Chapter 18
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 18*
Labari ya baza Unguwa an kawo kud'in auren Jannat dubu d'ari biyar, a kai ta shigowa Umma da Gwaggo murna wasu suna farin ciki wasu kuma suna bak'in ciki da hakan.
A daren Muhsin yazo wajan Jannat kamar yadda ya saba suna zaune a soron gidan suna hira yake ce mata, "Kinga Daddy ya d'auke nauyin komai yace hatta kayan d'aki shine zai zuba miki." Murmushi tayi kad'an tace, "nagode sosai Allah ya k'ara girma, amma bana tunanin Abba zai amince gaskiya."
"Meyasa bazai yadda ba to?."
"Haka ra'ayin sa yake."
Murmushi Muhsin yayi yace, "Zai yadda ma in sha Allah domin yanzu maganar da nake miki Daddy ya siyo komai na gidan wallahi, yanzu ya batun events dame-dame zakiyi?." D'an jim tayi kafin tace, "ni bana ra'ayin yin events ko d'aya gaskiya." zaro ido yayi yace, "meyasa bakya so?."
"Haka kawai."
"Tab ai kam gwara kiso dan za'a yi bama d'aya ba."
Murmushi tayi kawai bata ce komai ba suka cigaba da hira kafin yazo tafiya ya bata kud'i yace ta fara hidimar biki dasu.
Gida ta shiga ta ajjiyewa Gwaggo kud'in tace, "kinga ya bani wai na fara hidimar biki dasu." Gwaggo ta kalli kud'in tace, "to angode, ki ajjiye in Abban ki ya shigo sai ki nuna masa."
"Gwaggon kin san me yace min?."
Gwaggo ta kalle ta tace, "sai kin fad'a."
"Cewa yayi wai mahaifin sa ya siyo komai da za'a zuba a gidan ya d'auki nauyin kayan gidan gabad'aya."
Gwaggo ta rik'e baki tace, "toh amma naga ai wannan kamar aikin Abban kine ko?." Jannat tace, "nima shine abinda na gani ai." Gwaggo zatayi magana Abba ya shigo da sallama suka amsa sallamar ya samu waje ya zauna bayan ya huta Gwaggo tace, "Malam kaji wai mahaifin yaron nan yace ya d'auki nauyin komai da za'a zuba mata a gidan ta."
Abba ya kalle su yace, "d'azu ya kira ni a waya da kansa ya sanar dani hakan, duk da na nuna ban amince ba nima ina so nayi wani abun da za'a nuna ace mahaifin tane yayi mata amma yace shi duka yake so yayi komai shima ai y'ar sace, gaskiya ni bana son zak'ewa a akan irin wannan sabida gaba sai abin yazo ya jawo mata gori nan gaba." Gwaggo tayi shiru tana sauraren sa ya d'ora da cewa,
"Shima yaron ya same ni akan wai yana so mu tashi daga wannan gidan ko kuma a ruguje shi gyara, amma na hana nace masa nagode ya bari ayi auren duk abinda zai min sai ya biyo baya, bayan nan mahaifin sa ya aiko min da kud'i masu yawa wai nayi hidimar biki dasu amma gaskiya ni tantamar karb'ar kud'in nake."
Gwaggo da take sauraron sa tace, "tofa gaskiya ta bakin naka abin yayi yawa, yanzu ma kalli wanda ya bawa Jannat wai ta fara hidimar biki dasu." Kallon kud'in gaban Gwaggon yayi yace, "ita dan ya bata ai ba laifi bane daman ai zai bata d'in tunda auren ta zaiyi kuma yana da wadata a wajan su wannan ba komai bane, amma nidai gaskiya ina nazari akan yi mata kayan d'akin nan da suka ce zasu yi da kuma kud'in da aka aiko min dashi."
Gwaggo tace, "to Malam abinda ka yanke ai shikenan, in kaga baza ka karb'a ba sai a mayar sabida kar nan gaba abin yazo ya tab'a rayuwar auren ta in kuma za'a karb'a d'in shikenan ai alkhairi ne."
Abba yace, "Zanyi tunani akan hakan, Allah ya nuna mana lokacin."
Washe gari Anty Surayya da Yaya Binta suka zo gidan suka shiga aka yiwa Gwaggo Allah ya sanya alkhairi kafin su shiga wajan Umma, tunda suka zauna Umma zancen bikin Jannat take da irin alkhairi da iyayen Muhsin suke yi musu kawai take yi.
Tab'e baki Yaya Binta tayi tace, "Umma in nace miki bana son yarinyar nan sai ki dinga ganin aibu akan hakan, yanzu ki duba fa Imran baya nan ba'a san inda yake ba amma yarinyar nan zata zagaye ta auri mai kud'i ta barshi duk wahalar da yasha a akan ta ta tashi a tutar babu, ai inda kara koda auren zatayi yaci ace a bari Allah ya bayyana shi sai ayi, amma yanzu ba'a san inda yake ba ko a jikin ta ita zata auri dan sanata ta bar shi."
Baki Umma da Anty Surayya suka saki suna kallon Yaya Binta har ta kai k'arshe kafin Umma ta fara magana cikin fad'a tace, "meyasa ke wai baki da girma ne sai na jikin ki? Meye laifin Jannat in tayi aure? Ke kanki kince ba'a san inda yake ba wata k'ila ma yanzu zancen da muke ya mutu baya duniya shi kike so taita zaman jira ya dawo sannan tayi aure,? In ya dawo ma shine yace miki yana sonta? Wannan wanne irin shirme kike yi haka kawai sabida shi sai yarinya tak'i yin aure har sai ya dawo dawowar da ba'a san yaushe bace, ke in kece haka zakiyi? In da ma da soyayya a tsakanin su sai kice wani abu amma babu so a tsakanin su sai kuma ta zauna zaman jiran gawon shanu tana ji tana gani auren yazo ya gagare ta nan gaba, bara kiji wallahi kar na sake jin wannan maganar a bakin ki, ki taya ta farin ciki in kinga baza ki iya ba kiyi zaman ki a gida keda y'ay'an ki ba'a gayyace ku ba babu lallai babu dole, amma wannan maganar na sake jin ta a bakin ki wallahi sai ranki yayi mugun b'aci." Umma ta fad'a cikin fad'a sosai tana kallon ta.
Shiru tayi ta kawar da kai kawai Anty Surayya zatayi magana yara suka fara shigowa da kayan abinci da yawa, Anty Surayya ta kalle su tace, "kai ku kuma waye ya aiko ku?." D'aya daga cikin su yace, "wata ce a waje." Basu k'ara magana ba suka cigaba da shigo da kayan Umma suna kallon ikon Allah har aka gama.
Da sallama Mufeedah ta shigo gidan ya k'araso inda suke zaune ta zube har k'asa ta gaishe su dukkan su kafin Anty Surayya tace, "Bismillah zauna mana." Ba musu ta zauna tana murmushi Umma tace, "Mufeedah wata hidimar dai hallau?."
Murmushi tayi tace, "babu komai Umma an zama d'aya aii." Umma tace, "Allah ya saka da alkhairi ya baki miji na gari." Kunya ta kama Mufeedah ta rufe fuskar ta da mayafi tace, "Ameen Umma."
Su Anty Surayya ma sukayi mata godiya tace babu komai kafin su d'an yi kana tace, "Umma har yanzu babu labarin Imran ko?."
"Har yanzu Mufeedah shiru babu wani labari, ni jiki na yana bani ma kamar zuwa yanzu baya duniyar gabad'aya."
Da firgice ta kalli Umma tace, "A'a Umma ki daina fad'ar haka dan Allah, in sha Allah yana nan kuma Allah ya zai bayyana shi da gaggawa." Sai ga hawaye sharrrr sun fara zuba daga idon ta tayi saurin d'auko tissue a jakar ta ta goge idon ta.
Suka amsa da amin kafin Anty Surayya tace, "Lamarin ne dole mu d'auka hakan tun muna saka raii har mun cire." Bata iya amsa ba sai kanta da ta sake yin k'asa dashi kafin ta mik'e tayi musu sallama ta tafi dan kuka take buk'atar yi sosai zaman ta a wajan zai iya tarwatsa mata zuciya.
Da kallo Umma ta bita kafin ta dawo da kallon ta ga kayan abincin da yake jibge a tsakar gida tace, "ni sai nake ganin yarinyar nan badan Imran yana ma'aikacin ta kawai take hidima damu ba kamar akwai wani abun a ranta."
Anty Surayya tace, "son sa take Umma, duk da ban sani ba amma ni nasan haka ne domin yanayin ta kawai zaki duba ki tabbatar da abinda yake zuciyar ta."
Ajiyar zuciya Umma tayi tace, "Allah ya bayyana mana shi cikin k'oshin lafiya, ita kuma Allah ya saka mata da alkhairi."
"Amin, kinga mai son sa a nan to Umma ba irin Jannat ba." Yaya Binta ta sake fad'a cikin jin haushin Jannat.
Kallon ta Umma tayi tace, "wai baza ki daina min wannan shirmen banza bane wai?." Shiru tayi bata ce komai ba ta mik'e ta shiga d'aki.
Lokaci na ta tawowa na biki kamar wasa abu sai gaba yake yi har anci wata guda biki ya rage saura sati hud'u zuwa lokacin Jannat har Anty Surayya ta fara yi mata gyaran jiki.
Duk wani abu da ya shafi biki Umma ake samu ba Gwaggo ba koda Abban ne zai bada wani abun Umma zai aikowa, wannan karamci da suke nuna mata ya saka ta take farin ciki da hakan sosai domin har zuciyar ta tana jin dad'in yadda suke nuna mata itace uwar Jannat.
Yau ta kama alhamis kuma yau ne za'a kawo lefen Jannat su Anty Surayya da kawar ta Nafisa da y'an uwan Gwaggo dana Umma ana ta hidima tun dare har safiya, duk da maza ne zasu kawo amma haka akayi abubuwa da yawa wanda za'a basu dan kowa yasan baza'a kawo k'aramin lefe ba.
Da yamma kuwa aka kawo lefen Jannat kwati goma sha biyar ciki har da mukullin mota k'irar corolla S, Abba baiyi abinda yafi k'arfin sa ba ya bada tukwici dai-dai shi aka kuma bada abinda aka tanada domin su.
Bayan tafiyar su aka shigo da lefen aka fara gani ana taya Jannat da Gwaggo murna. Gida ya cika dammm kowa burin sa yazo yaga lefen da aka kawo dan cikin k'aramin lokaci labari ya baza unguwa lefen Jannat har da mota da gwalagwalai.
Anty Surayya ce ta dauke jakar da aka zuba gwalagwalai da mukullin motar ta b'oye sabida gudun sata.
Yadda ake shigowa ganin lefe ba'a cewa komai domin tsakar gidan Umma cika yake babu inda za'a tsuguna balle a zauna sabida mata.
Lefe sai an barka kowa yazo sai ya yaba dan kaf unguwar ma babu wanda aka tab'a kawowa kwatankwacin lefen Jannat, masu farin ciki sunayi masu bak'in ciki ma suna yi.
Bayan kwana biyu aka je aka gano inda Jannat zata zauna a nan kusa da gidan su Muhsin d'in dake wajen gari, da mamaki da kuma farin ciki su Anty Surayya suka dawo domin kuwa gida ne na gani a fad'a sama da k'asa gashi komai an zuba babu abinda babu a cikin sa, Anty Surayya tana zuwa Rungume Jannat tayi tana taya ta murna da farin ciki.
*☆☆☆☆.*
Mufeedah ce a zaune tana kallon Muhsin yana ta aikin lissafi da masu d'inki sai da ta bari ya gama sannan tace, "oh Yaya za'a yi aure." Murmushi yayi yace, "kedai ki zauna yarinya." Murmushi tayi kad'an tace, "yauwa ni kuwa ranar nan sai naga kamar motar ka ta shiga wani layi a sharad'a ina kaje a wannan layin?."
Kallon ta yayi da zai musa sai kuma yace, "nine mana a nan gidan su ai yake." Zaro ido tayi tace, "kuma sunan ta Jannat kace ko?." D'aga mata kai yayi alamun eh ta mik'e tsaye tare da dafe kai tace, "oh my god, Yaya kar dai Jannat k'anwar Imran ce? Ta tab'a baka labarin an nemi yayan ta an rasa?."
Kallon ta yayi kafin yace, "ta fad'a min mana kuma kamar yadda kika ce sunan sa Imran." Zubewa tayi akan kujera tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wallahi Yaya k'anwar Imran ce, meyasa baka fad'a min ba tun farko?."
Da mamaki yake kallon ta yace, "to in na fad'a miki me zakiyi?."
"Ai ko babu komai naje ayi hidimar bikin dani k'anwar Sweet ce fa, gaskiya baka kyauta min ba." Ta fad'a tana share hawayen ta ta mik'e ta fita daga d'akin nasa.
Da kallo ya bita ya tab'e baki ya bud'e drawer ya d'auko iv na d'aurin aure da yake ta aikin rabawa ya d'auki key d'in motar sa ya fita.
Mufeedah ma tana fita key ta d'auka na mota sai gidan su Imran ta tarar ana ta fenti tayi murmushi ta girgiza kai ta shiga gidan da sallama, Jannat da take zaune ta d'ago ido ta amsa idon su ya had'u dana Mufeedah.
Gaban Jannat ya fad'i tayi saurin d'auke idon ta domin baza ta tab'a mantawa da fuskar Mufeedah ba, tana ganin ta lokacin da tace tana son Imran ya dawo mata hakan ya saka ta d'aure fuska ba tare da tasan dalilin ta a aikata hakan ba, Mufeedah ta k'araso inda Jannat take ta zauna tace, "Sannu, Jannat ko?."
D'ago ido Jannat tayi ta d'aga mata kai jikin ta duka a mace tace, "Eh nice." Murmushi Mufeeda tayi tace, "nasan kin sanni Mufeedah wacce Imran suke aiki waje d'aya dashi ko?."
"Eh na gane ki."
"Ashe kuma ke d'in sirika tace ban sani ba?."
Da mamaki Jannat ta kalle ta tace, "sirikar ki kuma?."
"Eh mana, sai yanzu Yaya yake fad'a min wai kece wacce zai aura, kina nufin koda wasa Muhsin bai tab'a baki labarim k'anwar sa Mufeedah ba.?"
Wata irin fad'uwar gaba Jannat taji bata san dalilin ta ba ta d'ago ta kalle ta tace, "kece Mufeey d'in kenan?."
"Nice mana, ai bai kyauta min ba ace kece wacce zai aura amma bai fad'a min ba, naji haushin hakan sosai." Murmushi yak'e Jannat tayi kawai bata ce komai ba Umma ta fito.
Gaisawa da Umma cikin sakin fuska kafin Umma tace, "yauwa y'ata ga katin bikin k'anwar Imran ina gayyatar ki." Umma ta fad'a tana mik'a mata kafi yini. Karb'a Mufeedah tayi tare da yin murmushi tace, "Umma to ai nima gayyatar taki nazo yi domin da angon Jannat da ni uwa d'aya uba d'aya muke, nice kad'ai k'anwar sa nima shine kawai Yaya na."
Baki bud'e Umma tayi da mamaki tace, "amma baki tab'a fad'a mana ba?." Murmushi ta kuma yi tace, "wallahi nima Umma ban san Jannat bace nasan dai yace sunan ta Jannat amma ban kawo wannan Jannat d'in ba, yanzu ma ganin motar sa nayi a nan layin sai yake cemin ai a nan matar sa tace shine fa yake min bayani."
Cikin farin cikin Jannat ta samu sirikai na gari Umma tace, "To ma sha Allah naji dad'in hakan wallahi sosai, Allah ya sanya alkhairi."
Ta amsa da amin ta dawo da kallon ta ga Jannat tana murmushi.
Jannat kuwa gabad'aya ta kasa sakewa domin kuwa kunnen ta sai amsa kuwa suke mata na maganar Mufeedah a lokacin da take fad'awa Imran tana qaunar sa, so take ta kawar da tunanin amma ta kasa sai zafi da take ji a zuciyar ta, duk ta kasa nutsuwa sai gyara zama take cikin rashin sanin dalilin hakan.
Muryar Mufeedah ta katse ta tare da fad'in, "Matar Yaya Muhsin bani number ki sabida gaba." Runtse ido tayi domin ji take kamar ta mare ta haka ta daure ta bata number ta kira kana tace, "kiyi saving." Jannat tayi ta amsa kafin Mufeedah tayi sallama ta tafi tana tunanin abinda zata kawo gidan matsayin gudunmawa.
Umma ta kalli Jannat tace, "Kema baki san y'ar uwar sa bace?."
"Wallahi Umma ban sani ba yana dai cemin yana da k'anwa Mufeedah kinga nima bazan kawo itace a raina ba."
"Haka ne, naji dad'i ni wallahi domin yarinyar tana da hankali sosai, Allah yasa haka iyayen sa suke suma." Murmushi kawai Jannat tayi amma ta rasa dalilin da ya sanya gaban ta yake fad'uwa.
Muhsin kuwa yana fita daga gida gidan gona ya wuce da farin ciki a zuciyar sa, bayan ya faka a inda ya saba ajjiye motar ya fito ya shiga inda yazo. Masu tsoron k'ofar suna gano shi suka k'araso suka gaisa baice komai ba kawai ya bud'e k'ofar ya shiga.
A zaune ya hango shi ya fuskanci gabas yana sallah, k'arasowa wajan yayi yaga an tattare duka daud'ar da take wajan yana sallah. Tsaye yayi yana kallon sa har ya idar duk da a hankali yake yi kana gani kasan jikin sane babu kwari.
Da kallo yabi Muhsin kafin ya d'auke idon sa daga kansa ya cigaba da lazumin sa a zuciya, shi kansa Muhsin d'in ganin yadda Imran d'in ya kuma komawa sai da ya tsorata gaban sa ya fad'i dan yayi wata mahaukaciyar rama kamar an yanke naman jikin sa, sai idanu da suka yi waje.
Duk sai jikin sa yayi sanyi amma hakan bai hana shi aiwatar da abinda ya kawo shi ba yace, "Kamar yadda nake fad'a maka kana cewa k'arya ne bazai faru ba gashi nazo yau na tabbatar maka Malam Imran." Iv hannun sa ya ajjiye masa yana kallon sa yace, "ga katin d'aurin aure na da Jannat k'anwar ka kuma masoyiyar ka." Kallon katin Imran yayi yaga sunan Jannat rangad'au a jiki ga kuma sunan Abba ga kuma date da lokacin da za'a d'aura auren.
D'auke idon sa yayi daga kallon iv ya lumshe ido zuciyar da na bala'in bugawa da sauri, duk da bawai ya amince da Jannat zata aikata haka ba amma sosai yake jin bugun zuciyar sa, waya Muhsin ya d'auko ya kira layin Jannat akayi sa'a kuwa ta d'auka yace, "Amaryar Muhsin." A speaker Muhsin ya saka hakan ya saka Imran yaji sautin murmushin Jannaty tace, "Angon Jannat."
Runtse idon sa yayi da k'arfi ya dafe k'irjin sa sabida yadda yake bugawa da k'arfi ji yake zuciyar sa fitowa zatayi in bai dafe ba. Muhsin ya cigaba da fad'in, "Jannat kin san babu abinda nake so sama da naga ance yau kin zama ni na zama ke." Murmushi ta ya sake ji kana tace, "Kullum sai ka fad'i wannan kalmar kuma na fad'a maka hakan ta kusa tabbata da izinin Allah."
"Allah yasa Jaanaa, dan na matsu na mallake ki Allah ya sani." Wannan karan bata amsa ba sai murmushi da tayi ya kuma cewa, "Har yanzu babu labarin Yayan mu ko?." Jin abinda yace Imran ya d'ago ya kalle shi ya kashe masa ido d'aya yana murmushi daga can b'angaren tace, "Babu har yanzu wallahi, mun barwa Allah lamarin."
"Kar kiyi kuka mana Jaana."
"In na tuna Yaya na ji nake inda abinda yafi kuka ma yi zanyi."
"Nasan zaki so ace yaga auren mu dake ko?."
"Sosai kuwa Jaan, zan so a ce Yaya na ya aurar dani kamar yadda yake yawan fad'a min."
"Kar ki damu da izinin Allah zai bayyana a satin nan."
"Allah yasa, da nafi kowa farin ciki."
"Amin ya Allah, yanzu me kike yi?."
Numfashi ta fesar sannan tace, "gyaran jiki ake min."
"Awwnn yayi kyau, ki cewa mai gyaran ta gyara dakyau in gyaran yayi zan ninka mata kud'in ta." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ya sake cewa, "yanzu bara na k'yale ki ayi miki gyaran da kyau mayi magana anjima."
Ta amsa da toh suka kashe wayar a tare. Ba tare da yayi tunani ba yaga katin da ya ajjiyewa Imran duk ya jiqe ya kalli fuskar Imran sai yaga hawaye na sauka a kan kuncin Imran d'in yana d'iga a kan iv d'in.
"Wannan shine kwatankwacin uqubar Muhsin a duk lokacin da aka shiga gonar sa, ba kai mai zarrar d'aga hannu ka mare ni ba? Gashi ka mari fuska ta ni kuma na mari rayuwar ka har hakan ya jawo ka ga zubar da hawaye, na kwace maka wacce kake so kake kuma burin aure, ka raba ni da farin ciki na na wasu awanni ni kuma na raba da shi na har abadah, Jannat itace farin cikin ka na sani shiyasa na biyo hanyar da zan aure ta kana ji kana gani zan mata ciki ta haihu babu abinda ka isa kayi, ko a yanzu na barka naci riba domin gashi kana kuka a gaban ido na akan matar da tayi maka nisa a yanzu, inda Jannar na sonka yanzu ni take so, babu batun ka a zuciyar ta domin kaji me tace ai kawai tana so ka hallarci bikin tane ya saka take kewar ka, zan cika mata wannan burin nata kasan ina son abinda take so. Zaka ga bikin mu da idon ka, zaka kaimin matata har gida na da hannun ka kai kuma ka koma gida ka kulle kanka a d'aki kaita kuka ko kuma zuciyar ka ta buga ka mutu, izza ta kenan Malam Imran."
Duka yana jin sa amma a yadda yake jin kansa baya tunanin zai iya furta masa komai hakan ya saka shi yayi shiru baice komai ba sai hawayen da yake zuba daga idon sa wanda ya kasa tsaida shi.
"Saura kwana sha hud'u d'aurin auren mu dan haka gobe zaka bar nan ka koma gida ka d'an samu lafiya kafin lokacin yadda za'a ka ji dad'in yin rawa a bikin k'anwar ka."
D'auke iv yayi ganin ya kasa magana yace, "nasan zaka iya cewa zaka fad'awa Jannat nine na sace ka sabida ta fasa aure na ko? Eh nasan zaka iya tunda baka so ka rasa ta ni kuma ko a haka aka barni nayi nasara. Gobe zasu bud'e ka ka koma gida sai kuma munzo maka barka da kub'uta a matsayin mu na sirikan ka." Ya fad'a da wani mayaudarin murmushi yana ficewa cikin takun isa domin yana sane yayi masa maganar sace shi dan yasan fad'ar da yayi zai hana shi fad'awa kowa shine ya sace shi.
Yana fita ya sanar da masu tsaron sa yadda za'a fitar dashi gobe yana gama fad'a musu ya bar wajan yana murmushi mai kyau.