RABO AJALI..

18

by @hauwaausmanjiddarh

_*RABO AJALI...!*_


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''


*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*


1⃣8⃣


Kallan Neelah Jauro yayi cike da zallar tausayawa yace " matsalar mutanen garin nan ce,

Abpa yace " dan Allah Jauro jeka inda kake san zuwa, ka fad'a min abinda kake san fad'a min mana,

kasa gaba na sai fad'uwa yake yi, ajiyar zuciya Jauro ya sauke,

tare da cewa " eh kan mutanen mu ne, kasan muddin suka fahimci abinda ya faru da Neelah,

ta shiga uku dan gaba zasu saka ta, bama ita kad'ai ba, har ku,

kai sanin kanka ne idan haka ta faru ga mace a karkarar nan sai taji tamkar ta bar garin,

saboda yadda za'a sako ta gaba daga ita har iyayenta, musamman idan suka gane GUDUWA MIJINTA YAYI YA BARTA....!,

a nutsu Abpa ya sauke numfashi had'i da kallan Neelah,

wacce tayi lamo a cikinshi tana mayar da numfashi, yace " bakomai akwai Allah,

Ubangiji yaga da niyyar da nayi ai, kuma Allah ya sani na bashi auren Neelah ne,

ba dan komai ba sai dan na taimake shi, na tsairar dashi, na kuma ceci rayuwarshi amma tunda shi haka yaga ya dace ya saka min dashi,

ai shikenan ya kyauta, Abpa ya k'arashe maganar hawaye na gangaro mishi,

" Abpa kuka kake yi....!?


Cewar Neelah cikin sanyin murya, ido ya k'ura mata batare da yayi magana ba, 

hawayen na cigaba da gangaro mishi,

cikin sanyin jiki Neelah ta sanya hannu ta shiga goge mishi hawayen dake zubowa kan kumatunshi,

had'i da cewa " ka daina kuka Abpa ni ma na daina, nama warke na daina jin zafin,

k'ok'arin k'ak'aro murmushin k'arfin hali yayi ya mannawa fuskarshi,

yace " karki damu kinji Mamana...!?


A hankali ta d'aga mishi kanta tana murmushin itama,

sosai Jauro yaji tsananin tausayin su yayi mugun kamashi,

cike da tausayawa ya kalli Neelah yana murmushi yace " karki damu babu komai, 

in sha Allah gobe zuwa jibi zaki warke garau, ki rink'a zuwa gad'a da wasa wajen k'awayenki,

amma kada ki sake ki fad'awa kowa abinda yayi miki kinji Bingel....!?


Cikin sanyin murya ta d'aga mishi kai had'i da cewa " to, "yauwa Bingel ki rink'a shan jik'on maganinki,

kanta ta kuma d'aga mishi, kana ya mayar da kallanshi ga Abpa yace " to Malam ni zan wuce idan da wani abun sai a kira ni,

" nagode sosai Jauro Allah ya saka da alkhairi, me za'a bayar na magani.....!?


Murmushi Jauro yayi had'i da cewa " ka barshi bakomai nima ai 'ya ta ce,

" ashsha ayi haka....!?


"Amma yi, cewar Jauro yana fita daga bukkar, Abpa yace Allah ya bar zumunci, Jauro ya amsa da " amin,

da sauri Dada ta had'a kara da k'irare ta kunna wuta, cikin k'ank'anin lokaci ta dafa ruwan ta juye takai bayan bukkarsu,

kana ta koma bukkar ta sanar da Abpa ta d'umama ruwan,

" Mama na tashi kije kiyi wanka, rau-rau tayi da ido kwalla na k'ok'arin zuba mata,

tace " Abpa bazan iya taka k'afa ta ba, da zafi sosai, cikin tausayawa Abpa yace " yi hak'uri ki daure ki k'ok'arta,

ba musu ta soma k'ok'arin mik'ewa dakyar tana runtse ido had'i da cije leb'e,

bazata iya mik'ewa tsaye sosai ba, dole daga duk'e kamar me ruku'u ta d'an d'aga k'afar da nufin dakawa,

" wayyo Allah na tace tana fashewa da matsanancin kuka,

" Allah da zafi Abpa bazan iya ba, " sannu Mama na, ki daina kukan, bari na d'aukeki,

kafin tayi magana Abpa ya d'auke ta cak, ya kaita har inda ruwan zafin ke aje,

kana ya juya ya bar wajen, Dada da kanta ta cire mata kayan jikinta,

kana tace " to shiga ciki ki zauna, ido Neelah ta zaro a matuk'ar razane gami da cewa " cikin ruwan zafin Dada....!?


"Eh.. baki ga da magunguna a ciki ba, ki shiga ki zauna, kuka ta sanya tana cewa " Dada'am k'onewa zanyi idan na shiga fa,

batare da Dada tayi magana ba ta kama ta, ta zaunar cikin ruwan zafin,

tare da danna ta sosai, bak'ar azaba ce ta sanya Neelah kurma uban ihuuu,

had'i da fashewa da gigitaccen kuka tana cewa,

" Dada dan Allah kiyi hak'uri ban k'arawa, Allah da zafi sosai, dan Allah ki cire ni,

banza Dada tayi da ita har sai da taji ruwan ya wuce kana ta zubar dashi,

ta canja mata wani ruwan zafin, batayi kuka sosai kamar na farko ba, 

sai da Dada ta canja mata ruwan zafi sau uku, duk suna hucewa kana ta kyale ta,

tun a cikin ruwan Neelah ta soma gyangyad'i, saboda taji dad'in jikinta sosai,

da kanta ta tafa a hankali ta shiga bukka ta canja kaya, kana Abpa ya bata abinci ta d'an ci kad'an,

shima sai da Abpa ya matsa mata sannan taci tasha magani, bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita.


*********************************


Abuja...


Yadda Neehal yaga rana haka yaga dare, kwata-kwata bai runtsa ba, ko gyangyad'i bayyi ba,

balle bacci b'arawo ya samu damar sace shi, daya runtse idonshi babu abinda yake gani sai Neelah,

na ihuuu tana kuka had'i da bashi hak'uri tana rok'onshi kan ya kyaleta,

haka har zuwa lokacin kunnen shi bai daina amsa kuwwarta da ihuun da ta rink'a yi ba,

cikin ranshi yace " ko me take cewa da fullanci lokacin oho,

cikin soyayya Najwah ta sanya hannunta ta shafo fuskarshi,

tare da cewa " tunanin me ake yi ne yallab'ai....!?


A hankali ya kalle ta tare da jefa idonshi cikin nata, yana sakar mata da kyakkyawan murmushi,

yace " tunaninki mana, yayi maganar yana jawo ta jikinshi,

tayi murmushi tare da kwantar da kanta saman k'irjinshi tana shafawa a hankali,

" tunnani na kuma name bayan gani gareka.....!?


" Aiko ina tare dake bana daina tunaninki, so ai ba k'arya bane,

" haka ne my heartbeat, but ka daina tunani na idan muna tare, dan ina iyayin kishi dashi,

kanshi tunanin nawa dayake ziyartarka bayan yasan muna tare,

yayi murmushi yana kallanta yace " tashi muje muyi wanka,

nasan wata k'ila Mamy ta gama shirya breakfast mu ake jira,

baki ta d'an turo tare da cewa " ni dai sai dai ka d'auke ni,

kuma kayi min wankan ban iya tashi dan jiya ka wahalar dani sosai,

duk wata gajiyarka ka sauke ta kaina, tayi maganar tana langwab'ewa,

" ke dai raguwa ce, ke da kika kasa wani abun kirki, " au haka zaka ce ma...!?


" Eh mana, sai yawan rakin tsiya, aka dame ni da waya inzo-inzo ashe ba wani abun kirki za'a tsinana min ba,

yayi maganar cikin tsukana, tace " naji bakomai, kai ba gajiya kake yi da sex ba, in aka biya maka sai ayi 24hrs ana ta abu d'aya kamar machine,

" to ai hakan shine cikar namiji, bakiji ance kyan namiji da suffar kare ba,

" hmmm ni dai tashi muje muyi wanka, kar ma kazo da maganar k'ari dan ba iyawa zanyi ba,

k'asa yayi da muryarshi sosai cikin salon jan hankali, yana shinshinar wuyanta,

yace " kuma kamar kin san a hannu nake ba, d'an duka takai mishi tana ture shi, tace " to ba dai a gidan muke ba,

dan haka muje muyi wanka,

tuntsurewa yayi dariya yana mik'ewa yace " matsoraciya kawai,

ba abinda aka iya sai faman cika baki, amma tun daga first round kike karaya,

ya k'arasa maganar yana d'aukarta, tare sukayi wankan cikin so da k'aunar junansu,

kana suka shirya cikin shiga ta alfarma suka fita falo,

kitchen suka iske Mamy da 'yan aiki, suna had'a breakfast,

har k'asa cikin ladabi suka durk'usa suka gaida ita, ta amsa cikin fara'a da sakin fuska,

Mamy tace " kuje parlor ko dinning ku zauna kafin mu gama had'a breakfast d'in,

ba kunya babu Najwah tace " to...!, tare da wucewa parlor,

'yan aikin suka kalli junansu cike da mamaki, bayan an gama jera komai saman table,

Mamy tace " to Oganni Bismillanku, ba kunyar Najwah tashi, ta nufi dining,

Neehal na biye da ita a baya kamar rak'umi da akala,

gaba d'ayansu gidan har Daddy,

dasu Suhaima suka zauna dinning table suna karyawa, kasancewar weekend ne,

Daddy ya kalli Neehal tare da cewa " Son! baka bamu labarin k'auyen da kayi service ba,

muguwar fad'uwa gabanshi yayi, jin abinda Daddy yace, amma sayya dake yayi kamar bai ji ba,

Mamy tace " Son bani labarin dangin mu, nasan kaga karamci, kyautatawa da mutuntaka ko.....!?


" Hummm ni ko naga asalin halin Fulani, ni zan bada labarin su waye Fulani,

ni da aka alak'abawa aure dole, aka tilastani yin auren dole,

yayi maganar cikin ranshi a zahiri kuma yace " kai Mamy gaskiya dangin nan naku ba magana,

tayi saurin cewa " suna da kirki ko.....!?


"Ina suke da wani kirki, Allah zuciyarsu kamar ta kafiran farko,

wannan da a kafirai suka zo inaga da bazasu karb'i musulunci cikin sauk'i ba,

tuntsewa da dariya Daddy yayi sosai, harda kyakyatawa, 

Mamy ta b'ata fuska tare da cewa " uhnnnn an sosa masa inda yake yi mishi k'aik'ayi,

ai kuma Barebari akwai k'eta, da mugun abu, cikin dariya Daddy yace " ni dai bani na fad'a ba,

d'anki ne ya fad'a dani na fad'a sai ace nayi san kai, ido Neehal ya k'urawa abincin dake gabanshi,

tunowa da Malam Liman da yayi, da irin mutunci, karamci da kyautatawar da yayi mishi,

ya tuna irin maganganun daya fad'a mishi, cikin sanyin murya Neehal yace,

" babu inda babu na gari, kamar yadda babu inda babu mugu,

babu inda babu mutumin kwarai, mai kyakkyawar zuciya,

haka babu inda babu mutumin banza, Mamy akwai mutanan kirki masu karamci da daddako sosai a cikin Fulani,

akwai masu tausayi da jin k'ai, akwai wad'anda basa san suga wani d'an Adam,

cikin damuwa ko k'unci koda basu had'a komai dashi ba, 

a hankali Mamy ta d'ora hannunta saman hannun Neehal, tare da tsare shi da ido, 

ganin yadda damuwa ta fito k'arara a fuskarshi, a fili ya sauke ajiyar zuciya,

had'i had'i cewa " I'm very sorry Malam Liman I hope you forgive me,

ya fad'a cikin ranshi, kana ya cigaba da cin abincin batare daya k'ara magana ba,

 cikin barkwanci suka k'arasa cin abincin,

sai da sukayi kwana biyu gidan su Mamy sannan suka koma gidansu.


**********************************


K'auyan Sunkhanni


Sosai Dada ta dage da gasa Neelah da ruwan zafinl, had'i magunguna kala-kala,

har da wasu ma ta had'a bayan wad'anda Jauro ya bayar,

cikin kwana biyu ta warke ras kamar babu abinda ya same ta,

yadda kasan bata tab'a yin ciwo ba, ko sau d'aya Neelah bata tab'a tambayar ina BAK'ON D'AN BIRNI....! yake ba,

duk yadda Dada da Abpa suka yi dan b'oye fitar maganar Neelah,

sai da ta fita ta cika gaba d'aya k'auyan, akai ta tsegumi,

duk inda ka zaga babu maganar yi sai ta Neelah, kamar wacce akayiwa fyad'e,

ko akayi zina da ita, yadda kasan babu aure tsakanin su,

haka nan ya far mata, akayi ta ciccira maganar ana wayo da ita,

ana zaune wajen mai gari Malam Liman yana gefe, kasan bak'auyen mutum bai iya magana ba,

wani ya kalli Abpa yace " Malam Liman ashe haka bak'on d'an birni yayiwa 'yar wajenka....!?


Kafin Abpa yayi magana mutumin ya cigaba da cewa " kai ma maganinka kenan,

Allah ya k'ara, ace duk gari gaba d'aya kowa ya hana 'yarshi,

sai kai uba d'igimi ka d'auka ka bashi, Allah gwanda ma da yayi maka haka,

wani daga gefe yayi caraf ya amshe da cewa, " ah kai kuwa yaga d'an birni mai kud'i,

mai tarin abun duniya ko baka ga yadda bukkarshi take mak'are da kayan alatu na more rayuwa ba....!?


"Na gani mana, inaga shima abinda ya gani kenan, da tsinannan san abin duniya,

ya d'auki tilon 'yarshi ya bayar, ai gashi nan yayi maganinka ,

ya koyawa maka hankali bama kai ba har da masu halin karambani irin naka,

haka k'auyawan fulanin nan sukayi ta datsawa Malam Liman magana,

mara dad'in ji, yayi misu shiru baice musu k'ala ba, sai da mai gari yaga abin yayi yawa kana yayi musu magana sukayi shiru,

bak'in ciki ne ya sanya Malam Liman barin wajen ya nufi bukkarsu yana matsar hawaye,

a bakin bukka ya iske Dada da Neelah zaune suna hira, ganin halin da Abpa ya shigo ya sanya su mik'ewa,

da sauri suka tare shi, a tare suna cewa " lafiya...! meke faruwa....!?


Bai b'oye musu komai ya fad'a musu yana cigaba da sharar hawaye,

nan tsaye ya barsu ya shige cikin bukka bai fito ba sai da lokacin sallah yayi,

washe gari da wuri Dada ta tashi ta soma shirin fita gidan suna,

jarkokin gidan ta tab'a gaba d'ayansu taji babu ruwa, dan haka ta kwalawa Neelah kira,

" Neelah maza kije rafi ki b'ebo min ruwa da sauri,

" to, tace tana d'aukar tulu, ta nufi rafin tun daga nesa Neelah ta hango k'awayenta,

cikin d'oki ta soma kwala musu kira tana gudu danta taddasu,

amma babu wanda ya amsa mata, duk da sunji kiran da take yi musu, 

da suka jiyo sukaga tana gudu danta cimmusu sai suma suka sanya gudun,

da suka isa rafin da sauri suka soma d'iban ruwan dan kada ta iske su nan bakin rafin,

suna gaf da gamawa Neelah ta k'araso cikin hakki tace " kuna ji ina kiranku amma shine babu wanda ya amsa min....!?


Duk banza sukayi da ita babu wanda ya amsa, Neelah tace " amma kuna ji na fa kuka yi min shiru,

d'aya daga cikin su tace " ke..! mufa an hana mu kula ki da wasa dake a gidan mu,

gaba d'ayanmu ance kada mu k'ara yi miki magana, 

inba haka ba zamu kwashi irin FARAR K'AFARKI, 

dan gaba d'aya garin kowa cewa yake yi FARAR K'AFA ce dake,

saboda ba'a tab'a yiwa wata aure miji ya gudu ya barta ba, sai ke,

kasancewar Neelah yarinya k'arama ce yasa bata fahimci inda maganar su ta dosa ba,

dan haka ta matsa kusa da Sa'ade tana k'ok'arin tab'a ta,

da sauri Sa'ade tayi baya had'i da hankad'a Neelah baya ta fad'i,

tulunta ya fashe, tace karki kuskura ki tab'a ni, ki wasa min BAK'IN K'ASHINKI,

a zuciye Neelah ta mik'e tayi kan Sa'ade tana rarumar ta, gaba d'aya yaran suka fashe suna yi mata ihuuu,

had'i da cewa " ihuuuu wa zai bari mai farar k'afa ta tab'ashi ya kwashi k'ashin tsiya,

duk inda ta nufa sai yaran su fashe suna yi mata ihuuu, kuka Neelah ta saka gami da d'aukar dutse tana cewa " Allah sai na fasa miki tulunki kema,

cikin rashin sa'a Neelah ta samu Sa'ade akanta nan take kanta ya fashe,

jini ya soma zuba, azaba ta sanya Sa'ade sakin tulunta ya fad'i ya fashe,

Neelah tace " yauwa na rama, gobe ma ki k'ara tsokana ta,

ta fad'a tana barin wajen, da taje gida Dada ta tambaye ta ina ruwa da tulu, 

Neelah ta fad'a mata duk abinda ya faru, cikin matuk'ar tashin hankali Dada ta nufi bukkar Abpa,

jin an fara kiran Neelah da me farar k'afa tasan an soma camfata kenan a garin,

tare suka fito da Abpa daga cikin bukka, shima cikin tashin hankali,

dan ya san halin mutanen garinsu sarai, Abpa ya kalli Neelah tare da cewa " me suka ce miki.....!?


Neelah ta maimaitawa Abpa duk abinda ya faru, a razane Abpa yace " kin tabbata sunce miki mai farar k'afa, da bak'in k'ashi....!?


Kai ta d'aga mishi tare da cewa " eh..!, Abpa meye farar k'afa da bak'in k'ashin....!?


Kasa magana Abpa yayi illa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un da yake maimaitawa,

Dada na k'ok'arin sanya kuka Abpa yace " a'a karki sake ki bawa mak'iyanki damar gane damuwarki,

kada ki sake ki basu damar game lagwanki, duk abinda zasuyi suyi karki sake ki nuna musu damuwarki,

iyaka dai idan abun yafi k'arfinmu, sai mu bar garin,

cikin rashin fahimta Neelah tace " Abpa mu bar garinmu mu koma ina....!?


Murmushi ya k'ak'aro had'i da shafa kanta dan karta fahimci halin da ake ciki,

yace " yawon ci rani zamu wata k'ila amma,

dama baki tab'a zuwa kinga birni ba ko....!?


Murna ta soma yi tana tsalle tace " zaka saka ni makarantar boko Abpa....!?


"Sosai ma kuwa, yace yana k'ok'arin mayar da kwallar dake k'ok'arin zubo mishi,

kana ya mayar da kallanshi ga Dada yace " jeki shirya abinki ki tafi gidan sunan, kuma koda kinje karki sake ki nuna wata damuwa ko kina cikin wani hali,

balle su gane damuwar dake tattare dake, " wallahi Malam tsoro nake ji,

tayi maganar cikin sanyi Abpa yayi murmushi tare da cewa " karki ji tsoran komai,

shirya maza ki tafi, bata k'ara magana ba ta shirya ta tafi, 

da fara'a wasai a fuskar Dada ta isa gidan sunan ta gaisa da mutane,

yadda kasan babu abinda ke damunta, amma a k'ark'ashin ranta cike take fal da tsoro da fargaba,

gefe Dada ta samu ta zauna tana cigaba da gaisawa da mutane,

bata dad'e da zuwa ba saiga Babar Sa'ade daga ita sai d'aurin k'irji,

ta tsaya kan Dada cike da ruwan bala'i tana jijjige-jijjige,

tace " kalli abinda 'yarki ta yiwa Sa'ade, yanzu sabo da Allah ta kyauta....!?


Cikin fad'uwar gaba Dada tace " Allah ya baki hak'uri kin san halin yaran nan,

cikin masifa Babar Sa'ade tace " da hak'uri ta mutu sadakar nawa kika bani....!?


"Hikenan a cuci mutum a hana shi magana sai hak'uri kawai za'a bahi,

kun haifa mana masifa da bala'i cikin gari, duk kun addabi kowa,

Neelah ta zamewa mutane bak'ar daga, da masifa, hegiyar yarinya mai farar k'afa da bak'in k'ashi, 

kawai danna hana Sa'ade wasa da ita hikenan sai ta nemi kahe min d'iya,

to idan ma baki sani ba nice nan na hana Sa'ade wasa da ita saboda karta kwasa mata bak'in k'ahi,

kuma kowa a k'auyen nan yasan 'yarki farar k'afa ne da ita, haka Babar Sa'ade ta sanya Dada gaba tana zazzaga mata tijara da masifa san ranta,

sai da gaji dan kanta kana ta bar wajen, ita dai Dada babu abinda take yi sai bata hak'uri,

Babar Sa'ade na fita matan wajen suka soma yin magana k'asa-k'asa suna nuna Dada,

ganin haka ya sanya Dada mik'ewa tabar wajen, daga k'ofar bukkarsu ta d'ora hannu aka tana rusa kuka,

had'i da cewa " hikenan mun higa ukku mun lalace,

jin kukan Dada yasa Neelah da Abpa fitowa da gudu, suna tambayarta me ya faru,

sai dakyar Abpa ya lallashe ta tayi shiru, kana ta fad'a mishi abinda ya faru, Neelah na gefe na jinsu, 

sosai jikin Neelah yayi masifar yin sanyi, ta soma fahimtar halin da ake ciki, cikin sanyin jiki ta durk'usa gaban Dada had'i da sanya hannu tana goge mata hawaye,

tana cewa " kiyi hak'uri Dada in sha Allah sai sunyi danasanin abinda suke yi mana,

da yardar Allah wata rana sai labari, tayi maganar hawaye na gangaro mata,

Dada tayi murmushin k'arfin halin, tare da gogewa Neelah hawayen itama,

tace " Allah yasa Bingel, Abpa yayi murmushi hawaye na taruwa a idonshi.


******************************


Abuja....


Neehal kwance saman sofa bed yayi rigingine kanshi yana kallan sama, 

while Najwah na kwance samanshi tayi ruf da ciki, kanta saman k'irjinshi,

hannunta yana shafa kwantaccen gashin dake kwance saman k'irjinshi,

yayinda shi kuma yake shafa kanta yana wasa da gashin kanta,

kallo d'aya zakayi musu kasan suna cikin farin ciki, annashuwa da jin dad'in duniya da more rayuwarsu,

cikin so da k'aunar junansu Najwah tace " I love you dear,

yayi murmushi had'i da rolling sexy eyes d'inshi yace " I know, 

d'an shiru ne ya ratsa, Neehal yayi shiru tare da fad'awa duniyar tunani,

jin shirun yayi yawa yasa Najwah d'ago kanta ta kalle shi,

" Heartbeat..?


Ta kira sunanshi cikin tuhuma, ajiyar zuciya ya sauke a fili tare da cewa " na tambaye ki dear....!?


"Uhummm tambaye ni ina jinka, iska ya furzar daga bakinshi tare da had'iyar yawo,

kana yace " yanzu kawai kiji na k'ara aure bada saninki ba, ko zan k'ara aure ya zakiyi.....!?


Take duk wani annuri, farin ciki da walwalar da take tattare da ita suka d'auke cak,

batare da tayi magana ba ta mik'e, tana huci ta shiga kitchen,

" lafiya my Happiness, daga tambaya, ina zaki....!?


Yayi maganar a tare, a hankali ya mik'e yana k'ok'arin bin bayanta,

yaga ta fito daga kitchen rik'e da sharb'eb'iyar wuk'a a hannunta,

idonuwanta sun kad'a sunyi jajir tamkar wuta, sai fitar da huci take yi,

idonta kanshi ta saita wuk'ar ta yanke jijiyar hannunta dake wajen tsintsinyar hannun,

jijiyar da idan ta yanke mutum baya dad'ewa a duniya yake mutuwa,

jini ya soma bin hannunta yana bin wuk'ar, yana zuba k'asa a galabaice jiri na d'ibarta ta kalle shi,

tace " kaga yadda zanyi, zan kashe kaina ne dan bazan tab'a iya sharing d'inka ba,

ta k'arasa maganar a matuk'ar galabaice gumi yana bin fuskarta,

tsananin tsoro da firgice tare da tsantsar tashin hankali ne suka hana Neehal motsawa daga inda yake,

ko k'afarshi ya kasa motsawa balle ya taka zuwa gareta,

a hankali ta saki wuk'ar dake hannunta ta fad'i k'asa, idon Najwah na kanshi ta sulale k'asa,

k'arar fad'uwarta ne ya dawo da Neehal daga suman tseyan da yayi,

a zabure ya k'arasa gare ta yana kiran sunanta, hannu ta soma mik'a mishi,

idonta na lumshewa yayinda gumi ya jik'a ta sharkaf, takai k'ololuwa wajen galabaita,

cikin tashin Neelah ya isa gareta gami da d'agota yana kiran sunanta,

had'i da jijjiga ta, a hankali ta bud'e idonta ta d'aga hannunta dake da ciwon,

ta shafa gefen fuskarshi, tana murmushi tace " I love you dear,

na gwammaci mutuwa ta sau dubu danayi zaman kishi da wata a kanka,

na gwammaci na mutu danayi sharing d'inka inaji ina gani ka rink'a shiga d'akin wata,

kayi min alk'awarin kona mutu bazaka tab'a yin aure ba....! ta k'arasa maganar a galabaice, 

ihuuuu ya soma yi yana cewa bazaki mutu ba, bazaki mutu ba, ita kuma tana cewa " mutuwa zanyi,

tayi maganar jini yana fita daga bakinta.........................!






*Zaku ga ina amfani hi a matsayin shi, misali :- hikenan, a matsayin shikenan, ina yin Oral Hausa ne (k'auyanci) so ba typing error bane*



MOMYN ZARAH      'YARBAIWA