AZIZAN BABA

Episode 8

by @zinariya0102

Kaga Mutuwa akan ka, wannan yaron da gani baka neman albarka" BABA ya na faɗa yana tafiya zuwa ɗakin Tabawa ganin AZIZA sai kakkarwar sanyi take, BABA ya riƙi ce, da sauri ya ce "Aminu ta shi muje lambun baya, ka ciro min sassaƙen saiwowi yanzu zata samu sauƙi in sha Allahu, sannu AZIZAN BABA Ubangiji ya baki lafiya" Daddy da ya san ba zai iya hawa bishiya ba ya ce" to BABA bari muje AZEEZ ya ciro, ni jikin yayi nauyi" 

AZEEZ!AZEEZ! Daddy ya fara kwallawa AZEEZ kira, fitowa yayi daga ɗakin BABA ya na amsawa, Daddy ya ce " tawo muje ka ciro mana saiwowi da ganyayyaki a lambu" AZEEZ ya ce "me!!!! ni Daddy ba ni da lafiya kuma wallahi bantaɓa hawa bishiyaba ni bazan iya ba" 

"To kuwa yau sai ka hau ko zaka mutu, ƴar'uwarka ba lafiya kana wannan zance wuce mu tafi" AZEEZ ya coge yaƙi motsawa, sai da Daddy ya ce" watukun ni zan hau kenan" AZEEZ ya ce " a sa Munnir mana ba daɗi nake ji ba wallahi Daddy" Munnir ya ce" yaya bazan iya ba" Siyama tana tsaye bakin ƙofar ɗakin da aka sauke su ta kama labule tana kallon yanda ake son wahalar da Yayansu, da sauri ta saki labulan ta ɗauki waya dan sanarwa da Mami.



BABA ya ce " bari na nemi taimakon jama'a tunda ni ba ni da darajar da zan ce ayi min" Daddy ya ce "mu je BABA ni na hau bishiyar" AZEEZ ya bi su dan yasan Daddy ya manyanta bazai iya kama reshe ya hau bishiya ba.


AZEEZ ya ce "mu je in hau" Ni za'ayi wa garin nan Aminu ashe haka ka bari yaronka ya raina manya" BABA ya faɗa ya na miƙewa wajen lambunsa.



Daddy ya rasa abinda zai ce, haƙuri kawai yake bayarwa, AZEEZ na saka ƙafa ƙaya ta cake shi, "wash!!Allah" Daddy ne ya juya yana faɗin "me ne ne?" AZEEZ ya ce " maciji ne ya sareni?" BABA ya ce " a ina, ba dai awannan lambun ba" haskawa Daddy yayi ƙaya ce ta karce shi, "mtswww ƙaya ce fa, biyo nan ka hau waccen ita cen ka ciromin ganyen mangoron" AZEEZ da ya ke ta duba ƙafa ya ji sautin BABA daurewa yayi ya ƙarasa shiga ƙafar na yi masa zafi, kama bishiyar yayi ya rasa yanda zaiyi ya ɗane, Daddy ne ya ce bari in cicciɓaka" BABA ya ƙame ya na faɗin, "wannan yaro ba shi da dabara, duk ka sangarta shi na tabbata da AZIZA na nan da tuni ta gama kwaso saiwowin nan mtswww" 

AZEE ya zuciya yayi tsalle ya kama reshe ya haye ganyen ya cicciro ya na miƙawa Daddy, BABA ya ce "sauko ka hau waccen ta gwandar " AZEEZ da hannunsa yayi jajir dan bai saba ɗaukar komai ba, dan ko kaya sai an ɗauke masa idan ya cire, tausayi ya fara bawa Daddy, a hankali diro, ya na yatsina fuska, ko hutawa baiyi ba tunda ya zo yake wahala.



Bishiyar gwandar ta na da tsayi, kar BABA ya ce wani abu ya sa ya aro jarumta ya fara hawa kamar lizard(ƙadangare) nishi yake ya na haki, ya zauna ya fara ciro ganyen nan ma sai da BABA ya ce ya isa sannan ya sauko, ta lemon tsami ya hau ya nan ma ua ciro ya sauko, wata ƙaramar fatanya ya ba shi ya ce "ciro sassaƙen dogon yaron(neem plant) ɗin nan sai mu tafi" Daddy da yake riƙe da buhun ganyen ya ce "ka yi da jiki mana"AZEEXZ da yake jin bayansa ya riƙe ya ɗauki hoe ɗin ya fara sarawa a hankali, ganin zai ɓata musu lokaci BABA ya ce " gafara can jiki duk ya lalace ba ƙwari, ni lokacin da nake kamarka ni ne Shagon dambe, mazaje-mazaje" yanda BABA yake kuri ya bawa AZEEZ dariya, dan ƙwaƙwarar ture shi yayi faɗuwa zai yi.



Karɓar fatanyan yayi ya saro sassaƙen, Daddy ya kwashe, yana ta yi wa BABA sannu, AZEEZ ya ce "wai sai sannu kake masa bayan ni na yi wahalar" Daddy ya yi masa daƙuwa.



BABA ya karɓi buhun ya ce" idan ya gama shashancin sai ku tawo" ya ɗogara sandarsa da sauri ya bar lambun, Daddy ya kama hannun AZEEZ ya ce "mugani?" yayi jajir jini duk ya kwanta, cikin tausayi ya ce" kai kamar ba namiji ba, ka dinga aikin ƙarfi kar ka zama rago" 

AZEEZ ya ce" daddy dan Allah mu tafi gida wallahi nasan idan na kwana a gidan nan sauraye ne za su cinye ni ɗanye" Daddy ya ce "nan ɗin shine tushe na AZEEZ Kano karatun allo ya kaini, ni da kaina na sa kaina makarantar boko har kaga na kawo irin wannan matsayi, rayuwa cike take da ƙakubale" suna bin bayan BABA suna hira.



A cikin gida kuwa, abu kamar iska, su BABA na fita AZIZA ta tashi, ta zauna ta ce "Baba Tabawa wannan mutumin saura kaɗan ya kashe ni, taɓa nan ki ji, hantata ce ta ruguje ina ji tana zubowa" ta fara matse ƙwalla.


Baba Tabawa ta ce " kin dai bugu ne amma babu wani hanta da ta fashe, ki daina yi wa manya fitsara babu kyau" AZIZA ta sauko daga kan gadon ƙarfen Baba Tabawa na cuno baki ta fita, dan komawa ɗakin Inna sa bo da taji haushi.



Ji tayi Siyama na magana, "wallahi Mami, wai Yaya ne zai je ya shiga daji ciro magani, wai ya daki wannan yarinyar" 


Daga can Mami da ke tare da Kausar, an dubata ance haihuwa ba yanzu ba, suna mota dan zuwa gida, ta ce" kutmar uba ɗan nawa ne zai shiga daji, ina Alhajin?" Siyama ta ce" tare suka tafi, kuma har yanzu fa bai ci komai ba" 

Hakalin Mami ne ya yi masifar tashi, ta ce "bari in kira shi ya tawo kawai, wallahi akan haka sai dai mu rabu, wannan ai hauka ne watukun suna baƙinciki da ƴaƴan da na haifa da ɗansu sa bo da sunga yayi arziki dan kar mu ci, to ba su isa ba, a haka za su ƙare a wahale" Siyama ta ce" Mami daman haka suke?" 

Mami ta ce " kinga ni ai, ku masu dangin uba, kuna murna ko, kaɗan kuka gani ma, bari in kira shi ya dawo kawai"

AZEEZA da ta ji komai, ta zauna akan tabarma sai ta hau tari, Inna ta fito daga bayi ta ajiye buta ta na faɗin sannu AZIZA,Allah ya baki lafiya wannan tarin ya tada miki da shawara.



"Ga shi ku haɗa wuta a tafasa shi ayi mata sirace da shi," BABA ya faɗa yana sauri, Baba Tabawa ce ta karɓa, tana faɗin ina AZEEZ ɗin yake, bai ci komai ba" 

BABA ya ce " za ki yi abinda ke gabanki ko kuwa ba duk shi ya janyo wa marainiyar Allah ciwo ba, ya zage ƙarfinsa akan yarinya ya dinga duka, Allah ya isa kawai"



Daddy da jama'a suka tsare shi a waje sai gaisawa suke, AZEEZ ya shiga ya na ta faman susa duk jikinsa ƙaiƙayi yake.



Wanke ganyayyakin Baba Tabawa tayi ta ɗora akan wuta, Inna da ke dafe da AZIZA ta ce " ABDUL-AZEEZ sannu ga ruwa can ka je kayi wanka, sannu da ƙoƙari" AZEEZ ya ce " ina banɗakin, nuna masa Inna tayi, juyawa yayi yaga ƴar katangar ba ta da tsayi sosai kuma a buɗe yake ba rufi, ya ce "nan ne bayin?" 

Eh nan ne" AZIZA ta kwantar da kanta jikin BABA ta ce"BABA hanta ta ta fashe" BABA ya ce"inji uban wa ye ya ce miki haka" ta ce "ji nayi, anan ya naushe ni" ta nuna gefen cikinta.


AZEEZ ya tsaya yana kallon makirci ƴar ƙarama da ita,sai zancen masifa. "BABA ya ce, duk hassada da baƙincikin mutum nan gani nan bari, kurwar AZIZAN BABA ɗaci gareta"

BABA ya ɗauki buta jin an fara kiran sallar magriba, ya nufi bayi.



AZEEZ ya ce "indai ni maye ne kema mayya ce munafuka" Inna Gaji ta ce"dama haka kake babban kwabo ne?" 

AZEE da yake soshe-soshe ya ce" Inna wannan yarinyar tantiriya ce munafuka ce" 

Daddy ya shigo a gaggauce ya ce" ya jikin nata?" AZIZA ta ce"na sami sauƙi, kawai an riƙe min wuya na ne da tari, sai hanta ta da aka fasa min" sai hawaye sharrr.



Cikin tashin hankali Daddy ya ce "wana irin hanta AZIZA,Inna mu tafi asibiti" 

AZEEZ ya ce" makirci ne fa daddy ka taɓa ganin wanda ya sami matsala a ciki yana zaune"Daddy ya ce "kuma hakane, may be buguwa tayi, kar ka sake dukanta nagaya maka"


Siyama da Munnir da pretty su na tsaye, wayar AZEEZ ta shiga ringing, dubawa yayi zai fita, caraf BABA ya riƙe masa riga, "je kayi alwala mu anan jam'i ake yi"

Daddy ya ɗauki buta shima yayi alwala, "Hello mami" 


Duk inda kake ka dawo gida, meya kai ka daji iyi, kenan duk abinda na faɗa maka abanza ko?" 

AZEEZ ya ce " okay zanyi yanda kika ce" ya katse kiran.




Harara ya gallawa AZIZA, dai dai lokacin da ta ɗaga kanta,ai kuwa ita ma ta galla masa har da taɓe baki.

Ƙwafa yayi ya fita dan har ga Allah tsantsanin bayin ya ke.


Hotel ɗin da aka nuna masa ɗazu ya koma, ɗaki ya kama, ya na shiga ya fara cire kayansa, dan wanka kawai yake buƙata, anan tsakar ɗakin ya cire kayansa ya nufi toilet, wanka yayi sosai har lokacin isha, sannan ya ɗaura sabon towel ɗin da ya gani a drower.

Alwala yayi, ya fito.




Rasa kayan sawa yayi bai ɗauko komai ba, wayan ɗakin ya kira, ma'aikacin hotel ɗin ne ya zo, AZEEZ ya buɗe ƙofar ya ce" dan Allah ko akwai boutique nan kusa? saurayin ya ce" eh yallaɓai, akwai a cikin hotel ɗin nan" AZEEZ ya ɗauko wallet ɗinsa ya ba shi 30k ya ce" jalabi guda uku nake so, sai boxers uku, sai body spray biyu,ya faɗi sunan wanda yake amfani da su,please" angama sir" ya karɓi kuɗin ya tafi.




Angama dafa maganin aka ɗebo a baho AZIZA akayi wa sirace sai gumi take tare da atishawa" Munnir ya ce" Daddy dama ayi wa Yaya irin haka, shima ba shi da lafiya" Daddy ya ce " hakane ya ɗauki waya ya kira AZEEZ, "kana ina?"


AZEE ya ce " daddy ina hotel ba zan iya zama anan ba, ba ni da lafiya" 

Daddy ya cika da mamaki dan bai taɓa zaton ɗan da ya haifa zai raina asalinsa ba.

Ransa ne ya ɓaci ya ce " to duk inda kake ka dawo gida ina nemanka" ya kashe wayar, yana mai jin takaicin irin tarbiyyar da Mami tayiwa yaransa.



AZEE ya dafe kai ya ce" why, why daddy tunda muka zo wannan jarababbem gari nake fuskantar barazana na rasa rayuwata" knocking ya ji, ya buɗe leda sauryin ya miƙa masa, godiya AZEEZ yayi ya mai da ya rufe, riguna ne masu kyau size ɗin sa, body spray ya shafa ya sa ya tada sallah, magriba da isha, sannan ya ɗauki makulin mota ya rufe ɗakin ya fita.





AZIZA sai bacci take, rana ɗaya amma ta rame, Daddy ya ce idan har zuwa gobe bata warke ba asibiti za'a kaita.




BABA ya yi jugum yana tunanin rashin lafiyar AZIZA, ga abinci an dafa shinkafa ce fara da miya sai salad da kwai da Siyama ta ce a sa, sai naman zabi, lemon roba(minerals) da ruwa aka ajiye musu, dan Daddy ya san halin ƴaƴansa shiyasa da ya idar da sallah ya bayar aka siyo musu.

Sai cin abinci su pretty suke hankali kwance, AZEE ya shigo sanye da wasu kayan, BABA ya ce" ina ka je kai kuwa?" AZEEZ ya ce "masauki"

Ba BABA ba har Inna sai da ta maimaita masauki, 

AZEEZ ya ce "dan girman Allah daddy kar ka hanani kwana a can...........







Zinariya ce✍🏻