ZANEN ZABUWA

Chapter 22 end of book1

by @nanahaleema11

*ZANEN ZABUWA*


     ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1

*Page 22*


Abba kuwa office d'in Dr Ansar ya shiga ya zauna kana ya kalli Dr yace, "kace yau za'a bamu sallama ko?." Dr Ansar ya d'aga kai yace, "da izinin Allah da ya farka munga yanayin jikin sa sai a sallame ku."

"To nawa ne total na abinda aka kashe gabad'aya?."

"A'a Alhaji ai Mufeedah ta riga ta bada komai, hatta kud'in maganin da za'a bashi in an sallame shi ta biya."


D'an jim Abba yayi cike da mamaki dan bai kawo hakan a ransa ba domin har ya ware kud'i cikin kud'in da yake hannun sa na biki ya ajjiye dan yasan an kashe kud'i da yawa tunda private ne asibitin, gashi kuma Jannat ta kwanta itama ranar da aka kawo Imran itama an bata magani kuma, Girgiza kai yayi yace, "Toh shikenan nagode." Daga haka Abba ya mik'e ya fita.


Mufeedah kuwa ya hango a zaune yana d'an tab'a wayar ta ya k'araso wajan ya kalle ta yace, "Mufeedah." Jin Abba ya kira ta ya saka ta ta d'ago ta kalle shi tare da mik'ewa tsaye cikin girmamawa tace, "Na'am Abba."

"Ashe gabad'aya hidimar asibitin kece kika d'auki nauyi? Hidimar ai tayi yawa Mufeedah."


Murmushi tayi ta sunkuyawar da kanta tana wasa da hannun ta tace, "Babu komai Abba ai an zama d'aya."

Abba ya d'ora da fad'in, "toh angode Allah ya saka miki da alkhairi ya baki miji na gari." A la66an ta yaga ta amsa da Amin tana cigaba da murmushi.


Abba ya kalli sauran mutanen wajan yace, "naje na samu Dr nace a bani list na abinda aka kashe shine yake shaida min ai komai ta biya kuyi mata godiya kuma, tayi hidima sosai sai fatan Allah ya saka mata da alkhairi." Babu wanda baiyi farin ciki ba aka kuma yi mata godiya cikin nuna tsantsar murna da da jin dad'in hakan.

Ita dai kawai murmushi take yi tana wasa da hannun ta ko kad'an ta kasa cewa komai.


A lokacin Muhsin ya dawo wajan ya zauna daga can gefe yana aikin kallon Jannat da ta dake a zaune tayi tagumi da hannu biyu, bai san iya adadin soyayyar Jannat da Allah ya d'ora masa ba, kullum ninkuwa son ta yake a zuciyar sa ya k'agu ayi auren sa da ita ya kai gidan sa ko abinda yake ji a ransa zai sassauta. Nura ne ya shiga d'akin yaga Imran ya bud'e ido yana kallon sama da alama ya d'an jima da farkawa.


Nura ya k'arara inda yake ya zauna kusa dashi yace, "Abokina me kake tunani haka?."

Kallon Nura yayi ya lumshe ido ya bud'e a fuskar Nura yace, "Nura da gaske ne Jannat aure zatayi?." Nura ya d'aga masa kai alamun eh kana yace, "Da gaske mana Imran, ni da kaina Abba ya kira ni muka je asibiti aka yi musu gwajin jini ita da wanda Abba ya gabatar maka yanzu."


"Hasbunallahu wani'imal wakil, Nura k'irji na zafi yake min." Ya fad'a yana numfashi dak'yar sabida zafin da yake ji a ransa. Nura yace, "Sannu, ka daina saka damuwa a zuciyar ka ina ji a jiki na har yanzu Jannat taka ce Imran." Da glass d'in idon sa ya kalle shi idon sa ya tara ruwa yace, "ta yaya kenan Nura? Yau fa saura kwana shida akace ko bakwai ne a d'aura mata aure, ta yaya zata zama tawa Nura?." Ya fad'a cikin rauni da nuna zallar karayar sa a fili.


Dafa kafad'ar sa Nura yayi yace, "Kar ka bari ruwa ya fito daga idon ka mana Imran ka manta a halin da kake ciki ne, kayi hak'uri ka jure mu cigaba da addu'a bamu san abinda Allah ya b'oye ba." Ajiyar zuciya Imran yayi kana yace, "ni ba auren nata ne ma damuwa ta ba wanda zata aura d'in shine damuwa ta."


Sallama Dr ya hana Nura magana ya shigo yayi masa tambayoyi duka ya bashi amsa ya sake auna bp sa yaga ba laifi ya sauka sannan ya bawa Nura takardar sallama.


Bayan fitar likitan ya sanar dana waje duka suka shigo aka fara had'a kayan da suke d'akin wanda suka san anzo dashi. Jannat gabad'aya tasha jinin jikin ta ta kasa sakewa a haka har aka gama had'a komai suka fito,Nura ne ya rik'o Imran d'in suka fito daga d'akin aka samu Muhsin a tsaye yana jiran fitowar su.


A harabar asibitin suke a tsaye Mufeedah tazo ta bud'e motar ta tace, "kuzo mu tafi." Da kanta ta bud'ewa Umma da Gwaggo da Anty Surayya suka shiga baya. Har Mufeedah ta fara jan motar Jannat ta k'araso tace ta tsaya ta kuwa tsaya ta shiga gaban motar tata dan haka kawai taji baza ta iya shiga motar Muhsin Imran na kallon ta ba.


Imran ya kalli Nura yace, "Nura muje." Muhsin da ya k'araso wajan yace, "haba babban Yaya ka bari muje na sauke ku." Kallon sa Imran yayi yace, "ba gida zamu je ba, nagode sosai." Daga haka suka yi gaba abin su suka hau machine d'in Nura suka ja suka tafi.


Da kallo Muhsin ya bisu yana wani irin murmushi mai d'auke da ma'anoni da yawa ya shiga motar sa ya tafi dan Abba ma ya tafi.

Mufeedah har gida sai da ta raka su Umma sannan ta tafi gida suna ta yi mata addu'a har ta tafi.


Kasancewar Yamma tayi dukka an hallara a gidan Umma ana jiran shigowar Imran, har sukayi awa d'aya da dawowa shida Nura basu shigo ba sai daga baya akaji sallamar su kowa ya mayar da hankalin sa ga shigowar su.


Tass an aske sumar da ta taru a fuska da kan Imran sai kad'an da aka bari kamar yadda ya saba barin ta sosai yayi kyau sai ramar da take tare dashi har lokacin. K'arasa shigowa sukayi shida Nura suka zauna a tabarmar da take shinfid'e a tsakar gidan Anty Surayya tace, "Sannu Imran, kana jin dad'in jikin naka dai ko?."

D'ago idanun sa yayi ta cikin farin glass d'in sa ya kalle ta cikin maganar sa da bata fita sosai yace, "Da sauk'i, Umma zan d'an kwanta." Ya fad'a yana kallon Umman nasa da take ta kallon sa.


"Yamma tayi ai Imran ka bari ayi i'sha sai ka kwanta." D'an girgiza kai yayi yace, "Ina so na huta ne kafin lokacin sallah yayi." 

"To shikenan."

"D'akin babu k'ura?."

Umma tace, "Ai babu ranar da zata fito ta koma k'anwar ka bata gyara maka d'aki ba, D'akin ka lafiya lau yake kamar kana ciki."

Baice komai ba ya mik'e suka bar wajan shida Nura suka shiga cikin d'akin. 


Tun daga lokacin mutanen y'an unguwa suka fara shigowa ana taya Umma murnar bayyanar Imran mata da maza har dare Umma bata daina karb'ar mutane ba. Bayan sallar i'sha Imran yana zaune kusa da Umma Anty Surayya ta tafi gida sai Gwaggo da Jannat a zaune a wajan, abincin da aka ajjiye masa yake juya cokali a ciki gabad'aya bashi da sha'awar cin komai burin sa d'aya ya samu lokaci su tattauna da Jannat ya amayar mata da abinds yake zuciyar sa ko zai samu sassauci akan abinda yake damun sa.


"Imran!" Gwaggo ta kira sunan sa a tausashe. D'ago kai yayi ya kalle ta tace, "Baka jin dad'in abincin ne? In kana son wani abun ka fad'a sai ayi maka." D'an murmushi yayi kad'an yace, "A'a Gwaggo ciki nane kawai a cushe bana jin zan iya cin komai."


"Amma Yaya ya kamata kaci kasan fa yanzu kana da ulcer kuma in baka ci abinci ba ta yaya magani zai maka aiki?." Jannat da take ta kallon sa ta fad'a kamar zatayi masa kuka. Kallon ta yayi ya d'an lumshe ido ya bud'e su a fuskar ta kafin ya janye idon sa daga kanta ya debi abincin cokali d'aya ya kai bakin sa.


Cokali uku yayi gabad'aya ya ture abincin yana yatsine fuskar sa dan sosai baya jin dad'in jikin sa da zuciyar sa, "Imran ya akayi ka kub'uta daga hannun y'an garkuwa da mutanen?." Umma ta tambaya tana kallon sa.


Kallon Umma yayi kafin yace, "Umma waye yace y'an garkuwa da mutane ne suka sace ni?." Umma tace, "To in basu bane Imran waye zai sace ka? Ai kowa yasan aikin sune." D'aga kai yayi kafin yace, "Haka ne, Allah ne ya bani iko kawai sai gani na nayi a kan titi a lokacin idanu na basa gani gashi bana iya magana, k'afafu na basa iya d'auka ta hakan ya saka na buge da wani dutse shine naji wannan ciwon, in banda Allah ya kawo Mufeedah kan titin ba da ban san me zai faru ba."


Cikin jimami da al'ajabi Gwaggo tace, "Allah ya saka maka ya bi maka hakkin ka, in ba rashin imani ba ina zaka d'auke mutum daga cikin iyalan sa a kai shi wani waje kawai tsabar zalunci da neman kud'in haram." Jannat da take ta kuka tace, "Yaya to ya akayi basu kira sun nemi kud'in fansa ba?." Kallon ta yayi na wasu mintina har ta tsargu ta d'auke idon ta daga cikin nasa kafin yace, "Sun nemi number waya sai na hana dan bana so a tayar muku da hankali shiyasa nace kawai su kashe ni."


"Amma Imran ai ba'a haka rai ai yafi dukiya, yanzu da sun kashe ka fa?." Umma ta fad'a tana kallon sa. 

"Umma kenan, yanzu ko sun fad'i kud'in an basu kashe mutum suke yi, ni nasan in akayi muku wayar akace ku bada wani abun sai dai ku saida gidan nan ku aika da kud'in kuma k'arshe a kashe ni kinga anyi biyu babu kenan."


Gwaggo ta tausasa murya tace, "Amma Imran duk da hakan ai ba'a san inda za'a dace ba tunda addu'a ake tayi, yanzu dubi yadda suka wahalar da kai sun ja maka maka matsalar ido ga ciwo da dama a jikin ka, Allah dai ya saka maka ya bi maka hakkin ka."


"Ai yanzu Allah za'a yiwa godiya Gwaggo tunda gani na dawo babu wata nakasa a tare dani." Ya fad'a yana kallon su dan yaga gabad'aya sun d'aga hankalin su shiyasa yake k'okarin kwantar musu da hankali. Jannat da take kuka ta share idon ta tace, "Allah ya saka maka Yaya na ya bi maka hakkin ka." 


Kallon ta yake yi kawai ya kasa cewa amin sai lumshe ido kawai da yayi ya bud'e ya sunkuyar da kansa k'asa. 


Wayar Jannat ce da take kusa da Imran ce take ta k'ara alamun shigowar kira hakan ya saka shi d'auko wayar da niyar mik'o mata, idon sane ya sauka a akan screen d'in wayar ba tare da yaso hakan ba yaga jaan da emoji na heart a gaba yana yawo a jikin screen d'in. D'ago kai yayi ya kalle ta suka had'a ido baice komai ba ya mik'a mata wayar ba tare da yace mata kazil ba.


Ganin mai kiran sai ta kasa d'aga wayar jikin ta yayi bala'in sanyi bata san dalilin hakan ba har wayar ta katse, sake shigowa tayi ta sake katse a karo na biyu ta sake shiga a karo na uku. "Malama ki d'auki wayar mana kina ji tana ta k'ara" Gwaggo ta fad'a tana kallon ta.


Hannun ta har rawa yake ta d'auka ta kara a kunne ba tare da tace komai ba ta kashe ta mik'e tsaye ta shiga d'akin Umma, jim kad'an ta fito da mayafi sumi-sumi ta fita ba tare da ta kalli kowa ba.

Tana fita shima ya mik'e baice komai ba ya saka takalmin sa ya bar tsakar gidan ya shiga d'akin sa da yake soron gidan.


Har safe Imran bai sake ganin Jannat ba domin bai bari sun had'u ba kwanciya yayi yana jinyar kansa.

Da safe ma haka aka cigaba da karb'ar bak'i ana ta shigo murnar ganin Imran shi kuwa yana d'aki ko fitowa baya son yi ma. Kamar jiya dukkan su suna zaune a tsakar gida ciki har da Yaya Binta da Anty Imran d'in ya k'araso inda suke ya zauna yace, "Sannun ku." Anty Surayya tayi y'ar dariya tace, "kaine da sannu ai Imran, yau naji maganar taka ma ta kuma fitowa sosai ba kamar jiya ba."


Gwaggo tace, "abinda zance kenan wallahi." D'an murmushi yayi Yaya Binta tace, "Wallahi Imran yarinyar nan Mufeedah tayi hidima da kai sosai, tun baka nan ba'a kwana uku bata zo ba, kayan abinci kuwa kusan duk sati biyu sai ta kawowa Umma ga kud'i da take bayarwa, gaskiya yarinyar tana son ka dan wannan kulawar da take nunawa ba iya matsayin shugabar ka bane akwai wani abun a k'asa."


Jin abinda Yaya tace ya saka shi murmushi baice komai ba sai kallon mutanen wajan da yake yi kana yace, "Ina Jannat?." Anty Surayya tayi murmushi tace, "tana gidan Gwaggo kasan amarya tana ta shan gyara." Wani irin dummm yaji a zuciyar sa yayi tari kad'an kafin ya mik'e ya fita ba tare da yace komai ba ya fita daga gidan.


Gidan Gwaggo ya shiga ya same ta a zaune a inuwa ita kad'ai ya shigo da sallama, amsawa tayi ta mik'e tsare tare da fad'in, "Sannu da zuwa Yaya na." Bai amsa ba sai kallon ta da yake yi yana k'arasowa cikin gidan cikin taku a hankali yana bin ta da wani irin kallo da ya saka ta dole ta sauke idon ta k'asa. 


"Jannat!." Duk da maganar sa bata fita sosai hakan bai hana ta jin a yanayin da yayi maganar ba ta d'ago ta kalle shi gaban ta yana wani irin fad'uwa ganin irin kallon da yake mata tace, "Na'am Yaya." Matsowa yake a hankali har yazo gab da ita yana kallon cikin idon ta, da sauri ta sauke kanta kasa numfashin ta na wani irin fizga daga k'irjin ta, yanayin da tayi watanni bata ji shi a jikin ta ba taji yana taso mata yana kuma zaga ko wanni sassa na jikin ta.


"Ki gasgata min abinda nake ji kuma nake gani Jannat, da gaske ne rana e ta yau zaki auri Muhsin?" Cikin wata irin murya ya fad'a mai d'auke da zallar zak'i da jefa zuciya cikin karsashin mai sauraren ta. Lumshe ido tayi ta bud'e gaban ta na wani irin duka uku-uku yanayin ta ya canja gabad'aya hankalin ta ya kai k'arshe wajan tashi.


Shiru tayi ta kasa bashi amsa domin kuwa bata san me zata ce masa ba haka kawai ta tsinci kanta da kasa furta masa komai sai jikin ta da yake rawa sosai, "shirun ki ya tabbatar min da abinda nake ji gaskiya ne Jannat zaki auri Muhsin, Jannat ina alqawarin da kika yi min a kan Muhsin?."


D'ago ido tayi ta kalli idon sa taga wani ruwa ya taru a ciki har wani narai-narai yake a cikin idon sa ta sake mayar da kanta k'asa hawaye na sakko mata daga idon ta, "ki amsa min Jannat ina alqawarin da kika yi min? Ashe zaki iya karya wannan alqawarin da kika d'auka kika kuma ce baza ki karya shi ba har abadah Jannat?."


Girgiza kai take tana kuka tace, "kayi hak'uri Yaya banyi hakan dan na karya alqawarin dake tsakanin mu ba."

"To dan me kika yi?."

"Yaya kace kar na bari wani sab'ani ya shiga tsakani na dashi a kan haka nayi alqawarin ba akan kar na bari na fara soyayya dashi ba."


Duk da idon sa na masa ciwo bai hana shi ware idanun sa nasa ba yana kallon ta da kuma mamakin furucin ta yace, "Jannat ni Imran kika fad'awa ai fad'a na hana ki dashi ba soyayya ba right? Jannat kina cikin hankalin ku kuwa?." 


D'ago ido tayi ta kalle shi hawaye na bin fuskar ta tace, "Yaya na bayan b'acewar ka na shiga damuwa da tashin hankali wanda ban tab'a shiga irin sa ba, dalilin hakan na daina zuwa makaranta har hakan ya kaini ga maimaita aji da muka bari su Nafisa sukayi gaba suka wuce ni, Umma ta saka ni na koma makaranta ba dan naso ba sai dan bin umarnin ta kawai domin tunda ka b'ace na rasa nustuwar da zanyi karatu gabad'aya, wallahi Yaya taimako ne ya fara had'a ni da Muhsin ranar da muka tashi daga makaranta na kai dare wasu suka zo yin raping d'ina ya taimaka min, bai kuma takala ta da fad'a ba tun bayan b'acewar ka sai alkhairi."


Yana jin ta yana kallon ta kawai yana jin maganar ta har cikin zuciyar sa yake jin ta, "Jannat shine kika cire zoben alqawarin da na baki kenan kika bashi shi ya saka a hannun sa?." Kanta ta sunkuyar ta kasa amsa masa maganar sai hawaye da yake bin idon ta tana jin wani iri a zuciyar ta da jikin ta da kuma namakin ya akayi yasan ta bawa Muhsin zobe?.


"Why Jannat? Why zaki saurari Muhsin har ya kaiku ga maganar aure? Meyasa baki jira ni ba kika amshi soyayyar sa Jannat?." Jin yadda yake maganar ya saka ta kalle shi tace, "Da farko ban so na amince ba Yaya sabida bana jin zan so wani duniya bawan wanda naso a baya, nasiha su Umma suka dinga min suka ce na amince dashi dalilin da ya saka na amince kenan har maganar aure ta shiga tsakani."


"Why Jannat,! meyasa kika d'auki nasihar su kika amshi soyayyar wani bayan wanda kike so yana raye shima kuma yana sonki." Ya fad'a cikin murna mai nuna tsantsar raunin da yake ciki a lokacin.


D'ago ido tayi ta kalle shi hawaye na sake zuba a fuskar ta cike da mamakin abinda taji yana cewa, "Eh Jannat, nine wanda kike so har soyayyar ta ke kaiki ga kwanciya asibiti, nine wanda kika bani labari kika ce kina son sa ba kuma kya tunanin zaki cire soyayyar a ranki da na tambaye ki sunan sa kika ce min ya mutu, nine wanda kike so ya zama miji a wajan ki kuma uban y'ay'an ki, nine wanda zuciyar ki take so ba Muhsin ba, nine wanda kika tashi da son sa kika rayu da son sa kika kai yanzu da sonsa a ranki, nine wanda soyayyar sa ta zama ZANEN ZABUWA a zuciyar ki wacce babu ruwa ko k'arfe da zai kankare ta a zuciyar ki, nine wanda kike so Jannat! Ni Imran ni kike so a kaina kuma kike kwanciya a asibiti!."


Zuwa lokacin jikin ta fara rawa kamar an jona mata shocking hawaye na ambaliya daga idon ta, fat, fat, fat haka zuciyar ta take bugawa kamar zata cinke daga k'irjin ta, ranta na wani irin suya kamar an ciro shi an d'ora shi a kaskon wuta haka take ji, kasa d'aukar ta k'afafun ta sukayi ta zube a wajan tana wani irin kuka mai d'auke da zallar k'aunar Yayan nata da kuma tausayin kanta.


"Kasan da cewa kaine nake so Yaya ka barni nake shan wahala a baya? Ka san da hakan ka dinga wahalar da zuciya ta,? kasan da hakan kake zuwa ka tirke ni akan sai na fad'a maka wanda nake so bayan kasan kai nake so,? kasan da hakan kake bari rayuwa ta take shiga garari da tashin hankali bayan kana da yadda zakayi,? Meyasa baka nuna min ka fahimci yanayi na akan ka ba sai yanzu?!" Ta fad'a cikin murya mai amo hawaye kuma na zuba daga cikin idon ta.


"Ranar da na fahimci hakan a tare dake shine na kira ki a waya har nake ce miki koda nine wanda kike so d'in zaki iya b'oye min, kin tuna anyi hakan ko? Kin tuna nace miki da safe zan fad'a miki wani abu? A safiyar aka nemi aka rasa, na b'ace da wannan burin a zuciya ta Jannat, koda na kasance bana tare dake kullum cikin tuannin ki nake domin zuciya tana tare dake a koda yaushe, Ina son ki Jannat kamar yadda kike so na, na rayu da sonki kamar yadda kika rayu da sona, duka tsahon wannan lokacin ke na tsaya jira shiyasa ban tab'a kallon wata mace matsayin wacce zan so ko zan aura ba, ki fahimce ni kar kiyi min mummunar fahimta dan Allah" duk da yadda kansa yake sarawa hakan bai hana shi jurewa yana amayar mata da abinda yake zuciyar sa ba dan in ya cigaba da b'oyewa zuciyar sa zata iya fashewa.


Da wani irin firgici ta d'ago kai tana kallon sa jin abinda yace ya firgita ta dan batayi tunanin hakan daga bakin sa ba, idanun su suka had'u ya d'aga mata kai alamun eh kafin ya cigaba da fad'in,


"Ban tabbatarwa kaina ina sonki ba sai da na b'ace nayi nisa dake, a wannan lokacin na tabbatarwa kaina ke d'in zuciya tace, ke d'in rayuwa tace, ke d'in jinin jiki nace, ke d'in kece komai nawa Jannat, dan Allah dan annabin rahama kar ki cewa soyayya ta A'a k'anwa ta, domin son ki ZANEN ZABUWA ne a zuciya ta da gangar jiki na, Allah ne ya halicce shi a zuciya ta nima kawai jin sa nayi ba tare da nasan yaushe ya shige ni ba, ban san yacce zan kasance ba in na rasa ki a matsayin matata, domin ke d'in babbar jigo ce a cikin rayuwa ta."


Girgiza kai take hawaye na zuba daga idon ta ta mik'e tsaye kamar mahaukaciya tace, "ka makara Yaya na, lokacin da na so ka kai sai kake nuna ban kai matsayin ka soni ba har kayi fatan na kasance mata a gare ka, yanzu kuma na riga na amshi soyayyar wani an saka mana ranar aure yau saura sati d'aya kacal ya zama miji na na zama matar sa, rana e ta yau e yanzu na zama matar sa, kayi min halacci a rayuwa ta, ka sadaukar da farin cikin ka, lokacin ka, kuruciyar ka sabida ni, amma bazan iya rabuwa dashi a kanka ba Yaya na, bazan iya rabuwa dashi ba sabida abinda kayi min ba kai da iyayen ka kayi hak'uri....." ta k'arasa fad'a cikin kuka mai sauti sosai mai karya zuciya.


Hawayen da Imran yake ta rik'ewa yana hana su zubowa suka sakko masa suka gangaro ta cikin glass d'in sa suka samu makwanci a kuncin sa kana yace, "A dalilin b'ata na ya saka zaki aure shi, nasan da hakan kema kuma kin sani Jannat, domin da ina nan bai isa yazo kusa dake ba balle har yayi karanbanin cewa zai aure ki, yanzu kuma na dawo why zakiyi rejecting soyayyar da nazo miki da ita wacce kike da tabbacin ta gaskiya ce bata k'arya ba?."


Hawaye idanun ta ta share ta kalle shi tace, "Sabida bana son ka Yaya, ban tab'a jin ina son ka ba balle har nayi sha'awar shinfid'a rayuwar aure da kai ba, Muhsin nake so kuma shi ne wanda zan aura ba kai ba."


Zare glass d'in idon sa yayi haske ya kawowa idanun sa ziyara ga hawayen da yake zuba daga idon hakan ya saka shi saurin runtse idon sa ya matsa daga inda yake ya koma kusa da ita yana k'okarin bud'e idon yace, "K'arya kike yi Jannat, wallahi k'arya kike, ni Imran nine wanda kike so ba Muhsin ba ga idanun ki nan ya nuna hakan, na tabbata kuma kina jin hakan a cikin zuciyar ki, meyasa baza ki karb'i abinda zuciyar take kawo miki ba?."


"Bana son ka Yaya!, na fad'a maka bana son ka, in tak'amar ka da na so ka yanzu bana son ka ko kad'an ba kuma na k'aunar kasancewa matar ka har abadah, yanzu baka gaba na Muhsin shine kad'ai wanda yake cikin zuciya ta nake kuma burin auren sa, dan Allah kayi hak'uri ka nemi wata." Ta fad'a tana had'e hannayen ta waje d'aya sabbin hawaye suna sakko mata.


"K'arya kike Jannat kina sona, kuma ni zaki aura ba Mushin ba."

"Wallahi bana sonka kuma bazan aure ka ba."


Ya nuna kansa da yatsa yace,"Sabida shi yana da kud'i ni kuma takala ne shiyasa kike cewa bakya sona ko? Sabida shi yana da lafiya ni kuma yanzu bani da maraba da makawo shiyasa baza ki iya aure na ba ko?." Ya fad'a cikin karaya yana kallon ta duk da baya ganin ta sosai.


Da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a tace, "ba sabida haka bane, ni ba abinda nake nufi ba kenan."

"To sabida meye? Indai ba sabida haka bane meyasa baza ki amince da abinda zuciyar ki take so ba?."


"Sabida bana son ka Yayana, bana son ka, ka tsaya matsayin Yaya na kamar yadda kake fad'a a baya, ni kuma zan kasance matsayin k'anwar ka har abada kamar yadda kake fad'a kaima."


Kuka take yi sosai shima kuma kukan yake yi domin ya kasa jure abinda yake ji a cikin zuciyar sa zubar da hawayen shine mafita a gare shi, ya k'arasa inda take ya kamo hannayen ta yace, "Jannat dan Allah kar k'i amince da soyayya ta, in kikayi hakan dai-dai yake da rasa rayuwa ta Jannat, wallahi in na rasa ki zan iya rasa rayuwa ta gabad'aya."


Fizge hannayen ta tayi a fusace tace, "Na fad'a maka bana son ka, bana son ka akan me zaka takura min? Ana soyayya dole ne? Tunda nace bana yi ka k'yale ni ba kaine a zuciya ta ba yanzu, da naso ka kamar yadda kace amma yanzu baka da wani matsayi a zuciya ta in ba matsayin Yayana da kake dashi ba, dan Allah ka k'yale ni na auri wanda nake so kada maganar ka ta saka Abba yace bazan auri Muhsin ba, shi nake so ba kai ba, dashi zan rayu ba kai, kamar yadda kake ji in ka rasa ni zaka iya rasa rayuwar ka nima in na rasa Muhsin zan iya rasa rayuwa ta, kar kayi amfanin da power da kake da ita ka saka a fasa aure na da Mushin, matuk'ar hakan ta kasance sai na kashe kaina."


Zame yayi ya zauna ya had'a kai da guiwa yana ta kuka kamar mace ko yaro k'arami, zafi yake ji a zuciyar sa na tasowa daga cikin jinin sa yana zaga ko ina na jikin sa, ji yake kamar an kwashe jinin jikin sa ana tafasa shi a tunkuya yana farfasa haka yake ji. 


Sai da yayi kukan mai isar sa itama gana gefen sa tana nata kukan kafin ya share idon sa ya mayar da glass d'in sa ya k'araso inda take yace, "Kar ki damu Khadijah ina son ki duk kuma abinda kike so shi nake so, ina yi miki fatan alkhairi da fatan zaman lafiya keda Muhsin, ina rok'on Allah ya sa auren ku ya d'ore har aljannah, na cire soyayyar ki daga yau kamar yadda kika ce nayi, zan kuma nemi wata kodan na manta dake duk da nasan ba abu bane mai yuwa a gare ni ba, ki taya ni addu'a Allah ya bani ikon karb'ar k'addarar da ta tunkaro ni." Yana gama fad'ar hakan ya mik'e daga tsugunon da yayi.


Kansa ya dafe sabida wani irin sarawa da yake ji yayi ga idon sa da yake ganin biyu-biyu ya kasa bud'e shi ga jiri da yake d'aukar sa yana ganin tsakar gidan yana juya masa, baya yayi zai fad'i tayi sauri mik'ewa ta isa gare shi ta rik'o shi ta baya. Kwace jikin sa yayi ya juyo yana kallon ta ya lumshe idon ya sake bud'ewa yace, "kar ki damu zan bar wasiyayyar koda na mutu yanzu kar a fasa aurin ki da Mushin."


Yana gama fad'a mata hakan yayi hanyar da zai fita daga gidan amma ya kasa gane inace hanyar da zata kai shi wajen don dukka kafofin wayo yaga suna yi masa a idon sa, in yaga wannan a nan to zai ga wata a kusa da ita, hannayen sa duka ya saka ya dafe kansa sabida juya masa d'in da yake yi Allah ya bashi dama ya dafa bango Allah ya bashi ikon ganin k'ofar ya fita daga tsakar gidan cikin mugun yanayin da yake ciki.


D'urkushewa tayi a wajan tana sakin kuka mai d'auke da ma'anoni da dama wanda ita kad'ai ta san su.


*End of Book 1*🤝


_hmmmmm bazan ce komai ba domin nasan ku kanku kun san ya wannan lamari na soyayya zai kaya a Book2. ga Imran ga Muhsin ga kuma Jannat a gefe, waye me nasarar mallakar Jannat matsayin matar sa? In ta kasance mata ga Muhsin ya rayuwar Imran zata kasance? Anya tayi masa adalci duk da tarin d'awainiyar da yayi da ita a duniya amma ta juyawa soyayyar sa baya.? Me zai faru in ta gane Muhsin wanda ta bar yayan ta sabida shi shine ya sace Yayan ta, zata cigaba da zama dashi ko A'a. In ta kasance mata ga Imran Muhsin zai bar su su zauna lafiya kuwa? Wacce fansa Muhsin zai d'auka akan dukkan su? Ya zaiyi da soyayyar da yake yiwa Jannat wacce ku kanku kun shaida ta gaskiya ce? Shin ita Jannat d'in zata amince ta zauna da Imran baya tace ba shi take so ba,? Ina furucin da tayi na sai ta kashe kanta in hakan ta kasance,? Zata hak'ura ta zauna dashi ko A'a.?_


_Amsoshin wannan tambayoyi duka suna cikin Book2 hanzarta ki biya naira 300 ayi wannan tafiyar dake, ina tausayawa wanda bai shigo jirgin book2 ba dan ina da tabbacin zai ciza tsaya domin tafiya ce me d'auke da abubuwa da dama a cikin ta, domin biya tuntub'i wannan number 2347045242700 ku samu naku dan kar ayi babu ku, but only on WhatsApp please._


Wattpad @Nana_haleema 

Arewabooks @nanahaleema11.