30
***
*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE, DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI, TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
LITTATTAFAINA MASU ZUWA
_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_
3️⃣0️⃣
Cikin tashin hankali, kid'ima da matsananciyar razana taja baya tana nuna shi da hannunta,
ta kasa furta koda kalma d'aya sai bakinta dake rawa hak'oranta na kaf kaf,
duk ilahirin jikinta na tsuma kamar mazari,, nuna Neehal ta shiga yi da hannunta ta kasa magana,
kanta ta shiga girgizawa tana cewa " no! no! bashi bane, cikin mamaki Doctor ya kalle ta yace " Doctor NM kin san shine?
"Miji na ne! ta fad'a batare data sani ba,
a kid'ime ta nufi jakarta tayi zaman dirshan a k'asa,
ta zazzage jakar, hannunta na rawa ta d'auki wayarta, tayi dialing number Mamy,
Mamy nayin picking Neelah tace " Mamy ina Neehal?
"D'azu da safe naji Daddy yana sanar dashi zasuyi bak'in turawa daga Landon ya tafi Lagos ya tare su,
naji Neehal d'in yana waya Airport a aje mishi ticket d'in Lagos, amma dai ban sani ba koya tafi,
bata tsaya bawa Mamy amsa ba ta kashe wayar, had'i da fashewa da gigitaccen kuka,
Doctor da nurses nata bata hak'uri amma bata kulasu ba, sai da tayi me isarta sannan ta mik'e,
k'ara shiryawa tayi tsaf cikin shigar operation sannan tace " Bismillah mu fara aikin mu,
jiki a sanyaye Doctor ya kalle ta yace " zaki iya kuwa Neelah naga kamar bakya cikin nutsawarki?
"Bakomai! tace a tak'aice, sai da sukayi awa uku cur sannan suka kammala yi mishi aikin,
ta kalli Doctor tace " ka k'ara yi mishi gwaje-gwajen, a kaishi resting room,
batare data jira abinda Doctor zai fad'a ba ta fice, gidan da aka bata a unguwar Lekki ta nufa,
babu abinda babu a gidan dai-dai da cokali akwai a gidan, 3 bedroom plate ne, da babban parlor & kitchen da dinning area,
gaba d'aya bedrooms d'in da furnitures, haka ma parlor yasha Turkish sofa, d'aya daga cikin bedroom d'in ta shiga,
ta fad'a saman bed ta saki kuka mai cin rai, wanda idan za'a kashe ta bata san dalilin yin kukan ba,
a hankali ta mik'e ta shiga bathroom tayi wanka ta d'auko alwala, sallah ta fara gabatarwa, sannan ta shirya kayanta cikin wardrobe,
ruwan tea kawai tasha ta d'auki key d'in motarta ta fice, sai da Neehal yayi kwana biyar a asibiti sannan ya farfad'o,
tunanin shi komai normal sai dai ba um bare um'um baya iya magana, baya iya tafiya,
ko zama bai iyawa, Neelah ce komai nashi itake yi mishi komai, tun daga kan wanka, wanki saka pampers, ci da sha, ita ke mishi komai na rayuwa,
sai da Neehal yayi wata uku a hospital sannan aka sallame su, a lokacin ya fara zama akan walk chair,
gidanta ta kaishi ta cigaba da kula dashi, a b'angaren Najwah ko yau wata uku kenan har lokacin tana asibiti tana fama da jinya,
yayinda hankali ya tashi akayi ta neman Neehal amma ko d'oriyarshi basu samu ba, anyi cikiya a gidajen TV da redio da kafafen sada zumunta amma shiru,
dole suka dangana aka sanya malamai suna rok'on Allah ya bayyanashi,
duk lokacin da Mamy tayiwa Neelah magana tazo gida weekend sai tace ba dama saboda aiki yayi yawa sosai,
duk wani abu da kuka sani na buk'atar d'an Adam tun daga kan tsarki, wanka, alwala gyaran fuska da sauransu Neelah keyiwa Neehal.
Neelah zaune tana bawa Neehal abinci a baki, ya kafe ta da ido, tsaki taja had'i da dungure mishi kai tace " dalla Malam daina kallo na,
masifaffan banza kawai Allah ne yayi maganinka ya zaunar dakai waje d'aya, tayi maganar tana mik'ewa,
bata jima ba ta dawo d'auke da glass cup ta bud'e bakinshi ta zuba mishi magani kana ta bashi ruwan,
lips d'inshi ta kama ta murd'e da k'arfi tace " shegen bakin rashin kunya da bak'ar magana,
k'ara matse lips d'in tayi tace " bakin k'arya da munafurci, da wannan shegen bakin babu irin cin mutuncin da zagin da ban sha ba,
ta k'arashe maganar tana k'ara murd'e mishi baki, Neehal ya runtse ido da k'arfi, ta tsaya a kanshi tace " ja'iri ko zaka rama ne?
"Ko yanzun ma za'a k'are min zagi da cin mutunci ne?
D'urk'usowa tayi dai-dai fuskarshi ta yadda suna iya jin numfashin juna tace " ka manta lokacin da kace idan jiki na ya tab'a naka saika saka sosan k'arfe kayi ta gurzar wajen harya k'are...!?
Fuskarta d'auke da silent killer smile ta rungume shi, tace " to yanzu saikayi abinda kace zaka yi,
ta kuma cewa "ka tuna lokacin da kayi min kiss kayi ta kwara amai a Sunkhanni?
Bakinta takai kan nashi tayi mishi kiss caraf ya rik'e bakin tayi saurin zaro ido had'i da kwace bakin nata,
takai mishi rankwashi aka tana shafa lips d'inta tace " mugunta kamar bak'in arne,
har yanzu dai hali yana nan, muje na kaika band'aki nayi maka alwala kayi sallah,
ta fad'a tana tura kujerar dayake zaune akai, kayanshi ta fara cire mishi tayi mishi wanka,
sannan ta d'aura mishi alwala ta dawo dashi bedroom ta shirya shi tace " kayi sallar bari naje na gyara kitchen,
ido ya k'ifta mata alamar yaji dan ko hannun shi bai iya motsawa,
bata dawo d'akin ba sai da ta gama gyara kitchen ta d'ora musu abincin dare,
bathroom ta fad'a ta watsa ruwa, jallabiya kawai ta zura ta feshe jikinta da turare,
ta fita bata dad'e ba ta dawo d'auke da tray d'in abincinshi ta zauna a kusa dashi ta bashi a baki har ya k'oshi,
ta bashi magungunanshi yasha, "kana buk'atar wani abun, ido ya lumshe alamar ba komai,
batayi magana ba ta fita ta dawo d'auke da kayan gyaran fuska ta zauna ta soma gyara mishi fuska,
ido ya kafe ta dashi hawaye na k'ok'arin gangaro mishi tace " a a a a, mayar dasu bana san shauk'in k'arya,
ta fad'a idonta kan hab'arshi datake askewa, k'arar wayarta ne ya tsorata ta yanki Neehal da shever da take yi mishi aski,
ganin jini na zuba sosai ya rud'a ta, hankalinta yayi masifar tashi,
ta fashe da kuka tana bashi hak'uri " kayi hak'uri please wallahi bada gayya nayi ba mistake ne,
tana kuka wiwi tana goge mishi jinin while tana cigaba da bashi hak'uri, " am sorry Allah ba da sani na nayi ba,
a hankali ya shiga girgiza mata kanshi had'i da k'ok'arin motsa hannunshi,
da dare bayan tayi mishi wanka ta canja mishi kaya ta kwantar dashi saman bed, ta koma saman sofa ta kwanta,
dan bata barinshi ya kwana d'aki shi kad'ai, bacci ya soma d'aukarta kiran Nauman ya shigo wayarta,
sun dad'e suna shan love kana sukayi sallama, ana yin kiran sallah ta mik'e ta kaishi bathroom tayi mishi alwala,
ta dawo dashi d'akin sannan ta koma tayi alwala, tana kan sallaya tana azakar bacci ya d'auke ta,
bata farka ba sai 10:30 na safe da sauri ta mik'e zaune karaf suka had'a ido, murmushi ta sakar mishi had'i cewa " am sorry na barka da yunwa ko?
A gaggauce ta had'a mishi breakfast ta shigo bedroom d'in d'auke da tray ta aje saman table,
ta shiga bathroom ta d'auko roba da ruwa ta marclean & brush, sai da tayar dashi zaune ta tallafe bayanshi da pillows,
sannan tayi mishi brush takai ruwan bathroom ta zubar ta dawo ta bashi abinci yaci ya k'oshi ta bashi magani,
tace " nayi maka wanka ko zaka koma bacci?
Alamar tayi mishi wanka yayi mata da ido, batare datace komai ba ta cire mishi kayanshi,
ta tura shi zuwa bathroom, shever ta d'auko ta soma aske mishi hammata, tsaye tayi a kanshi rik'e da shever tana kallanshi,
deep down tana tunanin ta yadda fara aske mishi mararshi zuwa al'aurarshi,
shima ido ya k'ura mata deep down yana tunanin me take shirin yi?
A ranshi yace " badai askin gaba na take k'ok'arin yi b.....!, bai k'arasa tunanin da yake ba yaji hannunta saman mararshi,
idonta rufe gam a d'an tsorace jikinta na rawa ta sanya hannu ta kawar da joy stick d'inshi ta soma yi mishi asken,
idonshi ya lumshe yana fitar da numfashi a hankali a hankali, kan kace me joy stick ta mik'e samb'al,
d'ago kan da Neelah zatayi idonta ya sauka akan joy stick a tsaye k'em,
ido ta zaro bakinta bud'e cike da tsoro da mamaki, ta kalli Neehal kana ta mayar da kallanta kan joy stick,
" kambu! amma kai dai anyi bak'in jarababbe, dan tsabar masifa babu abinda ke motsi a jikinka sai ita?
"Komai naka a shanye yake amma saboda tsabar masifa ita sai da ta motsa?
"Aiko sai dai taci babu tayi maganar tana rankwashinshi aka,
" yauwa na tuna dama da wannan shegiyar abar me kama da rodi aka azabtar dani ko?
"Da ita kayi amfani ka wahalar dani, sai da nayi kwana biyu ban farfad'o ba, nasha bak'ar wahala,
sai da na gwammaci mutuwa, to wallahi sai na rama kai ma da itan duk sai kun d'and'ani irin bak'ar wahala da azabar dana sha,
ido ta runtse jikinta na tsuma ta damk'i joy stick d'inshi, ta murd'e ta da iya k'arfinta,
tana murza da cike da tsantsar mugunta, ido Neehal ya runtse da k'arfi, take jijiyoyin kanshi sukayi rud'o-rud'o gumi ya shiga karyo mishi,
duk ilahirin jikinshi ya d'auki rawa yana tsuma saboda azabar daya ji tana ratsa shi,
hannu takai kan bolls d'inshi ta shiga murza su cikin mugunta tana cewa,
" kaji kaima idan da dad'i, kaji irin abinda naji, shigiya me kama da rodi ta fad'a tana k'ara k'arfin matsar da tayiwa joy stick d'in,
bakinshi dake rawa ta murd'e had'i rankwashinshi aka tace " shegen munafukin bakin da yake zagi na,
bakin yin sharri, k'arya da munafurci, gwara ma na cire shi kowa ya huta,
babu irin zagi da cin mutuncin da ba'ayi min da bakin nan ba, bak'ar magana da gori nasha su, ta fad'a tana cije hak'oranta,
tare da murd'e lips da joy stick d'inshi da k'arfi, sai ta gaji dan kanta sannan ta k'arasa yi mishi wanka ta shirya shi,
ta kwantar dashi ta fita, gidan ta gyara tsaf k'anshi na tashi a ko'ina na gidan,
ta d'ora abinci sannan ta koma bedroom d'in ta iske yana bacci bargo taja mishi ta rufe shi ta koma saman sofa ta kishingid'a,
sai yamma ya tashi ta kaishi bathroom tayi mishi alwala bayan ya idar da sallah,
ta fitar dashi parlor ta kunna mishi labarai yana kallo tana yanke mishi farce,
bayan ta gama yanke mishi farcen ta had'o ruwan d'umi a baho ta sanya k'afafunshi ciki ta wanke mishi su tas,
sannan ta d'auke ruwan takai ta zubar, ta bashi abinci yaci ta bashi magani, bayan ya gama kallan labaran ta turashi zuwa bathroom,
shirya shi tayi tsaf ta kwantar dashi ta soma yi mishi tausa tana karanta mishi Facebook news har yayi baccin.
Bayan sati d'aya Neelah zaune k'asa Neehal na zaune kan kujerar zamanshi,
k'afafunshi saman cinyar Neelah tana yi mishi tausa da hannu d'aya,
while d'aya hannun tana rik'e da al'kur'ani tana karanta mishi, dan kullum saita sauke mishi izu uku zuwa biyar,
yayi shiru idonshi kanta ya tsare ta ido yana kallan fuskarta,
da yadda take motsa d'an tsukakken bakinta wajen sarrafa shi tana karatun Alkur'anin,
zazzak'ar muryarta na ratsa duk ilahirin jikinshi, a hankali ta rufe Alkur'anin ta kalle shi tace " tom mun gama na yau,
tayi maganar tana murmushi, ta mik'e a hankali ta mayar da Alkur'anin mazauninshi,
ta cire hijab d'in jikinta ta shiga d'aki ta d'auko kayan gyaran farce ta dawo ta gyara mishi farce tas,
ta kuma gyara mishi fuska, tana shirin mik'ewa wayarta ta soma ruri komawa tayi ta zauna kana ta amsa wayar,
d'an shiru tayi had'i da kallan Neehal tace " amma Doctor kasan ina patient a gida ko?
"Kuma sanin kanka ne bazai yiyu na fita na barshi shi kad'ai a gida ba, tayi maganar idonta kan Neehal,
" haba Neelah ki fahimce ni mana itama wacce za'ayiwa aikin tana buk'atar taimakon gaggawa,
dan Allah kizo, haka Doctor yayi ta rarrashinta harta amince zata zo,
cikin sanyin jiki ta kalli Neehal fuskarta a kwab'e kamar zatayi kuka tace " akwai patient a asibiti wanda za'ayiwa aiki yana buk'atar taimakon gaggawa,
ido ya lumshe alamar taje, murmushi tayi had'i da mik'ewa ta shafa kanshi, sai da gama yi mishi komai kana ta fita,
a gaggauce Neelah ta gama duba marar lafiyar ta dawo gida, tana shiga ta iske shi kwance k'asa ya kifo daga kan kujerar,
kanshi ya bugu ya fashe jini sai zuba yake, gaba d'aya jikinshi ya b'aci da kashi, kashin ya dame wajen ya b'ata mishi jiki,
idonshi kan robar ruwa da alama ruwan yake so, waya ta jakar hannunta tayi wulli dasu ta isa gare shi cikin tashin hankali,
ta d'ago shi ta rungume shi a jikinta, batare data damu da kashin dake jikinshi ba,
jikinta na rawa ta kafa mishi robar ruwan a baki, ya cafki ruwan bai d'auke kanshi ba sai da shanye ruwan tas,
cike da tausayinshi Neelah ta rungume shi tsam-tsam a jikinta had'i da fasa gigitaccen kuka,
tana cewa " am sorry, I'm so so sorry, I'm very sorry,
kayi hak'uri kaji laifi na ne dana tafi na barka kai kad'ai,
daga yau nayi maka alk'awarin ban k'ara tafiya na barka kai kad'ai,
tayi maganar cikin matsanancin kuka tana k'ara matse shi a jikinta,
" duk abinda nake yi maka ina yi maka shi ne kawai badan mugunta ko zalunci ba but am sorry,
zan aje aiki na na kula dakai danka samu cikekkiyar kulawa ta in sha Allah,
sai da taci uban kukanta ta kaji, sannan ta mik'e ta mayar dashi kan kujerarshi ta turarshi zuwa bathroom,
ta wanke shi tass ta canja mishi kaya ta feshe shi turarurruka, sannan ta dawo dashi parlor,
cikin nutsuwa ta shiga gyara parlor'n tana goge jini da kashinshi idon Neehal kanta hawaye na gangarowa daga idonshi,
ganin yadda take goge kashinshi amma babu kyankyami ko kyamar komai, cikin k'ank'anin lokaci ta gyara ko'ina fes, ko'ina ya d'auki k'amshi,
abinci da magani ta bashi, sannan ta kaishi bathroom ta kwantar dashi saman bed,
daga gefen gadon ta zauna k'afarshi kan cinyarta tana mammatsa k'afar (tausa),
tana karanta mishi littafin ruwan Bagaja, har sai da yayi bacci sannan ta mik'e ta gyara mishi kwanciyar ta rufe shi da bargo,
haka kullum Neelah keyi bata yin bacci sai Neehal yayi kuma har yayi baccin tana yi mishi tausa, had'i da karanta mishi labarai,
a cikin satin Neelah ta fara koyawa Neelah mik'ewa, cikin ikon Allah bata dad'e tana koya mishi ba ya iya tsayawa da k'afarshi,
sannu a hankali ta fara koya mishi tafiya, idan ya tsaya sai ta d'anyi baya kad'an ta wara hannunta alamar yazo,
idan yayi taku biyu zuwa uku kamar me tatata sai ya kifa kamar zai fad'i sai tayi saurin tare shi, ya fad'a k'inta,
abinda Neelah bata sani ba shine Neehal ya dad'e da warkewa dan tuni ya fara tafiya ya koma normal kamar yadda yake a baya,
yana yin pretending ne kawai, wanda shi kanshi idon za'a kashe shi bai san dalilin k'in bayyana samun lafiyarshi ba,
Neelah na zaune saman sofa while Neehal yana zaune kan kujerar zamanshi,
ya kafe ta da ido, lura da irin kallan da yake yi mata yasata yamutsa fuska tare da cewa " lafiya dai?
Bai kawar da idonshi ba bai kuma yi magana ba, tace " kana buk'atar wani abun ne?
"Still shiru Neehal yayi, Neelah ta turo d'an tsukakken bakinta tace " ni ka dai na kallo na ban san yawan kallo,
still bai daina kallan nata ba, cikin tsiwa tace " wai kai bazaka daina kallan nawa ba?
K'ara bud'e ido Neehal yayi yana kallanta wanda yayi hakan ne dama danya tsokane ta,
" maye kawai kaci kanka, amma nina fi k'arfinka, ta fad'a tana kawar da kanta daga gare shi, saura kad'an dariya ta kufcewa Neehal yayi saurin danne ta,
ta wutsiyar ido ta saci kallanshi taga har zuwa lokacin idonshi akanta,
a hasale tace " wai baka ji abinda nace maka bane?
Ganin bashi da niyyar daina kallanta yasata mik'ewa ta rankwashe shi aka,
had'i da murd'e mishi lips, ya runtse ido da k'arfi ya cafki hannunta ya d'an cija a hankali yadda bazata ji zafi ba,
hannun ta shiga yarfawa tana cewa " ka cije ni?
Yadda tayi tamkar gaba d'aya yatsan ya cire, " tab! aiko wallahi sai na rama, ta fad'a tana d'age mishi riga,
ta gartsa mishi cizo akan nononshi azaba ce ta sanya Neehal cewa " washhhh batare daya sani ba,
da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi idanuwanta waje tace " magana kayi?
Ido ya kafe ta dashi cikin ranshi yana addu'ar Allah yasa karta gane, tsoki taja had'i da dungure mishi kai tace " bak'in maye bari na barka maka parlon karka cinye ni,
tayi maganar tana shigewa bedroom had'i da banko k'ofa, ajiyar zuciya ya sauke yana shafa nononshi,
yana murmushi yace " Neelah kenan har yanzu halinki na nan babu abinda ya canja,
yana zaune saman sofa ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallan labarai yaji motsin fitowarta,
da sauri ya mik'e ya koma kan walk chair ya zauna, tana hamma gami da murza idonta ta fito daga bedroom d'in,
cak ta tsayar da hammar ta tana bin parlor'n da kallo, jarkar fresh milk ta gani kan center table,
ga snacks da sauran kayan ciye-ciye a ko'ina, parlor'n duk yayi kaca-kaca, bayan tsaf tabar parlor'n
kallan Neehal tayi cike da mamaki dan tasan daga ita sai shi a gidan, batayi magana ba ta soma k'ok'arin shiga kitchen,
karaf idonta ya sauka akan k'afar Neehal sanye da takalmi sosai mamakinta ya k'aru, dan a iya saninta baya saka takalmi, tayaya ma za'ayi ya saka takalmi mutumin da baya tafiya,
batayi magana ba ta shige kitchen, ajiyar zuciya ya sauke yana hamdala dabata gane ba,
da daddare as usual yana kwance tana yi mishi tausa da karatun labarai,
idonshi lumshe yana jin dad'in tausar sosai, jin shiru yasa shi bud'e idonshi, murmushi yayi ganin ta kifa kanta kan k'arfarshi tana bacci,
a hankali ya mik'e ya hawar da ita kan gadon sosai ya gyara mata kwanciya ya lullub'e ta da bargo,
fitilar d'akin ya kashe gaba d'aya yadda kota farka bazata gane baya nan ba, bathroom ya shiga yayi wanka ya canja kaya,
sallar nafila yayi had'i da karanta Alkur'ani, bayan ya gama ya shiga kitchen ya d'auko fresh milk da fruit yana sha,
batare daya sani ba bacci ya kwashi shi, bata farka ba sai da aka kira sallar asuba,
a hankali ta tashi zaune tana bin kanta da kallo cike da mamakin ya akayi ta kwanta kan gado,
ganin ta kasa tuna komai yasata kawar da tunanin tana shirin mik'ewa idonta yakai kan robar fresh milk da ragowar fruits,
kallan Neehal tayi da yayi kamar yana bacci amma a zahiri ba baccin yake yi ba,
sallaya da Alkur'ani ta kuma kalla cikin matsanancin mamaki,
tana ta sak'e-sak'e cikin ranta, baki ta tab'e had'i da mik'ewa ta shiga bathroom,
kai Neehal ya dafe tare da cewa " oh! God na manta ban kwashe kayan nan ba,
jin k'arar tab'a k'ofa yasa shi saurin komawa yadda yake, tsaye tayi a kanshi tana bin kayan jikinshi da kallo,
dan tasan bada kayan jikinshi ta barshi ba, ga k'afarshi harda safa, tunani ta farayi kala-kala cikin ranta,
cikin nutsuwa ta tasheshi ta tura shi zuwa bathroom ta tsaya kanshi, while Neehal Allah Allah yake yi tayi mishi tsarki,
hannu ta sanya ta soma yi mishi tsarkin, a hankali Neehal ya lumshe ido yana fitar da numfashi k'asa-k'asa,
bayan sun idar da sallah ta tambaye shi wanka ko abinci zai fara ci da sauri yayi mata alamar ta fara yi mishi wanka,
bata kawo komai cikin ranta ba ta shigar dashi bathroom ta cire mishi kaya,
ta soma yi mishi wankan, idonshi lumshe yana jin wani mugun dad'i na ratsa duk ilahirin jikinshi,
yana ratsa shi tun daga tafin k'afarshi zuwa tsakiyar kanshi, dakyar Neehal ya daure yayi controlling kanshi.
"Hello Mamy yi hak'uri na aje wayar ina kitchen, " ayya bakomai Neelah, ya aikin naki?
"Alhamdulillah, ya Daddy dasu Suhaira?
"Bakuyi waya dasu bane?
"Munyi amma tun shekaran jiya, " Daddy ne yace na kira ki na tambaya ki lafiya kika aje aiki?
Kallan juna sukayi ita da Neehal kasancewar wayar a hand free take yaji abinda Mamy tace,
dakatawa Neelah tayi da wankin k'afar da takewa Neehal ta rasa amsar da zata bawa Mamy,
ido Neehal ya k'ura mata yana tunanin dama da gaske take datace zata aje aikinta ta kula dashi ta aje d'in,
" haba Neelah ki tuna irin bak'ar wahalar da kika sha kafin ki cimma burinki,
murmushi Neelah tayi tare da cewa " Alhamdulillah Mamy ko yanzu na cika buri na,
Mamy tace " ki dayyi tunani kafin ki yanke hukuncin, " to in sha Allah Mamy, " Neelah har yanzu Neehal shiru babu ko labarinshi,
Mamy ta fad'a kuka na neman kufce mata, ido Neelah ta runtse hawaye na gangarowa daga idanta,
tace " am sorry Mamy kiyi hak'uri in sha Allah, Ubangiji zai bayyana shi, cikin sanyi Mamy tace " amin ya Allah,
saurin kashe wayar Neelah tayi ta durk'ushe had'i da fasa kuka tace " am sorry Mamy nasan kina cikin damuwa kan rashin ganin Neehal,
kuyi hak'uri da nisanta ku da nayi dashi ta fad'a tana fushewa da kuka, " nasan banyi muku adalci ba am sorry, k'ara kiran wayar Mamy tayi a karo na biyu,
sai data goge hawayenta ta saita kanta kana tayi picking wayar Mamy tace " na namanta ban fad'a miki ba,
gobe Nauman zai kawo su Nail hutu, ido ta zaro a tsorace tace " ina Mamy?
"Nan Lagos gidanki, "a'a please kar a kawo su Mamy gani nan zanzo dama na kusa zuwa ai,
cikin fad'a Mamy tace " ke kunji ni da yarinya, dan kinga na zuba miki kawai, shine kike yin abinda kikaga dama?
"Tun last month aka sanar da Daddy kin aje aiki, amma kink'i dawowa gida, ko weekend baki zuwa,
sannan yanzu za'a kawo yara kice a'a uban me kike yi a Lagos d'in?
"Uban me kike b'oyewa?
D'an shiru Mamy tayi kana cikin sanyin murya tace " Neelah kodai kina tare da Neehal?
Da k'arfi k'irjinta ya buga gabanta yayi muguwar fad'uwa, cikin rawar murya tace " na'am, hmm wanne Neehal d'in kuma Mamy shida yace bai sanni ba?
Ta k'arasa maganar tana watsa mishi harara had'i mintsininshi tace " munafuki,
gudan kar Mamy tayi tunanin wani abu yasa tace " ba damuwa Allah ya kawo su lafiya,
Mamy ta amsa da " Amin, Neelah tace " Mamy ya jikin Najwah kuwa?
Da shauk'i sai dai har yanzu bata farfad'o ba kinaji wai ashe huhunta ta cakawa wuk'ar,
so ta samu mummunan ciwo, cikin sanyi Neelah tace " ayya Allah ya bata lafiya,
bayan ta kashe wayar ta kalli Neehal daya tsaye ta da ido yana tunanin halayyar Neelah,
yayi mata sharri ta saka mishi da alkhairi, yanzu ta gama kuka saboda tausayin halin da mahaifiyarshi ke ciki kan rashin shi,
kuma harda tambayar lafiyar Najwah data nemi kashe ta, batare daya sani ba yace " keta daban ce Neelah, ya fad'a yana murmushi,
kallanshi tayi tana murmushi tace " gobe yaran mu zasu zo, karo na farko da zasu rayu da iyayensu a tare,
haka muma mu rayu dasu, " 'ya'yan mu kuma?
"Su waye 'ya'yanta?
"Yaranta ita da wa?
Neehal ya tambayi kanshi cike da mamaki dan har lokacin bai san Nail, Nailah da Neelmah yaran Neelah bane balle yasan yaranshi ne,
baki ta d'an turo tace " ina tsoran karsu sanar da Mamy kana nan,
kuma gashi harda Nauman za'a zo, kai ta langwab'ar tace " Allah yasa Daddy da Mamy su fahimce ni su kuma yi min uzuri,
kodan nasan Nauman bai tab'a tonamin asiri haka my dears, tayi magana tana murmushi, kallanta ta mayar kanshi tace " ja'irin yaro munafuki har da cewa baka sanni ba ko?
Ta fad'a tana take mishi k'afa, ya runtse ido, washe gari tunda wuri ta tashi ta gyara gidan ko ina yayi tsaf-tsaf,
ta dafa abinci ta jere saman dinning ta shirya ta shirya Neehal,
ta sanya shi gaba tana cewa " yaran mu nakan hanya, 'ya'yan mu zasu zo su rayu damu, zasu rayu da iyayensu,
jin knocking d'in k'ofa yasata mik'ewa da sauri ta bud'e k'ofar Nauman a gaba su Nail na biye dashi,
cikin d'oki ta fad'a jikinshi ta rungume shi tana cewa " I missed you so much my love,
fuska Nauman ya b'ata yana turo baki yace " ba wani nan nayi fushi,
kumatunshi ta rik'e tana murmushi tace " am sorry dear nasan nayi laifi ina bada hak'uri kaina bisa wuya na,
ta fad'a tana kama kunenta, dariya ya sanya yana mayar da ita jikinshi yace " baki laifi ai, light kiss tayi mishi a kumatu tace " thank you,
fuskar Neehal tamkar an saukar mishi da bala'i, ya had'e ta murtuk,
kwata-kwata babu annuri ko alamun fara'a, cikin shagwab'a Nail yace " Mom! kin manta da mu ne?
"Mom! Neehal ya maimaita cikin ranshi, sakin Nauman tayi ta rungume su gaba d'aya tana dariya tace " wace ni na manta da rayuwata,
Nailah tace " we misses you Mom, " aure Neelah tayi akan AURE NA!!!! ko me?
"Ina ta samu yara da suke kiranta da MOM!?
" 'Ya'yan waye?
"Waye mahaifinsu?
Neehal ya tambayi kanshi, ganin su Neelmah ba k'aramin k'ara d'aurewa kanshi yayi ba,
" su Neelmah 'ya'yan Neelah ne amma Mamy tace min yaran cousin sister d'in Daddy ne,
sai a lokacin abubuwa da dama suka shiga dawo mishi, tun daga kan maganganun da Mamy ta rink'a fad'a mishi,
zuwa kan abubuwan dataitayi mishi wanda ya kasa fahimtarsu, sosai kan Neehal yayi mugun d'aurewa,
ya rasa ta inda zai fara tunani, sai lokacin ya tuno lokacin da Nauman ke sanar dashi maganar cikin Pari d'inshi, idan bai manta ba yana America Nauman ya sanar dashi 'yan uku ta haifa,
" me hakan ke nufi?
"Su Nail yaran waye?
Ya tambayi kanshi, idon Nauman ne ya sauka akan Neehal da sauri ya saki Neelah,
ya nufi Neehal jikin Nauman na rawa ya rungume Neehal,
yayinda Neehal kejin tamkar wuta Nauman ke watsa mishi, " we missed you Aboki ina ka shiga muna ta nemanka?
Nauman ya fad'a siririn hawaye na gangaro mishi, cikin sanyin murya Neelah tashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
rungume ta Nauman yayi yana cewa " thank you so much da baki saka komai a ranki ba kika ceci rayuwar d'an uwa na kuma aminina,
nagode sosai Neelah, ke ta dabance Neelah kina da kyawawan halaye da d'abi'u kin cika cikekkiyar 'yar halak,
dariya tayi tana zamewa daga jikin Nauman, tace " bakomai ai duk yiwa kai ne koba komai zaici darajar Mamy, Daddy da YARAN DAKE TSAKANINMU,
TUNDA MUN SAMU RABON HAIHUWA A TSAKANINMU, dammmm gaban Neehal yayi muguwar fad'uwa tamkar saukar aradu,
jikinshi ya d'auki rawa da kerrrrma kamar mazari, daga Nauman har Neelah babu wanda ya kula da halin da Neehal ke ciki,
" Mom ina kika samu Uncle muna ta nemanshi?
"Mamy da Daddy har kuka suke yi, Neehal bai gama tsinkewa ya gaskata abinda yake tunani ba sai da yaji muryar Neelah na cewa,
" he's not your Uncle he's your biological father, wannna shine babanku mahaifinku,
so ba Uncle bane call him DAD! not Uncle tamkar saukar an buga mishi rodi gannnnnn! da aradu had'i da rugugin ruwan sama Neehal yaji Nail, Nailah, Neelam sun had'a baki sunce " DAD!,
zumbur Neehal yayi ya mik'e tsaye ya shiga nuna su da hannunshi duk ilahirin jikinshi na tsuma,
ya kasa furta koda kalma d'aya sai lips d'inshi dake ta faman rawa, cike da mamakin mik'ewarshi tsaye ta kalle shi baki bud'e...........!
KADA KU MANTA DA SUBSCRIBE PLEASE
MOMYN ZARAH 'YARBAIWA