RABO AJALI..

14

by @hauwaausmanjiddarh

_*RABO AJALI...!*_


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''


*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*


*ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA*


'''DEDICATED TO'''

*ZUWAIRAT UMMU MARYAM*


1⃣4⃣


Cikin zafin rai Neehal yace " wannan itace kalma ta farko da zaki fara yi min magana da ita.....!?


" Baki tambaye ni ya nake ba, baki tambaye ni lafiya ta da inda nake ba...!,

sai wani zancen banza kika fara yi min, good yayi kyau!,

saboda nayi waya dake ko bacci kirki banyi ba, & saida nayi tafiyar 4km,

amma shine kika yi min wannan tarbar ko....!?


"Baki tambaye ni duk abinda ya shafi lafiya da rayuwa ta ba,

babu tambayar yanayi ko halin danake ciki, saboda lafiyata da rayuwa ta basu dame ki ba,

sai zancen mace bayan kin san matuk'ar lafiyar Allah babu yadda za'ayi na d'auki lokaci haka banyi waya dake ba,

to hell with you Najwah, dakyar Najwah tayi k'ok'arin saita nutsuwarta,

tace " kayi hak'uri wallahi munanan mafarkai nake tayi ne,

" to da kike ta munayen mafarkai abinda ya kamata kiyi min yanzu kenan.....!?


"Ko ke a ganinki ta wannan hanyar ya kamata ace kin tarbeni....!?


" Ai da kike mugayen mafarkan ne ma ya kamata ki tambaye ni lafiya ta,

ya kuma kamata ki tsaya kiji abinda zance miki, amma dayake jahilin kishin ya gama rufe miki ido,

bama ki tsaya kin saurari halin danake ciki ba, balle ki tsaya kiji abinda zance miki,

imma a cikin wani yanayi ko mugun hali nake duk bai dame ki ba,

saboda rayuwata da lafiya duk basu shafe ki ba, basa kuma gabanki,

yayi maganar da d'an zafi, cikin matsanancin kuka har muryarta na shak'ewa,

tace " mafarki nayi kana rayuwa da wata mace,

yadda kasan rugugin saukar aradu haka k'irjin Neehal yayi muguwar bugawa da tsananin k'arfin gaske,

cikin rawar murya da d'an fad'a yayi k'arfin halin cewa " saboda ni fasik'i ne kuma mazinaci ne ko....!?


"Saboda ni babu abinda ke gaba na sai mata......!

wai ni tsaya ma dan Allah Najwah me kike d'auka ni ne....!?


"Wanne irin kallo kike min.....!?


" A layin wad'anne irin mutune kika aje ni, mazinaci, ko fasik'i ko mutumin banza ko me......?


Ya k'arasa maganar muryarshi na cracking, cikin muryar kuka tace " Allah ko d'aya bana yi maka kallan d'aya daga ciki,

kawai hankalina ne yak'i kwanciya, nutsuwata tak'i barina na samu salama,

tunane-tunane sunyiwa zuciyata yawa, kullum cikin tunani nake,

saboda jiki na yana bani abubuwa da dama,

ko nayi k'ok'arin k'aryata zuciyata da abinda jikina yake bani,

bana iyawa na rasa meyasa, but am sorry,

" saboda abinda kika sakawa ranki kenan, shiyasa kika k'i kyale kanki zama lafiya,

cikin lumana da kwanciyar hankali, ke kullum kina cikin yi min mummunan zato,

baki tab'a kyautata min zato na rasa dalili,

kuma abun yana matuk'ar damuna ace matata ta sunna itake yi min wani irin kallo,

itake zarginna, tak'i kyautata min zato, a zahirin gaskiya idan nace miki ban jin haushi nayi miki k'arya,

dan abun yana matuk'ar damu na, yana k'ona min rai na,

ke baki bar kanki kin samu nutsuwar ruhi da salama a zuciyarki ba,

nima baki barni ba, gaskiya ki canja, yayi maganar cikin k'arfin hali,

" to amma dai ai na baka hak'uri ko....!?


" Kuma na hak'ura ba, yayi maganar yana murmushi tamkar yana gabanta,

cikin k'asa da murya tace " to meyasa baka kira ni ba.....!?


"Kin k'ara kenan...!, idan ance kibar wannan sai ki komawa wannan,

kuma kin san dai babu abinda zai hanani kiranki matuk'ar babu wani abun ko.....!?


Cikin shagwab'a tace " me kuma nayi yanzu....!?


"Au bama kisan me kikayi ba kenan...?


" Eh! tace tana sakin murmushi, " tom tunda baki sani ba shikenan,

" a'a please ni dai ka fad'a min, ta fad'a tana neman saka mishi kuka,

" yi shiru dear daina kukan, kin san me kikayi.....!?


"A'a! tace tana gyara kwanciyar ta saman carpet, yace " ba yanzu na gama miki fad'an baki tambaye ni lafiyata ba,.....!?


"Eh...!, ta kuma bashi amsa, yace " yanzu instead of ki tambayi lafiyartawa,

sai kika kuma k'arawa kika tambaye ni dalilin dayasa ban kira ba,

cikin shagwab'a tace " ayya sorry my heartbeat, ya kake...!?


" Ban so tunda sai da na rok'a, yayi maganar yana kyaikwayon muryarta,

tana dariya sosai tace " au dama haka nake magana....!?


"Da baki sani ba....!?


" Ina kuwa zan sani tunda baka tab'a fad'a min ba, amma kaga ai na sani yanzu ko....!?


Sun dad'e suna waya cikin zallar so da k'aunar junansu, yadda kasan su fasa wayoyin su iske juna,

sun kai a k'alla 2hrs suna waya, kana Neehal yace " tom lokacin shiga aji na ya kusa,

kuma kin san sai nayi doguwar tafiya a k'afa ta 4klms kafin koma gida,

" ayya sorry my Happiness, yanzu sai yaushe kuma....!?


" In sha Allah idan na samu dama zaki sake ji na dear,

" kamar ya sai ka samu lokaci.....!?


"Kamar yadda nake fad'a miki, tunda ke baki ganewa, kanki kawai kika sani....!,

baki ta turo kamar yana ganinta tace " Allah ni dai a'a kawai kullum ka rink'a zuwa muna waya,

" tafiyar 8km kike so na rink'a yi kullum a k'afa....!?


"Eh! Allah ni dai ina san jin muryarka kullum,

" lalle uwa daban ce, lokacin dana ce zan rink'a kiran Mamy da Dady kullum cewa sukayi a'a,

saboda lafiyata da rashin tsoro, Allah yayi gaskiya daya fifita mahaifiya a saman kowa,

yayi maganar cikin ranshi, a zahiri kuma yace " baki tausayi na Najwah....!?


"Baki damu da tsaran lafiyata ba, baki san komai ba sai kanki, 

koma me zai faru ke dai na kira ko.....!?


" A'a ba haka bane ina san jin muryarka ne, Allah I really misses you so much,

" I know you missed me, amma sai kice kullum nayi tafiyar 8km,

aiko cewa nayi zanzo kullum muyi waya ke me cewa a'a na bari ce,

" kayi hak'uri....! ta fad'a cikin sanyi, murmushi yayi had'i da cewa " ai baki laifi ke kanki kin sani,

imma kinyi an yafe miki, tun kafin ma kiyi an yafe miki,

sai da suka k'ara yin wayar 1hr kana sukayi sallama dakyar suka rabu, 

bayan ta bashi Mamah da Nabeelah sun gaisa, zuciyar Neehal fess ya koma karkarar,

ji yake tamkar an bashi kyautar Aljannah saboda yadda yake jin zuciyarshi sakayau,

yana tafe yana murmushi kamar mahaukaci sabon kamu.


********************************


Ko data ta tashi daga bacci bata ganshi ba bata wani damu ba, bakinta ta kuskure da sauri,

bata tsaya yin komai ba ta nufi gidan su wajen Abpa da Dadanta,

a gindin murhu ta iske Dadanta tana hura wuta da baki, cikin mutuwar jiki ta zauna k'asa,

kwata-kwata fuskarta babu walwala, d'an kallanta Dada tayi,

kana tace " lafiya dai Bilgel....!?


Dada ta fad'a batare data daina hurar wutar ba, shiru Neelah tayi na d'an wucin gadi kafin tace " Dada'am dama kowa mijinshi baya sanshi....!?


Dakatawa Dada tayi da hurar wutar had'i da d'agowa ta kalle ta,

kamar zatayi mata magana sai kuma ta fasa ta cigaba da hura wutar,

Neelah ta cigaba da ciwa " meye aure, meye so me aure yake nufi, meye miji.....!?


D'agowa Dada tayi a karo na biyu ta kalleta sosai kana ta kauda idonta had'i da mik'ewa,

tana k'ok'arin barin wajen Neelah tace " Dada idan mutum yace baya sanka bazai tab'a sanka ba me yake nufi....!?


" Aure hanya ce ta neman Aljanna, hanya ce dake sada mutum da rahamar Ubangiji,

abu ne dake k'unshe da dukkan farin ciki, da jin dad'in duniya,

haka hanya ce dake kai mutum wuta, ko sada mutu da fushin Ubangiji,

kuma abu ne mai k'unshe da bak'in ciki, b'acin rai da damuwa, 

dole sai anyi hak'uri, juriya, an kawar dakai sannan za'a cimma nasararshi,

cewar Abpa (Malam Liman) yana shigowa,, fuskarshi d'auke da murmushi,

" miji kuma shine shugaban mace duniya da lahira, shine hanyar tsirarta, 

shi wani ginshik'i ne na rayuwar d'iya mace, wanda ba'a had'ashi da komai,, 

ba'a zaginshi, ba'a yi mishi musu ko gardama, ba'a so yana fad'a kina fad'a,

miji mutum ne da ake bawa girma, dajara da k'ima, da marta ba a d'aukake shi fiye da kowa a duniya,

" so kuma wata halitta ce da Allah ya halitta tsakanin kowacce irin halitta,

wacce duk bayanin da zanyi miki bazaki gane yanzu ba, sai zuwa gaba,

kasak'e Neelah tayi tana sauraron Abpa harya dasa aya,

kana tace " to Abpa idan mutum yace " baya sanya shikenan bazai tab'a sanka ba.....!?


"A'a Mamana, idan mutum yace baya saka yau me yiwa gobe ya dawo yace yana sanka,

haka idan yace yana sanka yau me yiwa gobe ya dawo yace baya sanka,

" to Abpa me akeyi aso mutum kuma me ake yi a daina san mutum....!?


" Ki zauna da suk wanda Allah ya had'a zama dashi lafiya,

ki zama mai kyakkyawar mu'amula tsakanin ki da mutane,

ki zama mai gaskiya, amana, tsoran Allah, tausayi da jin k'ai, 

mai ladabi da biyayya, ki kasance mai kyautatawa al'umma, 

ki guji duk abinda zai had'aki sab'ani da mutane, ki guji sab'awa mutane,

kiyi k'ok'ari duk wanda Allah ya had'aki zama dashi ku rabo lafiya,

ki gujiya zuciya da abin hannun mutane, kada ki kasance mai kwad'ayi, ko saka ido akan komai, ki tsarkake zuciyarki ki zauna da kowa lafiya, cikin aminci,

kada ki nufi kowa da sharri ko mugun nufi, 

" idan nayi haka zai so ni nima...!?


"Sosai ma kuwa tunda mijinki ne,

" miji na kuma Apba...!?


"Eh! mana Mamana mijiki ne,

" to ai shi yace ba miji na bane kuma bazai tab'a kira na da matarshi ba,

ajiyar zuciya Abpa yayi gami da satar kallan Dada, akayi sa'a itama shi take kallo,

basarwa Abpa yayi ya cigaba " kul..! Mamana daga yau karki k'ara zuwa kice yayi miki wani abu,

kada ku k'ara yin magana ko abu naji kin sake kin k'ara fad'awa kowa a duniya,

duk abinda yayi miki koya fad'a kiyi hak'uri wata rana in sha Allah sai labari,

duk abinda zai faru tsakanin ku ki barshi tsakanin ku, kada ki kasance mai fallasa sirrin aure dana mijinta,

cikin sanyin jiki tace " to Abpa meyasa yace ni ba matarshi bace......!?


Murmushi Abpa yayi irin na manya had'i da shafa kanta yace " bai isa yace ke ba matarshi bace tunda Allah ya riga da k'addara hakan,

Allah ya riga ya d'ora mishi nauyi da hak'k'inki, ruwanshi ne yaji tsoran Allah,

amma ke matarshi halak malak, haka kuma shima yake mijinki halak malak,

ke dai kiji tsoran Allah kiyi mishi biyayya, 

" Abpa zai so ni wata rana....!?


"In sha Allah zai so ki, ki dai kiyi mishi biyayya ki kuma ji tsoran Allah,

ki tsarkake zuciyarki ki zauna dashi bisa gaskiya da amana,

idan kika sake kika sab'a umarninshi ko kika cutar dashi, kika ha'ince shi,

Allah bazai tab'a kyale ki ba, sai ki d'and'ani azabatar Allah matuk'ar ba yafe miki yayi ba,

tana k'ok'arin yin magana Abpa ya mik'e had'i da cewa " ya isa haka Mamana, 

yanzu yana ina....!?


"Nima dana tashi ban ganshi ba, ido Abpa ya zare gami da tsuke fuska yace " bai sani ba kika taho....!?


"Eh mana! tace cike da k'uruciya, Abpa yace " kina san Allah yayi fushi dake ya kuma k'ona ki a wuta.....!?


" A'a...! Abpa ta fad'a tana zaro ido,

Abpa yace " to matuk'ar baki san Allah yayi fushi dake ya kuma k'ona ki a wuta,

kada ki k'ara fitowa ba tare da izinin mijinki ba, kada ki k'ara zuwa ko'ina har sai kin tambaye shi,

ya baki izini, idan bai barki ba ki hak'ura ko mutuwa zakiyi,

cikin sanyi tace " to dole ne idan zan fita sai na tambaya...!?


" Shalele na yayinda yara mata suka kai munzali basa fita daga gida batare da izinin na gaba dasu ba, sab'anin hakan yakanzo da matsaloli ga rayuwarsu,

" to Abpa'am, " yauwa Mamana maza tashi ki koma kinji, baki ta turo tare da cewa " ban ci abinci ba yunwa nake ji,

sai lokacin Abpa yakai dubanshi ga Dada yace " kin gama abincin ne....!?


"Na dai kusa..!, " yauwa to idan kin gama ki samu yaro yakai musu,

kana ya mayar da kallanshi ga Neelah yace " to kinji dai bata gama ba idan ta gama zata bayar akai miki,

shure-shuren k'afa Neelah ta soma cikin shagwab'a tana tab'e baki zatayi kuka tace " Allah ni dai yunwa nake ji Abpa,

" yi shuru Mamana, zaki sha fura...!?


Baki ta washe had'i da cewa " da zuma....!?


"Hummm sarkin kwad'ayi, akwai zuma, Abpa yayi maganar yana shiga bukkarshi,

ya d'auko kwaryar fura ya kawo mata, " gashi maza kisha ki tashi ki koma,

batayi magana ba ta amsa tana murmushi, sai da tasha ta isheta sosai, kana ta mik'e zata tafi,

Abpa yace " karfa ki sake ki biya ko'ina, ki koma bukkarku,

" to Abpa'am, ta fad'a tana fita daga bukkarsu.


******************************


A kishingid'a Neelah ta iske Neehal kanshi yana kallan sama,

fuskarshi d'auke da murmushi, kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin matsanancin farin ciki,

batayi mishi magana ba ta koma can gefe ta zauna had'i da kafeshi da ido,

ta rasa dalilin dayasa duk lokacin data kalleshi, take jin sanyin dad'i na ratsa dukkan jikinta,

ta rink'a jin sassanyar iska mai cike da ni'ima tana kad'awa a sassan jikinta,

a hankali itama ta soma sakin murmushi had'i da rausaya kanta, saboda tsabar shauk'in so.


_Ni ko nace dukkanku kuna cikin wani yanayi kun shiga coci marar fasto, Allah ya taro ku, Neehal yana mararin shauk'in Najwah, Neehal ta fara d'and'anar zak'in so, son maso wani k'oshin wahala.....!!_


Muryarta k'asa-k'asa ta furta  " Bodd'o..! (mai kyau ko kyakkyawa),

" ke wai mayya ce ....!?


Taji muryarshi ta bugi dodon kunnenta,, kanta ta kawar gefe batare datace komai ba,

" kallan uwar me kike yi min....!?


"Bakomai...!, ta bashi amsa cikin nutsuwa,

" shegiya mayya bak'ar daga, ko mayya ce sai kin ganni kin kyale ni,

hannu ta tafa had'i da cewa " ahayyeee...! bira wand'e, tayi maganar cike da zallar k'auyanci,

" ke..! dan uwarki ni kike yiwa shewa da ihuuu aka...!, sa'anki ne...!?


"Eh..! tace tana kama k'ugu had'i da jijjige-jijjige da murgud'a mishi baki,

irin fitsararrun k'auye

kauuuuui! kauuuuuu Neelah taji saukar zafafan marika guda biyu a jere,

tsananin azaba da zafi ne ya sanya ta durk'ushewa k'asa ta fasa gigitaccen kuka,

tana shafa kunci a rud'e, " ni sa'anki ubanki ne kona uwarki da zaki rink'a yi min iskanci kina yi min rashin kunya....!?


"Wallahi daga yau duk ranar da kika sake gigin yi min hauka da jakanta had'i da k'auyanci,

sai kin gane kuranki, cikin kuka tace " a toyi am, halled'e ba kad'o b'aleja,

" wallahi kika sake kika zage ni sai na karyaki,

" Allah hitai cakam bema, bi shirel, tayi maganar tana cigaba da kuka,

" kika k'ara magana da fullaci sai na baki bak'ar wuya,

yayi maganar yana take mata k'afa da iya k'arfinshi, ihuuun azaba ta saka had'i da k'ok'arin kwace k'afarta,

cigaba yayi da murza yatsun k'afarta cike da mungunta, harda cije lips,

sosai take kuka kamar ranta zai fita saboda azaba, tana kuma k'ok'arin kwace k'afar, amma ta kasa,

sai da ya gaji dan kanshi kana ya d'aga mata k'afar yana cewa " gobe ki k'ara dan ubanki,

da sauri ta sanya hannu ta damk'e yatsun k'afarta saboda rad'ad'in da suke yi mata,

kamar an saka wuk'a an datse su, sosai Neelah take kuka, ta had'a gumi sharkaf hawaye ya had'e mata da majina,

" kiyi minshiru...!, ya fad'a batare daya d'ago kai ya kalle ta ba, 

ko motsi batayi ba ta cigaba da kuka abunta, " ko kiyi min shiru ko yanzu na sab'a miki kamanni,

ya fad'a with care free, still bata yi mishi magana ba, ta cigaba da kukan,

tana rik'e da k'afarta, " ok yace yana k'ok'arin mik'ewa, da gudu Neelah ta nufi k'ofa,

sai da takai bakin bukkar ta juyo ta kalle shi tace " oho dai ni rayuwarka da zuciyarka na mara,

kuma sai dai bak'in ciki ya kahe ka, Allah lane, wande kutiri,

ta k'arasa tana fita da gudu, a fili Neehal ya maimaita " ni rayuwarka da zuciyarka na mara,

lips ya cije yana murmushin mugunta yace " you must pay, kema zan mari taki rayuwar da zuciyar,

Neelah bata dad'e da fita ba, yaro yayi sallama daga k'ofar bukkar,

Neehal yace " waye....!?


"Bingel...! (Yaro)


" Meye....!?


Neehal ya fad'a cike da k'osawa,

Yaron yace " daga gidan Liman aka aiko ni, " shigo Neehal yace batare da fargaba ko tsoron Neelah ce takaishi k'ara ba,

yaron ya shigo d'auke da tray yace " gashi inji Dadan Neelah tace a kawo maka,

" aje nan..!, yace a tak'aice, yaron bai kuma magana ba ya aje ya fita, ni'imtaccen k'amshi ne ya dagi hanci Neehal,

wanda yake matuk'ar bashi mamaki a duk sanda aka kawo mishi abinci daga gidansu Neelah,

k'amshin abincin ba k'aramin mamaki yake bashi ba, tunda yasan basu da kayan spices, 

basu kuma da kayan had'e-had'e na abinci, amma ya rasa yadda ake yi abincinta ke k'amshi da d'and'ano zakwaikwai,

sai lokacin Neehal ya tuna duk wayewar garin yau babu abinda yaci,

a hankali ya mik'e zaune daga kishingid'en da yake, ya jawo tray d'in gabanshi,

ya bud'a kwanukan, fura ya gani damammiya taji nono da madarar shanu,

had'i da zuma, sai dafaffen nama yasha daddawa da kayan k'amshi,

sosai ya ci naman da furar, kana ya d'an kwanta bai dad'e ba bacci yayi awon gaba dashi,

bai tashi ba sai da aka kira Sallah, ya tashi yayi alwala ya tafi masallaci,

bai dawo ba sai bayan sallar ishaa, yayi wanka ya kwanta batare daya damu da sanin halin da Neelah take ciki ba,

sai da ta tabbatar yayi bacci kana ta lallab'o ta dawo bukkar ta kwanta.


Washe gari da safe Neehal yana kan sallaya yana addu'a yaji sallamar su Mercy & Donyi,

cikin nutsuwa ya shafa addu'ar had'i da basu izinin shigowa,

"Mr Lagosa how you dare...!?


Suka fad'a suna zama k'asan carpet,

" broking English yace cikin ranshi, a fili kuma yayi murmushi had'i da cewa " Alhamdulillah, an you...!?


"Not bad...! Mercy ta fad'a tana tab'e baki,

Donyi zatayi magana Neelah ta shigo, bata kalle su ba bare tayi musu magana,

ta rab'e ta wuce can cikin bukkar ta tada sallah, 

Donyi tace " thanks to you Mr Lagosa,

since yesterday we're looking for you, but we didn't see you,

cikin rashin fahimta Neehal thanks for what, an why do you want see me...!?


" For the light sha, you're so kind & good person with fresh heart,

thank you so much Mr Lagosa, tunda Neelah ta idar da Sallah ta zauna tana kallan d'an tsukakken bakinshi,

da yadda yake sarrafa shi wajen yin magana, sosai ta k'urawa bakinshi ido, 

bata ko blinking, sarai Neehal ya lura da irin kallan da Neelah keyi mishi, 

batare daya kalle ta ba ce "ki ci kanki mayya kawai,

da sauri ta mayar da idonta k'asa tare da cewa "fauru,

bayyi magana ba dan baya san su Mercy su fahimci wani abu tsakanin su,

sun d'an jima suna hira kafin suka mik'e zasu fita, Donyi tana dariya ta d'ora hannunta,

kanshi had'i da cusa hannun cikin sumar kanshi tace " thank you once again Lagosa,

take duk wani annurin fuskar Neelah ya d'auke cak, ta kafe Donyi da dara-daran fararen idanuwanta,

wanda kallo d'aya zakayi musu ka hango zallar kishi da b'acin rai cikinsu،

murmushin yak'e Neehal yayi yana k'ok'arin zamewa idanuwanshi suka sauka akan Neelah,

ba k'aramin mamaki da al'ajabi had'i da d'imuwa suka kama Neehal ba,

amma saboda k'arancin shekarunta sai yak'i yarda da abinda ya gani tattare da ita,

Neelah dake durk'ushe tana jin zafi a ranta da zuciyarta, tana jin tamkar an kunawa k'irjinta wuta,

which is ita bata san me hakan yake nufi ba, bama ta san takamaiman abinda ke faruwa da ita ba,

duk abinda take yi Neehal na lura da ita, amma yak'i gaskata abinda ya gani.


Bayan fitarsu Mercy a gaggauce yayi wanka ya dawo d'akin ya d'ora ruwan tea, ya soya kwai,

ya zauna k'asan carpet yana ci, " zaka koya min turanci nima...!?


Tayi maganar cikin sanyi, banza yayi mata kamar baiji abinda tace ba,

" dan Allah ka koya min ina san in rink'a jin abinda kuke cewa idan kana magana da matan arna nan,

ina san na rink'a fahamar abinda suke ce maka, da abinda kake fad'a musu, dan bana san kana magana da wasu ni bana jin yaran,

tayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana,

cak ya tsaya da abinda yake yi, yayi k'asak'e yana k'ok'arin k'in gastawa,

a hankali ya juyo ya zuba mata ido na d'an lokaci yana san tabbatar da abin yake zato,

bayyi mata magana ba, ya cigaba da cin abincinshi ya gama ya fita.


After 2 months


Neehal kwance yana bacci yayinda Neelah ke durk'ushe gabanshi,

ta rafka tagumi hannu bibbiyu ta zuba mishi ido, tana kallanshi, 

tana jin farin ciki, nishad'i, annushuwa gami da tsantsar dad'i cikin ranta,

yayinda da sanyi had'i da ni'imtacciyar iska ke ratsa sassan jikinta,

daga b'angare d'aya tana jin wani abu yana tsargawa ta magunar jinninta, 

yana ratsa b'argo da jijiyoyin jikinta, yana bin magunar jininta tare da ratsa tsokar jikinta,

yana huda k'irjinta yana shiga cikin zuciyata, ta rasa dalilin dayasa duk lokacin data kasance tana kallanshi,

take ji wani irin yanayi marar misaltu a jikinta, 

tana jin abubuwa da dama idan tana kallan kyakkyawar fuskarshi,

takan tsinci kanta cikin farin ciki marar misaltu da iyaka idan tana tare dashi,

bazata iya misalta ko iyakance abubuwan da take ji idan tana kallanshi ba,

duk da Neelah bata san SO ba bata san me ake kira da SO ko SOYAYYA ba,

amma ta tabbatarwa kanta tabbas tana ji abu na daban kuma na musamman a kanshi,

wanda bata ji kan kowa, ba kuma ta tab'a ji kan kowa ba, bata da burin daya wuce taga tana kallanshi,

sosai take jin dad'in kallanshi, tana shagalta sosai idan tana kallanshi,

har takan manta kowa da komai da duniyar da take,

babban abinda yafi burgeta a fuskarshi bakinshi da hak'oranshi,

da kuma idonshi, abinda kuma yafi d'aukar hankalinta dariya ko murmushin shi,

abinda yafi jan hankalinta kuma maganarshi, da yadda yake yin maganar kamar baya so, sosai Neelah ke nishad'antuwa da kallan Neehal,

ta gama shagala da kallanshi, ta kafe shi da ido, wanda yasa hankalinta fita daga gangar jikinta,

harta mik'a hannu tana shafa fuskarshi batare data sani ba,

a hankali take shafa fuskartashi, batare data sani ba, which is ita harga Allah ba da wata manufa take yin hakan ba,

bama tasan takamaiman abinda take yi ba, kuma bata san abinda take ji ba saboda k'arancin shekarunta,

" bodd'o gorko am, ta furta batare data sani ba,

cikin bacci Neehal yaji ana shafa fuskarshi, fuskar ya d'an yamuta, tare da kawar da fuskarshi gefe,

hannunta ta kuma zurawa tana cigaba da shafa fuskarshi,

dole tasa Neehal ya soma bud'e idanshi jin ba'a daina shafa mishi fuska ba,

saurin ware idonshi yayi tangaram ganin Neelah zaune ta k'ura mishi ido fuskarta d'auke da yalwataccen murmushi tana shafa mishi fuska,

" bodd'o gorko am....! sark'e mata maganar tayi a mak'ogwaro sakamakon idonta daya sark'e cikin na Neehal.............!!!!


ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA


MOMYN ZARAH   YARBAIWA