6
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_
'''DEDICATED TO'''
*AISHA ALIYU GARKUWA*
6⃣
Cikin tsantsar tashin hankali da zallar firgici Neehal ya d'ora hannunshi saman bakinshi had'i da zaro dadaran idanuwanshi waje,
bak'on al'amarin da Neesah taji ne yasa tsayawa cak a sunkuyen da take,
hannayenta duka biyun saman fuskarta cike da mamaki,
dan tunda Neesah take bata tab'a sanin zafin mari da duka a rayuwar ta ba sai yau,
dan haka ta diririce gaba d'aya ta fita daga hayyacinta,
cikin rawar jiki Neehal ya k'arasa ga Neesah ya sanya hannunshi ya d'oga ta,
cikin shagwab'a Neesah ta kalli Neehal had'i da sanya kuka,
kamar k'aramar yarinya haka Neesah ke kukan cike da shagwab'a,
" I'm very sorry Neesah....!, cikin zafin rai Najwah tace " au baku daddara ba kenan....!?
Bai kula da maganar da Najwah take yi ba yace " kiyi hak'uri Neesah please,
cikin kuka tace " please kai ni bedroom d'ina,
" kam bura uba wallahi baki isa ba, a gaban nawa kike nufin zai shigar dake bedroom,
ni kuma na tsaya sokoko ina kallanku ko me....!?
Daga Neesah har Neehal babu wanda ya kula Najwah, idanshi kan Neesah yace " ina ne bedroom d'in naki....!?
Da hannu Neesah ta nuna mishi, yana rik'e da ita ya nufi hanyar data nuna mishi,
gaba d'aya idan Najwah ya gama rufewa bak'in kishinta yakai mak'ura,
jikinta na rawa ta sha gabansu tana huci tace " wallahi sai dai idan bana raye ne zaka shiga bedroom da wata 'ya mace,
amma muddin ina raye hakan bazata tab'a faruwa ba,
pure red eyes d'inshi ya d'aga ya zubawa Najwah cike da zallar bak'i ciki,
da takaicin halayyarta yace " gafara Najwah.....!,
" wallahi bazan matsa ba sai dai idan gawa ta zaku fara tsallakewa ku wuce,
" I said move, ki matsa ki bani hanya, yayi maganar cikin d'aga murya,
kuka Najwah ta sanya tana cewa " Allah ko kashe ni zaka yi bazan tab'a bari ka shiga bedroom da wata 'ya mace ba,
cikin zafin rai yace " haka kika ce....!?
"Eh....! ta bashi amsa cikin matsanancin kuka,
" who is she please....!?
Neesah ta tambaye shi, cike da jin kunya yace " she is my wife,
sosai Neesah ta zaro ido had'i da cewa " what....! she is your wife....!?
"Yes, yace kanshi k'asa, d'an guntun murmushi tayi had'i da cije lips tace " ayya no karka damu,
kuje kawai mayi magana letter Neesah ta fad'a tana shafa k'irjin Neehal,
cikin ranta kuma tace " I will definitely tech her a lesson,
ganin yadda Neesah ke shafa k'irjin Neehal tana cije lips yayi masifar d'agawa Najwah hankali,
a haukace Najwah ta kuma yin kan Neesah da niyyar da cakume ta,
da sauri Neesah ta k'ank'ame Neehal had'i da cewa " hey...! you idiot fuck your self,
waye ubanki cikin k'asar nan har da zaki shigo villa house ki mare ni,
na kyale ni sannan ki k'ara wani yunk'urin duka na,
ina tunanin kina hauka ne ko kuma kin samu tab'in hankali,
then...! get out from here ko in saka k'atti su fitar dake yanzu,
ta k'arasa maganar tana cusa hannunta cikin k'irjin Neehal,
da k'arfi Najwah ta runtse idonta cike da zallar bak'in ciki tace " mari kau na mari banza, ko kina buk'atar k'ari....!?
Cikin murmushi Neesah tace " oh! yeah karki damu ko mari nawa kike so kiyi min kiyi kawai kanki tsaye,
revenge day has come,
kana ta mayar da kallanta ga Neehal had'i dayi mishi kiss a baki tace " kaje mayi magana letter,
kanshi kawai ya iya d'agawa, ya taka da nufin d'aukar files d'in dayazo dasu,
Neesah tace " no ka barsu zamuyi magana,
bayyi iya cewa komai ba ya fita, da sauri Najwah tabi bayanshi har tana neman fad'uwa,
zuciyarshi na bugawa da k'arfi da k'arfi ya bud'e motarshi ya shiga,
yana ganinta tana nufarshi yayi saurin jan motar yabar wajen,
da sauri itama ta hau motar data zo da ita ta rama mishi baya da gudu,
a hankali yake jan motar idan ka ganshi sai ka rantse babu komai cikin ranshi,
amma can k'asan zuciyarshi Allah kad'ai ya san meke faruwa,
cikin nutsuwa ya bud'e motar ya fito batare daya rufe ta ba yayi shigewarta part d'inshi ya rufe,
dai-dai lokacin Najwah tayi parking jikinta na kerrrrma ta fita daga cikin motar tayi part d'inshi da gudu,
har tana yin tuntub'e,
jin k'ofar rufe yasa ta shiga bugawa tana kiran sunanshi,
Neehal kuwa dan kar yaji bugun k'ofarta da kukanta ya karya mishi zuciya,
yasa shi shigewa bedroom had'i da rufe k'ofa,
zama k'asa Najwah tayi tana rusa uban kuka had'i da bugun k'ofar da iya k'arfinta.
Direct part d'in Nana (mahaifiyarta) Neesah ta shiga da gudu tana rusa kuka wiwi kamar ranta zai fita,
a kid'ime Nana ta mik'e ta tari Neesah hankalinta ya kai mak'ura a tashi,
jikin Nana Neesah ta fad'a tana kuka cikin shagwab'a wanda hakan ba k'aramin d'agawa Nana hankali yayi ba,
" lafiya meke damunki....!?
Nana ta tambayi Neesah muryarta na cracking,
k'in yin magana Neesah tayi sai sautin kukanta data k'ara har da shid'ewa,
" soul meke damunki dan Allah ki sanar dani damuwarki....!?
Still shiru Neesah tayi, babu irin tambayar da Nana batayiwa Neesah ba amma tak'i magana,
jikin Nana na tsuma tayi dialing number President mahaifin Neesah,
bugu d'aya yayi picking, batare da Nana ta jira abinda President zai ce ba tace " ka bar duk abinda kake yi ka dawo gida ba lafiya....!,
gabanshi na fad'uwa yace " lafiya meke faruwa....!?
Bata b'oye mishi ba ta fad'a mishi abinda ke faruwa,
cikin matsanancin tashin hankali President yace " tun yaushe ta fara kukan....!?
"Tunda ta dawo daga wajen meeting d'in daka tura ta, lafiya lau ta fita ta dawo tana kuka,
" what....! me yaron yayi mata...!?
"Ban sani ba danna tambaye ta bata bani amsa ba,
cikin hargagi President yace " wallahi zan iya k'arar da zuri'ar Lagosa gaba d'aya kaf muddin wani abu ya samu 'yata,
yanzu zan kira ubanshi nayi mishi kashedi, gani nan zan baro duk abinda nake na zo,
yana k'arasa maganar ya kashe,
zuciyar President na zafi yayi dialing number Alhaji Bilal Lagosa,
sai da ta kusa tsinkewa kana yayi picking yana murmushi yace " ranka ya......!,
bai k'arasa ba, President yace " dakata dan Allah ba wannan ne dalilin dayasa na kira ka ba,
ga tilon 'yata can wacce nafi santa fiye da komai tana kuka tun bayan meeting da d'anka,
wallahi duk alak'ar dake tsakani na dakai zan iya rufe idona ruf na b'atar dashi muddin wani abu yayi mata,
yana kaiwa nan a magana yayi dropping call d'in,
sosai hankalin Alhaji Bilal Lagosa yayi masifar tashi, ba wai dan tsoran President ko dan wani ba,
a'a kawai dai saboda shi d'an kasuwa ne yasan kuma duk shaharar da yayi a duniya idan ya sake yayi fad'a da gwamnati akwai matsala,
cikin matsanancin b'acin rai da bak'in cikin duk kashedin da yayiwa Neehal,
amma bai ji ba sai da ya haifar mishi da matsala, Neehal na kwance yana tunanin mafita da abinda zai cewa Dady,
wayarshi ya soma ringing a hankali ya mik'a hannu ya d'auki wayar,
ganin sunan Dady yasa gabanshi mahaukaciyar fad'uwa a tsorace ya tashi zaune yana juya wayar,
had'i da tunanin abinda zai cewa Dady har wayar ta katse Dady ya sake kira,
Neehal bai d'aga ba yana shawarwarin abinda zai fad'awa Dady wayar ta sake katsewa,
ganin haka ya tabbatarwa Dady lalle akwai matsala babba,
dan haka take yayi cancel duk wani abu nashi yayo Nigeria,
a ranar Dady da President suka isa Nigeria kasancewar private jet ne dasu ba wani b'ata lokaci.
Ganin ya rasa mafita yasa shi tunowa da Nauman,
kanshi ya dafe tunawa da gayi da tun ranar da abin nan ya faru bai k'ara nemanshi ko tuntub'arshi ba,
haka bai ko je ya duba Umaima ba,
take yaji shi kanshi bai kyautawa aminin nashi na rai da rai ba,
cikin mutuwar jiki yayi dialing number Nauman,
Nauman na kwance saman bed ya d'aga kanshi sama yana kallan ceiling,
ya tsunduma duniyar tunanin yau kwana takwas kenan da zuwa gidan Neehal ,
amma kwata-kwata Neehal bai nemi shi ko a waya yaji ya yake ba,
bai kuma zo duba Umaima ba, sosai abin yayi mashi zafi da ciwo,
inda wani ne can daban yayi mishi hakan da babu abinda zaiji,
amma ace amininshi na mutuwa, lalle tabbas ya yarda mace tana iya shiga tsakanin d'a da iyayenshi,
balle abota, ringing d'in da wayarshi ta soma yi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya ke ciki,
ganin sunan Neehal ya sashi jan uban tsoki, had'i da gyara kwanciyar shi,
sau biyar Neehal yana kiran Nauman amma yak'i d'agawa,
ganin haka yasa Neehal sanin fushi Nauman yake yi dashi,
cikin mutuwar jiki ya mik'e yana sanye da kayan jikinshi,
sai neck tie da 'yar saman cot d'in daya cire,
ta k'ofar baya ya zagaya ya fita danya san har lokacin Najwah na zaune bakin k'ofa,
har ya fito ya shiga motarshi ya tayar bata sani ba, sai da taji k'arar bud'e get kana tayi saurin mik'ewa,
amma kafin ta isa gare shi har ya fice abinshi, ya barta nan tsaye,
da gudu ta fad'a mota tayi gidansu dan a zatonta gidan yayi,
hospital ya fara zuwa aka shida mishi Nauman baya nan yana gida,
dan haka ya nufi gidan, bayan yayi parking ya fito part d'in Mama mahaifiyar Nauman ya nufa,
a parlor ya iske ta suna zaune harda Umaima da k'anan Nauman,
cikin da girmamawa ya durk'usa har k'asa ya gaida Mama,
ta amsa mishi cikin sakin fuska, yace " Mama ya jikin Umaima....!?
"Lafiya lau, Alhamdulillah, cikin jin kunya ya bada hak'uri sosai kan abinda ya faru da Umaima,
Mama tace " haba ai ba komai Neehal Allah ne ya k'addaro da hakan zata faru,
dan haka karka wani damu kanka kaji...!,
kanshi k'asa yace " nagode sosai,
kana ya mayar da kallanshi ga Umaima fuskarshi a sake yana murmushi yace " ya jikin naki....!?
Kanta ta kawai gefe tace " nayi fushi Yaya, tunda sai yau zaka zo duba ni,
cikin murmushi yace " ayya sorry sister ban nan ne nayi tafiya, kiyi hak'uri kinji....!?
"Lah Yaya wasa fa nake yi maka, ka daina bani hak'uri,
Mama ta mik'e tana cewa " bari na kawo maka abinci,
da sauri yace " a'a Mama a k'oshe nake daga gida na fito,
ya fad'a duk da uwar yunwar da yake ji, amma bai jin tension zai barshi yaci komai,
tayi mamaki sosai dan tunda take bai tab'a k'in cin abincin gidan ba,
ido ta tsora mishi sosai kasancewar tayi mishi farin sani,
tace " lafiyarka kuwa Neehal....!?
Murmushin yak'e ya k'ak'aro yace " lafiya lau Mama, dan karta kuma yin magana,
ko ta tambaye shi wani abu wanda zai saka dole yayi mata k'arya,
shi kuma babu abinda ya tsana kamar k'arya, bai san yayiwa wani daban k'arya ma balle Mama dayake yi mata kallan tamkar mahaifiyarshi,
yace " bari na shiga wajen Nauman, " to kawai Mama tace,
kwance ya iske Nauman yayi rigingine kusa dashi Neehal ya zauna a bakin gado,
ya k'ura mishi ido, sarai Nauman yasan Neehal ya shigo amma yayi kamar bai sani ba,
murmushi Neehal yayi yace " Aboki kayi hak'uri mana tunda gani nazo,
Nauman baiko juya ya kalli Neehal ba balle yayi mishi magana,
dariya Neehal yayi yace " please ka tashi muyi magana,
d'an tsoki Nauman yaja batare dayace komai ba,
Neehal yace " eh..! naji dai bakomai,
tsoki Nauman ya kuma ja yace " you're my headache & my problem maker ,
kaje bani da lokacin magana dakai, kaje can ku k'arata,
" dan Allah ka tashi muyi magana ,
tsoki Nauman ya sake ja yace " please live me along,
" amma dai kasan babu abinda nafi tsana kamar tsoki ko....!?
Da sauri Nauman ya mik'e zaune had'i da cewa " nayi maka tsakin ya fad'a yana k'ara jan dogon tsoki yace " kayi abinda zaka nayi d'in,
dariya Neehal yayi yace " babu abinda zanyi, kaga yanzu ai gashi na tashe ka,
" har zaka ce min baka san tsoki naga matarka kusan kushe mu tayi ni da sister ta,
amma ko a jikinka, even waya ma ta gagara tsakanin mu,
wallahi yanzu ma nasan ba banza ce ta jawo ka ba, duk yadda akayi ta kuma b'allo maka wani ruwan shine kazo neman mafita,
" ni dai dan Allah kayi hak'uri ka tsaya muyi magana,
" ina jinka, Nauman yace had'i da komawa kwancen ya juyawa Neehal baya,
" yanzu a haka zamuyi maganar....!?
"To ba kunne ne ke ji ba, shiru Neehal yayi wanda yasa Nauman d'ago kanshi ya kalle shi yace " ko ba kunnan ne ke ji ba....!?
"Please ka tashi ka saurare ni muyi magana a nutse, ina cikin babbar matsala wallahi,
dariya Nauman yayi yace " ahab ai dama nasan ruwa baya tsami banza, uban me ta kuma b'allo maka.....!?
"Hummmm kai dai bari kawai Najwah ta b'allo min teku bama ruwa ba,
" me tayi ....!?
Nauman yayi maganar yana kallan Neehal
" jakwal ne sosai dan harda President da tilon 'yarshi Neesah da Dady na,
zumbur ya mik'e zaune yana zaro ido yace " meya faru....!?
Cikin sanyin murya Neehal ya fad'awa Nauman duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
idon Nauman nakan Neehal harya dasa aya, Nauman ya tab'a baki had'i da cewa " Allah ya kyauta to,
"Amin, dan Allah meye shawara....!?
" Wa ni kake nufin zan baka shawara akan wannan mahaukaciyar k'idahumar, mai dod'add'iyar kwakwalwar matar taka....!?
" Wallahi kwata-kwata Najwah bata da hankali, kai ni ina tantama ma kan lafiyar kwakwalwarta,
gaskiya ku kaita Dawanau likitan mahaukata ya duba lafiyarta,
ayi mace babu abinda ta iya sai tijara, tirere da bankad'a gaskiya ya kamata kayi maganinta,
ka kuma koya mata hankali tunda na lura bata da hankali kanta hayak'i yake yi.......!
kasa jure munanan maganganun da Nauman ke jefar Najwah dasu Neehal yayi,
da k'arfi ya runtse idonshi cikin ranshi ya soma danasanin fallasa da tona sirrinsu da ita da yayi wajen Nauman,
a hankali ya bud'e idonshi ya sauke akan Nauman daya kafe shi da ido,
Nauman yace " love is not blind an madness, is better ka farga daga duniyar makafarki ka dawo real world,
" ka ga ni dai bani shawara yadda zanyi da Dady yanzu,
" babu wata shawara da zata kareka kawai ka saurari Dady da abinda zai zaitar kanka,
yayi maganar yana shigewa bathroom.
Bayan Najwah ta k'arasa gida ta iske baya nan sosai bak'in ciki da takaici ya turnuk'e ta,
ranta ya bata ai kawai wajen Neesah ya koma bata hak'uri,
dan haka ta zauna nan tana dirzar kuka, a fusace Dady ya fito daga cikin mota batare daya bari ta k'arasa yin parking ba,
a parlor ya iske Najwah tana rusgar kuka wiwi bai damu da kukan ta ba,
yace " ke..! ina mijinki....!?
Sosai gabanta yayi razananniyar fad'uwa, bakinta na rawa tace " ban san inda yake ba,
jikin Mamy na rawa ta mik'e tana kallan Dady tace " lafiya Alhaji meke faruwa...!?
Bai bawa Mamy amsa ba yayi dialing number Neehal,
Neehal na ganin kiran Dady yace " ya Salam...!,
" lafiya...!?
Nauman yace yana saka kaya,
"Dady kawai yace bakinshi na rawa,
" to kayi picking mana, " no ban san me zan ce mishi ba,
" idan baka d'aga ba kana k'arawa kanka laifi ne, dan haushi zai sake ji, gwara ka d'aga kawai,
Neehal na shirin d'agawa kiran ya katse, ganin bai d'aga ba yasa Dady kiran layin Nauman danya tabbatar suna tare,
kiran na shigowa wayar Nauman, Nauman ya kalli Neehal yace " Dady ne,
Neehal yace " please karka d'aga,
" kamar yaya karna d'aga nima so kake ka ja min....!?
Neehal na shirin yin magana Nauman yayi picking cikin girmamawa ya gaida Dady,
bayan sun gama gaisawa Dady yace " ina Neehal....!?
"Gashi nan muna tare, " ka kawo min shi nan da 5 minutes,
" to in sha Allah, Dady bai kuma magana ba ya kashe wayar,
Nauman ya kalli Neehal yace " Dady yace na kai mishi kai, dan haka ka tashi muje,
jikin Neehal a sanyaye ya mik'e suka fita suka nufi gidan.
President zaune yana rungume da Neesah dake ta faman kuka cike da tsantsar shagwab'a,
President yace " please soul ki sanar dani abinda yayi miki,
Nana tace " wai me yayi miki ne soul....!?
Babu irin tambayar da President da Nana basu yi mata ba amma tak'i yin magana,
a fusace President ya mik'e had'i da cewa " wallahi duk uban da ya tsayawa yaron nan cikin k'asar nan sai na ga bayanshi,
da sauri Neesah tace " no Dad...!, karka yi mishi komai,
" idan kina san karna yi mishi komai ki fad'a min abinda yayi miki,
cike da shagwab'a tace " Dad kasan matarshi 'yar waye,
" yes...! nama je d'aurin auren ai 'yar Ubayyu ce General custom controller na k'asa,
cikin kuka Neesah tace " she slapped me....!,
" what.....!?
President da Nana suka ce lokaci d'aya,
"Eh...! mari na tayi saboda kishi,
tsantsar mamaki ne yasa President zama jiki ba kwari.
Nauman na gaba Neehal na biye dashi a baya suka shiga cikin parlor'n,
Mamy na zaune saman sofa yayinda Dady ke ta faman zarya,
Najwah na gefe dan tasan gaba d'aya laifinta ne,
k'asa suka zube had'i da had'a baki suka ce " Dady ina wun........!,
dakatar dasu yayi ta hanyar d'aga musu hannu yana kallan Neehal yace " me kayiwa 'yar mutane....!?
Kanshi ya sunkuyar k'asa batare daya ce komai ba,
baya Dady ya juya musu yace " Nauman tambaye shi me yayiwa 'yar mutane,
shima bayyi magana ba ya sunkuyar da kanshi k'asa,
Dady yace " baka ji na ne....!?
"Kayi hak'uri Dady...!, Nauman ya fad'a a d'an tsorace,
" Okey kasan abinda ya faru kenan....!?
Kanshi ya sunkuyar k'asa, gabanshi na fad'uwa,
Dady yace " nace ka fad'a min abinda ya faru ko....!?
Kallan Najwah Neehal yayi da jajayen idonshi, a hankali ta sunkuyar da kanta k'asa hawaye na zubo mata,
matsananciyar tsawa Dady ya daka musu gaba d'ayansu yace " baku ji na ne....!?
Jikinsu na rawa suka had'a bakin wajen cewa " Najwah ce ta mare ta,
"Me....!?
Dady yace, kana ya kuma cewa " mari.....!?
"Eh....!, cikin rawar baki Neehal ya fad'awa Dady abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
cikin b'acin rai Dady ya kifawa Neehal gigitaccen mari,
yace " dan uwanka ba sai da nace karka tafi da ita ba.....!?
"Duk irin kashedi da jan kunnan danayi maka kan karka jamin matsala ashe sai da ka ja min,
kasuwanci na dana yi shekara da shekaru ina ginawa,
cikin zafi, sanyi, rana, damuna shine zaka wargaza min...!?
" Kasan irin abubuwa da k'alubalan dana fuskanta kafin na kawo iyanzu....!?
"Idan ita mahaukaciya ce tana hauka kai ma mahaukacin ne....!?
Cikin matsanancin kuka Najwah tace " kayi hak'uri Dady ba laifinshi ban.....!,
kyakkyawan maruka guda biyu Dady ya d'auke ta dasu,
yace " dake nake magana ko dashi....!?
"Ko ni sa'anki ne da ina magana zakiyi min katsalandan,
ko'an fad'a miki kishi hauka....!?
" Haka kikaga saurin mata nayi....!?
" Kinjawa mahaifinki dan nasan wallahi President bazai tab'a kyale maganar nan ba,
damma yarinyar tana da hankali tasan me take yi ba irin ki bace,
cikin kuka Najwah tace " am very sor....!,
" sorry for your self nonsense kawai get out from here idiot tun kafin na fasa miki baki,
jikinta na rawa ta mik'e ta fita,
idon Neehal runtse gam yana jin tamkar zuciyarshi zata kama da wuta saboda bak'in ciki da takaici,
dan sosai yaji zafin marin da Dady yayiwa Najwah,
Dady ya kalle shi yace " ko zaka rama mata ne....!?
Kanshi ya sunkuyar k'asa had'i da cewa " wane ni Dady, dan Allah kayi hak'uri.
A fusace President ya d'auki wayarshi da niyyar yayi kira,
Neesah tace " no Dad ka barni na d'auki mataki da kaina,
Nana tace " me zakiyi.....!?
"Neesah ta mik'e zaune had'i da kallan President da Nana, tace " ba saboda kishin na rungumi mijinta yasa mare ni ba....!?
"Eh...! Nana tace, Neesah tace " abu biyu nake so, na farko ina son a kawo min mahaifinta da ita tare lokaci d'aya,
dukkansu su zo gaba na, dan ina san na yanke hukunci a gaban idonta,
President yace " uhummm sai na biyu,
a hankali ta mik'e tsaye had'i da takawa tace " na biyu so nake nayi MAGANIN JAHILIN KISHINTA,
ina so na koya mata hankali, I want tech her a good lesson ta yadda zata gane kuranta,
Nana tace " ban gane ba, me kike nufi....!?
" INA SANSHI INA SAN NA AURE SHI NANA, SO NAKE AURI NEEHAL BILAL LAGOSA NA ZAUNA DASHI MATSAYIN MIJI NA KUMA UBAN 'YA'YA NA.......!
Don't for get to follow, vote and comments
MOMYN ZARAH 'YARBAIWA