Chapter 19
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 19*
Jannat kuwa tana yanke wayar ta sauke ajiyar zuciya haka kawai take fama da bugun zuciya tun safe har yanzu ta rasa meyasa hakan, dauriya kawai take yi amma gabad'aya bata jin dad'in jikin ta.
Umma da ta shigo d'akin a lokacin ta kalle ta cikin kula tace, "Jannat akwai damuwa ne?." D'ago kai tayi ta kalli Umma sannan tace, "babu komai."
"Babu komai kike zaune baku tafi rabon katin ba? Tun d'azu Nafisa tazo tana jiran ki haka drivern da yake kai ku shima yana waje tun d'azu."
"Bana jin zan iya zuwa rabon katin nan kawai Nafisa taje ai tasan gidajen su y'an ajin namu."
Umma da ta karanci damuwa akan fuskar ta tace, "to ki fad'a min meyesa baza ki iya zuwan ba?." Tace, "Wallahi Umma fad'uwar gaba nake fama da ita yau gabad'aya bana cikin nutsuwa ta."
"Ki ta maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, zaki daina ji In sha Allah."
D'aga kai tayi alamun toh Umma ta fita ta barta Nafisa ta shiga d'akin da Umman ta fito ta kalle ta tace, "Jannat baza muje bane?." Idon ta a rufe tace, "gaskiya dai baza mu je ba Nafisa sai gobe."
"Meyasa?."
"Bana jin dad'i."
"Ayya sannu Allah ya k'ara lafiya, bara na sanar ra driver ya tafi mayi masa waya gobe." Kai kawai ta d'aga mata ta fita.
Tana fita itama ta mik'e ta fito tsakar gida ta saka slippers d'in ta nufi hanyar soro, Umma na kallon ta ta shiga d'akin Imran ta kullo k'ofar kamar yadda ta saba.
Murmushi Umma tayi ta girgiza kai tana mai jin tauyasin ta domin tayi babban rashi a rayuwar ta, a yanayin fuskar ta ta karanci tunawa da Imran tayi ya saka yanayin ta ya canja.
K'arewa d'akin kallo take tun daga kan rufin d'akin har kan ledar da take shinfid'e a d'akin gabad'aya mai zanen flower a jikin ta, murmushi tayi tunawa da lokacin da suke siyo ledar irin dramar da aka sha da mai siyarwa da yadda ta dinga tsokanar sa yana fad'a kamar zai mare ta sabida tace ledar batai kyau ba.
Dariya tayi ta d'auke kanta daga kan ledar ta d'aga kai ta kalli hotunan su shida ita wasu tana jaririya wasu kuma ta d'an girma, sauke idon ta tayi a wanda sukayi shida ita ranar saukar alkur'anin ta, yayi murmushi ita kuma tana dariya hannun ta rik'e da allon saukar tana kallon sa.
Ajiyar zuciya ta sauke ta k'arasa gaban hoton ta shafa fuskar sa idon ta a lumshe tace, "Ko ina da rabon sake ganin ka a rayuwa ta?" Sai hawaye ya fara zuba daga idon ta kamar koda yaushe baya tayi ta kwanta a akan shinfid'ar sa tana kuka sosai.
Khamshin turaren sa shi take shak'a tana sake zubar da hawaye cikin kewar yayan nata, dan ita kanta tasan tayi kewar sa fiye da tunani me tunani, sai da tayi kukan ya ishe ta dan kanta sannan ta mik'e zaune ta tankwashe k'afa tana sake kallon ko ina na d'akin har idon ta ya sauka akan wani littafi da yake ajjiye a inda kayan sa suke.
Mik'ewa tayi ta d'auko littafin a cikin sa akwai biro ta bud'e, lissafin sane kawai a ciki da kud'in da ya samu a wata da abinda zai siya nan gaba da wanda zai ajjiye duka shine a cikin littafin, bud'e shafin gaba tayi taga an rubuta, _Zan canjawa Jannat waya, zan siya make up kit babba, zan siya mata ringlight sabida d'aukar hoton wanda ta yiwa kwalliya, gabad'aya kud'in ya kama dubu d'ari da hamsin._
Sabbin hawaye sun suka sake zubowa daga idon ta ta share sabida kar ya b'ata masa littafi tace, "A kullum burin Yaya na ya inganta rayuwa ta ba ta kansa yake ba ta ni yake yi, ko me ya samu burin sa nayi farin ciki, nayi kewar ka Yaya na."
Biron ta d'auka ta bud'e sabon shafi da babu komai a jiki ta rubuta nayi kewar ka Yaya na da manyan bak'i ta zana heart a k'asan rubutun sannan ta mayar da littafin ta ajiiye.
Bud'e k'ofar aka yi hakan ya saka ta kalli wanda ya bud'e suka had'a ido da Anty Surayya tace, "in kin gama kukan kizo muje a cigaba da gyaran jiki." Babu yadda ta iya haka ta fito ta kulle k'ofar dan bata so k'ura ta shiga d'akin.
*☆☆*
"Mufeedah ba magana nake miki bane ba wai?." Mummy ta fad'a tana kallon Mufeedah da take zaune ta zuba ubam tagumi, d'agowa tayi ta kalle ta tace, "Mummy wallahi bana cikin yanayi mai dad'i zuciya ta wani irin bugawa take kamar zata faso k'irji na ta fito na rasa dalilin hakan, gabad'aya na rasa abinda yake damu na Mummy bana tunanin zan iya zuwa gidan gona yanzu."
Harara ta sakar mata tace, "Amma ai kin iya zuwa gidan su saurayin ki da ya b'ace yanzun ko?." Sake kallon Mummyn tayi kafin tace, "wai ma Mummy kaf ma'aikatan gidan nan a rasa wanda za'a saka yaje ya karb'owa Daddy kwai da kaji sai ni? Kuma fa nice nake zuwa koda yaushe dan yau nace bazan iya zuwa ba a aika wani." Ta k'arasa fad'a a sanyaye tana kallon Mummy.
"Baki da hankali ai daman shiyasa kike cewa a aika wani, in banda shirme a ina kika tab'a ganin an bawa bare abinda Daddyn ku zaici? Kin manta matsayin da yake dashi ne? Tsaf wani zaiyi amfani da wannan damar ya zuba masa sa wani abun a ciki dan ya kashe shi."
"To Mummy a aika Yaya Muhsin mana ai shi bai cika zuwa kamar ni ba."
"Kema kin san hidima tayi masa yawa yanzu balle ma kin san tun farko shi ba son zuwa gidan gona yake ba kece mai son zuwa, dan haka ki tashi kije a gyara kajin hausa guda goma a gaban ki su saka miki a leda ki saka a boot ki kawo min, sai kwai ki karb'o da yawa dan muma namu ya k'are kuma kin san dai zamuyi bak'i very soon."
Yatsine fuska tayi ta turo baki tace, "cika min mota kajin nan suke da karni kamar nayi amai."
Mummy tace, "ki d'auki mota ta in zaki tafi, Mufeedah a yau nake son abin nan gobe k'arfe bakwai Daddyn ku zai dawo kuma kin san lokacin ne na breakfast d'in sa."
Kallon Mummyn tayi tace, "toh zanje." Mummy ta sake maimaitawa tana kallon ta tace, "Mufeedah Allah kika manta ranki ne zai b'aci." Cikin k'osawa tace, "Bazan manta ba Mummy."
Mummy na barin wajan ta kwanta akan gadon idon a lumshe tana hango fuskar masoyin ta a idon ta, bud'e ido tayi ta dafe zuciyar ta tace, "na rasa meyasa yau nake jin fad'uwar gaba da gudun zuciya kamar yanayin da nake tsintar kaina a ciki in muna tare da Imran." Ta fad'a tana mik'ewa tsaye ta shiga band'aki.
Har dare Mufeedah bata je gidan gona ba dan ita tama manta gabad'aya banda tunanin Imran babu abinda yake yi tana kuka a haka bacci ya kwashe ta.
Kiran sallar da masallacin jikin gidan ya tashi Mufeedah ta mik'e zaune tana mutsikka ido, hannu ta kai ta kunna bed side lamp ta d'auki wayar ta ta kalli agogo sai a lokacin ta fahimci kiran asuba ta jiyo, mik'ewa tayi ta shiga tayi alwala ta fito tana yamma.
Maganar Mummy ta tuna ta zaro ido da sauri ta jawo abaya ta d'ora akan kayan baccin jikin ta ta tayar da sallah, lokacin da ta idar ta d'an zauna tana lazimi babu jimawa ta mik'e ta fad'a band'aki tayi wanka a gaggauce ta fito shirya cikin doguwar riga mai fad'i y'ar kanti ta yafa mayafin ta a ka ta fice da sauri.
A can gidan gona kuwa masu tsaron Imran ne suka bud'e shi suka shiga ciki suka same shi a zaune yana kallon gabas da alama addu'a yake yi, kallon juna sukayi kafin d'aya yace, "Bawan Allah ka tashi mu fitar da kai yau Allah ya amshi addu'ar ka." Yana jin su baice komai ba sai da ya shafa addu'ar sannan ya yunk'ura da niyar mik'ewa, baya yayi zai fad'i suka yi saurin tare shi k'afafuwan sa sai rawa suke don kuwa baza su iya d'aukar sa ba.
"Sannu." Shine abinda suka ce suka rik'e shi, a hankali ake takawa duk taku d'aya sai ya runtse ido sabida yadda k'afar tayi bala'in tsami ga jiri da yake kwasar sa ga wani irin azaba da cikin sa yake masa, suna fitowa daga d'akin suka cigaba da tafiya cikin doguwar rumfar da take wajan har lokacin gari baiyi haske sosai ba.
Suna fita daga rumfar Imran yaji kamar ana saka allura ana soka masa a cikin idon sa sabida hasken da ya kawowa idanun sa ziyara, ai da sauri ya kulle idon sa gam cikin muryar sa da take ciki yace, "Bana gani." Kallon juna suka kuma yi kafin su k'arasa wani kan tudu su zaunar dashi kana suce, "Ka rufe idon ka sosai hasken da ka gani ne ya jawo maka rashin ganin sai a hankali zaka warware, muna zuwa." Da sauri suka bar wajan da sauri dan basa so a zo a same su a wajan su shiga uku.
Imran yana ta zaune a akan tudun da suka ajjiye shi kusan minti talatin babu motsin su gashi baya gani balle ya samu abin hawa ya kai shi gida, mik'ewa tsaye yayi dak'yar ya taka da niyar yin gaba sai kuwa ya kifa ya fad'i a kan wani dutse dake wajan kansa ya bugu goshin sa ya fashe.
"Hasbunallahu wani'imal wakil." Shine abinda Imran yake furtawa kawai ji yake ina ma basu fito dashi ba dan azabar da yake ji a waje tafi ta cikin yawa.
Horn Mufeedah take dannawa ganin sa a kan hanyar shiga gate d'in gidan gonar amma ko gezau baiyi ba sai ma toshe kunnen sa da yayi, Mufeedah da take ciki mota ranta ya b'aci ta kalli agogo taga har shida da ashirin tayi taja tsaki ta fito daga motar ya k'araso inda yake dan ita fa duk a tunanin ta mahaukaci ne.
Jin motsi ya saka Imran ya bud'e bakin sa dak'yar yace, "A taimaka min dan Allah bana gani." Abin ka da abinda zuciya take so nan take zuciyar ta fara wani irin harbawa da sauri duk da bata ji mai yace ba, ba tare da fargabar komai ba zuciyar ta ta bata umarnin zuwa kusa dashi a hankali ta isa inda yake ta tsuguna kusa dashi ta saka hannu ta d'ago fuskar sa, zaro idanu tayi ganin kamar Imran d'in ta kamar kuma bashi ba, dan wannan Imran d'in yayi muguwar rama ga gashi ko ina a fuskar sa da kansa, "Ko waye ko wace ku taimaka min dan Allah bana iya ganin komai." Ya sake fad'a a hankali numfashin sa na sama da k'asa.
Bayyanar wushiryar sa yayin da yayi maganar taji wani abu tun daga tsakiyar kanta ya gangaro da gudu ya fita ta cikin yatsun k'afar ta, murmushi tayi muryar ta har rawa take hawaye na zuba a idon ta tace, "Imran!."
"Na'am, ko wacece ke ki taimaka min dan Allah." Ai bata jira ba ta fad'a jikin sa ta rungume shi k'am tana kuka sosai, matse shin da tayi ya saka shi runtse idon sa da k'arfi domin ba k'aramar azaba yake ji a cikin sa ba da gangar jikin ba da sauri ya furta, "Washhh."
Jin abinda yace tayi saurin d'agowa daga jikin sa tace, "Imran nice Mufeedan ka, yanzu zan taimaka ka kar ka damu zaka ji sauk'i." Ta fad'a tana kuka mai had'e da murmushi. Mik'ewa tsaye tayi ta kama hannun sa tace, "tashi muje asibiti."
Gigiza kai yayi yace, "bazan iya tashi ba." Kalle-kalle take ko zata ga wanda zai taimaka mata amma hanyar babu kowa, daga can nesa ta gano mai napep tun daga nesa ta fara saka masa hannu yana zuwa ya tsaya ta kalle shi tace, "Dan Allah taimaka min miji nane na saka shi a mota."
Bai musu ba yayi sauri ya fito ya kama Imran itama ta rik'e shi aka saka shi a bayan mota ta yiwa mai napep d'in godiya ta shiga motar ta bar wajan a guje, gudu take tana kuka tana waiwaye tana kallon sa har ta kusa dukan wata mota Allah yasa tayi saurin kaucewa, hawayen idon ta ta share ta d'auki wayar ta hannun ta har rawa yake tayi kira ta saka a speaker, ana d'auka tace, "Dr Ansar kana gida ko kana asibiti?."
Jin yadda maganar ta take rawa ya saka shi yace, "ina kan hanyar shiga asibiti yanzu." Hawayen ta share tayi kafin tace, "ina hanya yanzu kafin na k'araso har kaje, ganin na da emergency patient dan zan iya cewa ma unconsciously yake, pls a had'a komai before na k'araso yana buk'atar taimako da sauri."
"Okay babu damuwa sai kinzo."
Bata sake bashi amsa ba ta kashe wayar ta cigaba da shek'a uban gudu kasancewar sassafe ne babu motoci sosai hakan ya bata damar tafiya yadda take so.
Lokacin da tayi parking a harabar asibitin har Dr Ansar d'in ya tsayar da nurses a wajen suna jiran isowar ta, tana tsayawa suka isa wajan aka fito da Imran aka d'ora shi akan gadon da suka fito dashi ana tura shi a guje sai emergency.
Bin bayan su itama tayi a guje kafin ta k'arasa har an shiga dashi d'aki an fara bashi taimakon da sauri-sauri.
Waje ta samu ta zauna ta dafe kanta tana kuka sosai mara sauti ranta zai fita, bata san adadin mintinan da ta d'auka a wajan ba sai muryar Dr Ansar da taji yana yi mata magana ya saka ta ta d'ago.
"Mufeedah taso muje office ki huta kin jima a zaune." Mik'ewa tsaye tayi ta kalle shi tace, "ya mai jikin?." Kallon ta yayi kafin yace, "kizo muje sai nayi miki bayani." Ba musu ta bi bayan sa har office d'in sa ya nuna mata waje ta zauna shima ya zauna sannan yace, "akwai malaria mai zafi a tare dashi wacce har ta kai plus two, sannan akwai ulcer kuma tayi masa mugun kamu itace ta haifar masa da ciwon ciki, akwai weakness joint ma'ana gab'ob'in jikin sa dukka a sage suke duk yadda akayi ya jima bai motsa ba ko baiyi tafiya ba, akwai damuwa a tare dashi dan jinin sa ya hau sosai yadda ba'a so a shekarun sa, sai kuma ciwon da yaji a kansa, iya wad'an nan sune wanda muka gani da kanmu kafin kuma ya farka ya fad'a mu gani koda wani abun dan ya samu bacci yanzu haka."
Ajiyar zuciya tayi sai ta sake fashewa da kuka, kallon ta kawai yake da mamaki yana tunanin waye d'in ta haka dan shi dai yasan bai san shi a gidan su ba, "ki daina kuka mana Mufeedah ai zai samu sauk'i." Ya fad'a ciki rarrashi da kwantar da murya yana kallon ta.
Cikin kuka ta d'ago ta kalle shi tace, "Duka wad'an nan ciwokan da ka lissafa akan mutum d'aya? A hakan kuma waii ma ba'a jira ake ya farka aji koda wani abun." Dr yace, "to ya za'ayi ikon Allah kenan, amma waye shi a gidan?." Sai da ta goge idon ta sannan ta kalle shi tace, "Shine wanda zan aura."
Zaro ido yayi yana kallon ta kafin ya girgiza kai yace, "Kai! Ashe ango ne a kwance, kema ya kamata a duba ki to dan naga yanayin ki kamar ba dai-dai ba." Kanta ta dafe sannan tace, "kaina ne yake min ciwo sosai ga zazza6i da nake ji."
Baice komai ba ya mik'e tsaye ya had'a allura ya k'arasa inda take yayi mata yace, "Zai sauka in sha Allah, amma ki kwanta kyafi samun sauk'i." Mik'ewa tayi tare da girgiza kai tace, "A'a zanje na zauna dashi, daga hannun kidnappers ya kubto" Bata jira mai zaice ba kawai ta fice daga office d'in nasa.
Tana fita yabi bayan ta zuwa cikin d'akin ya ganta a tsaye a kusa dashi tana kallon yadda numfashin sa yake sama da k'asa kana gani kasan ba daidai yake fita ba, kuka take sosai ta juyo ta kalli Dr Ansar tace, "numfashin sa."
K'arasowa wajan yayi yace, "Ki kwantar da hankalin ki zai daina baki ga an saka masa oxygen ba?." Waje ta samu ta zauna tana kallon sa tana cigaba da kuka.
Wayar ta d'auko ta shiga jerin number's d'in da suke adane a wayar ta tana dubawa har tazo kan number Jannat ta danna kira. Har ta katse ba'a d'auka ba ta kuma kira nan ma ta kuma katsewa ba'a d'auka ba a karo na biyu, sake kira tayi a karo na uku sannan aka d'auka.
"Assalamu alaiki, Jannat ya kike?."
Daga can b'angaren Jannat ta yatsine fuska sannan tace, "Wa'alaiki salam, lafiya lau."
Sai da ta sauke numfashi sannan tace, "ki fad'awa su Umma naga Imran yanzu haka muna Diamond specialists hospital an kwantar dashi." Jannat da take kwance ta mik'e tsaye cikin tashin hankali tace, "banji me kika ce ba dan Allah maimaita."
"Abinda kika ji d'in shi na fad'a, Imran yanzu haka gashi a kwance a Diamond hospital."
Wayar hannun ta ta saki ta fad'i a k'asan d'akin ta fita a guje.
"Umma! Umma!! Umma!!!." Shine abinda Jannat take fad'a jikin ta na rawa kamar mazari hawaye na zuba a idon ta. Da sauri Umma ta fito ta k'araso inda take tace, "Ke Jannat lafiya."
"Umma anga Yaya na! An ganshi Umma, yana diamond hospital." Bata jira mai Umma zata ce ba tayi d'aki da sauri ta d'auki mayafi da kud'in ta da suke ajjiye akan madubin Umma ta fito a guje ta fita.
Kiran ta Umma take amma ina tayi nisa bama ta jin me take cewa, mayafi Umma ta yafa ta shiga gidan Gwaggo take sanar dasu yadda sukayi da Jannat suma basu yi k'asa a guiwa ba suka d'unguma suka tafi asibitin dan bata tab'a aikata irin haka ba balle suce k'arya take.
Jannat kuwa gani take mai napep d'in sam baya gudu dan gani take kamar ba tafiya suke yi ba, "Malam dan Allah ka k'ara gudu sauri nake yi" ta fad'a muryar ta na rawa tana kallon hanya, Baice komai ba ya cigaba da tafiyar sa. Dukan kujerar zaman da take kai tayi ji take ina ma ta jawo shi ya dawo baya ita ta karb'i tuk'in tayi da kanta.
A haka suka k'arasa asibitin bata jira ya tsaya ba ta dira daga ciki ta mik'a masa abinda ta d'auko gabad'aya ba tare da ta tsaya ta kalli nawa ta bashi ba tayi ciki a guje. Jikin ta har rawa yake yi gashi ta rasa inda zata shiga ga wayar ta ta barta a gida balle ta kira Mufeedah.
Dr Ansar ne yazo wucewa tayi saurin tare shi tace, "Dr dan Allah ina neman d'akin da aka kwantar da Imran, eh Imran" ta fad'a a rud'e tana kallon sa. Da hannu ya nuna mata kafin yace, "kar kiyi masa hayaniya a ciki." Kai kawai ta d'aga masa ta bud'e k'ofar d'akin ta shiga kamar an cillo ta.