28
***
*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE, DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI, TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
LITTATTAFAINA MASU ZUWA
_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_
2️⃣8️⃣
Neehal jin kalaman Doctor yake yi tamkar al'mara, ko a mafarki, ido kawai ya zubawa Doctor har ya dasa aya,
kafad'arshi Doctor ya d'an tab'a yace " kana ji na kuwa?
Cikin tashin hankali da zallar firgici Neehal ya d'agawa Doctor kai alamar eh,
duk ilahirin jikinshi na kerrrma, durk'ushewa k'asa yay had'i da d'ora hannunshi aka ya fasa rikitaccen kuka mai gunji tamkar mace,
" innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan min ha,
da sauri Nauman ya k'araso wajen yana tambayar abinda ke faruwa,
jikin likitan a sanyaye yayiwa Nauman bayanin komai, shi kanshi Nauman ya shiga firgici da jin abinda likitan ya fad'a,
cikin sanyin jiki ya durk'usa gaban Neehal, muryarshi na rawa yace " kayi hak'uri Aboki....!,
" hak'uri fa kace Nauman, wanne irin hak'uri zanyi?
"Shikenan bazan tab'a ganin kwai na ba, bazan ga gudan jini na ba, shikenan bani da rabon haihuwa,
na shiga uku Nauman wallahi ina cikin wani hali, rayuwata tana cikin garari,
batare da Nauman yayi magana ba ya mik'ar da Neehal yakai shi office d'inshi, sannan ya fito ya dawo wajen Doctor,
Nauman yace " yanzu babu yadda za'ayi, babu wata dabara da kake ganin za'a iya yi?
Kanshi ya girgiza cikin karaya yace " am sorry Doctor Nauman amma gaskiya munyi iyakar yin mu,
dole sai anyi hakan, shiru Nauman yayi kanshi k'asa, yana tunanin mafita,
" kai zaka saka hannu ayi mata aikin...!?
"Wa ni?
Nauman ya fad'a yana zaro ido, Doctor yace " eh ba naga kai ma Lagosa Family bane,
" eh cousin Brother mijinta ne, amma ba ruwa na, kada daga baya tazo tana kuka da ni,
tace ma had'a baki aka yi dani aka cuce ta, " please Dr Nauman bamu da lokaci ka taimaka kayi signing,
Nauman ya fuzar da iska yana kallan Doctor yace " ana baka kana k'in karb'a, ni fa bak'in saka hannu nayi ba, ina tunanin abinda zaije ya dawo gaba ne,
kai baka san halin matar nan ba wallahi tana iya bi na da wani sharrin,
dan haka ba ruwa, nayiwa su Daddy waya na sanar dasu yanzu zasu k'araso, Nauman na gama rufe bakinshi suka shigo,
cikin girmamawa Nauman ya tare su yayi musu bayanin komai,
" tayaya akayi hakan ta faru...!?
Daddy ya tambaya, Nauman yace " wallahi Daddy ban sani ba, "yanzu ina Neehal d'in yake...!?
"Yana office d'ina, Daddy ya juya zai bar wajen, Doctor yace " please Alhaji ka saka hannu a paper da za'ayi mata aikin,
d'an jimmm Daddy yayi sannan yace " muje mijinta ya saka hannu,
Nauman ya kalli Doctor yayi mishi alamar ka gani ko, k'asa suka iske Neehal zaune ya had'a kai da gwiwa,
saurin k'arasawa Daddy yayi yana cewa " Subhanallah, Neehal lafiyarka kuwa...!?
"Daddy bani da rabon haihuwa, bani da rabon ganin 'ya'ya na kamar yadda kuka ganmu,
wayyo na shiga uku Daddy Najwah ta cuce mu, cike da mamaki suka kalli Neehal gaba d'ayansu,
Daddy yace " me ya faru?
Neehal zayyi magana Doctor yace " please Alhaji a saka hannu dan bamu da ishashshen lokaci,
karb'ar takardar Daddy yayi daga hannun Doctor ya mik'awa Neehal yace " kayi signing,
kanshi ya girgiza hawaye na zubo mishi yace " no bazan iya ba, Daddy bazan iya saka hannu a cirewa Najwah mahaifarta ba,
idan nayi mata haka banyi mata adalci ba, Daddy yace " hakan da zakayi shine adalci a gare ta,
dan idan baka saka hannu ba, ba mahaifarta kad'ai za'a rasa ba, ita kanta za'a rasa, jin ance ana iya rasata yasa Neehal amsar paper da sauri ya saka hannu jin,
likitan ya amsa ya fita da sauri, ba'a jima ba su Naufal suka k'araso, tare da 'yan gidansu Najwah,
duk sukauyi jugum-juhum cikin jimami, ba'a fito da Najwah ba sai bayan sallar ishaa, rest room aka wuce da ita su Neehal na biye da ita,
jikinshi na rawa ya zauna bakin gadon da take kwance yana shafa kanta,
sai wajen k'arfe 9:10pm na dare Najwah ta farka, a hankali ta soma motsi tana yamutsa fuskarta,
hannunta me d'auke da cannula ta sanya ta dafe kanta, ta d'an jima a haka kafin ta bud'e idonta,
tana bin d'akin da kallo, ganin gaba d'aya dangi a d'akin yasata ware idonta dake a kumbure,
Mamy, Daddy, Babanta, Mamanta da yayyanta, Umairah da Naufal, duk tabi kowa da kallo, a hankali ta fara kalle-kalle tana neman Neehal,
hannunsa ya d'ora saman nata, a fili ta sauke ajiyar zuciya, ganinshi kusa da ita,
ganin yanayinshi da kammaninshi, da yadda tashin hankali da damuwa suka fito k'arara a fuskarshi,
yasa Najwah girgiza kanta, tana k'ok'arin tuna abinda ya faru sannu a hankali komai ya dawo mata,
cikin rawar jiki takai hannunta ta shafo cikinta, jin wayam, yasata saurin mik'ewa zaune,
ta shiga fisge k'arin ruwan dake jikinta, tana fisge cannular jini ya soma zuba,
bata damu da jinin datake zubarwa, ta sanya duka hannayenta tana shafa cikinta cikin tsantsar firgici,
jin cikin wayam bakomai yasata fasa gigitaccen kuka da kusan gaba d'aya asibitin sai da ya amsa,
kanta Neehal ya tallafe had'i da d'ora goshinshi kan nata hawaye na gangarowa daga rinannun idanuwanshi,
wad'anda tuni suka canja kala, dakyar, ya iya motsa lips d'inshi yace " shhhhhh, cikin matsanacin kuka ta soma cewa,
" wayyo Allah na shiga uku na rasa ciki na wanda nayi shekara da shekaru ina faman nema,
cike da tsantsar tausayi Mamy ta isa gareta ta sanya hannu ta d'ago ta, ta zaunar da ita ta shiga rarrashinta,
" wai meye asalin abinda ya faru...!?
Cewar Baban Najwah, idon Neehal cike tab da hawaye ya zayyane musu duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
Baban Najwah da Mamanta suka d'auki salati, Baban ya rufe ta da fad'a kamar zai dake ta Daddy da Mamy na bashi hak'uri,
sai da yayi me isarshi sannan ya kalli Mamanta da yayyanta yace " muje Allah ne da kanshi yayi maganin shegiya,
yayi maganar yana ficewa, matsowa kusa da ita Mamanta tayi a hasale tace " maganinki kenan idan ana baki shawara ana fad'a miki gaskiya,
sai ki rink'a ganin kamar ke kika iya ke kike kan dai-dai, Allah ya sani tun kina yarinya nake fama dake kan wannan bak'in halin naki,
nayi iya yina, na baki shawara nayi miki fad'a da nasiha amma kika k'i ji, gashi nan kin kai kanki kin baro,
kinja an cire miki mahaifa a banza akan bak'in kishinki....! hannu biyu Najwah ta d'ora aka ta kurma uban ihuuuu tana fisge-fisge, tamkar zararriya,
ta shak'i wuyan Neehal tace " da gaske an cire min mahaifa...!?
Kanshi ya sunkuyar k'asa hawayen dayake dannewa suka fara gangarowa, k'ara k'arfin shak'ar datayi mishi tayi,
cikin kuwwa da d'aga murya tace " Neehal da gaske an cire min mahaifa...!?
Kanshi k'asa ya d'aga mata kai alamar eh, k'asa ta sulale sumammiya,
cikin b'acin rai Mamy ta kalli Maman Najwah tace " yanzu sabo da Allah abinda kika yi kin kyauta...!?
Maman Najwah tace " abinda nayi ko kuma abinda tayiwa kanta?
"Duk abinda ya same ta ita ta jawowa kanta, ina ruwan wani ita tayi asara, kuma wallahi sai Neehal ya k'ara aure,
tana kaiwa nan tayi ficewarta 'ya'yanta suka rufa mata baya, girgiza Najwah Neehal yake yi yana kiran sunanta amma a banza,
da sauri Daddy ya fita ya kira Doctor, duk abinda ya kamata anyi mata bata fard'o ba, wasa-wasa har tsayin kwana biyar Najwah bata farfad'o ba, hankalin kowa yayi masifar tashi,
uwa uba Neehal ba'a magana dan yafi kowa shiga tension babu abinda yake iya ci,
ko ruwan tea sai Mamy tayi da gaske kafin yasha ya rame ya koje,
yana zaune gefenta ya kafe ta da ido hancinta manne da bututun iska (Oxygen) hannunshi cikin nata ya soma gyangyad'i,
dan rabonshi da bacci harya manta, jin yatsanta ya motsa yasashi saurin bud'e idonshi, ya zuba mata,
sai da akayi 3 minutes kafin ta kuma motsi, da sauri Neehal ya soma kira sunanta,
motsawa ta k'ara yi tana k'ok'arin d'aga hannunta, fita Neehal yayi da gudu ya kira Doctor,
a k'alla Doctor ya d'auki awa d'aya akanta kafin numfashinta ya dai-daita, aka cire mata oxygen, Doctor ya juya ya kalli Neehal da Mamy yace " daga yanzu tana iya farfawa a kowanne lokac.....,
sautin tarin Najwah ne ya katse Doctor, yayi saurin kallanta, a hankali ta bud'e idonta,
Doctor yayi murmushi had'e da cewa " Alhamdulillah ta farka, jikin Neehal na rawa ya rungume ta tsam a jikinshi,
cikin sanyin jiki ta zame jikinta daga nashi ta kalleshi ido cikin ido muryarta bata fita sosai tace " da gaske an cire min mahaifa Neehal...?
Cikin sanyin jiki yace " kiyi hak'uri Doctor yace dole sai an cire in ba haka ba ana iya rasa ki,
" k'ululun bak'in ciki ta had'eye cikin takaici tana hawaye tace " meyasa baka bari na mutu ba...!?
" Na gwammaci mutuwa ta akan cigaba da rayuwa babu haihu, shikenan bazan ga d'an ciki na ba?
"Wallahi rayuwata bata da wani amfani matuk'ar bazan haihu ba, nasan mutuwa zanyi,
tunda nasan kai bazaka zauna dani bana haihuwa ba, bazaka yiwa kanka illa ba, bazaka yiwa kanka sakiyar da ba ruwa ba,
nasan dole kayi aure, dole sai su Mamy sun saka ka ka k'ara aure,
dole kayi min.... kasa fad'ar kalmar kishiyar tayi, ta runtse idonta da k'arfi had'i da fashewa da kuka tace " shikenan na zama juya,
bazan tab'a haihuwa ba, ta k'ara rushewa da matsanacin kuka,
" kiyi hak'uri haka Allah ya tsara mana rayuwarmu, Allah ya k'addara bazamu tab'a haihuwa ba,
duk abinda kika gani muk'addari ne daga Allah, duk abinda kika ga Allah yayi akwai nufar yinshi dan Allah baya tab'a yin abu babu dalili,
baki sani ba watak'ila haihuwar ta zame nama bala'i, ko abinda zamu haifa ya zamewa duniya fitina,
muji dama bamu haihun ba, dan haka idan Allah ya hanaka koya baka kamata yayi kayi godiya wata k'ila hanakan da yayi shine mafi a'ala a gareka,
wata k'ila hakan shine mafi alkhairi da samun kwanciyar hankalinka,
ajiyar zuciya ta sauke dan ta d'anji sa'ida tana cigaba da kukan tace " toya alk'awarin mu yana nan har yanzu?
Murmushi yayi had'i da d'aga mata kanshi alamar eh, tace " ka tabbatar bazaka tab'a yi min kishiya ba har abada?
Kafin ya bata amsa ta cigaba da cewa " dan Allah ka tausaya min kar abin yayi min yawa,
kada kayi min kishiya, kada ka sab'a alk'awarinmu yanzu dan kaga bazan haihu ba,
hakanne zaisa na manta da abinda ya same ni, na manta da batun rashin haihuwa matuk'ar zaka zauna dani ni kad'ai bazaka tab'a yi min kishiya ba,
ta k'arashe maganar hawaye na gangaro mata, hannu ya sanya yana goge mata hawayen,
yace " ni bak'in ciki na d'aya da kike zubar min da hawayenki, ki daina kuka please indai kishiya ce bake ba ita har abada,
murmushin jin dad'i tayi had'i da rungumeshi, duk abinda suke akan idon Mamy da Daddy,
Mamy tayi murmushi had'i da cewa " kuna ja da hukuncin Allah, sai da Najwah ta k'ara wata d'aya a asibiti sannan aka sallame ta,
har aka sallame ta ko sau d'aya babu wanda ya dawo cikin 'yan gidansu, iyayen sunk'i zuwa sun kuma hana 'yan uwanta zuwa,
ranar da aka sallameta Daddy ya zaunar dasu yayi musu nasiha mai ratsa jiki da jijiya, Mamy ma tayi musu akan yarda da k'addara,
suka hak'ura suka koma rayuwarsu normal kamar baya, sai dai duk lokacin data kalli cikin Umairah ko mace me ciki sai ta ci uban kuka,
bayan watanni uku da sallamo Najwah Umairah ta haifi 'yarta mace mai kama da Nail sak,
aka saka mata sunan mahaifiyarta, ana kiranta da LINAH,
ranar da Umairah ta haihu kwana tayi tana kuka Neehal yana rarrashi,
da aka sanar da Neelah haihuwar cewa tayi sai tazo taga Baby sai da Naufal ya hana ta dan a lokacin suna gaf da fara exam,
Najwah da Neehal suka tattara gaba d'aya hankalinsu kansu Nailah suka d'auki son duniya suka d'ora musu,
suna jin su tamkar 'ya'yan cikinsu, babu yadda basu yi Mamy da Daddy su barsu wajensu ba amma suka hana,
ko d'aya daga cikinsu ma hana su Mamy tayi tace babu wanda zai raba mata kansu, dole saboda yaran suka dawo
part d'in Neehal dake gidan suka rungumi yaran hannun bibbiyu,
komai na yaran ya dawo hannunsu dai-dai da bacci idan zasu yi sai sun saka yaran tsakiya,
duk da har lokacin basu san iyayensu ba, basu tab'a ganin uwarsu ko ubansu ba.
BAYAN SHEKARA HUD'U
Sannu bata hana zuwa sai dai a dad'e ba'aje ba, cikin ikon Allah Neelah ta kammala karatunta cike da tarin nasarori,
cikin shekarun haihuwar Umairah biyu bayan Linah yanzu tana da yara uku biyu mata d'aya namiji me sunan Daddy ana kiranshi Nur,
sai mai sunan Umman Umairah ana kiranta da Khairi, duk shekara Neelah ke zuwa hutu amma bata tab'a had'uwa da Neehal ba,
duk lokacin da zata zo hutun Allah yana kawo akasin da Neehal baya nan yayi tafiya,
Neelah ta gaji da jin labarin Uncle da Aunty wajen yaran duk sanda zasu yi waya sai sun bata labarin Najwah da Neehal.
Yau kowa ka gani a gidan yana cikin farin ciki kasancewar a ranar ne Neelah zata dawo,
duk sun had'u a gidan Mamy, Umairah da yaranta da Naufal, Nauman, Nailah, Nail da Neelmah zaune a Airport reception suna jiran k'arasowar Neelah,
sanya take da doguwar riga mai kwalliyar duwatsu, (abaya) coffee color tayi rolling da mayafin abayar,
idonta manne da round glass kalar abayar jikinta, k'uruciya da zallar kyanta sun fita,
tayi masifar kyau, tamkar aljanna idan ka ganta sai ka rantse balarabiya ce,
tana janye da trolley d'inta, " masha Allah!, tsarki ya tabbata ga mak'agin halittar nan,
Nauman ya furta muryarshi can k'asan mak'ogwaro, "hey! you! tace tana murmushi cikin zazzak'ar muryarta,
ido Nauman ya lumshe tare da cewa " Allah yayi halitta a wajen nan, cikin farin ciki Umairah da yaranta dasu Nailah suka fad'a jikinta,
ta rungume su tana dariya cikin shauk'i da missing d'insu, gyaran murya Naufal yayi ya d'an b'ata face yace " mu dama an saba mayar damu saniyar ware,
Nauman yace " rabu da ita duk sanda muka zo taryarta ta saba nuna mana wariya,
" ayya sorry Hamma am, ta fad'a tana sakin su Umairah, ta rungume Naufal dan ita tana d'aukarshi ne a matsayin yayanta uwa d'aya uba kamar su Suhairah, dan haka bata jin komai danta yi hugging d'inshi,
hannu ya sanya yana shafa hanya yace " Doctor Sister am Spine Doctor,
k'anwata ta zama babbar likita yanzu, kanta dake kan k'irjinshi ta d'ago tace " da taimakonka ba,
Nauman ya kwab'e fuska cike da shagwab'a yace " saura ni hug d'in, yayi maganar yana wara hannuwanshi,
d'an duka ta kai mishi a k'irjinshi tace " ank'i d'in, duk suka saka dariya,
Najwah na zaune a parlor tana jiran k'arasowar su dukta k'agara taga Neelah Momyn su Nail, dan basu tab'a had'uwa ba,
saboda ta ganta tak'i bin Neehal India meeting akan company da Daddy zai bud'e acan, tace ta biyoshi daga baya,
tana zaune Nauman ya shigo yana janye da trolley yace " Mamy ga 'yarki nan ta dawo,
saurin mik'ewa Najwah tayi ta zubawa k'ofar da Neelah zata shigo ido,
ras! gaban Najwah yayi muguwar fad'uwa ganin kyau da k'uruciyar Neelah,
duk da tasan dole zata kasance mai kyau musamman idan akaga kyan yaranta,
ansan dole mahaifiyarsu ta kasance kyakkyawar, amma bata zaci takai haka kyau had'uwa, wayewa da k'uruciya ba,
dan kallo d'aya zakayiwa Najwah kaga wayewa, had'uwa, aji, gayu da ilimi, take taji bata san Neelah,
haka nan taji Neelah batayi mata ba, k'i da k'iyayyarta suka d'arsu cikin ranta, kallan Mamy dake rungume da Neelah cike da tsantsar farin ciki tayi,
" wannan ce Mamansu Nail..!?
Najwah ta tambaya cike da damuwar da ita kanta bata san tameye ba,
bakin Mamy a washe tace " eh! itace baku tab'a had'uwa ba ko?
Murmushin yak'e Najwah tayi batare data ce komai ba, Neelmah yace " Mom ga Auntyn mu da muke baki labari,
fuskar Neelah d'auke da kyakkyawan murmushi ta mik'awa Najwah hannu tace " sannu Auntyn yara bamu tab'a ganin juna ba,
amma labarin juna ya iske mu, cikin sanyin jiki Najwah ta mik'ewa Neelah hannu, tana murmushin yak'e idonta kan Neelah,
dan harga Allah kyan Neelah tsoro yake bata, ga kalar kwayar idonta abun tsoro kamar na maciji,
kafard'arta Nauman ya dafa yana kallan Najwah yace " she's my wife to be, guntun murmushi tayi mishi had'i da cewa " wish you all the best,
bedroom Neelah ta shiga tayi wanka ta sanya riga da siket na atamfa,
d'ikin yayi d'as a jikinta shape da k'irar jikinta ta fito, hip da mazaunanta tamkar d'ora mata su akayi,
cikin takunta mai kamar tana jin tausayin k'asa ta fita parlor, " ya salam Nauman yace yana dafe saitin zuciyarshi,
ido Najwah ta waro cike da mamakin kyan k'irar jikin Neelah, ita kanta mace saida taji wani iri inaga namiji,
lalle dole Nauman ya rud'e ya haukace a kanta dan samun mata irinsu a duniya za'a dad'e ana nema,
aiko dole tayi mugun takatsantsan akan mijinta, duk yadda zasu had'u ya ganta saita toshe,
dan duk namijin daya ga kyau da tsarin zubin halittar Neelah dole yaji wani abu, komai nata me kyau ne, dai-dai da farcenta yana da masifar kyau da burgewa,
skin d'inta sai shek'i take tana k'alli, ga komai nata tana yinshi ne cikin nutsuwa da aji, Najwah tayi maganar cikin ranta idonta kan Najwah,
watan Neelah d'aya da dawowa ta tafi Bauchi Houseman ship,
duk satin duniya Nauman a Bauchi yake yin weekend, sosai soyayya da shak'uwa mai mak'arfi ta shiga tsananin Nauman da Neelah,
duk wanda yasan Nauman yasan labarin Neelah, dan ba k'aramin so yake yi mata ba, yana mugun santa tamkar yadda yake son rai da rayuwarshi,
Neehal kam har k'osawa yake yi da labarin Pari, da sun had'u da Nauman bashi da wani labari sai nata,
idan a waya ne ma haka sai Neehal ya gaji ya kashe wayar, a kwana a tashi ba wuya a wajen Allah har Neelah ta kammala karatunta,
ta fito da first class, kasancewar masu irin karatunta basu da yawa a Nigeria d'ai-d'ai ku ne, yasa aka bata takardar aiki (offer) tare da gida a Lagos a unguwar Lekki, dayake a babban asibitin Lagos zatayi aikin,
da motar k'irar Prado 2020,
ta zama cikekkiyar likita tana da 22yrs yayinda yaranta keda 10yrs har sun shiga Jss1.
Tuni magabata suka shiga maganar auren Nauman da Neelah, aka tsayar da magana, Daddy yace a bari ranar birthday d'inshi sai a saka ranar bikin ayi shagali gaba d'aya kowa ya amince da haka,
dayake ranar birthday d'in Daddy d'aya da Nail, Nailah, Neelmah, da Linah yasa aka shirya babban shagali,
ga kuma saka ranar Neelah da Nauman, hall d'in gidan dayake matsayin nayin family meeting aka shirya,
yasha decoration, an k'awata wajen sosai da flowers, da fitilu, tsakiyar hall d'in round table ne aje d'auke da cakes kala-kala,
da candles da manyan gwalaben vine sosai aka kashe kud'i dan k'awata wajen,
Nailah, Linah da Khair kayansu iri d'aya, haka ma Neelmah, Nail da Nur, kayansu iri d'aya,
Najwah na sanye da doguwar riga blue black kalar kurta jikin Neehal (indian men dress), (suit, doguwa mai kawowa har gwiwa bakinta mai shape d'in triangle),
'yar cikin da wondon white color masu kamar yadi, kayan jikin Neehal iri d'aya dana Daddy da Naufal da Nauman sai dai bambamcin kala,
Neehal da Naufal sun suka Daddy da Mamy tsakiya, su Nail na gaba, Nauman na kusa da Neehal,
hasken wajen aka mayar mai d'an duhu (dumb light) aka karkata hasken ga bayan Neelah dake tsaye,
sanye da jar doguwar riga,
irin wacce indiyawa ko turawa ke sawa idan za'ayi party, ta saki gashin kanta ya sauka gadon bayanta,
takalmin k'arfarta high hill,
gaba d'aya hall d'in ya fara amsa kuwar zazzak'ar muryar Neelah na cewa " Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday Daddy & my dears, happy birthday to you,,
gaba d'aya aka soma tafi, a kunne Nauman ya rad'awa Neehal she's my wife to be, itace my Pari, bayanta Neehal ya k'urawa ido,
ganin irin kallan da Neehal keyiwa bayan Neelah yasa Najwah matse hannunshi dake cikin nata,
muryarta k'asa-k'asa yadda ba wanda zaiji abinda take fad'a tace " inaga so kake mu yadda hali anan ma, a b'ata ranar yau,
murmushi yayi had'i da d'auke kanshi daga kallan Neelah, ya sunkuyar da kanshi k'asa,
dai-dai lokacin Neelah ya juyo, ta fara takawa d'as-d'as, take zuciyar Neehal ta soma bugawa da tsananin k'arfi,
k'irjinshi ya soma yin sama da k'asa yana bugawa fat fat, duk tak'un da Neelah tayi yana tafiya da bugun zuciyar Neehal,
yana san ya d'ago ya kalle ta, amma tsoran kada hakan ya haifar da matsala ya sashi daurewa,
direct wajen Nauman ta nufa tana sakar mishi k'ayataccen murmushi, shima fuskarshi d'auke da murmushin,
" kayi kyau, ta rad'a mishi cikin wata irin murya, murmushi jin dad'i yayi yace " ke ai kinfi kyau kyau dear, shi kanshi kyau guduwa yake idan kina waje,
dariya ta d'anyi tace " ka fiya tsokana, kafad'ar Neehal ya dafa yace " let me introduce you to him,
baku tab'a had'uwa ba, he's my best friend, kana ya mayar da kallanshi ga Neehal yace " Aboki ga my Pari,
d'ago kanshi yayi fuskarshi d'auke da murmushi, karaf idonsu suka sark'e cikin na juna, a kid'ime cikin tashin hankali,
cike da zallar tsoro da firgici Neelah ta saki gigitacciyar k'ara data jawo hankalin kowa dake wajen,
tamkar mahaukaciya ta soma ja baya tana nuna Neehal, ta kasa furta koda kalma d'aya labb'anta sai rawa suke tamkar me jin sanyi,
takalmin k'afarta ya gurd'e ta tayi baya zata kifa, Nauman yayi saurin tareta, Naufal da Umairah , Mamy da Daddy suka yo kanta da gudu,
gaba d'aya wajen kallo ya koma kanta, tamkar zararriya ta shiga nuna Neehal tana ja baya daga zaunen, tana cewa " shine...! shine....! Mamy, Daddy shine...., Aunty Umairah kinganshi ya biyo ni..... d'if numfashinta ya d'auke ta fad'a jikin Naufal sumammiya..............!
PLEASE KADA KU MANTA DA SUBSCRIBE
MOMYN ZARAH 'YARBAIWA