29
***
*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE, DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI, TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
LITTATTAFAINA MASU ZUWA
_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_
2️⃣9️⃣
A razane Naufal ya sanya hannunshi biyu ya tallafe fuskarta had'i da kiran sunanta,
cak Nauman ya d'auketa ya fita daga hall d'in yana cewa " ruwa! ku bani ruwa jama'a ta suma,
jikin Daddy na rawa ya bud'e fridge ya d'auko robar ruwa ya b'alle ya zuba mata,
a fili ta sauke ajiyar zuciya had'i da fashewa da rikitaccen kuka batare data bud'e idonta ba,
jikin Mamy a sanyaye suka kalli juna ita da Daddy dan koda Neelah bata furta ba Mamy da Daddy sun fahimci komai,
Neehal na tsaye hannunshi sak'ale cikin na Najwah ya dake yadda kasan bai san abinda ke faruwa ba,
duk da kallo d'aya yayiwa Neelah ya gane ta, dan ko a gigin mutuwa ya ganta sayya gane ta,
deep down a matuk'ar tsorace yake, da mamakin daya cika mishi rai, yana yiwa kanshi tambayoyi da dama,
" shin Neelah ce Pari d'in Nauman?
"Tayaya akayi ta shigo birni ta waye haka?
" Ya akayi ta zama Doctor dan Nauman yasha fad'a mishi likita ce, tayaya duk hakan ta kasance?
Yayiwa kanshi tambayar yana gyara tsaiwarshi, kallan Neelah dake kwance yayi yana mamakin kyau da had'uwarta,
" yanzu wannan poor villager girl d'in ce ta zama tamkar hurul'in?
"Lalle kyau na k'auye sai dai rashin gyara da wayewa, ya fad'a cikin ranshi,
skin d'inta dake ta shek'i ya kalla ya tuna lokacin datake k'auye, ya kalli gashin kanta zuwa fuskarta,
mahaukaciyar fad'uwa gabanshi yayi ya tuna lokacin da yake amfani da ita, yadda take kuka yanzu sak a lokacin,
take komai ya dawo mishi ya rink'a ganin kamar a lokacin komai ke faruwa,
tsoro da fargabar da yake ciki suka tsananta, hankalinshi yayi masifar tashi, zuciyarshi ta shiga bugawa fat fat,
k'irjinshi ya soma yin sama da k'asa da tsananin sauri, idan aka yanka jikin Neehal a lokacin baza'a samu jini ba,
saboda tsagwaran masifar dayake ciki, amma dayake namijin duniya ne, baka isa ka gane halin dayake ciki ba,
dan binta yake da kallo tamkar yau ya fara ganinta, " wai meke faruwa ne?
Najwah ta fad'a tana kallan Neelah, bakinshi ya tab'e had'i da d'age gira d'aya yace " oho! ina zan sani,
" ka cuce ni! ka zalunce ni!, ashe dama kana raye amma baka tab'a waiwaya ta ba?
Tayi maganar cikin matsanancin kuka, cikin rashin fahimta Nauman da Naufal da Umairah suka kalli juna,
muryar Naufal na rawa yace " meke faruwa ne Neelah?
" Wannan shine MIJI NA, shine wanda Abpa na ya baku labari shine wanda aka AURA MIN 11yrs back,
tayi maganar tana nuna Neehal, " what?
Nauman da Naufal suka fad'a a tare suna mik'ewa tsaye, ido Najwah da Neehal suka had'a, bakin Najwah bud'e tace " me?
"Ke kina hauka ne?
"Kin san me kike fad'awa kuwa...?
Tayi maganar cike da izza, Umairah kam kasa furta kasa koda kalma d'aya tayi,
Daddy da Mamy suka zubawa Neehal ido, " wallahil shine mijina ko a gigin mutuwa na ganshi zan gane shi,
dan bazan tab'a manta fuskar bak'in kumurcin daya sare ni ba, wanda har yanzu ina d'auke da dafinshi,
a haukace Najwah tayo kan Neelah tamkar zata yagi naman jikinta, saurin rik'eta Neehal yayi,
ta shiga fizge-fisge tana k'ok'arin kwacewa, takawa Nauman yayi gaban Neehal had'i da nuna mishi yatsa yace,
" kayiwa wannan mahaukaciyar matar taka magana ta shiga hankalinta, wallahi muddin ta sake hannunta ya tab'a jikin Neelah sai nayi shari'a da duk uban daya d'aure mata gindi koda hakan yana nufin kawo k'arshen alak'ar dake tsakanina dakai,
yayi maganar yana kallan Neehal ido cikin ido, Neehal bayyi magana ba yaja hannun Najwah suka bar wajen,
gaban Naufal da Umairah dake tsaye tamkar an dasa su Neelah taje,
cikin matsanancin kuka tace " wallahi Allah ba k'arya nake yi ba, shine babansu Nail, he's their biological father Allah ba k'arya nake ba,
tamkar mahaukaciya ta juya gasu Daddy tace " Daddy Mamy Allah shine mahaifinsu Nailah ban tab'a sanin wani d'a namiji ba sai shi,
ganin yadda ta firgice ta zama tamkar mahaukaciya yasa Mamy ta rungumo ta jikinta,
ta kwantar da kanta saman k'irjinta tana shafa kanta muryar Mamy na rawa tace,
" mun yarda dake Neelah, wallahi tun ranar da kika haihu muka san yaran nan jininmu ne, mu muka haifi Neehal munfi kowa saninshi,
duk da yayi k'ok'arin dakewa wallahi yana cikin tashin hankali, bamu yi magana bane dan muna san muga me zayyi,
wacce k'aryar zayyi, da wanne salan rainin wayon zai zo,
cikin sanyin jiki Daddy ya d'ora hannunshi saman kanta yace " ni kunyarki ma nake ji Neelah,
wallahi kunyar had'a ido dake nayi, kunyar yi miki magana nake yi, na rasa ta inda zan fara, na rasa ta inda zan b'ullowa al'amarin,
Neehal yayi matuk'ar bani mamaki, amma bakomai gobe in sha Allah za'ayi ta tak'are,
Mamy ta kalli Umairah tace " zo ki kaita bedroom d'inta, saurin amsarta Nauman yayi ya nufi bedroom d'in da ita,
Naufal da Umairah suka bisu, cikin sanyin jiki ya zaunar da ita kan gado, ya zauna a k'asa a gabanta,
hannunshi cikin nata, Naufal da Umairah suka zauna saman gadon suka sanya ta tsakiya,
Naufal ya sanya hannunshi yana goge mata hawaye had'i da girgiza mata kanshi,
a hankali Umairah ta sauke ajiyar zuciya ta rafta tagumi hannu bibbiyu, tace " amma fa abun da mamaki ace Neehal ne ya aikata irin wannan aikin,
Nauman yace " ni tun a bayan naso na fuskanci wani abu, saboda lokacin daya dawo daga baukar k'asa yanayinshi yayi masifar canjawa,
sannan sau uku yana k'ok'arin fad'amin wata magana sayya share a lokacin har tambayarshi nayi yace min sirrin ciki sai hanji,
ashe abinda yake nufi kenan, haka lokacin daya dawo Nigeria daga Dubai,
danake bashi labarin Neelah bakiga tashin hankalin daya shiga ba, ya tsare ni yace sai na sanar dashi sunanta,
Naufal yace " Umairah kin tuna lokacin da muke cin abinci a dinning Daddy ya tambaye ki ina zaki wannan karon kika ce Taraba State k'aramar hukumar hard'o-koa'la?
"Eh na tuna a lokacin har kwarewa yayi, cikin muryar kuka Neelah tace " wannan dalilin ne yasa lokacin da muka ganka ni da Abpa muka nuna reaction,
Nauman yace " wayya abun ya kasance ne,
Neelah ta kwashe komai ta k'ara sanar dasu har fyad'an da yayi mata,
Nauman ya sauke numfashi yace " lalle mutum sai Allah wai ace duk yadda muke da Neehal bai tab'a sanar komai akan alak'ar ku ba, haka sukayi ta jajanta abun har aka kira sallah, a b'angaren Daddy da Mamy ma hakance ta kasance,
Neehal na zaune gefen bed ya rafka uban tagumi hannu bibbiyu, yayinda Najwah keta safa da marwa tana furzar da iska daga bakinta,
tana ruwan bala'i, "shegiya me kama da aljanna, an fad'a mata miji na mutumin banza ne?
"Ko an fad'a mata yana da arahar da zai iya auren kowacce kucakar mace?
"Shiyasa tunda na ganta naji na tsane ta, wallahi saina kashe ta, nice ajalinta, daga kan mijina ta daina ganin mazan mutane tace mijinta ne,
sai nayi maganin haukanta, dariya Najwah ta sanya harda dafe ciki tace " wonder shall never end,
inda ranka kasha kallo, zaka ga abin mamaki dayawa a duniya, kaji fa Dear bama ta sanka ba, ba ma saurayinta, bama kun tab'a yin soyayya ba, a'a saboda tsabar zak'ewa wai kai ne mijinta...!?
Neehal kam yau ba baka ba kunne, bai ma san wainar da take toyawa ba,
danya dad'e da barin duniyarmu, yana can duniyar tunani, yadda Neehal yaga rana haka yaga dare,
yana cikin tashin hankali da firgici da wayarshi tayi ruri sai gabanshi ya fad'i dan a zatonshi Daddy ne,
ranar Neehal ko masallaci bai fita ba a bedroom yayi sallarshi, hakan ya k'ara tabbatarwa Daddy da rashin gaskiyar Neehal,
k'arfe takwas na safe Daddy ya kira Neehal ya sanar dashi yazo babban falon gidan, jiki ba kwari ya amsa da to,
kowa ya hallara a parlor'n Daddy ya kalli Nauman yace " bud'e mana taro da addu'a,
bayan an shafa addu'a Daddy ya kalli Neelah dake zaune kusa da Nauman ya kira sunanta,
" Neelah, cikin da shashshiyar murya ta amsa " na'am, " kiji tsoran Allah ki sanar damu gaskiyar abinda ya faru tsananin ki da Neehal, shin meya faru shekaru goma sha d'aya baya?
Dammm! gaban Neehal yayi muguwar fad'uwa, Najwah aka tab'e baki had'i da cewa " uhmmmm tana wullawa Neelah kallan banza,
kan Neelah a k'asa cikin muryar kuka ta kuma fad'awa su Daddy komai, Daddy ya mayar da kallanshi ga Neehal yace " kaji abinda tace?
Ga mamakin kowa sai akaga Neehal yayi guntun murmushi had'i da kallan Neelah yace " ke kalle ni dakyau ni kika sani ko me kama dani?
Cak Neelah ta tsaida kukanta had'i sa kafe shi da ido, saurin kawar da idonshi yayi daga gareta ya mayar ga Daddy yace " Daddy ina kuka samo wannan mahaukaciyar?
"Dan gaskiya da alama ba lafiya take ba kanta da motsi, in ba mahaulaciya ba ina ta sanni har na aure ta?
"Wallahi ban santa ba Daddy, ban tab'a ganinta ba, kai ni a tsayin rayuwata ban tab'a ganin kome kama da itama ba balle na santa,
d'if kowa yayi cike da tsantsar mamakin Neehal, duk suka zuba mishi ido suna kallan tsagwaran rainin wayo,
a hasale Naufal yace " wallahi k'arya kake yi bak'in munafuki, annamimi, me zata amfana dashi idan tayi maka sharri?
"Meye ribarta idan tace kai mijinta?
Baki Neehal ya tab'e yace " kai kaga haka ita datayi min sharrin tasan meye ribarta,
" kaban mamaki Neehal, da duk abinda kayiwa yarinya k'arama bakinka bai mutu ba, baka tuba ba baka gane kayi kuskure ba, cewar Nauman yana huci,
" cool down guy, idonka ya rufe akanta ba lalle ne kaga laifinta ba,
" Umairah tace " Neehal kaji tsoran Allah meye ribar Neelah idan tayi maka k'age?
"May be dan kud'i tayi hakan ina ganinta a bata abinda take buk'ata ta tafi, kallanshi ya mayar ga Neelah yace " fad'i farashinki na biya....! tass tass! Mamy ta kifawa Neehal mari,
cikin b'acin rai, tace " wallahi k'arya kake yi, mu zaka rainawa hankali?
"Mu zaka mayar mutanen banza dan ubanka shege d'an iska marar mutunci?
"Me kake nufi da baka santa ba?
Muryarshi na rawa yace " ni fa ban santa ba, ban kuma tab'a ganinta ba, Mamy zatayi magana Daddy ya dakatar da ita,
ya mata umarnin ta dawo ta zauna, ba musu Mamy ta koma ta zauna,
gyaran murya Daddy yayi idonshi kan Neehal yace " kaji tsoran Allah ka tuna akwai mutuwa,
akwai kwanciyar kabari, akwai tsayewa gaban Allah, akwai hisabi, ka dubi girman Allah ka fad'i gaskiyar abinda ka sani, kai Neehal ya duk'ar k'asa,
gabanshi na muguwar fad'uwa tsoro da fargaba suka durarmishi,, ta wutsiyar ido ya saci kallan Najwah,
yaga ta zuba mishi ido, kallanshi ya mayar ga Mamy yaga shi take kallo, a hankali ya rink'a satar kallan kowa yaga idon kowa na ganshi,
banda Neelah data sunkuyar da kanta k'asa, ido ya rantse yana jinjina abinda zai fad'a, " muna jinka,
Daddy ya fad'a, "ni fa ban santa ba, Neehal ya kuma fad'a kanshi k'asa, Mamy zatayi magana Daddy yayi saurin d'aga mata hannu,
idonshi kan Neehal yace " kai da kanka da bakinka kace baka santa ba ko?
"Eh! ban tab'a ganinta ba, " ka tabbata baka tab'a ganinta ba?
Kanshi ya d'aga alamar eh, Daddy yace " ka kalle ta dai da kyau, Neehal ya kuma d'aga kai, " Daddy yace " zan kuma tambayarka a karo na k'arshe,
" Neehal kasan Neelah ko baka santa ba?
" Akwai wata alak'a a tsakaninku ko babu?
" Ban santa ba, babu kuma alak'ar komai a tsakaninmu, " Neehal kai da kanka da bakinka ka furta baka san Neelah, "eh! Daddy,
cikin takaici Daddy yace " wallahi tallahi tunda nake a duniya, ko a labari, k'issa da almara ban tab'a ganin bak'in munafuki annamimi irin Neehal ba,
kasan ina sane da ba'a Dubai kukayi karatu ba, ina kuma sane duk abinda ya faru?
Saurin d'ago kai Neehal yayi ya kalli Daddy, Daddy yace " eh! ina sane da abinda matarka tayi a Dubai aka kore ku kuka koma America, ko shima k'arya ne?
Kan Neehal k'asa yace " a'a, Daddy yace " tunda nake dakai na tab'a yi maka maganar kona nuna maka na sani?
"A'a Neehal ya kuma cewa, duk falon aka shiru babu abinda ke tashi sai sautin kukan Neelah,
cikin kuka Neelah tace " kaji tsoran Allah ka tuna in babu nan akwai lahira,
ka tuna duniya ba matabbata bac....., " dalla Malam rufewa mutane baki, shegiya annamimiya munafuka, ke kin isa ki zama matar Neehal, Najwah ta fad'a a hasale,
murmushin bak'in ciki Neelah tayi tace " ko kink'i ko kin so Neehal miji na ne kuma uban 'ya'y.....,
kukan kura Najwah tayi ta rarumi k'arfen labule tayi kan Neelah tana kuruwa,
" wallahi sai na kashe ki nice ajalinki, daga ke har wad'anda suka kawo ki, duk saina ga bayanku,
ni dama nasan ba asan zamanmu tare da Neehal shine aka fiddo sabon munafurci dan a shiga tsakanina dashi,
baya Naufal ya hankad'a Najwah yana huci ya nuna ta da yatsa yace " kul wallahi karki soma idan ba so kike mu aje tarihi ba,
d'ago Neelah Nauman yayi idonshi kan Neehal yace " baka ji abinda na fad'a maka jiya ba ko?
" Wallahi muddin hannun Najwah ya tab'a Neelah saina d'aure ta,
Mamy ta mik'e had'i da rik'e hannun Neelah ta kalli Neehal,
tace " kaje kai da Allah, in sha Allah sai Allah yayi mata sakayya,
ta inda baka tab'a tsammani ba, da yardar Allah sai ta rufa maka asiri tayi maka ranar da waccen lusarar matar taka bazata tab'a yi maka ba,
saika nemi taimakonta a lokacin da kud'i, ilimi gata da iyaye da dangi duk bazasuyi maka amfani ba,
in Allah yaso sai tayi maka abinda kai da kanka bazaka iyayiwa kanka ba,
sai ta zama jinka, ganinka, da gatanka sai ya zama da ita kake tak'ama, kallanta ta mayar ga Neelah ta sanya hannu tana share mata hawaye,
tace " kiyi hak'uri da sannu Allah zai saka miki, da izinin Allah sai kin rufa mishi asirin da wacce yayi miki dominta bazata yi mishi ba,
munafuki shege d'an iska marar mutunci, Mamy ta k'arashe maganar tana fashewa da kuka,
" karki yi mishi baki Taheerah ki barshi da Allah,
Daddy ya fad'a, zuciyarshi tana yi mishi zafin abinda Neehal yayi,
yasan kuma yayi hakan ne akan Najwah, " ka zuba ruwa a k'asa kasha hankalinka ya kwanta kasa mahaifiyarka kuka akan mace,
kai Neehal ya sunkuyar k'asa hawaye na gangaro mishi,
hannu Najwah ta d'ora aka tana ihuuuu " wayyo Allah na, na shiga uku dama nasan 'yan uwan Neehal ba k'aunata suke ba,
wayyo Allah na za'a rabani da miji na, wallahi baku isa ku raba ni dashi ba, duk abinda zakuyi sai dai kuyi ku gaji da tuggu da k'ullek'ullanku,
kallanta ta mayar ga Neelah tace duk akanki ake yi min haka ko?
"To wallahi sai na kashe ki, nice ajalinki tayi maganar tana nufar kitchen da gudu,
a haukace ta fito rik'e da wuk'a tayi kan Neelah gadan-gadan, saukar gigitattun marikan dataji a jere ne yasata tsayawa cak had'i da dafe kuncinta,
in slowly ta juya ganin Neehal yasa mamakinta k'aruwa, duk wajen babu wanda bayyi mamakin marin da Neehal yayiwa Najwah ba,
dan duk iskancan da take yi bai iyayi mata ko fad'a balle mari, wani lokacin ma ko b'acin ranshi bai iya nuna mata,
tana dafe da kuncinta ta nuna Neehal, kana ta nuna Neelah, ta kuma nuna kanta, muryarta na rawa tace " Neehal ni ka mara akanta?
"Yau ni Najwah ka mara akan wata mace?
Ta fad'a tana nuna Neelah, " tunda nake dakai baka tab'a saka hannu ka dungure min koda kaina bane sai yau akanta,
nasha yiwa mahaifiyarka abu, baka tab'a nuna min yatsa ba, nasha yiwa danginka da 'yan uwanka da kuke uwa d'aya uba d'aya abu baka tab'a nuna min yatsa ba,
nayiwa amininka rashin mutum baka yi min komai ba, nayiwa Basrah wanda sai da yaja aka kore mu daga makaranta,
amma ko fuskarka baka nuna min ba, nayi mana asarar gudan jinin mu baka yi min komai ba,
wanda daga k'arshe ma sai dai ka dawo kana rarrashi na, karo na farko dana nayi niyyar zan aiwatar da abu, ka hukunta ni tun kafin na aiwatar da abun,
" wallahi wallahi koda za'a kashe ni, sai na kashe ta tunda ka mare ni akanta,
tayi maganar tana k'ara damk'e wuk'ar hannunta, tana ja baya tana nufar Neelah, saurin shiga tsakiyarsu Neehal yayi yana rik'e Najwah yace " wai kina hauka ne?
"Eh! ina hauka Neehal, ta fad'a da k'arfi, "ina hauka akan sanka, dan haka matsa ka barni na rushe katangar dake neman shiga tsakaninmu,
dan wallahi sai kashe ta, " bazan matsaba Najwah, akan me zaki kashe ta?
"Me tayi miki?
"Me tayi min?
"Au tambayar abinda tayi min ma kake yi?
" Ko ka matsa na kashe ta kona kashe kaina, cikin biyu sai ka zab'i ni ko ita?
" Nace miki bazan matsa ba..! kafin ya k'arasa ta cukawa cikinta wuk'ar,
duk wajen babu wanda yayi tunanin haukan Najwah yakai haka,
ido kowa ya zaro cikin tsoro da mamaki, k'ara Neelah ta saki tana k'ank'ame Nauman,
ganin tana niyyar fad'uwa yasa Nauman d'aukarta cak ya kaita bedroom d'inta ya kwantar saman bed,
cikin tashin hankali Neehal ya soma jijjaga Najwah yana kiran sunanta, dakyar ta bud'e idonta,
muryarta na fita dakyar tace " na gwammaci mutuwata akan rayuwa da kishiya,
bazan tab'a iya sharing d'inka da wata mace ba Neehal, dan ni kad'ai aka halicceka, please karka yi min kishiy...!
d'if numfashinta ya d'auke babu wanda yayi k'ok'arin taimakawa Najwah, da gudu ya fita yana d'auke da ita,
ya sanya ta cikin mota yayi hospital, likitoci sun dad'e akanta kafin su samu masarar ceto rayuwarta,
sai dai bata fargad'o ba, fuskarta d'auke da oxygen, ya saka ta gata ya rafka tagumi,
abin daniya sun had'u suyi mishi yawa ya rasa inda sai saka ranshi yaji dad'i,
Doctor yayiwa magana aka bashi nurses biyu da zasu rink'a jinyar Najwah a asibitin danya san Mamy, da Umairah ba zuwa zasu yi ba,
haka ma Maman Najwah, muddin taji abinda ya faru sai buzun Najwah,
sosai Mamy da Daddy, Naufal, Nauman da Umairah suka rarrashi Neelah, sukayi ta bata hak'uri,
Nauman kam kamar zayyi hauka dan ji yayi ya tsani Neehal kamar yadda ya tsani mutuwarshi,
wajen sha d'aya na dare Nauman ya shigo gidan, abin takaici babu wanda ya tambayeshi ya Najwah,
ko kallan arziki babu wanda yayi mishi, ya wuce part d'inshi ya zube saman bed had'i dayin pillow da hannunshi,
dakyar Nauman ya matsawa Neelah ta d'an ci abinci, har k'arfe d'aya na dare yana gidan bai tafi ba,
ganin bashi da niyyar tafiya yasa Neelah yin baccin k'arya dan ya tafi, k'arfe biyu saura Neehal yaji k'arar mota,
ta window ya lek'a danyaga kowaye, ganin Neehal yasa shi jan tsoki, haka nan yaji yana jin haushin Nauman d'in,
wanka yayi ya sanya 3 quarter da white T-shirt, ya fito cikin sand'a ya nufi bedroom d'inta,
zaune ya iske ta k'asan tiles tana rusgar kuka kamar ranta zai fita, gashin kanta duk a barbaje,
a hasale ya isa gareta ya sanya hannu damk'i gashin kanta da k'arfi, ya had'a kanta da bango ji kake k'um,
idanuwanshi waje tamkar zasu fad'o k'asa ya shak'e mata wuya yace " dan ubanki uban wa ya kawo ki gidanmu...?
"Uban me kika zo yi?
"Zuwa kika yi k....! k'arar tab'a k'ofar da aka yi yasa shi kallan k'ofar had'i da d'ora hannunshi saman lips yace "shhhhhh,
" kinyi bacci ne Neelah?
Yaji muryar Mamy na fad'a, sakinta yayi yana yi mata alama sa kartayi magana, yana sakinta ta soma tari saboda wahalar shak'ar dayayi mata,
" kina lafiya Neelah?
"Mamy Neehal ne, ta fad'a da sauri kamar an fisgi maganar daga bakinta,
a hasale Mamy tace " bud'e k'ofar dan ubanka, sai da ya watsawa Neelah kallan banza kana ya bud'e k'ofar,
da sauri Neelah ta koma bayan Mamy tana kuka, ta rirrik'e Mamy gam, " uban me ya kawo ka d'akin nan bak'in munafuki?
"Am... am.... am, nuna shi Mamy tayi da yatsa tace " karka kuma, zayyi magana tace " kaji dai na gaya maka, taja hannun Neelah suka fice daga d'akin,
washe gari da yamma Neelah na zaune saman sallaya tana jan carbi wayarta ta soma rori, kamar ta share sai kuma ta jawo wayar,
saurin picking tayi ganin daga asibitin Lagos ake kiranta, muryar Doctor na rawa yace " Doctor NM kizo hospital da gaggawa,
akwai mara lafiya dayake buk'atar taimakon gaggawa, " am sorry bana jin dad'i bazan iya zuwa,
" no! Doctor karki ce haka ki taimaka kizo karkiyi abinda zai kasance har abada kina danasani da nadama,
mutumin yana buk'atar taimakon gaggawa yana iya mutuwa a koyaushe, ki taimaka kizo ki ceci rayuwarshi,
wannan ne aikinki na farko he's the first person da zaki fara yiwa operation please ki biyo jirgi kizo bamu da time,
yana gama fad'a ya kashe wayar, jikinta na b'ari ta fita parlor ta sanar da Daddy da Mamy,
Umairah tace " aikin ki ne farko ya kamata ace kiyi shi kina ciki nutsuwa amma yanzu kina cikin damuwa tayaya zaki iyayin aikin?
Mamy tace " a'a taje bakomai akwai Allah, da yardar Allah babu abinda zai faru sai alkhairi,
Ubangiji yafimu sanin tana cikin damuwar ai yasa hakan ta kasance, dan haka karta k'i zuwa ta ceci rayuwar wanda Allah ya talak'anta rayuwarshi a hannunta,
bamu san dalilin da yasa Allah yayi hakan ba may be hakan yana daga cikin mafita daga matsalarta,
Allah baya tab'a yin abu babu dalili,, Daddy yayi murmushi had'i da dafa kanta,
yace " karki ji tsoron komai, karki bari damuwarki da matsalarki ta hanaki aiwatar da aikinki na ceton rayuwar al'umma,
dole ke kad'aice zaki iya cetar rayuwarshi tunda duk Lagos ke kad'ai ce spine Doctor,
idan ba ke ba babu wanda zayyi a hospital d'in, kije kiyi aikinki kinji Daughter, kanta ta d'aga cikin sanyi tace " to! Daddy nagode da kuka k'ara min gwarin gwiwa,
" Allah yayi miki albarka, Ubangiji ya tsare min ke ya baki nasara da sa'a suka amsa da amin,
k'arfe 6 a garin Lagos tayiwa Neelah, kasancewar wannan ne karo na farko da zata fara operation,
yasa gabanta yake fad'uwa yana dukan uku-uku, tana shiga asibitin ta iske an gama shirya komai ita kawai ake jira,
a gaggauce ta shirya ta shiga theater room, while gabanta na tsananta fad'uwa,
cikin ranta ta fara addu'o'i tana takawa, idonta runtse, " bismillah, wani Doctor yace mata yana mik'a mata file,
a hankali ta bud'e idonta ta karb'i file d'in tana dubawa, ganin babu sunan marar lafiyar yasata cewa " sunanshi fa?
"Babu wanda ya sanshi hatsari yayi a hanyar airport da aka duba motar ba'a samu komai nashi ba,
har wayoyinshi ma babu kin san yanzu da anyi had'ari mutane basa ta komai sai ta dukiya, ko cetan rayuwar mutum ba'ayi,
" kuma ba'a samu kowa nashi ba?
" Ko wanda ya sanshi ma ba'a samu ba, police ne sukayi duk abinda ya kamata,
bata k'ara magana ba tayi signing a file d'in ta aje gefe ta nufi gadon da mara lafiyar ke kwance,
ba zato ba tsammani idonta ya sauka akan NEEHAL BILAL LAGOSA!.................
KADA KU MANTA DA SUBSCRIBE PLEASE
MAMYN ZARAH 'YARBAIWA