AZIZAN BABA

Episode 7

by @zinariya0102

Yeeee Baban birni oyoyo" faɗawa jikin Alhaji Aminu Dollars ta yi,hijabin nan yayi ciɗin-ciɗin da datti, duk su na zaune a ƙatuwar tabarmar da Baba Tabawa ta karɓe su.

"ke haba AZIZA ya haka, tashi kar ki ɓata masa kaya" Baba Tabawa ta faɗa, Daddy da ya dafa kan AZIZA ya na murmushi ya ce" barta Baba, ma sha Allah, AZIZAN BABA ta girma",Siyama da Pretty su na zaune kusa da BABA, Munnir ya na gefe AZEEZ da ya coge a jikin katanga kan kujera ya na ta cin magani, BABA ya ce" kun sha hanya sannunku da zuwa" Inna Gaji ta shigo tana fara'a ganin Daddy da iyalansa" 

ruwa Baba Tabawa ta ɗebo cikin kwanon sha fari tas da shi, AZIZA ta ce" Baban birni zan biku anan Inna duka na take yi" Daddy ya ce" da naji daɗi ƴata ta dawo ku sa da ni" murmushi tayi ta jin farincikin ganin Daddy.

Tunda ya shigo bai yi wa koma magana ba, gaishe da inna ya fara yi, "au ABDUL- AZEEZ ya ka yi zauniyarka anan" AZEEZ ya shafa kansa ya ce"nan ɗin ma ai is okay Inna" AZIZA ta ta tashi ta nufi wajen BABA ta ce " BABA ba sai mun tashi anan ba kawai mu bi Baban birni" 

Murmushi Daddy yake yana fatan Allah ya sa ya amince ya bi shi".



Fura Baba Tabawa ta ɗauko da kindirmo mai kyau wanda BABA ya shigo da shi, sanin Aminu zai zo, yau ko gobe.


BABA ya ce " ki barni da su babu wanda zai raba AZIZA da BABA sai Allah" Inna ta shiga kitchen ta hau haɗa wuta, AZEEZ da yake jin yunwa sosai har ɗaya bai karya ba, Sammani ɗan maƙota ne ya shigo da ƙanƙara manya-manya wacce Baba Tabawa ta ba shi kuɗin babur yayi sauri ya shiga cikin gari ya sayo.


Ta gama dama furar ta sa ƙanƙarar dan su ji daɗin sha, pretty da ta ƙagu ta ce"Baba ki zuba min haka" AZEEZ ya ce "daddy ina jin yunwa?" ga abinci nan kana gani" 

AZEEZ ya nuna kanshi ya ce"ni zan sha wannan abun, bazan iya ba" BABA ya ce "idan ka sha ka raina ubanka, wai Aminu waye ya ce ka zo da wannan yaron?" Daddy ya ce "ayi haƙuri" AZEEZ ya miƙe ya nufi ƙofar gida.


Yara ne cike a jikin motarsu driver da ya sauka a ɗakin ƙofar gida ya kwanta baccin gajiya ya ɗauke shi.

AZEEZ ya ja uban tsaki, kiran Mami yayi kamar zaiyi kuka, daga can Mami da ke zaune tare da khairat autarsu a hospital.



"hello AZEEZ kun isa?" 

"eh Mami yunwa zata kashe ni, bazan iya cin abincin gidan ba, nayi nayi dan na danne zuciyata bazan iya ba" Mami ta ce" what kar ka ce min har yanzu baka ci komai ba?" AZEEZ ya ce" har yanzu Mami wata fura suka kawo, ga wannan ƙazamar yarinyar ganinta ma tayar min da zuciya yake"

Mami ta ce" yi sarching ka duba ba za'a rasa restaurant anan ba" AZEEZ ya amsa da okay, ya kashe wayar.

Yaran ne suka zagaye shi suna kallonsa da irin shigar da ke jikinsa,  wasu na shafa mota wasu na kallon AZEEZ, "oh my God Daddy ka kawo mu garin mayu" ɗakin da driver yake bacci ya shiga, kamar haɗin baki AZIZA ma ta fito ɗauke da fura a ƙoƙo, Baba Tabawa ta aiko ta kai wa driver, sanye take cikin rigar saƙi da zaninta, kanta ba ɗankwali, babu sallama ta faɗo ɗakin, "Malam ga hi"AZEEZ da ke tsaye ya ji sautin muryarta. "kee!!!!mahaukaciyar ina ce za ki faɗo ɗaki ba sallama" AZIZA ta ajiye ƙoƙon fura, driver da ya farka jin sautin AZEEZ.




"Ni ba mahaukaciya ba ce ahee" ta faɗa ta na murguɗa baki, zaro idanu AZEEZ yayi ganin ƴar tatsitsiya da rashin kunya, hannu ya ɗaga da niyar marinta sai ya janye ya na ganin bazai iya taɓa ta ba, kar ya shafi datti, "ni zaki yi wa fitsara" abun duka ya shiga nema dan ya zaneta, mugun son girma ne da shi.


Ko firgita AZIZA ba tayi ba ta na tsaye ta kama ƙugu ya taɓata ayi masa taron dangi, driver ne ya ce" haba ƙanwata ba'a yi wa babba rashin kunya , mutanen ƙauye da yakana aka sansu" AZIZA ta ce " baka ganin abinda ya ce min wai mahaukaciya dan ya ganshi babba to wallahi tallahi ba na tsoron a mutu balle ayi rai" ta faɗa tana tattafa hannuwa.


Zuciya ta ciyo AZEEZ ya kai mata mangari da bayan hannusa, AZIZA ta kwasa a guje ta yi cikin gida tana ihu, BABA da Daddy da suke alwalar sallar Azahar su ka tashi a tare, Baba Tabawa ta fito da sauri, tana gyarawa su Siyama masauki.



Inna Gaji ta baro kitchen da take suyar zabbin da aka kama aka yanka, "ke lafiya ke da waye?" Daddy ya faɗa ganin yanda take burgima kamar mai iska, " wannan baƙon ne dan na kai furar ya hauni da zagi da duka" woyyo cikina na shiga uku na lalace, ta riƙe ciki gam tana malelekuwa a ƙasa, 

Waje BABA ya nufa dan daman a ciki yake da AZEEZ yana fita ya ganshi ya na niyar shiga mota, "kai ABDUL-AZEEZ me ya haɗaka da AZIZAN BABA, ko kashe min ita zakayi iye?" 

AZEEZ ya kalli BABA ya ce "ni sa'an ta ne da zata zageni"

BABA ya ce "to Allah ya isa, kai da ganinka ba ɗan arziki ba ne, ka je dan kanka, na ɗaga maka ƙafane darajar kai baƙo ne" 

Ya juya ciki, AZIZA kuwa da ke tari takeyi, aikuwa ta shiga yinsa ba ƙaƙƙautawa har da amai, shinkafar da ya ci duk sai da ta dawo.



Ran Daddy ma da ya ɓaci, sai rarrashin AZIZA yake yi, Siyama da pretty da suka ga yanda ake tayiwa yarinyar sai suka ji sun tsaneta.



BABA ya ce "Aminu ni bance ka zo da kowa ba ka zo min da wannan yaron naka da ba ganin girman kowa yake ba, wannan yarinyar marainiya ce watukun a gabana da raina ɗan ka bazai iya riƙe min ita ba, to ni bazan lamunta ba, ka ja masa kunne"Daddy ya ce " ayi haƙuri BABA ba za'a ƙara ba in sha Allahu.



Sai da AZIZA ta gama amai, sai zazzaɓi ya rufeta yau tun safe ta ke kuka.

Baba Tabawa ce ya rarrasheta suka shiga ɗaki, kwanciya AZIZA tayi tana ta kakkarwar sanyi,BABA ya ɗauko turaren mayu, ya ce " ungo nan Tabawa turara mata ba musan wana irin dangi Aminu ya ɗauko ba" Daddy da ya san, sun san Mami ba ƙaunarsu take ba, ya sunkuyar da kai.




Masallaci suka fita tare suka nufa, ba bu AZEEZ ba bu mota, driver ma yayi alwala ya nufi masallaci, bayan an idar aka ga ɗan BABA ya zo, nan aka fara yiwa BABA maula, Daddy ya dinga ba su sadaka , addu'a ake tayi masa da fatan gamawa da duniya lafiya.



Sai da ya bar garin yayi tafiya mai nisa ya fara gano bank da plazas, slowly ya yi ya fara gangara gefen titi, wasu masu sai da fetur (black market) ya tambaya "Assalamu alaikum" suka amsa" wa'alekumussalam" dan Allah ko akwai restaurant anan kusa?" 

"eh idan ka yi gaba can wajen motel (hotel) zaka ganshi daga dama" AZEEZ ya yi godiya ya ƙara gaba, ba nisa sosai da inda ya bar matasan parking yayi ya tsallaka titin ya shiga wajen, Ten to Ten restaurant yaga an sa, daɗi yaji sosai, sanin breach ɗin na Kano ne, shiga yayi ya zauna.



Wata budurwa ce sanye da blue riga da black skert ta tawo ɗauke da list pepar ta kawo masa, dubawa yayi, ya zaɓi, fried rice, da chicken, sai ya zaɓi 5alive drink sai ruwan Swan.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka kawo masa, sosai ya ci ya ƙoshi ya ɗauko wayarsa ya kira Mami sanar da ita inda yake yayi.

Ƙara zuga shi tayi akan kar ya yarda ya ci wani abu a gidan kar su yi masa surkulle wai shima su magance shi kamar yanda suka yi wa Daddy.



Take away yayi sannan ya biya bill ya fito dan tafiya, komawa yayi dan kar Daddy ya san ba son zama a gidan yake ba.


Su na dawowa ɗakin BABA suka shiga, Mannir ya na ɗakin Inna suna ta hira dan shi babu ruwansa, bayan kowa ya ci abinci, Daddy da ya ga AZEEZ bayanan, ya share shi, tunda ba yaro ba ne, da zai neme shi.

Siyama ta kwanta dan huta gajiya kafin yamma tayi su ɗan zaga gari.





BABA ya gyara zama ya ce"Aminu na kira ka ne, akan makarantar su AZIZA ina so muje ka ɗauki mataki akan dukan da ake mata, kuma inaso mu je can wajen malam Isuhu ka sa ayi mata sauka kuma a dinga nema mata tsari abinda ya sa na kira ka kenan".



Murmushi kawai Daddy yake ya ce" ni na ɗauka ko bani ita zakayi in tafi da ita kano" BABA ya ce " a'a babu wanda zan bawa AZIZAN BABA da gida ma zan sauya dan babartaku ma ba ƙyaleta take yi ba, Aminu ansa min jika a gaba, nema ake aga bayan mu" sai ya fashe da kuka.


Daddy ya ce "kayya za'ayi duk abinda kake so BABA, babu abinda za'ayi muku, ni da son samune ma ka bi ni birni mu zauna tare, kuma inason biya muku Hajji wannan shekarar, kai da su Inna, ita AZIZAN sai ku bar min ita idan ku ka dawo sai ku taho da ita" BABA ya kalle shi gami da ƙanƙantar da ido ya ce" Allahu akbar! ashe da rabon zan koma makka, amma gaskiya sai dai tare da AZIZAN BABA zamu tafi, dan babu wanda zan bawa riƙo"

Daddy ya jinjina kai, ya ce "to BABA duk abinda ka ce haka za'ayi" tunani Daddy yayi na sa AZIZA ta sa BABA ya dawo Kano da zama.




AZEEZ ne ya shigo da sallama BABA ya ɓata rai, dan shi duk abinda zai taɓa AZIZA to baya son shi.

"BABA sannu da hutawa" AZEEZ ya faɗa ya na wucewa kan shinfiɗarsa ya kwanta, burgeshi kawai tayi.

Daddy ya ce" ina kaje?" AZEEZ ya ce " restaurant naje daddy" Baba Tabawa ce ta shigo ta ce "Malam AZIZA fa ba lafiya" 

A ruɗe BABA ya tashi yana faɗin "subhanallahi dukan wannan ja'irin yaron ne, idan ka sa wani abu ya same ta sai na ɗaureka alkur'an"

AZEEZ ya ce "Allah ya sa ma ta mut........





Zinariya ce✍🏻