Chapter 21
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 21*
A rud'e Jannat ta kalle su dukkan su tace, "ban fahimci mai kake nufi ba?." Abba ya kalle ta yace, "Jannat dakata mana, Dr kuyi mana bayani yadda zamu gane kun saka mu a duhu."
Ajiyar zuciya Dr Ansar yayi kana yace, "Ba wani abu bane bai kai yadda kuke tunani ba, kun san in mutum ya jima a duhu idon sa baya ganin wadataccen haske har na tsahon wani lokaci idon sa yana samun matsala, haka in mutum ya dad'e a haske sai daga baya ya shiga duhu shima idon sa yana samun matsala amma na farko yafi illa, abinda ya faru da patient d'in ku kenan, duk yadda akayi ya jima sosai a wajen da babu haske yanzu kuma fitowar sa haske sai ya kasance idon nasa ya gaza karb'ar haske dole sai da wani taimako, ku kwantar da hankalin ku ba wani abu bane na tayar da hankali, zamu bashi maganin da zai taimaka masa wajan ganin sannan zamu bashi glass da zai dinga amfani dashi."
Hannu Jannat ta d'ora a ka ta fashe da kuka tace, "yanzu kana so kace Yaya na ya makance kenan?." Girgiza kai yayi yace, "A'a bai makance ba a haske ne baya gani baki ji bayanin da nayi yanzu ba? Shima kuma nan da wani lokaci da izinin Allah idon nasa zai dawo dai-dai amma sai ana shan magani."
Cikin tausayin Imran Abba yace, "To yanzu yaushe zai fara karb'ar maganin?." Kallon Imran d'in Dr yayi kafin yace, "a yanzu zamu d'ora shi a kan maganin amma kafin nan zamu fara zuwa a duba idon nasa mu bashi Medical glass dai-dai da yanayin abinda muka gani."
Mufeedah tace, "Dr in kana ganin abin bazai yu ba ka sanar dani kawai." Dr ya kalle ta yace, "kar ki damu Mufeedah babu abinda bazai yu ba a nan ba sai an fita waje ba."
"To maganar tasa da bata fita fa?." Gwaggo ta tambaya tana kallon Dr. "A'a ita ba matsala bace, mura ce tayi masa yawa ta rik'e ma'kwogwaron nasa shiyasa maganar bata fita amma a hankali zata washe."
Ragowar likitocin ya kalla kafin wasu nurses maza guda biyu su shigo a tura gadon da Imran yake kai a nufi inda za'a yi gwaje-gwaje a kan idon.
Sun jima sosai da tafiya wajan awa biyu ana zaman jira kafin suga an turo gadon an dawo dashi yana kwance idon sa a rufe ruf.
Dr Ansar ya sake shigowa ya kalli su Abba yace, "In sha Allah komai zai zo da sauk'i ku kwantar da hankali ku an saka masa magani a idon yanzu, komai zai daidaita da izinin Allah."
Bayan kwana biyu.
Har lokacin Imran yana asibiti a kwance baya magana ba kuma ya gani har lokacin sai dai ya motsa kai kawai, ana ta saka masa magani a idon, Jannat ta rame sosai cikin kwanakin kullum cikin damuwa take duk da Muhsin yana iya bakin k'okarin sa wajan ganin yana d'ebe mata kewa amma da sun rabu zata koma gidan jiya.
Mufeedah ma dai gata nan dai kawai kullum tana hanyar asibiti dan da ita ake jinyar da ita ake wuni har dare sannan ta koma gida.
Yau ta kama kwanan Imran shida a asibiti inda bikin Mushin da Jannat ya rage saura kwana takwas d'aurin aure, yana zaune a kan gadon kamar koda yaushe ya sunkuyar da kansa yana aikin tunanin da ya saba kullum, shi kansa bazai ce ga abinda yake damun sa ba, ya warware sosai ya samu lafiya sai dai matsalar ido da kuma ta magana, dukkan su suna d'akin suna hirar biki banda Jannat da bata saka musu baki sai danna wayar ta da take yi kawai.
Anty Surayya tace, "Jannat d'in tace wai ta fasa ko wanne event d'in da za'ayi in aka d'aura aure shikenan tunda Yayan ta bashi da lafiya." Umma ta kalle ta tace, "Meyasa kika fasa?." Kallon Umma tayi ta sauke numfashi tace, "haka kawai Umma."
Shigowar Dr's guda uku ya saka sukayi shiru suka amsa sallamar su aka gaisa, wajan Imran suka nufa da yake zaune d'aya daga ciki yace, "Sannu Imran, ya jikin naka?." D'ago kai yayi kamar zai yi magana cikin maganar sa da bata fita sosai yace, "Da sauk'i." Kallon juna kowa yayi a d'akin da matuk'ar mamaki Anty Surayya tace, "Imran daman ka fara magana kayi mana shiru?."
Bai amsa ba likitan ya cigaba da cewa, "daure ka bud'e idon naka a hankali." Ba musu ya fara bud'e idon har ya bud'e su duka a cikin d'akin yana juya k'wayar idon nasa. Likitan yace, "kalle ni." Ba musu ya d'aga idon ya kalle shi yace, "kana gani na sosai?."
Girgiza kai yayi yace, "gaskiya bana ganin ka sosai."
"Yana maka zafi idon kamar da?."
"Yana yi amma ba kamar da ba."
D'auko wata takarda Dr d'in yayi ya mik'awa Imran yace, "kalli kaga kana ganin rubutun jiki."
Kallo yake amma babu abinda yake gani a ciki sai hasken takardar hakan ya saka ya mik'a masa yace, "bana ganin komai." Girgiza kai Dr yayi suka bud'e ledar da aka shigo dashi aka d'auko medical glasses guda uku masu fad'i amma ba sosai ba basu suyi irin siraran nan ba aka mik'a masa d'aya daga ciki aka ce, "Saka wannan ka kalli ka kalli rubutun ka gani."
Ba musu ya karb'a ya saka a idon sa ya kalli takardar ya d'aga ya kalle shi yace, "ina ganin rubutun ba sosai ba."
"Ciro min glass d'in." Ba musu ya cire ya mik'a masa ya sake mik'a masa wani yace, "Saka wannan mu gani."
Imran ya saka ya kalli rubutun ya d'ago ya kalli Dr yace, "ina ganin rubutun sosai." Dr yace, "Me aka rubuta a jiki?."
Kallon rubutun yayi yace, "an rubuta na warke a jiki."
Dr yayi murmushi yace, "D'ago kanka ka kalle ni ka fad'a min kalar kayan da yake jiki na." D'agowa Imran d'in yayi ya kalle shi kana yace, "Ka saka bak'ar suit mai duhu sosai."
Gabad'aya suka had'a biki suka ce, "Alhamdulillah." Likitan ya mik'a masa hannu suka gaisa yace, "Congratulations Imran ka samu sauk'i sosai." Murmushi Imran yayi kad'an kafin yace, "yanzu kenan sai da glass zan dinga gani sosai?."
D'aga kai yayi yace, "Gaskiya dai rashin glass a idon ka dai-dai yake da raguwar ganin ka, kuma glass d'in zai taimaka maka wajan kare rana domin idanun ka ka yanzu basa son rana kasancewar ka jima baka ga haske ba sai a hankali komai zai dawo dai-dai, amma fa duk da haka koda zaka iya zama babu glass d'in tsakani da Allah ganin ka tarrr kamar da ya tafi za dai kaji sauk'i sometimes basai ka saka ba amma sakawar yafi amfani domin zaka fi gani kuma zai taimaka maka tunda na magani ne."
Girgiza kai Imran yayi baice komai ba Dr ya kalle mutanen d'akin da kowa yake sauraron su yace, "Alhamdulillah kamar yadda kuka ji nace ya ji sauk'i sosai idon sa kuma ya samu lafiya amma sai da taimakon glass ganin zai inganta, kamar yadda nayi muku bayani a baya zaman da yayi a duhu ne ya haifar masa da wannan matsalar zamu bashi maganin da zai dinga amfani dashi zai daina masa ciwo gabad'aya amma dai glass d'in ya zama koda yaushe yana tare dashi kodan sabida rana, da k'ura da kuma hayak'i, yadda kuka ji kuma ga maganar sa tana fita daman mura ce itama a hankali zata washe ta koma kamar da."
Abba yace, "to bayan wad'an nan babu wani abu kuma?." Dr Ansar yace, "akwai hawan jini a tare dashi lokacin da aka kawo shi dan na fad'awa Mufeedah ma, to jinin ya sauka a yanzu haka amma bai koma dai-dai ba har yanzu akwai abinda yake damun sa wanda ya b'oye a zuciyar sa har hakan yayi silar da jinin yak'i sauka, bama so mu d'ora shi a akan magani ne dan da ya fara sha shikenan ya zame masa jiki kullum sai ya sha har ya bar duniya, shekarun sa sunyi kad'an da wannan yanayin gaskiya shiyasa muke saka masa ruwan da zai saukar da jinin amma har yanzu bai koma yadda ake so ba. Sai ulcer wacce daman kowa yasan sai da abinci, kar a dinga barin sa baya cin abinci domin tayi masa kamu sosai wanda in yana jin yunwa bai ci ba hakan zai jawo masa ciwon ciki mai tsanani."
Abba ya sake cewa, "To shikenan Dr mun gode." Dr Ansar ya sake cewa, "Zuwa anjima da yamma zamu bashi sallama tunda Alhamdulillah ya samu lafiya. amma ya gujewa shiga hayaki, k'ura, rana da kuma abinda zai saka shi zubar da hawaye a wannan lokacin, wad'an nan abinda na lissafa in bai guje su ba zasu hana idon sa warkewa da wuri hakan yana daga cikin amfanin glass d'in idon sa, Allah ya k'ara lafiya." Daga haka suka fita aka bar su a d'akin Imran dai tana zaune a kan gadon idon sa manne da glass d'in kansa a k'asa.
"Imran!." Abba ya fad'a muryar sa a tausashe yana kallon sa tare da k'arasowa inda yake. Kansa ya d'ago ya kalli Abba ta cikin glass d'in idon sa, rik'e hannun sa Abba yayi yace, "Sannu Imran." Dak'yar ya fizgi maganar bakin sa yace, "Yauwa Abba."
Dukkan su wajan suka nufo kowa yana yi masa sannu hakan ya saka shi dole ya d'ago ido yana kallon su d'aya bayan d'aya. Lokacin da idon sa ya sark'e dana Jannat yaga yadda ta yayi ja da alama kuka tasha ya lumshe idon sa ya furzar da iska a bakin sa yayi mata murmushi, itama murmushin tayi masa ta zagaya d'aya b'angaren ta zauna kusa dashi tace, "Yaya na yanzu kana gani na?." Idon sa yana cikin nata ya d'aga mata kai alamun eh, hawayen da suke mak'ale a idon ta ya zubo tace, "Ni magana nake so kayi min."
"Ina gani Jannat, gaki nan kina kuka." Ya fad'a yana shafo hawaye idon ta ya nuna mata. Mik'ewa tayi cikin farin ciki ta rungume Anty Surayya tace, "Alhamdulillah Yaya na ya samu lafiya, yeeeee Allah nagode maka." Ba k'aramar dariya ta bashi ba duk da yanayin da yake jin zuciyar sa hakan bai hana shi jin nishad'i ba domin ba k'arya yayi kewar ta ba kad'an ba,yayi murmushi kad'an ya dawo da kallon sa ga sauran mutanen.
Dukkan su murmushi suke har Umma da take tsaye tana kallon su, Mufeedah ce ta shigo d'akin a lokacin ta k'araso wajan da sauri tace, "Sannu." Mayar da kallon sa yayi wajan ta yayi murmushi yace, "yauwa Mufeedah nagode." Wani irin farin ciki Mufeedah taji yana zaga ta har ta kasa b'oyewa tayi murmushi mai kyau tana kallon sa, yau shine yayi mata murmushi har da kiran sunan ta yace mata ya gode, ina zata kai wannan farin cikin ita kuwa.
"Ina Yaya Binta?." Ya tambaya yana kallon su. Gwaggo tace, "yau ta tashi yaro babu lafiya shiyasa bata zo ba."
"Allah ya bada lafiya." Ya fad'a yana kallon wanda yake shigowa.
Murmushi Imran yayi ganin Nura ne yana zuwa suka gaisa Nura yace, "barka da samun lafiya aboki na." Cikin farin ciki Nura yake fad'a shima yace, "nagode Nura."
Kallon Abba yayi yace, "Abba da gaske ne abinda na ji ina kwance a nan?." Abba ya kalle shi yace, "me kaji Imran?."
"Da gaske ne saura kwanki tayi aure?." Dukkan su sai da gaban su ya fad'i har Abban, shi kansa Abba bai san dalilin fad'uwar gaban da yaji ba akan tambayar da Imran d'in yayi ya daure ya murmushi yace, "eh Imran, rana e ta gobe za'a d'aura mata aure."
Wani irin dummm Imran yaji a zuciyar sa ya runtse idon sa ya tafi hutun wasu seconds ba tare da ya bud'e ba, kallon sa Abba yayi ya d'an tab'a shi yace, "Imran lafiya?." Numfashi ya fesar yace, "babu komai Abba."
Abba zaiyi magana akayi sallama aka shigo cikin d'akin, dukkan su amsawa sukayi tare da kallon wanda suka shigo d'in. Salim ne da Muhsin suka k'araso inda su Abba suke suka duk'a har k'asa suka gaida kowa na wajan kafin Muhsin ya mik'e ya mik'awa Imran hannu yace, "Sannu Yaya Imran ya jikin naka?." Imran da yake kallon ikon Allah ya dake ba tare da ya nuna wani abun ba ya mik'a masa hannu yace, "Da sauk'i."
"Allah ya k'ara lafiya." Ya amsa da amin yana kallon sa shima kuma shi yake kallo ko wanne da abinda yake zuciyar sa, Abba ya katse su da fad'in, "Muhsin ga Imran Yaya d'aya tilo wajan Jannat, Imran ga Muhsin shine wanda zai auri k'anwar ka Jannat, sannan kuma Yaya ga Mufeedah shugabar wajan aikin ku kuma wacce take ta d'awainiya da kai." Imran kamar bai ji mai Abba yace ba domin kallon Muhsin kawai yake yi shima kuma shi yake kallo yana jifan sa da wani mayaudarin murmushi wanda su biyu ne kad'ai suka san ma'anar sa.
D'auke idon sa yayi daga kallon Muhsin ya kalli Jannat suka had'a ido duk sai ta dabarbace kamar mara gaskiya ta rasa abinda zatayi kawai sai ta matsa daga kusa dashi har lokacin ita yake kallo, kasa nutsuwa tayi jin yadda idanun sa suke yawo a jikin ta hakan ya saka ta koma can gefe bata kuma d'ago idon ta ta kalle shi ba. Bai amsa ba kawai ya jinginar da kansa ya lumshe ido kalaman Abba suna yi masa yawo a kansa.
Kamar an d'auki guduma an maka masa a tsakiyar kansa haka yaji da sauri ya rik'e jijiyoyin kan nasa yace, "Washhhh Allah." Da sauri Gwaggo tace, "Lafiya Imran?."
"Kaina." Shine abinda ya iya furtawa har lokacin yana rik'e da kansa.
Da sauri Muhsin yace, "bara naje na kira Dr." Ya fad'a yana fita da sauri kamar gaske jim kad'an sai gasu da Dr yana zuwa kawai bp d'in Imran ya auna sannan ya jawo wata locker da yake kusa da gadon Imran d'in ya d'auki drip ya jona masa.
A haka yadda yake zaune bacci ya d'auke shi Dr yayi musu alamun da su fito a bashi waje ba musu dukkan su suka fito Jannat jikin ta a sanyaye kamar an mata duka.
Bayan sun fito aka kullo k'ofar Dr yace, "Gaskiya akwai abinda yake damun sa wanda in ya tuna yake tayar masa da hankali, ba yanzu muka fita nake ce muku jinin sa an d'an samu ya d'an sauka ba? To yanzu ya hau sosai har yana k'okarin ya d'ara na dah. Tabbas akwai abinda yake zuciyar sa wanda ya tuna yanzu ko aka tuna masa shine dalilin da ya saka jinin sa ya sake yin sama, ruwan da na saka masa zai saka jinin nasa ya sauka."
Jinjina kai Abba yayi ya tafi duniyar tunani yana so ya tuna dalilin shigar Imran wannan halin, daki-daki yake nazarin komai yana girgiza kai shi kad'ai ya san abinda ya fahimta akan lamarin.
Ita dai Jannat duk ta zargu gani take kamar tana da hannu a cikin wannan yanayin da ya shiga shiyasa gabad'aya ta rasa sukuni sai zare idanu take yi.
Muhsin kuwa inda motar sa take ya koma tunawa da yayi ya bar wayar sa a ciki, ya bud'e motar ya d'auko yana niyar juyowa Salim ya tare shi yana fad'in, "Yanzu kai a zuciyar ka kana ji kayi dai-dai kenan?." Da mamaki Salim yace, "uban me nayi to?."
"Au bama kasan me kayi ba kenan? Ka duba halin da ka jefa wannan bawan Allah da karancin shekarun sa, ga hawan jini, ga matsalar ido, ga matsalar magana, ga ciwon jiki, gashi ka raba shi da k'anwar sa da yake mutuwar so, anya Muhsin kana da imani kuwa?."
Hannayen sa ya hard'e a k'irji yana kallon Salim yace, "bani da imanin sai ka sammin na naka in kai kana dashi, sau nawa zance maka bana son wannan maganar ne wai?." Salim yace, "Wallahi dole nayi maka maganar nan domin abinda kayi baka nuna imani a cikin sa ba sam, ka d'auke mutum ka b'oye shi a cikin d'aki mai duhu har tsahon wasu watanni dalilin hakan ya haifar masa da matsalar ido yanzu kuma ka zagayo zaka aure masa wacce yake so, wannan wanne irin rashin imani ne da qik'ashewar zuciya Muhsin?."
"Mtswww kanka ake ke ji ni ina da abin yi in kai baka dashi, kuma bara kaji duk abinda nayi wa Imran banyi dana sani ba har yanzu zuciya tana fad'a min dai-dai nayi, ka danna b'ata bakin ka wajan wannan maganar domin baza ta amfane ka da komai ba." Ya fad'a yana wucewa ya bar Salim a tsaye yana bin sa da kallo har ya shiga cikin asibitin.
_Oh ready an fara payment na book2 naira 300 ne har ynzu, kad'an ya rage mu kammala book 1 domin biya tuntub'i wannan number 2347045242700 but only WhatsApp._
Wattpad@ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11