls ki daina fad'ar hakan a kansu, infact basu da kwad'ayin kud'i ko kad'an ban tab'a bawa mahaifin ta wani abu ya karb'a ba sai dai yace na barshi, ki daina fad'ar hakan bana so Mummy."
Daddy yayi murmushi yace, "Kar ka damu Son nima nayi bincike duka akan yarinyar da kuma iyayen ta basu da matsala ko kad'an har zuciya ta na amince da auren ku, but kunyi genotype?." D'aga kai yayi yace, "Eh d'azu Abban ta ya saka ya kira ni ya tura mu muka je akayi, bama iya genotype mukayi ba harda hiv, infection, hb sag, da sauran su kuma komai normal."
Girgiza kai Daddy yayi yace, "Okay good, yanzu me kake so ayi?."
"Kawai ka tura gobe aje a tsayar da rana, kuma bana so a d'auki lokaci ni wata d'aya nake so a saka."
Daddy yace, "gobe yayi wuri Mushin ka bari jibi friday kenan sai uncle's d'inka suje su nema naka auren nata, sai a tafi da kud'in aure dana saka rana ko?." D'an b'ata rai yayi yace, "Daddy friday yayi nisa gaskiya."
"Baiyi nisa ba Son ai kamar yau ne, yanzu me kake so a kai?."
D'an jimm yayi kafin yace, "Five hundred thousands." Kafin Daddy yayi magana Mummy ta riga shi da fad'in, "Gidan talakawan za'a kaiwa dubu d'ari biyar? Me zasu yi da ita?."
"Mummy gaskiya bana son haka." Ya fad'a ransa a b'ace yana cin magani. Daddy ya kalli Mummy yace, "ya isa ki barshi yayi abinda yake so tunda auren ta zaiyi."
"Kar ka damu son za'a kai dubu d'ari biyar d'in kamar yadda kace, sai kuma me kake so?."
"Daddy ina so in an kai na canja musu gida na kuma bawa mahaifin ta kud'i da zai juya a hannun sa." Daddy ya girgiza kai yace, "duka wannan babu damuwa Son duk abinda kake so kayi sai kayi min list."
Da farin ciki yace, "Thanks you Daddy." Baii kalli Mummy ba ya mik'e ya wuce su da sauri yana murmushi abin sa.
Ita dai Mufeey tunda aka fara maganar bata ce komai ba har aka gama tunanin masoyin ta take yi.
A daren ya sanar da Jannat ranar friday iyayen sa zasu zo daga nan kuma suka cigaba da hirar masoya.
Kamar yadda aka ce ranar friday bak'i suka iso suka samu tarba daga wajan Abba da y'an uwan sa da kuma y'an uwan Baba mahaifin Imran, sun karb'e su hannu biyu cikin girmamawa suma kuma basu nuna wani abun ba duk da sunyi mamakin inda Muhsin d'in ya d'auko auren.
Cikin girma da arzuk'i aka gabatar musu da abin sha kafin a fara tattaunawa. Basu jima sosai ba sukayi sallama suka tafi Abba kuma ya shiga wajan Gwaggo yace ta saka hijjabin ta suje gidan Umma sai ya fad'a musu yadda akayi da bak'in.
Bayan Gwaggo ta sanar da Umma shigowar Abba ta saka mayafi Abba ya shigo da sallama ya zauna yace, "kamar yadda kuka sani yau dai an kawo kud'in auren Jannat." Ya fad'a yana saka hannu a aljihu ya fito da damin kud'i farare kar bandir biyar ya ajjiye yace, "gasu dubu d'ari biyar aka kawo har sa rana, toh kuma su nan da wata d'aya mai zuwa suke so ayi biki amma na fad'a musu yayi kusa sunce nawa muke so a tsayar nace sai munyi shawara, ya kuke gani?."
Umma tace, "Toh sai nake ganin a barshi nan da wata biyu a k'ara wata d'aya tunda dai yarinyar nan ita kad'ai ce damu kuma iya k'arfin mu zamuyi baza muyi abinda yafi k'arfin mu ba, shi wannan kud'in da aka kawo yanzu mu fara ragewa a fara yi mata kayan d'aki da d'an abinda baza'a rasa ba in yaso na hidimar biki za'a nema amma ya kuka gani?."
Abba yace, "kune masu yanke hukunci ai abinda kuka ce hakan za'ayi ai." Umma ta kalli Gwaggo tace, "kiyi magana to muji taki shawarar." Gwaggo ta girgiza kai tace, "duk abinda kika yanke nima ina bayan sa."
Umma tayi murmushi tace, "to a barshi a hakan tunda dai ga kud'i yanzu a hannu zasu iya ayi mata gado da kujera har da kayan kitchen ma, indai babu damuwa a barshi nan da wata biyu in Allah ya kaimu." Ajiyar zuciya Abba yayi yace, "Allah ya kaimu, dan abinda za'a k'ara a kashe ai bazai gagara ba in sha Allah."
Umma ta amsa da amin Abba ya fita aka barwa Umma kud'in auren a hannun ta.
In naga comments da yawa akwai new update an jima🤸🏼♀️🥰
_Oh ready an fara payment na book2 naira 300 ne har ynzu, domin biya tuntub'i wannan number 2347045242700 but only WhatsApp._
Wattpad@ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.