25
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
LITTATTAFAINA MASU ZUWA
_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_
2️⃣5️⃣
Cikin kid'ima da tashin hankali yayi saurin mik'ewa tsaye zumbur,
a matuk'ar tsorace duk ilahirin jikinshi na kerrrrma yana kalle-kalle wanda idan za'a kasheshi bai san dalilin faruwar hakan ba,
k'arar fad'owar da yayi daga saman gadon ne ya farkar da Najwah daga baccinta,
saurin mik'ewa tayi ganin yanayin da yake ciki, " lafiya! mike damunka my life....!?
Tayi maganar tana k'arasawa gabanshi, k'ok'arin motsa lips d'inshi ya soma yi yana san yin magana amma ya kasa,
ganin haka ya Najwah rungume shi, gami da shafa kanshi had'i da bubbuga bayanshi kamar baby,
lakur yayi a jikinta yana sauke ajiyar zuciya had'i da fitar da numfashi har ya samu nutsuwarshi ta dawo.
**********************************
Cikin matsanancin mamaki Umairah tasaki baki had'i da zaro ido tace " 'yan uku....?
Fuskar Nauman cike da murmushi tamkar shi akayiwa haihuwar,
yace " yes of course, kinga ikon Allah ko...?
Hannu Umairah ta mik'a ta amshi Baby daga hannun nurse had'i da washe baki,
tace " Alhamdulillah! Alhamdulillah ala kullu alin Allah mun gode maka abisa wannan kyautar,
lalle *RABO AJALI...!* ne sau d'aya tak fa ya tab'a sex da ita amma kaga dayake *RABO AJALI...!* ne har 'yan uku,
nasan duk inda mijin Neelah yake a fad'in duniya na tabbatar sai ya ji a jikinshi,
Naufal da farin ciki ya hana shi magana yana rungume da Baby boy d'aya a k'irjinshi,
idanuwanshi lumshi yana jin wani irin sanyin dad'i na ratsa duk wata gab'a dake jikinshi,
zuciyarshi nayi mishi sanyi yayinda yake ji dama yaranshi ne,
ina ma shi Allah yayiwa wannan ni'imtacciyar kyautar mai cike da rahama,
a hankali so da k'aunar yaran ke ratsa magudanar jiki da tsokar jikinshi,
nurses suka fito daga Theater room suna tura gadon da Neelah ke kwance zuwa rest room,
da sauri suka bi bayan nurses d'in Nauman da Naufal na rungume da Baby boys,
while Umaira na rungume da Baby girl, kan bed aka kwantar da Neelah had'i da jona mata drip,
d'aya daga cikin nurses d'in ta kalli su Umairah tana murmushi tace " to Auntyn Babies a bada su za'a sanya su cikin kwalba,
cikin rashin fahimta Naufal yace " kwalba kuma wacce iri?
Nurse d'in zatayi magana Nauman yace " eh! dole za'a saka su a kwalba na 1 to 2 month's,
" akan wanne dalili....?
Cewar Umairah idonta kan Nauman, sai da yayi murmushi kana yace " bakwaini ne basuyi kwari sosai ba,
suna buk'atar cikin mahifiyarsu, Umairah tace " to amma dai ai a bari su Daddy su zo su gansu tukunna ko...?
Nauman yace " rufa min asiri ni na isa, yaushe su Mamyn zasu k'araso...?
Ya fad'a yana kallan Naufal, sai lokacin Naufal ya tuna ba'a sanar dasu Mamy ba,
kanshi ya dafe had'i da cewa " ya Salam..!, Umairah ta kalle shi had'i da cewa " me..!?
" Gaba d'aya mun manta bamu sanar dasu Daddy ba, yayi maganar yana dialing number Daddy,
Daddy dake zaune kan sallaya yana azkar kafin ketowar alfijir wayarshi dake saman bed ta soma ruri,
har wayar ta gama ringing bayyi picking ba, k'ara kiran wayar Naufal yayi a karo na biyu,
harta kuma tsinkewa Daddy bai d'aga ba, Umairah tace " baiyi picking ba...!?
" Eh ina ga yana azkar ne, ya fad'a yana mayar da wayar cikin aljihunshi tare da mik'ewa,
ya kalli Nauman yace " muje muyi sallah, batare da Nauman yayi magana ba ya kwantar da Babyn hannunshi,
haka ma Naufal kana suka fita, a masallacin asibitin sukayi
sallah suna fitowa kiran Daddy na shigowa wayar Naufal,
cikin girmamawa ya gaida mahaifin nashi kana ya sanar dashi Neelah ta haihu,
Daddy yace " masha Allah me aka samu...!?
" 'yan uku ta haifa Daddy biyu maza d'aya mace, da sauri Daddy yace " 'yan uku fa kace Naufal...!?
Naufal yayi murmushi had'i da cewa " wallahi kuwa Daddy amma CS akayi mata kuma bakwaini ne,
" Alhamdulillah Allah ya raya Ubangiji ya bata lafiya, ga mu nan zuwa,
ko da Daddy ya sanar da Mamy haihuwar sosai tayi farin ciki had'i da yin addu'o'i,
k'arfe takwas na safe driver yayi parking a harabar hospital, Daddy da Mamy da su Suhaira suka fito,
cike da d'okin ganin Baby Suhaima ta nufi cikin hospital Daddy yace " to gand'oki kun san d'akin da suke ne....!?
Kansu suka girgiza alamar a'a, Mamy tace " to da ina zaku....?
Waya Daddy ya ciro ya kira Naufal ya sanar dasu sun k'araso,
Naufal ne yayi musu jagora har d'akin, saman table Naufal ya aje basket d'in abincin da su Mamy suka kawo,
cikin girmamawa Umairah ta durk'usa har k'asa ta gaida Mamy da Daddy, suka amsa cikin fara'a,
itama su Suhaima suka gaida ita, gaban gadon da Neelah ke kwance Daddy da Mamy suka je while tana ta baccinta kasancewar har zuwa lokacin allurar baccin da akayi mata bata sake ta ba,
Daddy ya shafa kanta yana murmushi yace " sannu kamar tana jikinshi,
Suhaira tace " Daddy bata jinka fa bacci take yi,
Daddy yace " au haba bacci take yi....!?
Suhaira tace " eh! Daddy yace " ai ban sani ba, yayi maganar cike da barkwanci,
gaba d'aya aka saka dariya, Daddy da Mamy suka taka zuwa gaban gadon da aka kwantar da yaranta,
ido Daddy da Mamy suka k'urawa yaran had'i da yin shiru suka kafe yaran da ido batare da sun furta koda kalma d'aya ba,
a hankali Daddy ya d'ago kanshi ya kalli Mamy itama ta kalle shi, had'i da sauke ajiyar zuciya a tare,
ganin irin kallan da Mamy suke yiwa yaran yasa Umairah mik'ewa ta nufi wajen,
tana cewa " lafiya Mamy....!?
" Daddy me....! kasa k'arasa maganar tayi saboda mahauciyar fad'uwa da gabanta yayi,
dan sai a lokacin ta kula da tsananin kamar yaran da family'n Lagosa,
cikin tsoro da firgici Umairah ta sanya hannu ta rufe bakinta, gami da zaro idanuwa waje, cikin rawar baki ta kira sunanshi " Naufal, " lafiya...!?
Naufal yace, batare da tayi magana ba ta shiga nuna mishi yaran da hannunta,
da sauri Naufal ya nufe su danshi a zatonshi ko wani abun ne ya samu yaran,
" lafiya meke faruwa...!?
Naufal ya kuma tambaya a karo na biyu, jikin Daddy a sanyaye ya sanya hannu ya d'auki Baby girl,
yana dubbuba ta sosai, karaf idon Daddy sauka akan tauwadar Allah dake kumatun Babyn wacce gaba d'aya zuri'arsu birni da k'auye suna da wannan shaidar tauwadar Allahn,
koyaya ka had'a alak'a ta jini da ahalinsu dole za'a ganka da wannna shaidar,
cikin sanyin jiki Daddy ya kalli fuskar sauran yaga suma dukkansu suna da ita,
bakin Mamy na rawa tace " Alhaji kalli goshin yaran ga irin gashin goshinka nan,
wanda gaba d'aya yaranmu na dashi tun daga kan Naufal har zuwa kan auta,
bakin Umairah bud'e tayi saurin kallan fuskarsu taga d'an kwantaccen gashin daya zarto ya b'ullo saman goshinsu,
tabbas irin na Daddy ne wanda gaba d'aya 'ya'yanshi na dashi, jikin Mamy na rawa ta juya gefen kunnansu na dama,
danta k'ara tabbatar da zarginta, aiko ta ci karo da d'an k'ullutun da ake haihuwar yara dashi a zuri'arsu,
taga gaba d'aya suma yaran nada su, haka gaba d'ayan Lagosa Families na dashi,
kallan Naufal Daddy yayi rungume da macen a jikinshi,
cikin fushi Daddy yace " ka cuce ni, ka b'atawa zuri'armu suna,
duk irin tarbiyar dana baka amma da irin wannan sakayyar zaka saka min,
ashe dama haka kake Naufal....!?
" Ka b'ata wayonka ka tarwatsa dukkan yardar da nayi maka,
ka kuma bani mamaki, Daddy ya k'arasa maganar jikinshi na tsuma,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan min ha,
abinda Naufal ya shiga maimaitawa kenan yana dafe da kanshi, tare da yin baya taga-taga zai fad'i,
bango ya tokare shi, danshi kanshi ya ga zunzurutun kamar Babies d'in da ahalinsu,
shi kanshi ya san tabbas duk inda yaran suka fito daga cikin zuri'arsu ne,
kallan da Mamy da Umairah ke jefanshi dashi ne yasa shi cewa " wallahi tallahi na rantse da girman Allah,
ban tab'a ganin Neelah ba sai ranar da Umairah tazo da ita, k'afata bata tab'a taka Taraba ba sai ranar da muka je da Umairah,
nasan bani da mafita, bani shaida ko bakin kare kaina daga zargi,
Allah ne kad'ai zai fitar dani amma walla......! tassss tassss Daddy ya kifawa Naufal gigitattun marika guda biyu a jere,
cikin zafin rai Daddy yace " ni sa'an ka ne da kake neman raina min hankali..?
"Idan ba kai ne ubansu ba uba waye uban su?
" Kai kanka ka tabbatar duk wanda yayiwa yaran nan kallo d'aya yasan daga tsatsanmu suka fito,
sannan tsabar ranin wayo kace bakai ne ubansu ba, Daddy ya fad'a jikinshi na rawa kamar mazari,
kuka Umairah ta fashe dashi tana cewa " to idan babu wani abu tsakaninku meyasa ranar da muka zo gida ta haukace....!?
"Kuma meyasa ranar da mukaje garinsu mahaifinta yace " ina ta kuma samo ka...!?
" Wallahi nima ban sani ba, amma na tabbatar akwai wani abu a k'asa,
dan ni bani da wata alak'a da Neelah ko yaranta, Billahil azim,
abu d'aya ne zai warware wannan abun shine DNA test, shi kad'ai ne zai fitar ni,
ya kuma bayyana gaskiya, a fusace Mamy dake tsaye ta kasa magana tace " DNA d'in ubank....!
salatin da Neelah tayi ne ya hana Mamy k'arasa fad'ar abinda tayi niyya,
saurin goge hawayenta Umairah tayi had'i da nufar Neelah, a hankali Neelah ta soma bud'e idonta,
tare da sanya d'ayan hannunta marar cannula ta dafe kanta, while d'ayan na dafe da mararta,
bakinta yana maimaita salatin Annabi, a hankali -a hankali Neelah ta ware idonta tun tana ganin dishi-dashi harta fara gani tar,
a hankali idonta ya sauka akan Umairah, cikin k'arfin hali ta sakar mata murmushi,
had'i da soma k'ok'arin mik'ewa zaune, cikin nutsuwa Umairah tayi saurin rik'e ta,
jikin Naufal a sanyaye ya fita ya kira Doctor kasancewar Nauman ya tafi gida tun kafin zuwan su Daddy,
tare suka shigo da Doctor ya dudduba ta jad'i da cire mata k'arin ruwan, ya kalli Daddy yace " kar'a bata madara ko abinci me nauyi,
Daddy ya amsa mishi da to, kana Doctor ya fita, kasancewar lokacin da Neelah ta farka,
sama-sama taji maganganun Mamy dana Naufal yasata kiran sunan Daddy da Mamy a hankali,
" Daddy....! Mamy....!, cikin sanyin jiki suka amsa, tana daga kwancen cikin muryarta da bata fita sosai tace,
" kada ku zargi Hamma na akan abinda bashi damasaniya akai, kada ku alak'antashi da abinda bashi da alak'a dashi,
wallahi tallahi Daddy Hamma bashi da alak'a dani da yaran nan,
asalima ban tab'a ganinshi ba sai ranar dana zo garin nan, yana dai kama da Baban su ne sosai,
dan nima ranar dana fara ganinshi nayi zaton shi ne, sai daga baya na fahimci kama ce kawai,
amma wallahi bashi bane babansu, bashi da wata alak'a ko dangantaka da abinda na haifa,
na rantse da Ubangijin sammai da k'asai na rantse da girman Allah, ta k'arashe maganar hawaye na zubo mata,
jin irin rantsuwar da tayi yasa zuciyoyin Daddy da Mamy da Umairah suka yi sanyi,
had'i da sauke ajiyar zuciya, Daddy ya matsa kusa da ita ya shafa kanta had'i da cewa,
" kada ki damu Neelah na yarda da abinda kika fad'a amma tabbas jiki na yana bani yaran nan jini na ne,
akwai dai wani abu wanda mu bamu san dashi ba Allah ne kad'ai yasani, sai dai muyi addu'ar Allah ya baki lafiya yaran kuma Allah ya raya su Ubangiji ya amfani rayuwarsu,
duk aka amsa da "Amin, Mamy ta sanya hannu ta gogewa Neelah hawaye,
ruwan Lipton Umairah ta had'a mata kana ta taimaka mata ta tashi zaune ta shiga bata tea d'in a baki,
bayan an nutsa Mamy ta kalli Naufal da Umairah tace " ku tafi gida ku kintsa inyaso kwa dawo da yamma,
ba musu suka tafi, yayinda su Suhaima ke ta k'ok'arin tab'a yaran Mamy ta hana su,
bayan sallar ishaa Umairah da Naufal suka shigo d'akin, suka iske Neelah zaune tana shan tea,
Umairah ta aje basket d'in abincin da suka shigo dashi, ta k'arasa ta zauna bakin gadon,
fuskarta d'auke da fara'a tace " ya jikin naki....!?
Muryarta a hankali ta amsa " da sauk'i, Naufal yace " ya yaran...!?
D'an tsukakken bakinta ta turo kana tace " ni ina ruwa na dasu, tayi maganar cike da yarinta,
Naufal da Umairah suka zaro ido had'i da cewa " ban gane ba ruwanki dasu ba....!?
Mamy tayi murmushi tare da cewa " wallahi tun bayan tafiyarku nake ta fama da ita,
amma ko ganinsu tayi tak'i, ta tab'a su ma tak'i balle ta d'auke su,
nayi harna gaji amma ko kallan inda suke tak'i yi, Umairah tace " kai Neelah please kar laifin mahaifinsu ya shafe su,
cikin shagwab'a Neelah tace " Allah ba haka bane, Naufal yace " to yaya ne?
Mamy tace " kasan fulani akwai kunya da kara, ga kawaici, "uhmm kaji san kai cewar Daddy yana shigowa,
Mamy ta kalleshi tace " to ko ba hakan bane...!?
" Wa ni na isa nace ba haka bane, yayi maganar yana rik'e hab'a alamar tsoro, duk suka sanya dariya,
bayan an nutsa Daddy yace " ya kamata a yiwa yaran nan hud'uba,
Naufal ya kalli Neelah yace " wane sunan kike ganin ya kamata a sawa yaran?
Murmushi tayi had'i da cewa " duk yadda kukayi dai-dai ne, ni bani da wani zab'i, kuyi duk yadda kuke so,
sosai suka ji dad'in kalaman Neelah har ransu, cikin jin dad'i Daddy yace " a'a ki fad'i idan kina da sunan da kike son a sawa yaran ki,
baki ta zumb'uro gami da cewa " ni ba yara na bane, yaran Aunty Umairah da Mamy da Hamma'am ne,
su za'a tambaya sunan da za'a saka musu, duk sukayi murmushi
cikin ransu suna yaba hankalinta,
dukda ta kasance yarinya k'arama, Daddy yace " to ya sunan Babanki da Mamanki...!?
D'an shiru tayi kana tace " Daddy a saka sunanka dana Mamy da sunan Hamma na,
babu sunan wanda ya dayace a sakawa yaran nan bayan sunayenku,
Naufal zayyi magana ta langwab'e fuska gami da cewa " please Hamma,
sosai Daddy da Mamy suka ji dad'in jin tace a saka sunansu, sunyi farin ciki sosai,
Daddy yayiwa yaran hud'uba, macen aka saka mata sunan Mamy Taheerah za'a rink'a kiranta da NAILAH,
sai mai sunan Daddy Bilal za'a rink'a kiranshi da NAIL, Naufal yace " please Daddy a saka sunan Neehal instead of nawa,
ina da burin idan Allah ya bani haihuwa na saka sunanshi,
batare da Daddy yayi magana ba yayiwa d'ayan Baby boy d'in hud'uba da sunan NEEHAL,
za'a rink'a kiranshi da NEELMAH,
k'arfe 11:10pm na dare Mamy ta kalli su Umairah tace " ku tashi ku tafi gida,
Umairah tace " a'a Mamy ni zan kwana da ita ki tafi gida, Mamy tace " ya aza'ayi haka Umairah...?
" Ai dole ni zan kwana da ita, idan wani abu ya taso cikin dare fa, dole sai babba,
dole badan Umairah ta so ba suka tafi, da daddare Nauman yasa aka saka yaran cikin kwalba,
bayan sati aka sallami Neelah daga hospital direct gida Mamy ta wuce da ita,
duk da Umairah taso su wuce can gidanta da Neelah, amma Mamy ta hana tace dole sai anyi mata wankan jego na kwana arba'in,
bayan wata d'aya aka dawo da yaran daga hospital, sunyi b'ul-b'ul dasu gwanin sha'awa,
kyau da kamanninsu da Neehal ya k'ara fitowa sosai,
ranar da aka maido yaran Umairah na gidan suna zaune bedroom d'in Neelah suna hira,
suka jiyo kukan Baby daga falo Umairah ta kalli Neelah tace " badai har sun iso ba?
Baki Neelah ta tab'e tare da cewa " ni ina zan sani..?
Batare da Umairah ta kuma magana ba ta mik'e ta fita parlor, zaune ta iske Nauman, Mamy da Daddy kowanne rik'e da Baby d'aya,
ta k'arasa fuskarta d'auke da murmushi tace " har sun iso kenan Mamy...!?
Tayi maganar tana mik'a hannu ta amshi Baby girl,
macen nata kuka da alama yunwa take ji, Mamy ta kalli Nauman tace " takwara yunwa take ji,
kuma har yanzu Mamansu bata da wani Maman arziki, Nauman yace " madara da babies food za'a rink'a basu ,
yanzu zan fita na siyo, Daddy yace " Nauman ya maganar Nurses d'in da za'a samu masu kula dasu?
" An samu da tare dasu ma zamu taho, guda hud'u kace ko?
Daddy ya amsa da " eh guda hud'u, biyu su rink'a yini dasu, biyu kuma su rink'a kwana dasu,
inyaso sai a ninka muku albashinsu sau uku, Nauman ya amsa kana ya fita bai jima ba ya dawo,
da kayan ciye-ciyen Baby nik'i-nik'i tare da nurses 4, Umairah tayi musu bayani so ake su rink'a kula da Baby,
idan yau biyu suka kwana gobe sai wasu biyun su kwana, bayan salary d'in su za'a rink'a basu ninkinshi,
aka yi musu bayanin mahaifiyarsu yarinya ce bazata iya shawayar dasu nono ba madara da baby food za'a rink'a basu,
bedroom d'in kusa da Neelah aka basu aka jibe kayan baby kamar za'a bud'e shago su kansu nurses sunyi mamakin kayan,
washe gari Daddy yasa aka yanka rak'uma uku da shanu da raguna akayi walimar sunansu,
sosai Daddy ya kashe mak'udan kud'i aka ci aka sha, akayi hani'an,
koda Mamy tayi mishi magana akan kud'in da Daddy ke kashewa murmushi yayi tare da cewa " wallahi Taheerah duk inda yaran nan suka fito jininmu ne,
jikokinmu ne kuma kome daran dad'ewa gaskiya zata bayyana, itama Mamy sosai ta gamsu da maganar Daddy,
bayan suna Umairah taso abata yaran da Neelah su koma gidanta,
Mamy tace " ya za'ayi a baki yara har uku keda ko haihuwar fari bakiyi ba,
ki dai bari idan sun girma saiki d'auka, dole tasa Umairah ta hak'ura badan taso ba.
BAYAN WATA HUD'U
Sosai Neelah ta warke sumul yadda kasan bata tab'a yin jinja ba, tana gama arba'in Umairah ta matsala dole ta koma gidanta,
daga b'angare d'aya tuni Neelah ta koma makaranta ta tattara gaba d'ayan hankali da nutsuwarta akan karatunta,
ta dake da karatu boko da arabi, ya zamana duk makaranta an santa saboda tsabar k'ok'arinta,
duk set d'insu babu mai k'ok'arinta ita ke d'aukar 1st position a gaba d'aya set d'insu,
daya set result suke yi makarantar ba class by class ba,
duk wani Quiz da Competition da ita ke zuwa, haka ma a b'angaren islamiyya nan ma tayi fice sosai,
dan har musabak'a take fita, tayi fresh sosai, dan koda taje hutu sunkhanni mutane da dama basu gane ta ba,
yayinda da Abpa da Dadanta suka ji dad'in ganin yadda ta canja,
haka da suka ji labarin abinda ta haifa sunyi mamaki sosai.
Su Nail sun k'ara girma dan suna da wata shida da haihuwa har sun fara rarrafe,
farare tas-tas dasu wanke hannu ka tab'a, sosai suke samun kulawa,
yayinda suna k'ara girma tsananin kamarsu da mahaifinsu na k'ara fito,
Mamy na zaune a falo wajen k'arfe tara na dare, ta jiyo Nailah ta tsandara kuka,
dayake tana da rigima sosai da me sunan Neehal (Neelam) suna da rigima sosai,
jin an d'an jima bata daina kukan ba, yasa Mamy mik'ewa ta shiga bedroom d'in,
ta iske ta zaune dankwarkwar cikin gadanta, Mamy tayi murmushi had'i da d'aukarta tace " rigimammiya,
tana d'ago ta taga pampers d'in jikinta ta jike da fitsari, "k'azama! Mamy tace tana dariya, kana ta sauke ta kan gado tare da cire mata pampers da rigar jikinta,
gaban Mamy ne yayi muguwar fad'uwa lokacin da idonta ya sauka akan rowar dake gefen cikin Nailah _(rowa ne wani bak'in abu ne me kamar tabo)_
ido Mamy ta ware sosai danta tabbatarwa kanta abinda ta gani, ganin tabbas rowar ce (Lagosa Family mark),
yasa jikin Mamy na rawa ta aje Nailah ta nufi Nail da Neelmah hannunta na rawa ta d'age musu riga taga gaba d'ayansu suna da ita,
hannu Mamy ta d'ora aka had'i da fasa kuka tana cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
tayi maganar tana fita da gudu had'i kwalawa Daddy kira a razane........!
PLEASE 🙏 SUBSCRIBE MY YOUTUBE CHANNEL IF YOU'RE MY REAL FANS & YOU REALLY LOVE ME! ❤️
***
KUYI SUBSCRIBE YOUTUBE CHANNEL D'INA DOMIN SAMUN LITATTAFAN HAUSA, GIRKE-GIRKE MAGUNGUNAN MATA, DA SAURAN SU, IDAN HAR DA GASKE KA/KIN KASANCE MASOYI TA GASKIYA KUMA KUNA YI MIN SOYAYYA TA HAK'IK'A KU DAURE KUYI MIN SUBSCRIBE DAN TA WANNAN HANYAR NE KAD'AI ZAKU NUNA SOYAYYARKU GANI NAGODE
MOMYN ZARAH 'YARBAIWA