AZIZAN BABA

Episode 11

by @zinariya0102

Hhhhh ni nasan banyi haihuwar asaraba, AZEEZ ina so ka ƙwatowa mahaifinku ƴanci, dan sun haife shi ai su suka halicce shi ba, Allah ya amsa addu'ata ko ba ni a doron ƙasa nasan ba za ka bari wasu su cinye dukiyarku ba,ina goyon bayanka ɗari bisa ɗari"

AZEEZ ya saki murmushi ya ce" nasan abida suka fi so yanzu kuma sai na sa sun tsaneta, nasan ba ni da lokacin da zan karanci halayen kowanne daga cikinsu saboda zan tafi Spain,ki yi haƙuri idan na dawo komai zai sauya Mami"

sosai ta ƙara zuga shi akan ƙin dangin uban nasa, sai da ta kwantar masa da hankali sannan sukayi sallama.


Wanka yayi ya sa aka kawo masa abinci ya ci, yayi sallar isha, ya fara sana'ar shi,kallon bf tare da istimna'i, jinsa yake kamar ba shi ba, nishaɗi a fili yayin da zuciya take cike da ƙunci mara dalili, sai da ya biyawa kansa buƙata sannan ya tashi yayi wanka ya kwanta sai lokacin ya ke nadamar abinda ya san Allah yana kallonsa, duk da ya ɓoyewa mutane, a haka har bacci ya ɗauke shi,

Sama-sama ya ji ringing ɗin wayarsa, buɗe ido yayi ƙarfe bakwai har da kwata na safe,da sauri ya tashi,ya nufi toilet wankan da yasan sai ya shafe mintina ya hau yi, da sauri da sauri,sai da ya kuma ɓata minti talatin sannan ya gama ya yi alwala ya fito wata rigar jallabiyya ya zura ya tayar da sallah asuba takwas da minti biyar sannan ya idar, duba wayar yayi Daddy ne ya kira shi.



Bin kiran yayi, Daddy da yake tsaye tare da BABA a ƙofar gida, dan zuwa makarantar su AZIZAN BABA,a jawa malaman kunne, duk da Daddy ya san kawai rigima ce irin ta BABA amma dole ya lallaɓa shi, indai ya na son gamawa da duniya lafiya.


Ganin AZEEZ ya bi yo kiransa ya ce " ka zo zamuje ziyara, cikin gari kuma zamu je can mai Kwangwalen" AZEEZ ya ce" in sha Allahu gani nan zuwa"

BABA ya ce " shin za ka zo muje ko kuwa ƴan'uwanka kawai kake son gani, kasan Allah Aminu akan AZIZA zan iya rabuwa da kowa ku ba ka damu da jibgarta da akeyi ba ko, ni fa saboda haka na kira woka ba wai dan wani abu ba"

Daddy ya yi murmushi ya ce" ayi haƙuri, ni ma ai bazan so a taɓa AZIZA ba,Allah dai ya raya mana ita"baki Baba ya washe ya na amsawa da amin amin, Allah yayi maka albarka ya ƙara arziki" su na tafe suna hira, har makarantar su AZIZA, suna ganin Alhaji Aminu dollers wanda duk ƙasa babu wanda bai san shi ba, hotunansa sun ba zu a ko ina, shi ne shugaban ƴan canji a jahar kano, cikin girmamawa suka tashi su na gaishe da BABA da Daddy, BABA ya ce " ga sunan Aminu kullum Allah ne da kullum sai sun daki AZIZAN BABA"

Malaman da suka san halin BABA, suka fara ba da haƙuri, Daddy yayi murmushi ya juya baki, cikin harshen turanci ya fara magana, i knew my father, sorry for his behaviors bec....."Ƙwal ubanka Aminu ni zaka yi wa shegantaka, me kake faɗa iye?"

Malaman suka fara ce wa BABA ya ce za'a rufe mana makaranta dan Allah kuyi haƙuri, ka ba shi haƙuri BABA" 

Wani farinciki ne ya lulluɓe BABA, ya washe baki , ya ce " a'a ai ba'ayi haka ba, abinda nake so da ku shi ne kar ku ƙara dukanta idan kuka ƙara wallahi sai na sa an rushe makarantar gaba ɗaya" Daddy yayi shiru ya barsu suna ta fama da lallaɓa BABA, sai ya hau fara'a ya na sa musu albarka, Daddy ya basu ƙudi yana yi musu godiya dan ganin sun karanci BABA kuma sun iya zama da shi, abun yayi masa daɗi.


"thank you sir, may Almighty Allah bless you and your family, may Allah protect your parents, 

Safe journey sir.


BABA zai yi magana Daddy ya kamo shi yana faɗin" na dai gayamuku ku kiyaye" suka tafi BABA ya ce" dan sunga ba ni da ƴaƴa a kusa sun ɗauka banda kai, kai ne kaɗai Namiji a yanzu amma ka zama jigo ga kowa, ba na tsoron uban kowa a garin nan" har suka ƙarasa faɗar maigari suna hira, babu wanda ya san ganin Daddy a birni yana wahala, dan duk zuwa ƙauyen da zaiyi asirance yake tafiya babu hawa flight bare body guards, sosai yake taka tsantsan da iyayensa,kar a san inda suke ba tsaro a yi garkuwa da su.



Maigari ne ya tari BABA, da martabawa BABA da Daddy suka zauna bayan angaisa BABA ya ce" ni na ce yazo a kira min Malam Barau ayi wa ƴarsa da jikata tsakani agaban ɗa na, saboda ko da nan gaba yasan da maganar" Maigari ya ce "haba BABA abu ai ya riga da ya wuce, kayi haƙuri a madadin Malam Barau muna mai ƙara baka haƙuri" Daddy ya ce" babu komai ranka ya daɗe, Allah ya kiyaye gaba" duk da bai san abinda ya faru ba, rigimar BABA tafi tashi idan yaga Aminu ya zo.

Anan ma Daddy sai da yayi sadaka sannan su ka tashi dan komawa gida.




AZIZA da tayi baccin dole, akan kar ta saki baki ta faɗi maganar da zatayi sanadin salwantar da ƴartsanoninta, sai da Inna Gaji da Baba Tabawa suka gama haɗa karin kumallo, Farfesun zabbi da tea da irish da kwai sukayi wa ƴan birni, dan sun san ba su iya shan kunu da ƙosai da safe, su Munnir da Siyama duk sunyi wanka sun ɗauki gayu irin na su, AZIZA ta fito ganin su pretty tsaf sai kishi ya tashi, ta nufi randa ta hau ɗiban ruwa,Inna Gaji ta ce" me zakiyi da ruwan nan haka?"AZIZA ta ce "nima wanka zanyi?" Inna Gaji ta ce "to yau kuma, ikon Allah" Baba Tabawa ce ta ɗauko bokitin ta zuba ruwan zafi ta ce mu je kiyi wankan ai kin kyautawa kanki" su na shiga banɗaki AZIZA ta ce" shi ne kuka bari baƙi suka rigani wanka, salon su ce min ƙazama ko" Baba Tabawa tayi dariya ta ce "kai tun yanzu AZIZA kinsan kishi, to Allah ya baki da sauƙi ko da yake mace ce ke" AZIZA ta ce "Baba ni fa ko, kinsan wa zan aura hahhh?" ta ƙarasa da dariya Baba Tabawa ta ce" a'a sai kin faɗa, AZIZA ta ce " Maigari zan aura" sosan da ke hannun Baba ne ya faɗi ta ce" ke kar na ƙara jin wannan shirmen sokuwa me zakiyi da tsoho to ko ubanki Abdul-azeez Allah yaji ƙansa ya girme masa bare ke".

Aikuwa faɗar kalmar ubanta da Baba ta faɗa ya ɓatawa AZIZA rai, ɗif tayi har aka gama wankan ,sanin da mutane a gidan ne ya sa bata fito da kumfar ba, dan kar pretty tayi mata dariya sai da aka ɗaura mata ɗankwali sannan ta fito ta kurma uban ihu "wayyo Allah ta zagi Babana yana kabarinsa akwance, na shiga uku na lalace Malaminmu ya ce duk ɗan da yake yin abu sai an taso Babansa a kabari an nuna masa,an zagi Babana bai yi komai ba" Inna Gaji ta fito tana kamata da tambayar waye" 


Ba kunya ta nuna Baba Tabawa ta na kuka har cikin ranta take ƙaunar Babanta duk da bata taɓa ganinsa ba,Inna Gaji ta ce " haba Tabawa ai duk abinda AZIZA tayi miki ba kya zagi ubanta ba ko dan darajar shi ɗin ke kika raine shi" Baba Tabawa ta ce" ta ya zan yi haka Yaya wallahi ba haka ba ne, kinsan halin AZIZA fa Yaya"

AZEEZ ne ya shigo gidan ganin su Siyama da su Inna Gaji anyi cirko-cirko ga AZIZA sai kuka take a hannun Inna Gaji, an sa Tabawa a gaba kamar wacce tayi sata, ya ce "me ke faruwa?" Siyama ta ce" uhmm ai Yaya gidan nan akwai kallo wallahi wai wannan aka zaga"

AZEEZ ya yi mata kallon banza ya ce" am zage ta ɗin, tashi anan ko na dake ki na daki banza" Inna Gaji ta ce" to ɗan halak ka fasa, wanda ya fasa baya ƙaunar iyayensa, ni daman ba yau na san hali ba, to aniyar kowa ta bi shi"

AZEEZ da yake jin haushin AZIZA ya bi ta bayan Inna Gaji ya je wajen Baba Tabawa ya ce" ki yi haƙuri BABA daman wannan yarinyar ni nasan munafuka ce, duk ku kuka ɓata ta ai, ga shi nan ke ma baki tsira ba, jiya Innar ai akayiwa" 

AZIZA ta miƙe ta ce "Allah ya so ni bana zagin manya, kowa ya ganni ya ga musulma wasu fa, ana ganinsu anga arna....Saukar mari ta ji wanda ba ta san ta inda ya sauka ba, dan AZEEZ akwai tsawon hannu.


Inna Gaji ma kan sai da ta dafe kunci, kafin ya sauke yaji an ɗauke shi da mari tasss.......A zuciye ya ɗago, idonsa ne ya faɗa cikin na Daddy, "yauwa Aminu kayi dai-dai"

ce war BABA.


Wata wutar ƙiyayya ce ta ƙara ruruwa a zuciyar AZEEZ.

AZIZA kuwa gigicewa tayi dan marin har cikin idonta ya sauka, Baba Tabawa ta riƙeta duk da a ruɗe take, tsakanin harshe da haƙorima ana saɓawa bare kishiyoyi).


Inna ta ce" kinga Tabawa cikata ba na son munafurci ba ke kika fara ba, ki sa ƴa a gaba da zagi ta uwa ta uba, ai kinsan da wayonta sarai mtswww" BABA ya kalli Tabawa wacce ta hau rantse-rantsen ba ta yi ba, Daddy ya ce"dan Allah ku yi haƙuri maybe laifi ta aikata,kuma dole ne a tsawatar wa da yaro.


AZEEZ da baya ji kuma baya gani, marin ne kawai yake masa kai komo a ransa, akan AZIZA aka mare shi, alwashin azaba da bala'i kala-kala wanda zai gana mata a sanadin marin da Daddy yayi masa wanda rabon da a taɓa shi tun yana yaro ƙarami.




BABA ya kamo AZIZA wacce take ta sauke ajiyar zuciya, ya ce "Tabawa ba zan ga laifinki ba saboda ba ki san darajar haihuwa ba, ba ki san zafin ta ba, shiyasa kike cutar yarinyar nan, amma idan da kara ai jikar Gaji jikar ki ce, Musa a baki Fir'auna a zuci" abun ne ya ƙonawa Baba Tabawa rai, ɗakinta ta nufa tana fashewa da kuka.




Siyama da Munnir da mamaki ya kusa kashe su, tunda suka ga an mari babban yaya, BABA ya ja uban tsaki ya na ce wa" yi shiru AZIZAN BABA duk wanda ya kwana lafiya shi ya so, babu hegen da ya isa ya taɓaki na bar shi ko waye kuwa"

Inna Gaji ta ce " ga kayan karin kumallo can angama Ɗan su(sunan da take kiransa da shi kenan) Daddy ya wuce kan tabarman ya zauna su Siyama ma suka zauna, AZEEZ kuwa ko motsi baiyi ba yana nan tsaye idanunsa sunyi jajir ganin marin da akayi masa a gaban ƙannensa.



Inna Gaji ta ce"auta ka zo ka yi karin kumallo" AZEEZ da ƙar ya furta kalmar Azumi nake, duk da ba shi yake yi ba, control ɗin fushinsa yake so ya koya akan dangin mahaifinsa, Daddy ne ya fara ce wa AZIZAN BABA, " zo nan ni zan baki da kaina my daughter, daɗi BABA ya ji, AZIZA ta koma kusa da Daddy, su pretty sai kallonsu suke, gani suke yafi sonta akansu, hararata kawai Siyama take a fakaice.



Inna Gaji ta ce "Aliya ta zo, shekaran jiyan nan, ta bar saƙo a faɗamaka idan ka zo" Daddy da ya san da shi take, dan idan zatayi masa magana bata faɗar Ɗansu ɗinma kawai farawa take.

Daddy ya ce" to Inna me ta ce?" 

Su Siyama suka baza ear dan kwasar rahoto,Inna ta ce " jari take so ka kuma bata, dan wancen duk ya ƙare sun cinye"

Daddy ya ce" okay ba matsala ai zanje har mai kwangwalan ɗin yau in sha Allah" Inna ta ji daɗi sosai, ta ce" to Allah ya ƙara arziki" 

Munnir ya ce"daddy nima za ni" 

BABA ya ce "ai dukkan ku zaku kai ziyara dangi Manniru" 


Baba Tabawa kuwa ta na ɗaki, ko fitowa taƙi yi, AZIZAN BABA da ta ƙo shi, ta tashi ta nufi ɗakin Baba Tabawa tsayawa tayi gaban AZEEZ ta kalle shi, ta gigiza kai gami da ɗane baki, sannan ta wuce, kallonta kawai yake ganin babu alamar tsoronsa a idanunta.

Tana shiga ɗakin ta nufi jikin Baba Tabawa ta fara share mata hawaye ta ce" ki yi haƙuri Babata, ki daina zagi babu kyau" Baba Tabawa da iya gaskiyarta take ƙaunar AZIZA ta rungumeta ta kuma fashewa da kuka, ta ce" AZIZA bantaɓa haihuwa ba, amma hakan ba shi ne zai sa ace bansan darajar ƴaƴa ba, ba laifi nayi wa Ubangiji ba da bai bani haihuwa ba, wannan ƘADDARATA CE (Book ɗin da nake matuƙar so da ƙauna, ina typing ina hawaye), Ina fatan Allah ya sa sanadin samun rahmata ne a lahira" 

AZIZAN BABA ta ce" Allah sarki Babata ai Malamin mu ya ce duk wanda Allah bai bata haihuwa ba, to a ranar lahira Allah ya na jin kunyarsu, kuma zai shigar da su aljanna saboda haƙurin da sukayi"

Murmushi Baba Tabawa tayi ta ce" ta shi in miki kwalliya yau kayan sallah za'a sa ko" AZIZA ta sa dariya ta na murna.

Nan da nan ta shiryata tsaf, AZIZA ta fito, su Daddy har sun shirya za su je gidan Gwaggo Zainab da Gwaggo Maimuna, daga nan sai su wuce Kwangwalan gidan Gwaggo Aliya.



"AZIZA zo mu tafi mana" Daddy ya faɗa ganin ta fito, AZIZA ta girgiza kai ta ce" bazan je ba, su Habibu su dinga dukana, suna ce wa ni na hanasu zuwa gidan nan, wai BABA sai yayi ta yi musu masifa, ni kam bazan je ba" AZEEZ ya ce " ai ke annoba ce kowa gudunki yake mtsww" ya yi sauri ya fice kafin BABA ya furta komai.


Aikuwa ya hau "laƙadja'akum aniyar kowa ta bi shi, Aminu dole sai an nemawa yarinyar nan maganin baki da sammu da makaru, maƙiya ko ta ina sun zagayeta, ba a gidan ba ba,a wajenba, ba a nan ƙauyen ba ,ba'a marayarba" Daddy ya ce" hakane BABA bari mu dawo sai muje wajen Malam Yusuf ɗin" BABA ya washe baki ya na faɗin "to a dawo lafiya, Allah ya tsare" su ka fita driver har ya fito, AZEEZ ya na mota zuciyarta kamar ta fashe, gani yake duk abinda yayi wa AZIZA bai isa ya goge marin da Mahaifinsa yayi masa akan ta ba,ƴar ƙauye, ƙazama, ƙwaila, mtsww ya ja tsaki bayan sunayen da ya kirata da su.

Daddy suka shiga motar, driver ya ja dan yasan gidajen ƴan'uwan daddy.



Inna Gaji ta shiga yarwa da Baba Tabawa gabaici a tsakar gida.........




Zinariya ce✍🏻