19
by @batulmamman
Mai martaba ya kalli Alh. Zahraddin da Khalid. Nutsuwa da rashin hargagin uba da ɗan sun yi matuƙar burge shi. Abi daban ya tsammaci gani daga garesu na nuna rashin jindadi.
"Ga mahaifinta zai yi mu ku ƙarin bayani."
Cikin rashin jindaɗi Hakimi ya labarta musu yadda Humaira ta same shi shekaranjiya da wannan batu. Mutum mai dattako yarinya ta sa shi sunne kai a gaban waɗanda ya girma a shekaru.
"A wajen na fatattaketa. Nayi zaton magana ta wuce kenan. Sai kawai ɗazu Mai martaba ya aike min da saƙon yana nemana. Wallahi Dini ba don a nan mu ke ba da jikinta ya faɗa mata."
Murmushi Alh. Zahraddin ya yi da rarrashi ya bawa Hakimi haƙuri.
"Wannan ba abin ɗaga hankali bane. Don Allah ka yi haƙuri. Duk ƙuruciyar yaro in ya kawo ƙorafi yana da kyau a saurare shi."
"Ni dai ki ka kunyata Uwata amma duk da haka ba zan so ɗana ya aureki ki hana masa kwanciyar hankali ba." Anti Baturiya ta furta babu wani alamun zancen bakinta ya kai zuci.
"Idan hukuncin a hannunki yake zaman me ku ke yi min a nan?" Sarki Mamman Bello Maituta ya yi maganar idanunsa a kanta.
Shiru tayi kamar an ɗinke bakin. Buƙatarta ta riga ta biya tunda ta samu ta faɗi irin hukuncin da take so.
Gyaran murya Sarki ya yi "Khalid akwai wani abu tsakaninku ne wanda ka ke ganin zai iya sanya ƴar uwarka canja ra'ayi?"
"Babu ranka ya daɗe." Ya bashi amsa a ladabce.
"Ita ma ta ce ba ka yi mata komai ba. Auren dole ba ya cikin abin da zan taɓa goyon baya. Amma ina ƙoƙarin ganin bamu kunyata gidan nan ba tunda haɗa kanku ku ka yi sannan iyaye su ka sani. Shi yasa nake son neman hanyar gyara al'amarin."
Yanayin Alh. Zahraddin sai ya karyar da zuciyar duk wanda yake wurin. Tsabar tashin hankali sai ya yi kama da an ƙara masa shekaru akan nasa. Jawabin Sarki na son gyara ɓarakar tun bata faru ba ne yaji ba zai iya yarda ya faru ba. Sun haɗa ido da Anti Baturiya yafi sau uku tana murmushin da ya fassara da na nasara. Ya kuma kula da irin kukan Humaira wanda babu makawa bai yi kama da na wadda bata son auren ba. Sai dai ace an tilasta ta tayi abin da ran ta ba ya so.
"Allah Ya baka yawan rai ko ina iya tofa wani abu domin warware matsalar?"
"Ina jin ka Dini."
"A matsayinka na ƙanin Nani kana cikin waɗanda su ka san yawan takun saƙar dake tsakanina da yayata. Da yaran nan su ka kawo maganarsu duk mun yi farinciki. Mun saka ran aurensu zai ɗinke duk wata ɓaraka da mu ka taɓa samu."
"Wannan haka yake" cewar Hakimi yana fatan kada gayyar ta watse.
"Canjin ra'ayin Humaira tun yanzu ni abin farinciki ne a gareni. Da yanzu sai anyi auren ayi ta samun matsala. Maimakon ƙarfafa zumunci mu dawo mu na abin kunya akan ƴaƴa. Saboda haka ina nemawa Humaira alfarmar don Allah ka amince a soke maganar aurensu da Khalid."
Hankali a tashe Hakimi ya ce "haba dai Alh. Dini. Ya za ka biyewa shirmen ƙuruciya? Wa za ta aura in ba shi ba?"
Anti Baturiya ta fara murnar ganin haƙanta ya cimma ruwa sai taga Hakimi zai ɓallo ruwan. A fakaice ta ɗan taɓa Humaira. Nan take kuwa ta kama kuka da magiya. Duk abin nan Alh. Zahraddin ya yiwa Khalid inkiya da ido akan kada ya ce uffan.
Bayan gajeruwar muhawara saboda Alh. Zahraddin ya gama ƙulewa, dauriya ce kawai yake yi. Sarki ya dube su ya ce ya soke maganar. Washegari sai su sanar da mutanensu ta waya. Tunda dama akwai auren ƴan uwan Humairan ba sai an gayawa duniya ba.
*
Da su ka fito Alh. Zahraddin karɓarmukullin motar ya yi ya ce da Khalid ya koma baya.
"Baba zan iya tuƙin." Ya ce da raunin murya.
"Ba na son musu."
Sannu a hankali ya dinga jan motar har gida. Masu gadi ne su ka fara mamakin ganin matuƙin motar tun a waje. Yana shiga ciki kuwa ƴan uwa su ka yi caaa akan motar. Kunyar abin da zai faɗa musu kaɗai ta ishe shi. Ana ta yi masa sannu da zuwa ya amsa da ka.
"Ka daure zuciyarka ka fito." Shi ne abin da ya ce da ya juya ya kalli Khalid.
Zuƙatansu duk babu daɗi su ka fito. A bakin ƙofa su ka iske Ansar da Sumayya su na fitowa.
"Ansar shiga da ɗan uwanka ɗaki. Don Allah ka zauna da shi har na zo."
To kawai ya ce ba tare da tsawaita magana ba. Ido ba mudu ba ai ya san ƙima. Kana ganinsu ka san babu lafiya. Sumayya bin Alh. Zahraddin tayi sama da sauri. Ya juyo ya dubeta.
"Ki koma ki ce da masu shirin tafiya wajen biki su dawo."
"Baba?"
"Ki yi sauri Andalin." Za ta juya ya tsayar da ita "su waye daga nan a wurin?"
"Su Ya Siddiqa ne. Daga gidan Ya Nurain su ka tafi."
"Je ki kiyi abin da na saka ki."
Da ikon Allah ya ƙarasa falon dake haɗe da ɗakinsa. Bai yi mamakin ganin Haj. Zatu tana ta kai gwauro da mari ita kaɗai ba. Da ta gan shi bata iya jira ya iso ciki ba ta bi shi bakin ƙofar tana tambayarsa abin da yake faruwa. Agogon hannunsa ya kalla sai ya ɗaga mata hannu don ta dakata da tambayar. Ko zama bai yi ba ya ciro wayarsa ya kira Siddiqa. Sai da ya kira sau biyu saboda ƙida sannan ta ji ta ɗauka.
"Ki saurare ni da kyau Siddiqa. Ina so ki bi duk wanda ki ka san daga bangaren Hajjaju ya zo wurin nan ki faɗa musu su taho gidan nan a sirrance."
Gumi taji ya karyo mata "Baba me ya faru?"
"Kin san Haj. Nafi?" Ta gane ta. Yayar marigayiya Ramatu ce wadda ta riƙeta "ita ma ki faɗa mata na ce duk ƴan uwansu su taho."
Ƙara shiga tashin hankali tayi. Ta fara faɗawa su Lubna da Ummu tunda tebur ɗinsu ɗaya sannan ta tafi neman Haj. Nafi. Dattijuwar mata ce wadda su Imam su ka mayar kaka tunda ita ta riƙe mahaifiyarsu. Kan ka ce kwabo wuri ya soma hargitsewa kuwa. Don ma Siddiqa ta tsaya tsayin daka wurin ganin ta ba a zauna ƙananan maganganu ba. Tana faɗin saƙon Ummu kuma tana tabbatar da an fita da sauri. Ɓangaren zaman dangin su Haj. Nafi su ma kusan duk waje ɗaya su ke. Tashin su ne lokaci ɗaya ya janyo aka fara magana.
Anti Ramlatu ta baro inda take karɓar baki ta tsayar da Siddiqa.
"Siddiqa lafiya? Ya naga ana ta fita?"
Saƙon Baba ta faɗa mata wanda a take ta ga wani irin ɓacin rai ya saukar mata.
"Lallai Yaya Baturiya" ta furta da ɗacin rai.
Ba ta raba ɗayan biyu ta san cewa ita tayi wani abin. Anti Zayya ta tafi nema tunda har yanzu bakinsu ɗaya. Ta ja ta gefe ta soma masifa.
Jikin Anti Zayya ma ya yi sanyi don sai da ta nemi kujera ta zauna.
"Wallahi babu ruwana Ramlatu. Ta faɗa min ba za ayi auren nan ba komai runtsi. Nayi ta bata shawarar indai haka ne gara tun kafin a kai kuɗi ta lalata komai. Da naji shiru nayi zaton ta fasa."
Anti Ramlatu harda hawaye ta ce mata "ai mugu ba ya amsa sunansa sai ya yiwa kansa mugunta. Yaya Dini da Khalid ba su da asara wallahi. Kuma ki faɗa mata Nani ta tozarta ba wani ba. Khalid kuma in anyi duniya don Sayyidina Rasulullahi aurensa ranar asabar ba zai tashi ba."
Tana gama faɗin haka ta kama hanya ta fita. Tun a mota ta kira maigidanta wanda ya kasance ɗaya daga cikin ƴaƴan Madakin Kano ta faɗa masa komai. Yana Kaduna wajen aiki inda abokiyar zamanta take.
"Yallaɓai ba zan taɓa yin gaban kaina ba. Ina hanyar gidan Yaya Dini yanzu. Idan ka lamunce min zan faɗa masa ka bawa Khalid Ayshe."
"Ramlatu kada ɓacin rai yasa ki ƙulla abin da zai ƙara janyo fitina fa" ya gargaɗeta "gaggawa daga shaiɗan take."
"Shi yasa zan kira ta ita ma kafin na ƙarasa. Izininka kawai nake nema. Nayi maka alƙawarin ba zan tilasta ta ba."
"Allah Ya baki ladan zumuncin da ki ke son gyarawa Ramla. Ki sani cewa tun lokacin da ki ka raba kanki da halayyar su Baturiya darajarki ta ƙaru a idanuna. Duk duniya babu abin da ya kai zaman lafiya da kyautata zumunci daɗi."
Kanta wani irin girma ya ƙara da wannan yabo. Ita ma shaida ce. Tun rasuwar Nani da ta canja tsarin rayuwarta miji ya dawo mata fiye da farkon aurensu ma. Godiya tayi masa sannan ta kira Ayshe. Yarinyar ajinta huɗu a Jami'ar kimiyya ta Wudil (KUST). A gida ta baro su suna shiryawa ita da ƙannenta za su je wurin kamun. A iya saninta bata da wani tsayayye. Amma duk da haka ta fayyace mata komai bayan taji ba su riga sun fita ba.
"Kin amince?"
Murmushi Ayshe tayi. Wannan shi ne tsintar dami a kala. Ita a su wa za ta ce bata son yayanta Khalid? Duk wani ɗan Kawu Dini ma ai abin so ne. Balle Khalid da yafi dukkaninsu sakin fuska da jan mutane a jiki.
"Ki yi min magana, mun kusa isa gidan."
"Mama na amince" sai ƙit ta kashe wayar.
Ƙannenta dai kasa gane kanta su ka yi saboda wani irin juyi da take ta faman yi tana hamdala. Bata taɓa sako Khalid cikin irin mazan da take son aure ba saboda ganin yafi ƙarfinta ta kowacce fuska. Sai gashi addu'arta ta samun miji nagari ta sami karɓuwa a lokacin da bata taɓa zato da tsammani ba. Keɓewa tayi daga idanun kowa ta kai goshinta ƙasa cikin godiya da yabawa ƙudurar Al-Musawwiru.
*
Yayinda Haj. Zatu take ta salati cikin jimami bayan ya gama faɗa mata, Alh. Zahraddin zama ya yi ya riƙe kansa a falon . Bata ankara ba sai ganin zubar hawayensa tayi.
"Alhaji don Allah..." ita ɗin ma kukan ta kama yi.
Hawayen ya share da tafukan hannayensa ya ce "Hajjaju a yau na ƙara sanin cewa lallai mutum ya guji zama silar wanzuwar wani aiki mara kyau. Domin ko ya tuba babu lallai waɗanda ya ɗora akan turbar aikinsa su bari."
"Haka ne" ta sami kanta da cewa duk da bata gane me yake nufi ba.
"Nani ce ta fara janyo min ƙiyayyar ƴan uwana akan auren Ramatu. Wallahi ba don anyi gwaji an tabbatar min da ciwonta ba da haka kawai ta rasu zan ce zuciyarta ce ta buga da baƙincikin dangina."
Yana wannan magana basu san cewa Imam da duka ƙannensa su na ƙofar ɗakin ba. Harda Siddiqa da shigowarta kenan Sumayya ta faɗa mata. A wajen Khalid su ka ji abin da ya faru. Shi ne Imam ya ce su je su lallashi mahaifin nasu domin yadda Ansar da Sumayya su ka ce sun gan shi ya ɗaga musu hankali.
Sallama su ka yi da kansa ya ce su shigo. Da dai Ansar ya ganshi garau ba yadda su ke tsammani ba sai ya juya. Haka ma Siddiqa.
"An nuna min fin ƙarfi akan ƴar da ban haifa ba. Shi ne ku ma za ku tafi don ku nuna min ba ni ne mahaifinku ba?"
Da sauri su ka dawo su na bashi haƙuri. Ya dubi su Imam ya ce da su,
"Ni da Nani mun yafewa juna kafin ta bar duniya. Ina so don Allah kuma ku yafe mata. Kada wannan abu yasa ku ƙullaci tsohuwata dake kushewa." Ya ƙarashe maganar da wasu hawayen da bai san dasu ba.
Mazan babu wanda bai yi hawaye ba. Siddiqa da Sumayya kuwa kafaɗunsu ya rungumo yana lallashinsu. Ansar dubansa ya dinga a nutse yana lura da hawa da saukan numfashinsa domin gujewa afkuwar wani abu.
"Ku share hawayenku mu je mu bawa mutanen ƙasa haƙuri. Sai ku kikkira abokananku. Nima bayan isha abin da zan yi kenan in sha Allahu."
Imam nazarinsu ya yi gabaɗaya. Ya auna mutumci da ƙimar mahaifinsu wanda ga dukkan alamu su Anti Baturiya ta so zubarwa wanwar. Tabbas idan ba a ɗaura auren nan ba ranar asabar tayi galaba. Shi kan shi Khalid ba ƙaramin taɓuwa zai yi ba. Don ya yi imanin ƙarairayi marasa tushe za a fara yamaɗiɗi da su wanda za su taɓa mutumcinsa.
Gaban Haj. Zatu dake zaune akan kujera yaje ya durkusa a gabanta. Su na kallonsa ya kama hannun ya riƙe. Ya ɗora ɗaya hannun ya rufe shi.
"Shekarun baya Baba ya nemi alfarmar ki shigo gidan nan a matsayin uwa a garemu. Duk da yadda amincewarki ta taɓa zumuncinki da su Nurain amma kin jure kin yi mana riƙon ƴaƴan cikinki."
"Tsoro ka ke bani Imam. Mene ne?"
"Alfarma nake nemawa ƙanina a wajenki."
"Ni kuma Imam?" Ta ɗaga ta dubi su Alh. Zahraddin sai taga dukkansu ita da Imam su ke kallo.
"Umma don Allah kada a fasa auren nan ranar asabar. Ki yi min izini in nemawa Khalid aure yanzun nan."
Jikinta ya bata tun bai faɗa ba. Jajayen idanunsa dake ƙoƙarin ɓoye ainihin ciwon da abin da ya faru ya janyo ta kalla. Sai ta gyaɗa kai. Ya kuwa juya inda har yanzu Alh. Zahraddin ke tsaƴe da ƴan matansa ya ce,
"Siddiqa."
Gabanta ya faɗi domin yana kiran sunanta su ka haɗa ido da Khalid. Ba shiri ta sake ɓoye fuskarta a jikin Alh. Zahraddin. Imam ya waiga yaga Khalid tsaye a kusa da Yusuf.
"Dalla can don ubanka ba za ka matso ba?"
Yusuf da Muhammad su ka sa hannu su ka turo Khalid gaba su na dariya. Da ya tsaya a gefen Imam kasa magana ya yi.
"Ba za ka ce komai ba?" Imam ya ce yana jifansa da kallon takaici.
Khalid ya juya ya kalli Haj. Zatu tana ta murmushi "Umma me zan ce?"
"Kar ka bada mu mana." Cewar Ansar shi ma yana yi masa irin kallon da Imam ke masa.
Hannuwansa ya haɗe wuri guda ya kalli Siddiqa da ta kasa ɗago kai.
"Zo mu je."
Shiru.
Sumayya ta taɓota da sauri " Ya Khalid na magana."
"Gaskiya Ya Khalid kana bada mu. Wa ya sani ma ko shi yasa waccan ƙyarmasasshiyar ta ce ta fasa." Yusuf ya faɗa shi ma yana mai bin sahun su Imam wajen harararsa.
Khalid ya sha kunu "ita ba ku ga abin da take yi bane? Siddiqa don Allah zo mu je."
Hannunta Alh. Zahraddin ya ɗan matsa shi ne ta sami ƙwarin gwiwar ɗago kai a hankali ta kalle shi.
"Ina?"
"Zance mana. Ko a haka za a yi auren ban gabatar da kaina ba?"
Sakin hannunta Alh. Zahraddin ya yi ya ɗan turata gaba. Ai kuwa kunya ta sa ta fita da sauri hannuwanta a kan fuska. Khalid ya bita shi ma da saurin yana cewa,
"Jira ni mana."
"Whooooohhhhhh"
Ihun da su ka saka sai da Haj. Zatu ta toshe kunnuwa. Sumayya kuwa ɗan yatsa tasa ta danne hancinta gefe ɗaya ta kama guɗa. Kowa ya yi mamakin yadda ta iya sosai.
"Weldone Andalin. Amma ranar naki auren wa zai yi?" In ji Yusuf
"Ni ne nan" Ansar ya ce kai tsaye
"Tashin hankali." Cewar Alh. Zahraddin shi ma yana dariya.
Ƙasa da awa guda da dasa musu baƙinciki da shiga halin ƙaƙa-nika yi sai gashi gidan ya kaure da murna. Ƴan biki da aka ce su taho nan Haj. Zatu ta kirowa manyan ciki na dangin mamansu Imam da irin su Mamma. Alh. Zahraddin da kansa ya yi musu bayanin biki ba zai tashi ba. Yana so don Allah su bashi zuwa Magriba ayi kamun Siddiqa a gidan.
Haj. Nafi tashi tayi ta rungume Haj. Zatu.
"Riƙon da ki ka yiwa yaran nan Allah ne kadai zai biyaki. Yau gashi kin fitar damu kunya irin wannan da za ta ja mana gori da aibatawa. Madalla dake Haj. Zatu. Allah Ya dubi lamarinki kema."
Rufe bakin Haj. Nafi ke da wuya sai ga Anti Ramlatu ta shigo. Kusan kowa na falon harda Alh. Zahraddin. Duk ta dame fuskarta da kwalli saboda kukan da tayi a mota. Kusa da shi ta ƙarasa sai ta kuma fashewa da kuka.
"Allah Ya jiƙan Nani. Allah Ya yafe mata kurakurenta."
"Amin Ramlatu" aka dinga amsawa.
"In sha Allahu sai dai a tada ita akan alkhairin da ta assasa na son ganin mun haɗe kawunanmu."
"Amin. Zo mu je ki ji abin alkhairi." Ya ce yana shirin fita.
"Yaya Dini dakata. Nima da alkhairin nazo. Da izinin Allah aure ba zai tashi ba. Indai Khalid ya amince ranar asabar a ɗaura aurensa da Ayshe."
Kallon kallo taga ana yi ta murmusa "in sha Allahu ba za a ji kunya ba. Kaga yanzun nan na gama waya da ita kuma ta amince."
"Allah Ƙadiran ala Mayyasha'u." Cewar Aljazira "in wani ya ƙi ka da wuni, wani zai so ka da kwana."
Anti Ramlatu ta je gaban Haj. Zatu ta riƙe mata hannu "ki sanar da Khalid ɗin. Idan shi ma ya amince sai mu je ki kama (kamun biki) ƴarki. Ba zan baki amanarta ba domin ke ɗin me amana ce."
"Ramlatu zo mu yi magana." Alh. Zahraddin ya furta yana kallon Haj. Zatu.
Ita kuwa da ta gane me yake son yi sai tayi saurin katse shi "Khalid ya karɓa in Allah Ya so. Sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba."
Kallonsu Anti Ramlatu ta kama yi. Haj. Nafi sai tayi mata bayani cikin lumana. Ga mamakinsu sai ta faɗaɗa murmushinta.
"Arziƙi kenan! Allah Ya hana shi ɗaya Ya musanya masa da biyu. Wallahi bani da matsala indai ba shi ne ya ce baya so ba. Arziƙi ne ko ba haka ba?" Ta goge hawaye tana mai kallon Haj. Zatu.
Ita ɗin ma hawayen ne ya zo mata domin tana iya ganin farinciki a fuskar wa da ƙanwarsa.
*
Takwas na dare bayan an sanar da sabon ango da amarensa cigaban da aka samu aka kama matan a gidajensu. Haj. Zatu da su Mamma su ka tafi gidan Anti Ramlatu. Tuni ta kira wasu cikin ƴan uwanta da ƙawaye sun shirya tarbar baƙi.
Anti Ramlatu da su Haj. Nafi harma da Anti Zayya da matan Zanna su kuma su ka kama Siddiqa. Zanna kansa cewa ya yayi ba don kada abin ya yi yawa ba tabbas da sai ya ƙarawa Khalid da tasa ƴar.
Daga gidan kamun kai tsaye Haj. Zatu gidan Inna ta wuce. Dama dai ta kira babban wan Abbansu Siddiqan a waya ta sanar dashi. Ta kuma kira ƙanwarsa wadda ta kasance babba a cikin mata domin da su ma aka yi kamun Siddiqan. Don cewa tayi a jira dangin mahaifinta tunda ba za ta aurar da ita da kanta ba. Da izinin Inna aka yi komai.
"Umman Nurain kinga ikon Allah ko? Muna ta damuwa da rashin auren Siddiqa ashe gida ɗaya su ke kwana da mijin" Inna ta faɗi tana dariya.
"Haƙiƙa Allah ke da lokaci" ta ce da ƴar damuwar da ta bayyanar mata.
"Kada ki ce min auren su biyun ne yake damunki?"
"Inna ina jiye mata. Zama da kishiya baƙuwar rayuce a gareta." Cewar Haj. Zatu
"Amma kuwa kin bani mamaki Umman Nurain. Ƙaddara ba kowa da tashi ba? Na zata za ki duba haka akan rayuwarki. Kin taɓa tunanin wannan rayuwar da ki ke ciki har bayan mutuwar Aminu?"
"Yi haƙuri Inna. Da ma ina duba lamarin ne. Aure lokaci guda da kishiya. Idan da ace daga baya kishiyar ta zo bayan sun saba ko ita ta shiga ta same ta zai fi sauƙi. Amma yanzu dukkaninsu rayuwar baƙuwa ce a garesu."
"Allah da Ya haɗasu rana guda ba tare da sani ko shirin ɗayansu ba Shi zai bayar da yadda za'ayi a sauke haƙƙin juna. Na san ki. Indai tarbiyarki ta ɗauka to in sha Allah babu mai kuka da ita."
Sun rabu da ƙarfafa gwiwa daga Inna wanda yasa Haj. Zatu samun sauƙin tunanin da ya addabi zuciyarta. Yanzu abin da ya rage mata kawai shi ne sanya Siddiqa da shi kan shi Khalid ɗin a gaba da su dage da ƙiyamul laili daga nan har ayi auren. Domin a zaune take yanzu auren zai shiga bakunan al'umma. Da masu faɗin alkhairi da ma waɗanda sharri za su faɗa. Kowa zai sami abin cewa akan auren saurayi ga mata biyu rana ɗaya.
***
Dare tsayi ya yiwa Nurain tun bayan sun yi waya da Haj. Zatu. Kafin ayi kamun ta kira shi ta sanar da shi. Cewa ya yi kawai zai taho da safe da wuri. Sagir ma wani iri ya ji zancen. Ga auren haɗi ga shi mata biyu lokaci ɗaya.
Jirgi su ka biyo don duk wucewar daƙiƙa ƙaruwar tashin hankali ne a wajen Nurain. Gida su ka wuce. Su Al'amin su na ta murnar ganinsu. Ko abincin da Lubna tayi musu tayi basu iya ci ba. Wanka kawai su ka yi ya kira Siddiqa ya ce ta fito za su gidan Umma. Yadda ya haɗe fuskarsa ita da Sagir shiru su ka yi a motar.
Sun sami wuri sun zauna su huɗu. Sagir da Haj. Zatu su ka gama murnar kammala karatunsa. Ta nanata masa in sha Allahu za ta yi walima idan sun koma Abuja.
"Umma abin da yake gabanmu mai mahimmanci ne" Nurain ya ce da ƙosawa.
"Murnar gama karatun yarona ma abu ne mai mahimmanci." Ta sake duban Sagir "Doctor da ciwon kai na kwana. A duba ni a bani magani."
Su uku su ka yi dariya. Ta dubi Nurain ta girgiza kai "Yaya nasan maganar auren nan ce da ta taso bagatatan. Amma ka kwantar da hankalinka. In sha Allahu ba za mu ji kunya ba. Kayan ɗakin da mu ka haɗa mata na wancan auren suna nan."
"Umma ni fa ba zancen da nake yi ba kenan."
"Ina jin ka to" ta dawo da hankalinta gare shi.
"Wannan aure Umma in dai ni zan ɗaura shi to don Allah ina roƙonki da ki ce an fasa."
"Hujja. Bani hujja" ta ce ranta yana zafi. Ta rasa me yake damunsa.
Baya son ganin ɓacin ranta amma a iya tunaninsa wannan aure zai iya janyo mu su zagi daga mutane. Bai taɓa jin irin wannan auren na mata biyu lokaci guda ba wanda bai shiga bakin duniya ba. Abu na biyu kuwa yana ganin an wulaƙanta masa ƙanwa ne kawai za ayi mata aure irin wannan.
"Marainiya ce Umma, ta yaya zan goyi bayan ayi auren huce haushi da ita? Ba fa auren soyayya bane amma ace har su biyu? Tunda ya sami ƴar uwarsa don Allah Umma a cireta daga wannan lissafin"
"Na fahimceka. Nima duk wannan tunanin nayi amma kamar yadda nawa auren ya zo a ƙaddara ita ma haka ya zo mata."
"Amma ai duka babu dole a ciki."
"Kaga bana so mu sake maimaita tarihi. Kayi sau ɗaya na dinga lallaɓawa saboda ina ganin baka da wata mahaifiyar bayan ni. Soyayyar mahaifinka a zatona ita tasa ka ƙi auren da nayi. Da kuma kishin kada ace ina ƙarƙashin wani, ƙila ya raba ni da ku. To amma Siddiqa ƴata ce. Ba tare mu ka haifeta da kai ba saboda haka kada ka kuskura ka kwatanta min wannan shirmen."
"Umma?" Ya kira sunanta da mamaki.
Ranta a ɓace ta ce "Naga take takenka tun a waya jiya. Ƙarshen zance dai ace ni da Siddiqa mun yi auren kuɗi ko? To mun yi ɗin."
Shi ma nasa ran ya yi sama. Ba ya son ɗaga murya tunda uwa ce.
"Ba haka nake nufi ba. Ni ina duba mana abin da duniya za ta ce."
"Ta daɗe bata ce ba. Duniyar da ko me kayi ba za ka taɓa burge mutanen cikinta ba. Mai wayo a cikinta shi ne mai yiwa Allah da ManzonSa ɗa'a. Mai kuma karɓar ƙaddara da hannu bibbiyu."
"Tunda an bashi ƴar uwarsa ai bai kamata a haɗa masa da Siddiqa ba."
"Ba ka wajen. Baka san yadda abin ya gudana ba. Babu wani hali ko ƙofar cire Siddiqa daga ciki. Shi yasa mu ka amince da sahalewar Inna da iyayenku maza."
Iyakar tunani Nurain ya yi kuma bai ga inda Siddiqa za ta jidaɗin auren nan ba tare da an sami masu binta da ƙulli ba. Khalid da ƴar uwarsa da zai aura dangin juna ne. Masu kuɗin da ba don darajar auren Umma ba da ko a titi ƙila ba za su kallesu ba. Ita kuwa Siddiqa bare ce. Agola wadda take cin arziƙin mijin mahaifiyarta. Mahaifinta bai yi suna sama da tsakanin ƴan uwa da abokan arziki ba. Duniyar Alh. Zahraddin da danginsa ta yi musu fintinkau. Anya idan ya bari Siddiqa ta shiga cikinsu bai saya mata rayuwar gori ba? Uwa ta auri uba ita ta auri ɗa?
"Allah Ya sani Umma ba da mugun nufi na zo da zancen nan ba. A wurina tsare mutumci yafi komai."
"Na fi ka sanin haka. Ina so kawai ka dinga bawa zuciyarka haƙuri ne akan duk abin da ba yin kanka bane. Rayuwa tana tafiya ne akan tsarin Allah ba muradin mai ita ba. Wasu lokutan dai ana yin dace su zamo abu ɗaya."
Ya san gaskiya take faɗa amma zuciyarsa tayi nisa akan nata tunanin.
"Yanzu idan ya su ka kasa zaman lafiya laifinta za a fi gani saboda ita bare ce."
Ya dubi Siddiqa. Hannu ta dunƙule ta tallafi goshinta. Idanunta a rufe tana hawaye.
"Idan ba kya son auren nan ki faɗa min gaskiya. Nayi miki alƙawarin tsaya miki."
"Yaya ina so. Don Girman Allah ka bar maganar nan. Nagode da kulawarka amma in sha Allahu babu komai."
Tashi tayi za ta fita ya daka mata tsawa. Alh. Zahraddin da su Khalid sun ji. Daga gidan Sarki su ke. Sun amsa kiran da ya yi musu akan za a aiko da lefen amaren biyu daga gidansa. Sannan ya ba wa Khalid wani gidansa mai ɓangare biyu a Abuja.
"Idan Umma ta amince saboda ɗan mijinta ne ke ba dolen ki bane. Ki barshi ya auri ƴar uwarsa ki jira naki lokacin."
"Yanzu ne lokaci na Yaya. In sha Allahu zan auri Ya Khalid tunda mahaifiyata ta amince." Sai kukanta ya ƙaru ta durƙushe a wajen. Ko bai faɗa ba ita ma bata maraba da zama da kishiya irin wannan. To amma karamcin mutanen gidan yafi ƙarfin su rufe ido su ce sun fasa saboda kada tayi kishi da kowa.
Gaban Sumayya faɗuwa ya yi da su ka ji me ake tattaunawa a falon. Alh. Zahraddin zai shiga falon sai Khalid ya riga shi. Kuma da ya shiga ɗin rufo ƙofar ya yi.
Wurin shiru ya yi da su ka gan shi. Kai tsaye gaban Nurain ya je ya tsaya.
"Doctor don Allah ka kwantar da hankalinka. In sha Allahu zan riƙe Siddiqa amana."
Alamun jin kunya ne su ka bayyana a wajen Nurain. Sai dai kuma akan abin da yake tunanin gaskiyarsa ne ba zai ja baya ba.
"Ni dai don Allah da ka haƙura tunda ba a ɗaura ba. Na tabbata ba sonta ka ke ba. Da ku na soyayya ba za ka nemi wata ba. My sister is a second option and I am not happy about it (ƙanwata zaɓi na biyu ce kuma bana farinciki da hakan)."
Gyara tsayuwa Khalid ya yi saboda yana son lallai maganar ta mutu yanzun nan. Tabbas kallon ƙanwa yake yiwa Siddiqa duk tsayin lokacin nan. Sai jiya da Imam ya nuna masa ita da madubin da bai yi tunanin ɗauka ba. Ya yi imanin abin da yaji a wannan lokacin ƙarfinsa yafi soyayya. Ita ƙila ta dusashe. Amma Siddiqa da Ummanta da su ka zaɓi rufa musu asiri shi da mahaifinsa sun taka wani tudu da babu sauka. Soyayyar da ake ta faɗa ya san za ta zo domin tana hanya. Irinta wadda aka riga aka yi aure kuwa za ta fi komai daɗi da shiga rai.
"This is not about you Doctor. Rayuwar Siddiqa ce kuma tana son yi tare dani." Ya yi mata kallon neman amsa. Sai ta gyada kai tana hawaye sai ya ce "ba zan faɗa maka wadda nafi so ba domin sirrina ne. Ina dai son ka sani cewa in sha Allahu babu wadda mahaifiyarta za ta yi nadamar aura min ita."
"Tashi ki wanke idonki."
Nurain yana kallo ta bi bayan Khalid. Su na fita ya sake rufe ƙofar.
"Yanzu me kenan kayi? Ka ƙureta har ta zaɓi wani akan ka." Cewar Umma ita ma tana tashi.
"Ba zan ɗaura mata aure ba Umma. Tunda dai kuna ganin gidan nan da danginsu sun fi mu to in sha Allahu ba zan ƙara saka baki akan wata matsala irin wannan ba."
"Babu damuwa amma ina so ka saurari wasiyyata."
Gabansa ne ya faɗi ya juyo ya kalleta.
"Muddin kana raye da rai da lafiya ban yarda wani ya taɓa waliccin ƴaƴana ba sai kai."
Ba tare da ta sake cewa komai ba ta tashi ta fita ita ma. Yaji wani irin abu yana sukar zuciyarsa. Amma taurin kai da kafiya su ka hana shi lashe amansa ya daidaita da mahaifiyarsa tun a lokacin.
"Sagir tashi mu tafi."
Tashi Sagir ya yi sai kawai ya rungume Nurain. Ƙirjinsa har yafi na Nurain ɗin azabar zafi saboda abin da zuciya ta ɗarsa masa. Duk zancen da aka yi ko sau ɗaya Umma da Siddiqa basu nemi jin ta bakinsa ba. Tunda Nurain ya soma maganar auren Siddiqa ya zamana kamar ba ya wajen. Duka zantukansu a junansu su ka yi. Babu wanda ya ambaci sunansa kamar shi ɗin baya cikinsu. Kamar shi ɗin ba sa son shi yadda su ke son Nurain. Tunda Nurain ɗin yana ƙaunarsa hakan ya wadatar da shi. Haka aka yi lokacin auren Umma. Yanzu an sake yi masa. Certificate ɗinsa da ya bata ma a wajen ta barshi. Nurain uba ne a gare shi domin baya taɓa yin wani abu bai ji ta bakinsa ba.
*
Wanke fuska Haj. Zatu tayi a banɗaki sannan ta fito ta sami Sumayya a ɗakin.
"Andalin yaya ne?"
"Umma ki yi haƙuri."
Bagarar da ita tayi da sauri "rabu da rigimar yayan nan naku. Tashi ki kira min Dr. Sagir ya zo mu yi hirar yaushe gamo. Ɗan uwansa ya caja min kai ko takardun sakamakonsa da ya bani ban sami damar dubawa ba."
Da Sumayya taje ba sa falon. Ta tambaya aka ce sun fita. Da sauri tayi waje sai dai tana zuwa Nurain na fizgar mota a guje ya fita daga gidan.
***
HAƊUWA MAI CIWO