CHAPTER 21 ( DIAMOND IN THE DIRT)
by @deejasmah
WANI RABON.........🦋🦋🦋
Elegant Online Writers ( E.O.W)
Khadeejah Bint Ismail ( deejasmah)
In dedication to all single ladies out there........
Arewabooks @ deejasmah
WhatsApp @***
N.B WhatsApp only not call😁
CHAPTER 21 ( DIAMOND IN THE DIRT)
This whole chapter is dedicated to my role model my mentor and also my joy giver that's non other than my dear mom, Hajiya Ummi she's been my supporter,fan and also my editor she use to go through my work and choose the best story line for me shukran ummi Allah ya k'ara girma da lafiya mai amfani and the chapter is also dedicated to every mother out there Allah ya kiyaye mana ku ya k'ara muku lafiyar raino da tarbiya......
"......Faheemah wata mace ce wacce a gani da ido ta kan burge maza da dama sai dai a bad'ini ita ba tai dai dai da tarbiya da tsarin zama matar wani ba saboda kasancewar ta 'ya ba kamar kowa ba shin Sir ka shirya jin wace ce Faheemah? shin in kaji ita ko wacece zaka rabu da ita ta cigaba rayuwarta cikin rufin asiri da kwanciyar hankali " girgiza kai yayi yana kallona kafin yace " Bazan k'yale ta ba but I'll love her,cherish and be proud of her the way she is ban fara son Faheemah don in daina ba but don in rayu da ita cikin ko wani yanayi da hali da zata kasance a ciki "
Lumshe ido nayi ina mai jin kalaman shi a kowace b'angare da sashe na zuciya ta tabbas soyayya d'aya ce sai dai k'arfin ta da tasirin ta a zuciyar masu yinta ya banbanta from one individual to another yau kam na tabbatar da hakan daga bakin Sir Arshad wai wannan wani irin so ne yake min haka ? Tun bai san ko ni wacece ba ya aminta da ni ya kuma yarda yai rayuwar shi tare dani a kowani hali da zan kasance
_"Don't be fooled Faheemah ko kin manta irin kalaman Masud a baya ne ? Kin manta da cewa shima ya miki kwatankwacin wainnan maganganun wanda hakan yasa kika saki jiki kika sakin mishi ragamar rayuwarki gabad'aya amma me yayi ? rabuwa dake yai a ranar da kike tunanin matsalar ki ta kawo k'arshe, hmm in barci kike ki farka domin kar ki bari abunda ya faru baya ya kuma maimaita kan shi "
_
Sune kalaman da wani b'angare na zuciya ta ta gargad'e ni dashi a take kuma na farfad'o daga gushewar tunanin da na tafi d'agowa nayi ina kallon shi da shima idon shi yake kaina saurin sauke nawa nayi jin bazan iya jure kallon shi ba don sak'on dake a rubuce a idanuwar shi mai k'arfi ne babu komai a idanuwar shi face tsantar gaskiya da kuma tabbatar da kalamanshi gare ni kawar da komai nayi a hankali nace " na tabbatar in kaji ko ita waye you won't think twice wurin canja ra'ayinka but kar ka damu bazan zarge ka ba saboda tun farko I've known and accepted my fate how is it don haka yarda da ni ko akasin hakan ba wata matsala ba ce a yanzu kuma zaka ji ko wacece Faheemah.............
The only thing I know while growing up was Mamie is a single mother,sai dai bansan ko muna da mahaifi ko bamu da shi ba abu d'aya dana sani kuma na amince dashi shine Mamie tsayayyar mace ce
Ban tab'a sanin wata mace a rayuwata wacce tafi Mamie ba ita d'in mace ce mai kamar maza she's strong,religious and pious a koina a kowani yanayi zan buga k'irji in yi alfahari da mahaifiyata domin ita d'in uwace wacce samun irinta sai an tona
A kowani hali muke tana nan tare damu ta tsaya mana a dukkan wani lamura namu bata tab'a bamu damar da zamu ga cewa muna buk'atar wani a rayuwarmu bayan ita d'inba ita ce Bilkisu Abubakar Sadauki jarumata abar alfaharina
Tunda muka taso a tare da ita ban tab'a jin ta ambaci suna na mahaifinmu ko danginta ba balle nashi tun muna tambaya a shekarun yarintar mu har muka gaji da tambayan domin bata tab'a gaya mana kalma d'aya akan shi ba
We are happy with our life saidai farincikin mu ragagge ne tunda bamu da wani ginshik'i ko bango daga Mamie sai ni kasancewa ta babba sai Arifah da take bina sai Fadeel autanmu sun d'auke ni a matsayin uwa, uba,yaya namiji da basu dashi,k'awa a mafiya lokuta mun rungumi juna baka tab'a jin kanmu saboda tsantsar fahimtar juna da muke dashi .
Dukda hakan a bangare na Ina fuskantar wani k'alubale a rayuwata tun daga randa na fara soyayya a rayuwata har izuwa rana mai kamar ta yau ban tab'a farinciki a soyayya ba kona fara bai wani d'ore wa zan tsinci kaina a cikin tsaka mai wuya
Ouch, so sorry, that was so rude of me not introducing my self (smiles).
Well, I'm Faheemah Abubakar sadauki, a 25 year old graduate of Business admin daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria I'm at 5"8 with slender but curvy figure I am a content creator and also a secretary of the executive department na Matawalle Global and this is the story of my life.........
Mu uku ne a wurin Mamie wato ni,Areepha wacce yanzu take 100l a KASU sai fadeel dake IJMB a CBS KASU shima akwai matuk'ar shak'uwa respect soyayya da kuma kulawa tsakanin mu muna rayuwa ne moderately bamu da matsalar komai a rayuwa sai dai irin wacce bazaa rasa ba Mamie is a nurse and also a lecturer a nursing department dake KASU bazan ce ga lokacin da tai karatun ba domin ta shi nayi na ganta tana aikin
Ba zan ce asalin garin mu ba domin bud'an ido nayi na ganmu a zaria a Falladan dake sabon gari LGA inda take aiki a wani clinic a samaru a hankali kuma ta koma school a ABU ta karanci B.Nsc lokacin muna primary ni da Areepha shikuma Fadeel nursery har service d'inta a zarian tayi shi aiki ta samu a General hospital kaduna hakan yasa muka tattaro muka dawo nan da ita bayan ta kama haya a cikin Hayin banki
Gidan k'arami ne falle uku ne d'akunan a had'e da juna sa wa tayi aka had'e mata suka koma 2 bedroom sai d'ayan kuma ya zama parlor d'inmu mu muna a guda d'aya ita kuma tana d'aya register tai mana a school Fadeel islamiyya ma ta binciko mana mai kyau da nagarta gidanmu kusa da nasu Noosrah ne don katanga ce ta raba mu ma gidan babban gida ne sosai don Baba tun da can ya na da abun hannun shi
Farkon tarewar mu ne Mamie ta d'auke mu muka shiga mak'ofta ta gabatar da kan ta a matsayin sab'uwar mak'ofciyar su kusan duk inda muka shiga da fara'a ake tarban mu gidan Alh Abdullah Maikwanoni ne k'arshe knocking mukayi maigadi ya bud'e gidan tsaf da shi gaishe da Mamie yayi inda tace mai tazo wurin matan gidan ne " Hajiya Ammi ko Mama ?" Shine tambayar da yai mata
Kasancewar ba ta san su ba yasa tace "dukansu " okay yace tare da mana jagora parlourn Mama kasancewar ta uwargida da sallama muka shiga a d'age da kallon rashin sani ta amsa gaisawa sama-sama inda Mamie tai mata bayanin cewa mu ne wainda muka tare a gidan kusa da su cewa kawai tayi Allah sarki daga nan bata sake magana ba ganin haka mukai mata sallama muka fita
Cikin rashin k'warin guiwa muka nufi d'akin Ammin sallama mukayi a bakin k'ofa amsawa akayi tareda cewa mu shigo wata farar mata ce zaune a kujera cikin fara'a tace " ahh ahh sannun ku da zuwa barka ku zauna mana" gaisawa akayi faran-faran ta sa aka kawo mana ruwa sai kuma tace " sai dai kuma kamar ban gane fuskar na " murmushi Mamie tayi kafin tace " wallahi fa mak'ofta ne nan gidan kusa daku shekaran jiya muka tare "
Fad'ad'a fara'arta tayi tana cewa "kaiii Masha Allah ya bak'on wuri ?" Sannan ta tambayi sunayen mu cikida girmamawa muka amsa mata mun d'an jima a parlorn nata kafin muka baro gidan bayan ta mana alk'awarin shigowa ita ma aiko bayan kwana biyu sai gata da 'yarta Noosrah yarinya mai son mutane da tsananin kirki a ganin farko ta shiga cikin mu tamkar an saba hakan yasa muka saki jiki da ita kusan sa'a ta ce a yanayin jiki ma zamu iya zuwa kai d'aya a kauri while na fita tsayi
Ba school d'inmu d'aya ba domin su wata makaranta mai tsananin kud'i suke zuwa while mu kuma namu ta masu matsakaicin k'arfi ne islamiyya ce akai sa'a makarantar d'aya muke zuwa sai dai aji ne bambancin mu saboda ni na fita aji dukda hakan tare muke zuwa mu dawo tare
Cikin lokaci k'ank'ani Mamie ta fara sabawa da mutane a unguwar musamman saboda yanda take bada taimakon gaggawa idan ciwo yazowa mutum ko kuma wurin tallafin nak'uda da dai uzururruka da ya kan taso a lafiyance amma kuma aminiyarta d'aya ce k'wal wato Ammi kusan komai za tayi sai tayi shawara da ita haka zalika itama Ammin hakan ne kuma ya sake hab'aka shak'uwar dake tsakaninmu da Noosrah wata tsohuwar baba ne Mamie ta samo domin taya mata aiki musamman a lokacin da bata nan har kwana takeyi damu in Mamie tana night
A hankali muke lallab'a rayuwar mu ba ma shiga cikin jama'a sosai in mun fita islamiyya ne ko school sai kuma gidan su Ammi Baba mutum ne mai tsananin kirki da son mutane ya rik'e mu tamkar 'ya'yan sa lokuta da dama ya kan siyo abu yai knocking gidanmu ya bamu ko kuma ya bama yaranshi su kawo mana hakan ne ya tsananta tsanar Mama a kanmu domin ita har gani takeyi kamar son Mamie yake yi hakan yasa ta tada bori ma'ishi toh da yake ya isa da gidan shi yai mata tas kuma ya nuna mata cewa idan da bai son ta toh yanzu haukan da take zai iya sawa ya so ta har ya aure ta
Hakan yasa ta wanko k'afa har gida ta cima Mamie mutunci wai ba'a san taba ba'a san asalinta ba amma tazo zata hana su kwanciyar hankali a gidajen su tun da nake ban tab'a ganin fad'an Mamie ba sai ranar kuma har kawo iyau bata tab'a fad'a da kowa kwatankwacin yanda ta wanke Maman tas tace mata ba mijin ta ba babu wani namiji a gabanta amma in tasa tsiya sai ta aureshin taga abinda zata yi ta taso za tai magana Mamie ta wanke ta tas ta kuma ce ta bar mata gida
Babu dad'ewa aka kawo mata tallahn wani gida da yake ta bada cigiyan gida mai d'an dama tana son siya su Baba ta sanya suka tsaya mata har siyan gidan ya kankama akayi komai da shaidu muka tare a gidan namu wanda yake kusa da titi wato inda muke yanzu kuma yafi kusa da islamiyyan da muke zuwa duk da nisan da mukayi da bestie hakan bai sa shak'uwar mu ragewa ba sai ma k'aruwa
A haka har na fara secondary school a Air force command secondary school dake cikin airforce base kaduna a mashin nake zuwa dawowa ma hakan in kuma na samu 'yan unguwa mui trekking mu dawo gida a lokacin kuma girma ya fara bayyana a jikina inda kuma a nan kyawun nawa ya fara bayyana wanda ya zama mafarin bayyanar matsala ta..........
A gajiye nake tafiya kasancewar ban samu mashin d'in da zai kaini gate ba ga kuma wahalar da muka sha na exams d'in jss 2 Q.E wato mock da muke yi ( duk wanda yasan AFCSS ya san nisan dake tsakanin ta da gate d'in Nafbase kuma samun abun hawa a ciki yafi wahala akan waje saboda ga su nan birjik a wajen suna lodi shikuma fitowa sai kaci saa kake samu musamman in kai d'aya ne ) hakan yasa na fara takawa a k'afa kafin Allah ya turo min d'auki a lokacin na had'u da shi tsaye sanye da uniform farare tas da su idon shi a kaina
Ganin farko sai da bugun zuciya ta ta tsananta yayinda wani yanayin da ban tab'a sanin ya na existing ba ya sake kashe jikina gajiya ta ta sake tsananta kawar da idona nayi daga kan shi ina mai korar yanayin da nake ji cikin wata murya mai amo da karsashi naji ance "hey beautiful " waigawa nayi ina kallon inda maganar ta fito shi d'inne dai had'iyar yawu nayi ina jiranshi har ya k'araso
Gaishe shi nayi cikin girmamawa wacce itace tsakaninmu da soldiers d'in amsawa yayi yana cewa " where are you going like this?" Ya tambaya bayani nayi mai na cewa gida zan tafi kuma ban samu abun hawa ba ya tausaya min sosai don alamun galabaita sun nuna a jikina cewa yai in tsaya ruwa ya kawo min sannan ya kira gate aka turo min mai mashin har inda muke godiya nayi masa ainun kafin na hau na wuce koda na sauka na bawa mai mashin d'in kud'i sai yace inje kawai an biya min
Tun daga ranar ban sake ganin shi ba har saida muka kammala exams muka tafi break sai dai tunanin shi ya na raina amma ban bar kowa ya fahimci mai nake ciki ba har bestie kuwa ko da muka dawo break ban ganshi ba ban kuma san inda zan ganshi ba don ko sunanshi ban sani ba amma surar shi ya na nan zuciyata daram
Tun ina sa ran ganin shi har na cire rai na cigaba da harkokina ba wai don na hak'ura ba aa sai don cewa banda yanda na iya a raina may be ma can wani garin aka kai shi tunda dama su sojoji haka aikin su yake maida hankalina nayi a karatuna yayinda tunanin shi yak'i barin zuciyata
Har muka fara shirin JSCE a ranar nayi latti saboda rashin samun abun hawa har aka tsare mu a assembly ground ina duk'e kaina a k'asa na jiyo muryanshi yana magana da wani soldier da sauri na d'ago kaina ina kallon inda yake tsaye shi d'inne sai girma da kwarjinin da ya k'ara kasa d'auke idona nayi daga kanshi shi kuma bai ma kula dani ba har suka gama maganar da zasuyi juyowar da zaiyi idanuwan mu suka sark'e cikin na juna da sauri na d'auke nawa idon yayinda kunyar kamanin da yai ya cika min ido
Fasa tafiya yayi ya koma wurin wanda ya tsare mu d'in magana yai mai akanmu sun d'an jima kafin wancan yazo cewa yai duka su tafi amma ban dani tsoro ne ya kamani ganin an sallami kowa ni ance in tsaya Allah dai yasa ba dukana zasuyi ba kodai saboda na kalle shi ne yasa hakan dama fa su sojoji na small thing dey vex them na furta a raina cikin rashin mafita na bishi a baya har zuwa inda yake tsaye
Sara mai yayi ya wuce bayan ya bashi umurnin tafiya cikin rawar baki na gaishe shi sai dai ga mamaki na murmushi ne a fuskar shi yace " beautiful how are you?" Fine sir na furta da rawar murya har ya lura da cewa a tsorace nake da shi hakan yasa yace " No beautiful don't be scared,I'm not doing anything to you so, rest assured " ajiyar zuciya na sauke still dai ban wani kwantar da hankali ba tunda ban san dalilin shi na tsayar dani ba
Ganin nayi shiru yasa shi cewa "well,my name is MISBAH ADAM (M.ADAM) and what's yours ?" A hankali na bashi amsa murmushi yayi yace "nice name can we be friends?" wani yawu na had'iye ina mai tsoron hakan a raina saboda ban tab'a sanin akwai wani abota tsakanin mace da namiji ba sannan kuma Mamie tai mana kashedi da sakin jiki da wasu mazan da ba muharramin mu ba
Ganin nayi shiru yasa shi cewa " issokay beautiful, go to your class bye " yana waving hannunshi bye na furta nima Ina mai nufar inda classes d'inmu suke nayi missing 1 period already don a k'ofar class na had'u da teachern gaishe shi nayi ya amsa tareda mun fad'an lattin da nayi hak'uri na bashi tareda cewa bazan kuma ba better yace tareda wucewa zuwa staffroom
Yanzu kam kusan kullum sai mun had'u da shi in yana kusa ya min magana in nesa ne kuma d'aga min hannu kawai yake yi ni kuma murmushi kawai nake yi in wuce a hankali kuma muka fara shak'uwa friendship d'in da ya nema ban san yaushe nai giving in ba har da bashi number wayan da Mamie ta bar mana saboda emergency
Before we notice it mun fad'a soyayyan juna wanda daga baya ne muka fahimci cewa tun ranar farko ne muka fara son juna (love at first sight) ya sanar min halin da ya shiga a lokacin da ya tafi ragement course na 6 months ban bari Mamie ta sani ba amma both bestie da Areepha sun san da zamanshi har tsokana ta suke yi akan yanda idanu na ya rufe akan shi turashi osun akayi hakan yasa muka daina had'uwa gabad'aya sai dai waya shima time to time
A hakan har na mukayi WAEC a lokacin ne ya buk'aci ganawa da Mamie saboda yana son a san da zaman shi a gidanmu don kusan kowa na gidansu sun san da soyayyar dake tsakanin mu tsoro ne ya kamani saboda nasan kashedin Mamie akan kula samari rasa inda zan sanya kaina nayi
Shiru nayi a d'aki ina zaune tunani nake ta ina zan b'ullowa lamarin dukda dai Mamie tana wasa da kuma sakewa damu bata d'aukan shirme ko kad'an bestie ce tai tsaki ganin tagumin yai yawa tace " wai ke hajiya meye kika zo kika sani a gaba haka " ajiyar zuciya na sauke ina cewa "like there's a problem,saboda har yanzu na kasa sanarwa Mamie akan Misbah and he's coming on Saturday "
Dariya ta fashe dashi tareda cewa " ke dai 'yar fari ce wallahi just tell her now,at least she knows that you are matured enough and Mamie won't be mad at you for falling in love rather she will be proud of you tunda har kika ga dacewar sanar mata,so babe don't hesitate just tell her " dafe goshi nayi kafin nace " you just don't get me babe, bawai tsoron gaya mata nakeyi ba kawai ban san yadda zata karb'i zancen ba ne shiyasa " shiru tayi tana nazari kafin tace kawo kunnenki kiji
Yessss na ce da k'arfi tareda rungume ta cikin nishad'i nace " thanks babe you are a life saver " tashi nayi Ina cewa toh sai anjima ni na wuce gida dariya ta kwashe dashi wai tunda naji maganin matsalata ai dole in tafi gida banyi magana na fito daga d'akin nasu ina shiga wurin Ammi sallama nai mata sannan muka wuce gidanmu tare
Sanda muka shiga bata dawo ba fira muka zauna yi dasu Areepha inda rabin maganar su ta biki na ne yanda kasan irin abun ya kusa d'innan dariya ma suke bani da al'ajabin d'okin su har lokacin islamiyya yayi muka wuce da yake muna tilawa ne yanzu saukan mu bai fi 2 months ba
Sai bayan magrib na shiga d'akin tana zaune akan dadduman da ta idar da sallah hannunta rik'e da carbi zama nai gefen dadduman ina jiran ta idar addua tayi ta fasha na taya ta shafawan kallona tai da alamun tambaya d'ukar da kai nayi ina wasa da yatsun hannu na kallona tai da kyau kafin tace " lafiya dai ko?"
Gyad'a kai nayi cikin I'ina nace " lafiya lau maaa " girgiza kai tayi cikin kulawa tace " but it doesn't look like that,what are you not telling me dear?" kallonta nayi cikin k'arfin hali da tuno maganar bestie nace " uhmm nothing Mamie dama someone wants to see you..." Wani kallon da ta jefamin yasa na kasa k'arasa maganar yayinda bugun zuciya ta ya tsananta d'ukar da kai nayi don ban san mai zance a gareta ba cikeda da mamaki tace " and who is that...........? Had'iye yawu nayi da k'yar don ban san me zan ce ba kuma.........................
Manage please wallahi k'yuiya nake ji 😁
#vote
#comment
#share
#add
Love y'all😍
Deejasmah🦋🔐❤