24
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
LITTATTAFAINA MASU ZUWA
_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...! 300*_
_*ABU A HUDU...!*_
*_DA KAMAR WUYA...!_*
_*SAKI NA DAFE...!*_
2⃣4⃣
Murmushi Nauman yayi had'i da cewa " ban san sunanta ba,
Neehal yace " please ka tuna mana, Nauman yayi shiru yana tunani,
amma ya kasa tuno sunan Neelah, kanshi ya girgiza a hankali yana cewa " wallahi na kasa tuna sunanta,
a fili Neehal ya sauke ajiyar zuciya batare daya ce komai ba, har Nauman ya gama cin abincin Neehal bai kuma cewa komai ba,
washe gari Neehal da Nauman suka bazama Neeman admission a Oxford university,
Allah ya taimaki Neehal cikin sati biyu an shiga na uku suka gama komai,
while duk abinda suke Daddy na sane dasu, ido ya zuba musu,
bayan Neehal ya gama komai da komai, ya sanar da Najwah sosai tayi farin cikin jin zasu koma karatu,
koda Neehal ya sanar da Daddy cewa next week yake son su kuma Dubai makaranta Daddy bai nuna mishi komai ba,
yayi mishi addu'ar fatan alkhairi, ya amsa da amin, bayan kwana hud'u jirgin su Neehal ya d'aga zuwa America.
************************************
Sunkhanni
Duk inda kake tunanin k'unci da matsatsin rayuwa Neelah ta shiga,
sosai take cikin damuwa dan ba hali ta fito ko kewayen bukkarsu sai yara su biyo ta suna yi mata ihun tayi cikin shige,
dole ta koma zaman bukka, ya zama na ko k'ofar bukkarsu bata fitowa,
idan kaga ta fito daji zata je idan tana buk'atar band'aki, ko idan zatayi sallah,
Abpa da Dada na cikin bukka, Neelah ta fito ta nufi daji dan tanasan kewayawa,
bayan ta gama biyan buk'atarta ta taso da niyyar komawa bukkarsu,
dandazon yara wanda a k'alla zasu kai 20 suka shiga binta a baya,
suka yi mata ihuuu tayi cikin shige, wasu na d'iban k'asa suna bud'a mata a jikinta,
wasu na jefanta da duwatsu, haka suka taso ta gaba har bukkarsu suna jefanta da duwatse,
Dada da Abpa suna daga cikin bukka suka fara jiyo ihuuun yara suna cewa " ku bud'e ta tayi cikin shege,
ihooo me abin kunya, ganin yadda yaran suka jiwa Neelah ciwo,
ga jini yana ta zuba daga jikinta yasa Abpa saurin k'arasawa gareta,
ya tsugunna dai-dai tsayinta yana goge mata jinin dake zuba,
cikin muryar kuka Neelah tace " dan Allah Abpa ka barni na bar k'auyen nan,
ka barni nayi nesa da mutanen nan marasa inamani da tausayi,
wad'anda basu san tawakkali ko milk'alil zarratun ba,
Abpa zayyi magana ya jiyo muryar Dada na cewa " Malam tunda nake dakai, tunda kake yanke hukunci akaina har Allah ya kawo mu ka fara yanke hukunci akan Neelah,
ban tab'a bud'ar baki nace maka komai ba, ban tab'a yi maka musu ko nayi jayayya da maganar ka ba,
ban tab'a fitowa na nuna maka hukuncinka akan mu bayyi min ba,
ko yayi min ko bayyi min ba ina hak'uri na amsheshi hannu bibbiyu,
a yau ina san nayi abinda ban tab'a yi ba a iya tsayin rayuwarmu,
ina san na saka maka baki a harkar gida da hukuncinka, ina san na rok'e ka alfarmar daka bar Neelah ta koma birni,
shiru Abpa yayi yana sauraren maganganun Dada harta dasa aya,
yau karo na farko a rayuwarshi daya ji Dada ta kira ainahin sunan Neelah,
haka ta saka baki akan maganar shi, ya d'an dad'e kafin ya d'ago ya kalli Dada yaga tayi mishi k'uri da ido,
a hankali ya mayar da dubanshi ga Neelah, yaga itama ta kafe shi da ido,
murmushi yayi had'i da cewa " shikenan bakomai,
duk da Neelah bata jin dad'i hakan bai hana ta yin tsalle ta fad'a jikin Abpa ba,
ya rungume ta yana dariya yace " kin fa girma yanzu Bingel,
cikin bukkarshi ya shiga ya d'auko takardar da Umairah ta rubuta mishi number,
lokacin da zata tafi ta bashi tace koda ya canja shawara ya kirata,
in sha Allah zata zo ta d'auki Neelah, bukkar Mani me waya Abpa ya nufa,
bayan ya isa sun gaisa da Mani kana Abpa ya mik'a mishi number yace " dan Allah kira min wannan number,
Mani ya amshi number tare da cewa " Malam Liman ka san cikin karkarar nan babu hanyar sadawar kira,
dole sai mun tsallaka rafi munje hayin dutse kana zaka iya magana,
Abpa yace " ashsha bakomai muje, suna tafe suna hira har suka isa,
batare da b'ata lokaci ba Mani ya kira number Umairah,
Umairah na kwance saman sofa kanta saman k'irjin Naufal, yana ta rarrashinta kan tafiyar Neelah,
sosai Umairah ta shiga damuwa tun bayan tafiyar Neelah,
jin wayarta na rori yasa Naufal mik'a hannu ya d'auko ya mik'a mata,
batare data amshi wayar daga hannunshi ba tace " waye....!?
"Number ce kawai ba suna, fuska ta d'an ya mutsa kana tace " barshi bazan amsa ba,
wayar ya mayar ya aje a inda take, har wayar ta katse basu kuma bi ta kanta ba,
aka kuma kira, amma bata d'auka ba, sai da aka kira sau biyar bata yi picking ba,
Mani ya kalli Abpa yace " to basu d'aga ba,
Abpa yace " shikenan mu tafi, Naufal yana shafa kan Umairah yace " dear...!,
" uhnnnn tace, ya cigaba da cewa " bai kamata keda kike huld'ar jama'a a kira ki k'i d'agawa ba,
tunda kin san a koyaushe ana iya kiranki dan neman taimako,
d'an shiru tayi kana tace " kira number, ba musu Naufal yayi dialing number,
kasancewar su Abpa basuyi nesa da barin wajen network ba,
wayar ta soma k'ara, Mani ya duba wayar ganin number da Abpa yabayar a kira mishi ce,
yasa Mani d'aga wayar had'i da mik'awa Abpa yace " Malam Liman gashi sun kira,
jikin Abpa na rawa ya amsa yana cewa " to to masallah, jin muryar Abpa da Umairah tayi yasa ta saurin mik'ewa zaune,
sallama Abpa yayi mata ta amsa cikin zumud'i bakinta na rawa tace " Abpa ya Neelah tana lafiya...?
Murmushin jin dad'in yadda ta nuna damuwarta akan Neelah yayi ,
kana yace " tana nan lafiya, na kira ne dama danna sanar daku idan ba damuwa kuzo ku tafi da ita,
idan kun samu lokaci, baki Umairah ta washe tana mik'ewa tsaye tace,
" aiko gamu nan yanzu ma da izinin Allah, Abpa yayi murmushi tare da cewa " karki matsawa kanki ki bari ku shirya a nutse,
" a'a Abpa yanzu ma a shirye nake dan baka san yadda nayi kewar Neelah bane,
" to shikenan ba damuwa Allah ya kawo ku lafiya,
" Amin ya Allah cewar Umairah tana dropping call d'in, cikin zumud'i ta kalli Naufal dake zaune ya kafe ta da ido,
while deep down gabanshi na muguwar fad'uwa jin wayar da take yi, " oya zuwa Taraba ya kamamu dear,
Abpa yace muje mu taho da Neelah, murmushin yak'e yayi yayinda gabanshi ke cigaba da fad'uwa,
batare data jira jin abinda zaice ba ta rik'o hannunshi tana cewa muje mu shirya mubi jirgi.
Gaf da sallar Magrib su Umairah suka isa bukkarsu Abpa,
sosai Neelah tayi farin cikin ganin Umairah, bayan sun ci abinci anyi sallar isha sukayiwa su Dada sallama suka bar k'auyen Sunkhanni,
bayan fad'an da Abpa yayiwa Neelah kan rik'on amana da gaskiya,
a ranar suka kuma biyo jirgin dare suka koma garin Abuja, washe gari suka je har gida suka sanar dasu Daddy dawowar Neelah,
sosai dukkansu sukayi farin cikin dawowarta musamman su Suhaira,
kasancewar an riga an gama komai na makarantarta tun farkon zuwanta,
yasa babu wani b'ata lokaci ta fara attending school, boko da Islamic, bayan malaman dake zuwa gida suna yi mata lessons,
haka ma a school bata dawowa gida bayan an tashi tana tsayawa school lesson,
sosai Neelah ta dage da karatunta ta mayar da gaba d'aya hankalinta kan karatu,
bata kwanciya bacci har sai ta haddace gaba d'aya abinda aka koya mata,
Allah kuma ya taimake ta cikinta ba mai matsawa bane bata wani laulayi, kamar ma ba mai ciki ba.
BAYAN WATANNI UKU
Cikin Neelah ya cika watanni bakwai amma dayake yarinya ce da akwai k'uruciya tattare da ita,
yasa take yin abu gabagad'i dan lakuta da dama sai Naufal da Umairah sun tsawata mata,
haka ma idan taje gidansu Mamy, taita biyewa su Suhaila suna guje-guje da tsalle-tsalle sai Mamy tayi mata da gaske kana,
haka a b'angaren karatunta ta mayar da hankali sosai dan da zuciyarta da ruhinta,
take yin karatun ta k'udurce a ranta koda zata rasa rayuwarta wajen neman ilimi sai dai ta rasa,
amma bazata tab'a sarewa ba, hakan yasa take yin karatun a zuciye cike da son cimma burinta,
haka duk wani abinda Neelah ke buk'ata,
Umairah da 'yan aiki ne keyi mata, Umairah ta hanata yin komai, babu abinda take yi sai dai ta ci ta sha tayi karatunta,
haka ma Nauman da Naufal suna bata kulawa sosai ita da abinda ke cikinta,
tun cikinta na 5 month's suka fara siyayar kayan haihuwa,
zuwa 6 month's sun gama siyan komai na haihuwar,
Neelah na zaune saman bed k'afuwanta cikin ruwa tana karatu, jin wani abu ya tsarga mata a mararta yasata zabura,
a hankali-a hankali ciwon da take ji ya fara tsananta yana yin gaba-gaba,
tun tana cije lips harta fara murk'ususu a k'asa ta fasa kuka,
jin azaba ta tsananta har tana neman sak'ewa yasata fara rarrfe tana daga durk'ushen,
ta isa ga wayar landline dake d'akin tana daga durk'ushen ta had'a uban gumi,
jikinta ya jik'e sharkaf da gumi ta latsa kira, cikin bacci Umairah taji ringing,
tana daga kwance ta laluba ta d'auki kan wayar landline dake kan bedside d'inta,
tana kara wayar a kunnenta ta jiyo shashshekar kukan Neelah, dakyar ta iya cewa " kizo Aunty zan mutu,
a zabure Umairah ta mik'e had'i da dirowa daga kan gadon tana kiran sunan Naufal,
cikin nutsuwa ya bud'e idonshi ganin yanayin da take ciki yasashi saurin mik'ewa,
yana cewa " lafiya...?
" Neelah... kawai ta iya cewa a kid'ime ya mik'e yana cewa subhanallahi,
tare suka shiga bedroom d'in Neelah ganinta durk'ushe yasa su k'arasawa gareta da sauri,
ganin halin datake ciki ya k'ara razana su, suka rud'e sosai, dan ta fita daga hayyacinta dara-daran idanuwanta sun fito waje sunyi jajir dasu kamar garwashin wuta,
gashin kanta duk a yamutse, sanyin ac bai hanata jik'ewa da gumi ba,
da sauri Naufal ya koma bedroom ya sanya jallabiya da 3 quarter ya zari key d'in mota,
bedroom d'in Neelah ya koma batare da b'ata lokaci ba ya d'auke ta cak yayi hanyar fita,
saboda rud'ewa Umairah bin bayanshi tayi ta manta da babu kayan arziki a jikinta,
tana k'ok'arin fita harabar gidan kanta ba ko d'an kwalli, yace " a haka zaki fita...?
Sai lokacin Umairah ta kula da jikinta batare datayi magana ba ta koma ciki da gudu ta zira doguwar riga had'i da bulla hijab,
a bayan mota inda aka kwantar da Neelah ta zauna tare da d'ora kan Neelah akan cinyarta tana shafa kanta gami dayi mata sannu,
A harabar hospital yayi parking ya fito ya d'auke ta yayi cikin hospital da gudu had'i da kwalawa Doctor kira,
jikin Doctor da nurses na rawa suka nufo Naufal, babu b'ata lokaci suka karb'i Neelah aka shigar da ita labour room,
Naufal da Umairah na tsaye gaban labour room suna ta safa da marwa,
cikin sa'a Nauman yazo zai fita yana rataye da cot a kafad'arshi,
ganinsu ya yasashi yin turus cikin sanyin jiki ya k'arasa inda suke, " lafiya Big B....?
A d'an razane ya jiyo ya kalli Nauman, da sauri Umairah tace " Neelah ce take labour, " what....?
" Wanne irin labour?
Nauman ya tambaya a k'agauce, Naufal yace " eh tana cikin labour room,
cikin mamaki Nauman yace " but cikinta is 7 months fa, bai jira jin abinda zasu ce ba ya shiga labour room d'in,
sai bayan 3hrs da shigar Nauman kana ya fito yana goge gumi da sauri Naufal da Umairah suka isa gareshi,
Nauman ya sauke numfashi kana yace " bakawaini zata haifa,
amma duk da haka bazata iya haihuwa da kanta ba, saboda k'ugunta yayi k'ank'anta da fitar d'a, kuma nak'uda take yi mai bak'ar wahala,
har yanzu abu d'aya ake,
cikin tashin hankali Umairah ta fasa kuka tana fad'ar " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
cikin karaya Naufal yace " to yanzu meye abin yi...?
Nauman ya numfasa had'i da cewa " gaskiya ina ganin ayi mata CS kawai dan tana shan bak'ar wuya,
idan aka tsaya b'ata lokaci komai yana iya faruwa,
" dan Allah kayi koma meye please, Nauman yace " ai na riga da nasa hannun ayi mata aikin kum........
" kazo Dr AA yana kiranka, Nauman bai kuma magana ba ya juya ya koma cikin labour room d'in,
batare da b'ata lokaci ba aka gama duk wani shirye-shirye aka shigar da Neelah Theater room,
ana kwala kiran sallar asuba dai-dai lokacin Naufal da Umairah suka jiyo kukan Baby daga cikin Theatre room,
kallan juna sukayi had'i da mik'ewa tsaye,
fuskar Nauman d'auke da fara'a ya fito hannunshi d'auke da Baby girl,
Umairah tayi saurin nufarshi tana sauke ajiyar zuciyar, bakinta na rawa tace " ya Neelah....?
" Neelah zaki fara tambaya ko Baby...?
Yayi maganar yana murmushi Umairah tace " a'a ni ta Neelah nake yi,
Nauman zayyi magana nurse ta fito rik'e da wani Baby a hannunta,
cikin mamaki Naufal ya kalli Nauman yace 'yan biyu ta haifa....?
Cikin murmushi Nauman yace " ba 'yan biyu bane 'YAN UKU TA HAIFA BIYU MAZA D'AYA MACE,
da sauri Umairah da Naufal suka kalli Nauman gami da had'i bakin cewa " 'YAN UKU....?
Dai-dai lokacin da yaran Neelah suka tsandara kuka yayin fad'owarsu duniya,
Neehal ya farka a gigice daga daddad'an baccinshi, tare da fad'owa k'asa timmm daga saman bed,
a rud'e ya farka ya had'a uban gumi sharkaf yana ta nishi tare da kalle-kalle kamar zautacce......!
MOMYN ZARAH 'YARBAIWA