37
://***
*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE, DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI, TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
LITTATTAFAINA MASU ZUWA
_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_
3️⃣7️⃣
Shiru d'akin yayi babu wanda ya furta koda kalma d'aya, sai sautin kukan Najwah dake tashi,
cikin sanyin jiki Najwah ta zame k'asa ta zube gaban Neelah tana cigaba da kukan batare data iya cewa komai ba,
cikin ranta tana tunanin yau wacce tafi tsana fiye da kowa da komai a duniya tayi mata abinda 'yan uwanta, uwa d'aya uba d'aya suka kasa yi mata,
wacce ko k'aunar ta bud'e idonta ta ganta bata yi amma gashi ta rufa mata asirin da duk duniya babu ne rufa mata,
tayi mata abinda uwa ko ubanta bazasu iya yi mata ba, tayi mata kyautar da Allah ne kad'ai yake yinta, wato kyautar d'a, cikin muryar kuka tace " I'm sorry, I'm so so sorry Neelah,
nagode sosai ina rok'on Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, ta fad'a muryarta na sark'ewa,
fuskar Neelah d'auke da murmushi ta sanya hannu ta d'ago Najwah ta zaunar da ita a kusa da ita,
tace " tsakanin mu babu godiya tunda abu d'aya ne yayi mu, dukkan mu dodo d'aya mukewa tsafi,
yaran Neehal yaranki ne, dan haka har abada sun zama naki, nayi miki alk'awarin su kansu yaran bazasu san bake ce kika haifesu ba,
shiyasa nake san ki shayar dasu, ta fad'a tana gogewa Najwah hawaye, cikin nutsuwa Neelah ta mayar da kallanta ga Neehal dake tsaye hard'e da hannuwa a k'irji,
ta marairace fuska tace " I'm sorry na yanke hukunci batare dana tuntub'eka kona shawarceka naji ta bakinka ba,
a hankali ya taka ya isa gabansu ya sanya hannu ya shafa fuskar Neelah yana murmushi,
yace " ai abu me kyau kikayi, nagode sosai Neelah, kinyi abinda ba kowacce mace ce zata iya yinshi ba,
ya fad'a cike da tausayawa, " tom! Maman twins munyi yara, kuma naga kamar suna kama dake ma,
ya fad'a yana zama kusa da Najwah, Najwah ta sanya dariya had'i da d'an kai mishi duka tace " tunda suna kama dakai ai dole suyi kama dani, ya goce yana dariya,
" kuyi hak'uri iyayenmu na yanke hukunci batare dana nemi izini daga gare ku ba, Neelah ta fad'a tana kallan iyayensu,
cikin sanyin jiki suka sauke ajiyar zuciya, suka shiga kallan juna deep down suna jiinjinawa Neelah,
" mun gode miki sosai Neelah Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, Ubangiji ya biyaki, Allah ya saka miki da gidan aljanna ya shirya muku zuri'a,
Abban Najwah ya fad'a hawaye na gangarowa daga idonshi, gaba d'ayansu suka amsa da Amin ya Allah, Umman Najwah tace " bamu da bakin da zamuyi miki godiya,
baku da kalmar da zamuyi miki amfani da ita wajen nuna miki tsantsar farin cikin mu, iyakaci dai muyi muku addu'ar Allah ya had'a kanku,
ya raya muku zuri'arku ya had'e kan yaranku, ya baku zaman lafiya da fahimtar juna, tayi maganar muryarta na sark'ewa,
Mamy, Umairah dasu Suhaima da kowaccensu ke d'auke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe suka matsa kusa da Neelah cikin farin ciki,
suna yi mata godiya, Mamy ta shafa kanta, tana murmushi tace " Allah yayi miki albarka, Ubangiji ya albarkaci rayuwarku data yaranku gaba d'aya, suka amsa da amin ya Allah.
Cikin nutsuwa Daddy yayi gyaran murya ya soma da cewa " Alhamdulillah Alhamdulillah ala kullu halin,
ina godiya ga Allah daya had'e mana kan zuri'armu suka fahinci junansu, Allah ya k'ara had'e kansu,
shi kishi ya zama dole, dan Allah ya halicci shi a jikin kowacce irin halitta, har wad'anda ba bil Adama ba,
har dabbobi suna da kishi, haka hadisi yazo mana Annabi SAW yace " duk wanda baya kishin iyalinshi bazai shiga aljanna ba,
sai dai kishin wasu yana zama hauka, dabbanci da rashin hankali wanda ko dabba bata yin haka,
akwai matakan kishi da mutum zai kiyayesu dan gudun fad'awa kishin halaka wanda zai iyakai mutum aikata aikin nadama,
na farko a babin adalci mu sani cewa " _gairatul mar'a amrun jiblat alaihi faliza latu akaz'alaihi_ kishi wani abu ne da Allah ya halicci dukkan halitta akai, dan haka baza'a iya raba mutum da kishi ba,
shiyasa Malaman musulunci irinsu Ibn Rajab da Imamun Taba'i Allah ya rahama alaihi,
suka ce ba'ayiwa mata azaba akanshi _illa anta 'ta'adda_ sai dai idan kishin nata ya wuce gona da iri,
wato tayi zalunci akanshi, ta zagi wata, kota ci mutuncin wata, ko k'arya, ko cutar da wani, ko duka kota raba wani da ranshi,
to anan ta wuce gona ana iya yi mata ukuba akansa, baya da haka yazo a cikin Hadisi Irwa'ul Garib jiz'i na 7 shafi na 80,
Annabi SAW ya gaya mana kishi kala biyu ne akwai kishin da Allah yake so akwai kishin da Allah baya so,
yace " _Innaminal khaira mayi hibbullahi anza wa jannah wa minha mayif khudhullahu anza wa jannah_
daga cikin kishi akwai wanda Allah yake so akwai wanda Allah baya so, kishin da Allah yake so shine akwai damar aikata mummunan zato na aikata haramun a cikinsa,
misali mace ita kad'ai ce awajen mijinta, yayi tafiya daya dawo sai taga condoms a cikin kayanshi,,
bayan bai tab'a yi mata amfani da condom ba, kuma ajikin rigarshi taga alamar jan baki da hoda na mace,
to wannan tana iyayin kishi da zargi akansa saboda zina aramunce,
kishin da ba'a so shine kishin haramta halak, ki haramtawa mijinki abinda kike da tabbacin Allah bai haramta masa ba,
ki damu kanki akan binciken wayarshi, da wayarshi tayi k'ara ki kai hannu zaki d'auki, idan yayi wanka zai fita ki dame shi da tambayar inda zaije,
idan yayi dare bai dawowa ba ki sakawa kanki zargi yana wajen wata, haka idan ya tashi k'ara aure ki damu kanki da al'umma,
ki hana kowa zaman lafiya,
bayan kin san Allah ya halatta mishi k'arin aure, dan da farko ma cewa akayi ku auri mataye bibbiyu, uku-uku,
hurhud'u sai dai idan bazakuyi adalci a tsakaninsu ba saiku auri d'aid'aya,
baya ga haka akwai Hadisin da yazo cikin Fathul Bari Jiz'i na 9 babi na 325 Annabi tsira da aminci su k'ara tabbata a gare shi,
yayi mana bayanin illar mummunan kishi da cewa " _Innal gaira latu uk'usuru asfalal wajibun a'ala_
ma'ana lalle mace mai zurfaffan kishi irin wanda ba'a so bata iya gane inane zurfin rijiya yake, wato bata ganin gabanta,
daga kishin ya motsa saita yanke hukuncin da zatayi danasani daga baya, duk matar da take da makahon kishi bazata tab'a rabuwa da nadama da danasani a rayuwarta ba.
hanyoyin da zaki iya magance irin wannan mummunan kishin na farko akwai addu'a ki zama mai yawan addu'a da ambatan Allah kina mik'a dukkan lamuranki gareshi,
na biyu yawan rik'o da Alkur'ani, ya zamana kina yawan karanta Alkur'ani, idan baki iya karantawa ba ki rink'a sauraronshi,
saboda yana korar shaid'anu, yana wanke dattin zuciya,
na uku yawan neman tsarin Allah daga shaid'anu ki yawaita fad'ar A'zubillahi minal shaitanin rajim,
na hud'u yawan musabaha ma'ana mata mu rink'a gaisawa da juna hannu da hannu muna yin musabaha,
abu na biyar yawan kyauta da kyautatawa, mace ta zama tana da yawan kyauta da kyautatawa jama'a hakan zai saka muso junanmu,
abu na shida yawan fad'ar alkhairin mutane koda kishiyarki ce, kamar yadda ya faru tsakanin matan Manzon Allah SAW,
lokacin da akayiwa Nana Aisha k'azafin aikata Zina, wanda yazo cikin sutarul Nur Allah ya wanke ta,
yazo a cikin Hadisin Bukhari wa Muslim Annabi SAW ya tambayi abokiyar zamanta Zainab mezatace akan Nana Aisha, me take gani akan zargin da ake yi mata,
sai tace " Ya Rasulillahi na kiyaye jina da gani na, bana fad'ar abinda banji ba ban gani ba, bazanyi mata k'arya ba,
ta cigaba da cewa wallahi ni ban san komai ba akan Aisha ba sai alkhairi,
haka Annabi SAW ya tambayi Nana Aisha me zakice akan Zainab, Nana Aisha tace " wallahi ban tab'a ganin mace mai addini da ibada irin Zainab ba,
kuji fa kishiyoyi ne Nana Zainab ta samu damar yiwa Nana Aisha sharri a sake ta, amma tak'i yin hakan, haka itama Nana Aisha ta yabi kishiyarta Nana Zainab,
bayan Nana Aisha tace a lokacin da suke tare duk cikin matan Annabi SAW babu tsararta wacce suke competition irin Zainab,
abu na bakwai yawan bincike da zargi, ki guji yawan binciken wayan mijinki da sabgoginshi, binciken harkokin miji kamar wayarshi, chart, sms, email bada izininshi ba haramun ne,
a k'asar Saudi Arabia saboda yawan bincikar wayoyin miji da mata keyi shike assasa mutuwar aure kashi 20 cikin 100,
dan haka walata jassasu kada kuyi bincike, haka Daddy yayi musu nasiha mai ratsa jiki yana kawo musu musalai da dama, wanda yasa jikin Najwah yayi mugun sanyi, ta gane kuskuranta,
har Daddy ya dasa aya Najwah na kuka kamar ranta zai fita, cikin sanyin jiki ta zame k'asa ta durk'usa bisa gwiwowinta, a gaban Neehal,
tace " dan Allah ka yafe min nasan na tabka kurakurai da dama abaya, wanda yasa ni kaina nake jin kunyar kai na,
nasan na k'untata rayuwarka, na saka cikin matsanancin bak'in jiki, na jawo maka abubuwa da dama wad'anda bazasu fad'u ba, dan Allah ka yafe min,
ta fad'a cikin matsanancin kuka, a hankali ya sanya hannu ya d'ago ta, yana murmushi yace " Alhamdulillah na godewa Allah abisa wannan ni'ima da yayi min,
wacce ban tab'a tunani ba, ko'a mafarki ban tab'a zaton Najwah ta zata karb'i gyara cikin sauk'i ba,
na yafe miki duniya da lahira nima ina fata Allah ya yafe min, dan ba ke kad'ai ce me laifi ba, har ni ma ina da laifi, na kuma taka rawa akan duk abubuwan da suka faru,
nayi miki alk'awarin bazan tab'a yi miki kishiya ba, nayi miki alk'awarin dake kad'ai zan rayu, kamar wanda ya tara sani da Allah,
na shiga hurumin Ubangiji, haka duk abinda kike yi ban tab'a nuna miki kuskuranki ba, ban tab'a gaya miki abinda kikeyi ba dai-dai bane,
so kinga nima me laifi ne, sai da mu taru muyi ta Intigfari, " nagode sosai, Najwah tace tana juyawa ga iyayensu,
ta kuma zubewa ta nemi yafiyarsu, gaba d'ayansu suka yafe mata, ta bawa Nauman, Naufal, Umairah, Suhaima, Suhaira da Suhaila hak'uri akan abubuwan datayi musu abaya, duk suka yafe mata, suma suka bata hak'uri,
yayyanta suka matso kusa da ita,
Haleem yace " I'm sorry sister duk abinda kikaga munyi miki munyi miki ne saboda gyara, danki gane ba akan dai-dai kike ba,
amma muna sanki kamar yadda muke san kanmu, duk lokacin da wani daga cikinmu ya dake ki, koyayi miki fad'a sai munta rarrashinshi saboda yana shiga matsananciyar damuwa,
da sauri ta fad'a jikinsu ta k'ank'ame su tana sakin kuka, suka shiga rarrashinta,
ganin yadda take kukan yasa Abbanta cewa " to wanne suna za'a sawa jikokin nawa?
Nauman yana murmushi yace " a bani su nayi musu hud'uba, namijin ya fara yiwa hud'uba ya sanya mishi sunan Abban Najwah Ubayyu, macen kuma sunan Ummanta Sakina,
ya d'ago kanshi yace " na saka musu sunan Abban Najwah da Umman Najwah, za'a rink'a kiran macen da Nawal, namijin kuma Nawar,
sosai farin ciki ya k'ara kama Najwah jin an saka sunan iyayenta, a ranar da daddare aka sallame su,
bayan Nauman ya bawa Najwah magungunan da zata sha ruwan nono yazo mata, Mamy taso tafiya da Neelah amma Neehal ya murje idonshi yace bai san magana ba,
dole Mamy ta hak'ura tasa aka samo musu 'yan aiki guda uku, da tsohuwa d'aya da zata rink'a kula da yaran,
Najwah ta hana tsohuwar yiwa yaran komai, ita take yiwa yaranta komai, dan Allah ya jarrabeta da masifar san yaran fiye da komai da kowa,
tana jin zata iya rabuwa da kowa akan yaranta, shiyasa bata barin kowa ya tab'a mata su, ta tattara gaba d'aya hankalinta kan su,
bayan wata d'aya Najwah tsaye a kitchen tana tafasawa yaranta ruwa, Neehal ya shigo, ta baya ya rungume ta,
yana shak'ar k'amshin jikinta, cikin kasalalliyar murya yace " I love you so much NEELAH, kece rayuwata, ke haske ce a gare ni, kin bani dukkan farin cikin duniya,
muryarta na rawa tace " Najwah fa?
Kasancewar ba'a cikin hayyacinshi yake ba yasa bai gane muryarta ba, saida yayiwa wuyanta kiss,
kana yace " idan ana maganar mata kya saka wannan?
"Wannan ai ba mace bace, kima daina kiranta da mace dan lusara ce, da k'arfe ta runtse idonta had'i da dunk'ule hannunta ta had'iye kududun bak'in cikin,
take duk ilahirin jikinta ya d'auki tsuma kamar mazari gumi ya shiga keto mata, Neehal ya cigaba da magana,
" ni fa ban san dad'in aure ba sai da na aure ki, ban san dad'in mace ba sai na aure ki, ban san meye so ba sai akank........!,
sark'e mishi maganar tayi a mak'ogwaro yayi baya da sauri ganin Najwah tsaye gabanshi ta koma mishi asalin Najwah daya sani,
ido ta kafe shi dashi na tsayin lokaci, kana tayi murmushi had'i da girgiza kanta ta fice batare datayi magana ba,
saurin bin bayanta yayi yana kiran sunanta, ta shige bedroom d'inta,
ta zauna saman bed had'i da d'aukar Nawar tana bashi ruwa yayinda da hawaye ya cika mata ido tab,
jikinshi a sanyaye ya shigo d'akin ya zauna kusa da ita muryarshi k'asa yace " I'm very sorry, kiyi hak'uri,
ke kanki kin san har abada ba'a tab'a canjawa tuwo suna, I love you, babu wata mace dazata zo ta shiga gabanki,
babu macen da zata fiki a waje na babu wallahi har abada, bakya ganin yarinya ce ita, dole sai an had'a mata da wayo da yaudara,
ina yi mata dad'in baki ne kawai ita tana haihuwa ke bakya haihuwa kinga sai mu ajeyeta matsayin me haifa mana 'ya'ya ko?
"Amma ni ba wani santa nake yi ba, me zanyi da ita 'yar k'auye kawai zubin can, har yau har gobe kece star a zuciyar Neehal Bilal Lagosa,
kece uwar gidanshi, duk abinda kikaga nayi yaudara ce, ya k'arasa maganar yana yi mata kiss,
" k'araso mana Neelah..! Najwah ta fad'a tana murmushi, dam gaban Neehal yayi muguwar fad'uwa,
" no! dama shigowa nayi na tambayeki idan kin gama kizo mu shiga kitchen, " ok ba damuwa bari na gama shiryasu Nawal,
da k'arfe Neehal ya runtse idonshi, " shet!, OMG! ya fad'a cikin ranshi, Najwah batayi mishi magana ba, sai data gama shirya yaranta,
sannan ta juyo ta fuskanshi a nutse tace " kasan me hali har abada baya canja halinshi, karkaga kamar zuciyata ta mutu ne,
ko bana kishinka, ba haka bane ina nan yadda nake, haka kuma kishi na yana nan babu inda yaje, dan haka idan kana neman zaman lafiyar gidanka da 'ya'yanka,
ka nutsu ka tattara gaba d'aya hankalinka waje d'aya ka zama cikekken namiji me magana d'aya,
karka zama zulwajahaili me fuska biyu, kada ka rink'a d'iban maganar matanka kana kaiwa junansu wannan geba kenan,
idan ba haka ba zaka kunnowa kanka wutar da bazaka iya kashe ta ba, ka zama tsayayya namiji a gidanshi me jajircewa,
dole a cikinmu saika fi san d'aya tunda d'an Adam ne kai me rauni, amma kana iya controlling kanka,
kana iya b'oyewa ka kyautatawa kowaccenmu, dan idan kace haka zaka cigaba nima zan d'ora daga inda natsaya,
sai muga waye a ciki, waye zaifi shiga uku, muddin kana san zaman lafiya ka kiyaye gaba, sannan dan Allah kada ka k'ara zo min da maganar matarka kaga muna zaune lafiya,
akwai kyakkyawar fahimtar juna a tsakaninmu, tana girmamani ina ganin mutuncinta, ina kuma santa tsakani da Allah, ina jinta kamar 'yar uwata Nabeela ba kishiya ba,
dan ban tab'a d'aukar Neelah a matsayin kishiya ba so karka bari na bud'e d'ayan idon nawa na fara kallanta a matsayin kishiya,
idan ka tuna min da abinda ya wuce kaine a ciki dan haka kaima ka kama kanka ka rik'e girmanka, kada ka zama munafukin mata please,
zayyi magana tayi saurin cewa " I don't want argue with you so please jeka rarrashe ta, ka barni da yara na,
murya ya marairace had'i da langwab'ar da kanshi yace " taji abinda nace please?
"Wallahi taji komai dan kana shigowa ta shigo, ni na d'auka ma tare kuke, " dan Allah muje ki bata hak'uri ki tayani rarrashinta,
ya fad'a muryarshi na creaking, mik'ewa tayi tana dariya tace " kunfi kusa tare na ganku, dan haka inzaka je ka rarrashi matarka kaje,
" please! yace kamar zayyi kuka, tace " dani na aikeka, ka zage ta, maganin maza irinku kenan, Allah ya k'ara, inka fita ka rufe min k'ofar, ta fad'a tana kwanciya,, " au haka ma zaki ce?
Ganin batayi mishi magana ba yasa shi fita jikinshi a sanyaye ya nufi part d'in Neelah, ya iske ta tsaye gaban wardrobe tana ninke kaya,
kanshi k'asa cikin alamun jin kunya, yana shafa kanshi yace " I'm sorry please, kiyi hak'uri, batare data kalle shi ba tace " wani abu ne ya faru?
"Ni dai dan Allah kiyi hak'uri, " me kayi min da kake bani hak'uri?
"Eh I knew I made a mistake but I'm very sorry, " bakayi k'arya ba ai, duk abinda ka fad'a babu k'arya a ciki, iyakar gaskiyarka ka fad'a, so meye abun damuwa?
" In sha Allah bazan kuma ba, na fad'a mata hakan ne dan nayi calming down d'inta, " au baka ji abinda ta fad'a maka ba kenan!?
"Baka ji shawarar data baka ba?
"Naji mana, " shine kuma zaka kuma?
Ta fad'a bata kalli inda yake ba, a hankali ya ja baya ya durk'usa k'asa muryarshi na rawa kamar zayyi kuka yace " dan girman Allah kiyi hak'uri,
da sauri ta isa gareshi ta durk'usa kusa dashi had'i da d'ora hannunta saman lips d'inshi tace " shhhhh! ,
bakomai ya wuce amma please ka d'auki shawarar data baka dan shawara ce me kyau, ta fad'a tana kallan kwayar idonshi,
cike da tsantsar shauk'in juna suka had'e bakinsu, kasancewar tunda ta haihu babu abinda ya shiga tsakaninsu, a hankali yakai hannunshi saman boobs d'inta ya soma shafawa, yana fitar da nishi,
ganin abun na neman wuce gona da iri yasata saurin mik'ewa tana dariya, da sauri ya rik'ota, cikin kasalalliyar murya " please,
a hankali tayi k'asa da kanta kamar zata had'e bakinsu, sai kuma ta waske ta fice da gudu tana dariya,
shima dariyar yayi yana kallan bayanta, watan Neelah d'aya da kwana biyu da haihuwa Suhaima da Suhaila suka haihu rana d'aya,
murna wajen Nauman kam ba'a magana,
Suhaima ta haifa mishi santalelen yaro san kowa k'in wanda ya yarasa, Suhaila ta haifi 'ya mace kyakkyawa, kwana biyu da haihuwarsu Suhaira ta haihu ta haifi 'ya mace itama,
d'an Nauman yaci sunan Neehal, 'yar Suhaila taci sunan Mamy, 'yar Suhaira taci sunan Mamansu Nauman Fatima,
murna da farin ciki kam ba'a gama family kowa sai murna yake,
Neehal da amininshi zaune zaman mota suna hira Nauman ya kalli Neehal yace " ka tuna wani lokaci a baya mun tab'a zama haka muna hira?
"Wasu lokuta dai, Neehal ya fad'a, Nauman yayi murmushi kana yace " ka tuna ranar da muke zaune adai-dai nan na fad'a maka baka san soyayya ba,
baka san me ake kira da so ba, na fad'a maka komai daran dad'ewa wata rana zaka had'u da macen da kake so,
na fad'a maka dole zaka k'ara aure ka k'aryata ni ka tuna?
Dariya Neehal yayi had'i da shafa kanshi yace " abokina baka da mantuwa, ashe baka manta ba?
"Ya za'ayi na manta, idan baka manta ba ai munsha yin haka dakai, har ita Najwah da kanta ta tab'a fad'a maka ko ka manta?
"Kaima baka manta ba bare ni, d'an dukanshi Nauman yayi yana dariya yace " shege uban cika bakin tsiya,
a lokacin kayi ta cika baki kana kurin babu macen dakake so kamar Najwah, bazata tab'a san wata mace bayanta ba,
kace bazaka tab'a yi mata kishiya ba, a lokacin idan ina hanaka na ko ina baka shawara ma haushi na kake ji, to yanzu ga yadda Allah yayi lamarinshi,
Neehal yayi murmushi me sauti had'i da d'aga kanshi sama yana kallan sararin samaniya yace " hakan da Allah yayi shine mafi alkhairi gare mu baki d'ayanmu daga ni har Najwah ba,
shiyasa Annabi SAW yace " idan zaka so abu kaso shi saya-saya dan wata rana yana iya komawa mak'iyinka,
haka idan zaka k'i abu kak'i shi saya-saya dan wata rana yana iya komawa babban masoyinka,
sau da yawa alkhairinmu yana binmu muna gudu izuwa sharrin mu, haka zai iyayuwa alkhairin mu yana dama mu muyi ta yin hagu,
Allah yayi ta nuna mana alama amma muk'i ganewa, shiyasa cin alwashi, d'agawa, kuri da cika baki basu dakyau,
dan rayuwa, mutuwa, k'addararmu duk ba a hannunmu suke ba, a hannun Allah me komai da kowa suke, Ubangiji shike tsarawa kowa rayuwarshi,
mu bayi ne a gare shi, bamu da ikon zab'arwa kanmu rayuwa, bamu da ikon yankewa kanmu hukunci akan rayuwarmu,
sai dai mujira hukumcin Allah, na godewa Allah da baisa nayi *SAKI RESHE...!* ba, nagodewa Allah dayasa alkhairi na yayi ta bi na dukda gudun da nake yi,
Ubangijin sammai da k'assai, wanda yayi kowa da komai, wanda yake kwacewa daga hannun wanda yaso ya bawa wanda yaso,,
me ikon zartar da duk wani hukunci akan kowa da komai, mutum da aljan, ya k'addara min rayuwa ta haka da mata biyu,
ya zartar da hukuncinshi akaina, yayi nufinshi akanmu, ina kuma godiya a gareshi abisa ni'imomin da yayi min, Alhamdulillah ala kullu halin, Nauman ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi yace " lalle Aboki na yayi hankali girma ya kama mu, murmushi Neehal yayi yace " bakaga su Nailah sun shiga 14yrs ba,
dan haka dan uban mutum ya nutsu dan kwanannan za'a fara zuwa neman aure wajenshi, suka saka dariya tare.
Bayan wasu watanni
Sosai shak'uwa da kyakkyawar alak'a ta shiga tsakanin Najwah da Neelah, ta yadda tare suke gudanar da komai na rayuwarsu,
tun daga kan harkokin gida girki, kula da yara, kula da mijinsu, tare suke zuwa biki ko suna da duk wani taro da za'ayi,
haka ma tare suke business duk wani harkokin kasuwancinsu tare suke yi, Allah ya zaunar dasu lafiya cikin fahimtar juna, yayinda Neehal ke k'ok'arin faranta musu gaba d'ayansu,
yana k'ok'arin b'oye soyayyar Neelah da take azalzalarshi, duk wani abu tare yake yi musu, sun had'e kansu sun zama tamkar uwa d'aya uba d'aya ba kishiyoyi ba,
mutane har mamakin had'in kansu suke yi, Neehal yaso amsar su Nail Mamy da Daddy suka hana suka ce tunda aka haife su anan,
anan zasu zauna dan sun saba dasu sosai, idan ya kwashesu shikenan gabansu babu kowa kenan,
dole ya hak'ura duk da yaso had'e yaranshi waje d'aya, gaba d'aya Lagosa Family suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali babu wata matsala,
daga b'angare d'aya Najwah tana kula da yaranta, sun girma sunyi wayo sosai, Allah ya zuba mata matsananciyar soyayyar yaran,
ta tattara komai nata ta d'ora akansu, idan kana san kaga haukan Najwah ka tab'a mata yaranta,
anan zaka tabbatar da har lokacin halinta yananan babu inda yaje, dan tana iya rufe ido ta zazzagawa mutum ruwan bala'i,
ta hana 'yan aiki ko kusantar inda yaran suke balle suyi musu wani abu, ita take yiwa yaran komai,
mutane na mamakin mugun son da Najwah ke yiwa su Nawal, saboda su ta daina kwana d'akin Neehal,
saboda yace mata bai kamata su rink'a kwana dasu ba, tunda sunyi wayo sosai, batayi mishi magana ba ta kwashe yaranta ta fice mishi daga d'aki,
dayayi mata Magana sai ce mishi tayi akan yaranta tana iya rabuwa da kowa da kowa ciki kuwa harda shi, tana iya hak'ura da aure ma gaba d'aya,
tun da kowa yaji abinda ta fad'awa Neehal kowa ya shafa kanshi lafiya, aka fahimci Allah ne ya kamata ta hanyar jarrabarta da son yaran,
dan haka kowa ya zuba mata ido ana kallan ikon Allah.
Kin san me Ba'ad Ruhi?
Kanta ta girgiza batare da tayi magana ba, a hankali ya d'ora kanshi saman kafad'arta,
yayinda hannuwanshi ke saman cikinta idanuwanshi lumshe yana lasar wuyanta, yace " ki shirya nan da 3hrs jirgin mu zai tashi,
da sauri ta juyo tana kallan fuskarshi tace " ban gane jirginmu zai tashi ba, tafiya zaka yi kome?
"Tafiya zanyi kodai tafiya zamuyi?
"Ina zamuje Sunkhanni, daga can zamu wuce Landon, tsalle tayi ta fad'a jikinshi tana dariya cike da murna, tace " dan Allah da gaske kake?
"Eh! mana, cikin farin ciki ta rungume shi tsam tana jera mishi kiss a fuska, "oh! wannan duk murnar ganinsu Abpa ce?
"Kai ko ba dole ba, nafa dad'e ban gansu ba, tun zuwan da mukayi kafin a mayar da auren mu, duk sanda nayi maka magana sai kace ba yanzu ba,
" to yanzu da lokacin yayi ba gashi zamu je ba, ya fad'a yana k'ok'arin had'e bakinsu, ta d'an kawar da kanta, tana kallanshi tace " to Aunty Najwah fa?
D'an shiru yayi yana tunani kafin yace " ba damuwa zanji da ita nasan yadda zanyi da ita, ya fad'a yana shigewa jikinta,
a hankali ta zame jikinta tana turo baki tace " please ni dai ka fara zuwa kayi magana da ita tukunna,
idan ka dawo kome kake so sai kayi, zayyi magana tayi saurin had'e bakinsu, ta tsotsi lips d'inshi sosai,
kana ta zame bakinta a hankali tace " please! , "ina ai baki isa ba sai an gama tunda aka fara, dariya ta saka had'i da tura shi waje ta rufe k'ofar,
yayi dariya gami da girgiza kanshi ya nufi part d'in Najwah, zaune ya iske ta, tana bawa Nawar nono,
ta d'aga kanta ta kalle shi tana murmushi, shima murmushin ya sakar mata ya k'arasa inda take, yayi mata kiss ita da Nawar,
kana ya zaune fuskarshi cike da damuwa, " lafiya dai ko na ganka cikin damuwa?
Sai da yaja d'an guntun tsoki kana yace " Daddy ne ya aike ni Landon, gashi zan d'an dad'e shiyasa nake san tafiya da d'aya daga cikinku,
gashi ke kina shayarwa ban san yadda za'ayi ba, " kaga idan tafiya kake san yi da matarka ka fad'a kanka tsaye ba sai ka tsaya kana 'yan kame-kame ba,
kuje Allah ya tsare sai kun dawo danni bata ku nake ba ta yara na nake yi,
zayyi magana tace " yaushe ne tafiyar?
Jikinshi a sanyaye yace " yau, ido ta d'an zaro tana murmushi tace " kace sai da ka gama shirya komai sannan kazo zaka raina min hankali,
kuma na tabbatar Neelah bata sani ba, dan inda ta sani data fad'a min, " eh bata sani ba, kuma ina jin tsoran na fad'a mata,
tace bazata je ba saboda ke, so please ki gaya mata, tunda ke kin yafe, shiru tayi na d'an lokaci kana tace " ba damuwa tashi muje na fad'a mata,
ba musu Neehal yabi bayan Najwah suka shiga part Neelah ganin bata parlour yasa su nufar bedroom d'inta,
Najwah ta zauna kusa da ita a bakin bed, had'i dayin k'asa da muryarta tace " mijinki ne zayyi tafiya, shine yake tambayar dawa zai tafi a tsakaninmu,
nace mishi ni na yafe ku tafi, d'an satar kallan Neehal tayi ya kashe mata ido d'aya, Neelah tayi saurin mik'ewa, tana cewa " tab! nima bazani ba tunda kema bazaki ba,
jin abinda Neelah tace yasa Neehal saurin kallanta, ta kashe mishi ido, ya gane plan ne, a hankali Najwah ta mik'e ta isa gaban Neelah tace " please ki bishi mana, kinga ni ina da yara,
bai kamata ya tafi dame goyo ba bayan ga marar goyo, baki Neelah ta tura tare da cewa " ki kaisu gidan Umma mana,
ganin suna neman raina mata yawo yasa Najwah cewa " kuma fa haka ne kin kawo shawara,
bari naje nasa akaiwa Umma su, tunda Nabeela na gida, lips Neehal ya cije had'i da harar Neelah yana yi mata alamar tayi wani abu,
ganin Najwah na niyyar fita yasa Neelah saurin shan gabanta tace " shikenan bakomai zan bishi dan karkiji babu dad'i kice kin rok'i alfarma a waje na naki'i yi miki,
Najwah ta tuntsure da dariya had'i da cewa " munafukan banza, ana so ana kaiwa kasuwa, nasan bakinku d'aya, wai ni zaku mayar gara,
Neelah zatayi magana Najwah tace " kinga ni nayi nan yarana na can na barsu su kad'ai, ta fad'a tana ficewa,
suka bi bayanta da kallo deep down suna mamakin Najwah, yayinda Neehal yake ganin kamar ba ita bace,
basu d'auki lokaci ba suka shirya tsaf suka fito janye da k'atuwar trolley biyu, suka shiga part d'in Najwah, tana zaune tana kallo,
tayi saurin mik'ewa tana cewa " har kun shirya?
A kunyace Neelah ta amsa da "eh?, Najwah ta d'an kai mata duka tana dariya tace " munafuka kunyar kuma ta uban meye?
Neelah tayi dariya batare datace komai ba, har bakin mota Najwah ta raka su, Neehal ya rungumeta tsam a jikinshi, had'i dayi mata kiss yace " I love you so much, I love you more much, zanyi missing d'inki Dear,
ya fad'a kamar zayyi kuka, d'an dukanshi tayi k'irji tana dariya tace " I love you too, nima zanyi missing d'inka,
" kinga jeki shiryo kawai mu tafi tare gaba d'ayanmu, baya tayi tana dariya tace " bayan ba'a so ayi tafiyar dani ba,
ido ya zaro yana dariya yace " a'a fa Dear, hannu ta d'agawa Neelah tana dariya tace " a tabbatar an samowa su Nawar k'anne,
danna lura mijin naki sharp shooter ne, daya hau ake harbuwa, yayi wuf zai rik'e ta yana dariya, tayi saurin shigewa part d'inta tana dariya,
basu dad'e da isa Airport ba jirginsu ya d'aga zuwa Taraba, a Airport d'in Taraba suka iske mota na jiransu,
murna fal ta cika Neelah yau zataga Abpa da Dada, kanta kwance saman kafad'arshi, tana bin hanya da kallo,
da sauri ta d'ago kanta mamaki ya cika ta, ganin shinfid'add'i'yar kwalta shinfid'e a hanyar k'auyensu,
anyiwa ruwan rafinsu dayake haurowa gada titin yabi ta kan gadar, anyi manya-manyan kwalbati (hanyar ruwa),
ga street light, mamaki bai gama kashe ta ba sai da taga gaba d'aya Sunkhanni babu bukka sai gidajen zamani,
masu kamar estate, irin na Barhim, Fatima Shema, da Sardauna, na Katsina State, irin wad'anda kwankwaso yayi a jahar Kano, kowanne gida 3 bedrooms plat ne, da kitchen, da bathroom, gidajen sunyi kyau sosai,
ga wutar lantarki da ruwan fanfo an kai musu, da makarantu boko da islamiyya, tun daga primary har secondary,
da babban masallaci, da asibiti, anyi mordernizing k'auyen ya zama tamkar babban birni, kanta ta d'aga ta kalli Neehal tace " anya kuwa Sunkhanni ne nan?
Yaa shafa kanta yana murmushi yace " sosai ma kuwa, kuka ta fashe dashi had'i da d'ora kanta saman k'irjinshi,
tana cewa " nasan kune, nasan kune kukayi komai, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Ubangiji yasa kufi haka Alla.....!,
ya d'ora hannu saman lips d'inta had'i da cewa "shhhhhhh! ya isa haka,
yi shiru kada su Abpa su ganki kina kuka ko?
Ya fad'a yana goge mata hawaye, ta d'aga mishi kai, hawayen farin ciki na gangarowa daga idonta,
" please a zagaya dani naga garin kafin muje gida, ba musu yayiwa driver umarnin ya zagaya dasu,
Neelah ta fahimci duk wanda ke garin an bashi gida d'aya, harda masari marasa aure, anyi musu babbar kasuwa,
wacce itace zata zama center kasuwanci a gaba d'aya k'aramar hukumar Hard'o-koa'la,
gidan Abpanta yasha bam-bam da saurin gidajen danshi harda bene, ta gane nan ne gidansu bayan driver yayi parking a k'ofar gidan,
ta fito jikinta a sanyaye zata shiga gidan, daga bayanta taji an kira sunanta, ta juya a nutse,
ganin gaba d'aya jama'ar garin ya bata mamaki,
" mun zo neman gafararki ne a bisa abubuwan da mukayi miki a baya, dan Allah ki yafe mana, mun san ke alkhairi ce a gare mu,
kuma haihuwarki a cikinmu abin alfahari ne garin nan, muna farin cikin kasancewarki 'yarki, k'anwarmu, sannan 'yar uwarmu,
dan Allah ki yafe mana, Malam Liman da Dada sun yafe mana saura ke, kasa danne kukanta tayi, ta fashe da matsanancin kuka tana cewa " Alhamdulillah, Allah kaine abun godiya, na yafe muku nima ku yafe min, a hankali Neehal ya tallafeta ya shige gidansu Abpa,
bayan sun ci abinci sun natsa Abpa ya bata labarin komai, yace Neehal yayi-yayi dashi ya koma birni yak'i, ganin haka yasa shida Naufal da mahaifinsu sukayi musu wannan aiki,
yanzu haka ma suna shirin bud'e company a garin saboda samarwa mutanen garin aikinyi, kuma sun fad'a mishi sunanta za'a sakawa companyn,
Abpa da Dada sukayi ta saka musu albarka suna yi musu addu'ar neman tsari, bayan anyi sallar ishaa Abpa da Neehal suka shigo tare,
sai da suka ci abincin dare suka d'an tab'a hira kana Neehal ya kalli Neelah yace " muje ko?
"Ina tace tana kallanshi?
"Gidanmu mana, ya bata amsa yana kallanta, " ba'a nan zamu kwana ba?
Batare da yayi mata magana ba rik'e hannunta, suka fita, ya sanya hannu ya rufe mata ido, sai da suka k'arasa inda zasu sannan ya bud'e mata ido yace " ga inda zamu kwana nan,
a hankali ta bud'e idonta ta kalli inda ya nuna mata, baki ta bud'e saboda mamaki tace " wow! dama ba'a rushe wannan bukkar ba?
"Tab! waya isa ya rushe wannan bukkar idan ba Allah ba, ko kin manta nan ne tushe mafari?
"A nan muka fara rayuwa, ya rad'a mata a kunne, sosai bukkar ta burge Neelah ganin yadda aka gyara ta, aka mayar da ita irin bukkokin turawa na k'asar waje,
irin na 'yan China, bukkar tayi masifar had'uwa, kan Neelah bai gama kuncewa ba sai da ta shiga cikin bukkar,
tsarin bukkar irin tsarin wajen shak'atawar turawa ne na bakin ruwa,
bakinta bud'e tana bin cikin bukkar da kallo komai yayi mata, musamman cycle bed d'in dake ciki,
a hankali ya tako ya rungume ta ta baya yana lasar kunnenta yace " me kika tuna?
"Abubuwa da dama ta bashi amsa, tana murmushi, kunnenta ya d'an cija had'i da hura iska, yace " kamar me?
Yadda yayi mata ya hana ta magana, a hankali ya soma canja salon zuwa wani irin yanayi,
ya zura hannunshi ta k'asan rigar yana shafa cikinta, had'i da yin wasa da cibiyarta, while yana tsotsar wuyanta, a hankali ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya,
ganin sak'onshi na isa inda ya dace yasa guge zip d'in rigarta ta fad'i k'asa, cikin salo yana yi mata tafiyar tsutsa a bayinta,
ya zare mata bra, had'i da juyo da ita ya had'e bakinsu, ya shiga tsotsar lips d'inta, yana tsantsar harshenta,,
yayinda hannunshi ke kan boobs d'inta yana aiki murza nipple's d'inta, a hankali yayi k'asa da bakinshi yana lasar duk inda yaci karo dashi, ya tsotse wuyanta tas,
kana ya d'ora bakinshi kan boobs d'inta yana lasa had'i da tsotsar su, while d'aya hannunshi yana shafa sassan jikinta,
bayanta , cibiyarta, cinyoyinta da mararta, a hankali ya mayar da bakinshi cibiyarta zuwa mararta yana lasa,
sosai Neelah ta gigice ta fita daga hayyacinta, ta soma nishi, sai da ya gama tsotse mata ko'ina tas ya lashe ta tsaf, kana ta kwace kanta ta soma gigita shi, ta shiga tsotsar shi, tana sucking nipple's d'inshi,
yayinda d'aya hannunta ke murza d'aya nipple's d'inshi,
a hankali ta mayar da bakinta kan sandar girma ta soma yi mishi sucking tana murza shi, sun dad'e suna hot romance kafin su zube saman bed, suka fara raya sunnah , Neehal ya zage yana kashe arna,
sai da suka d'auki lokaci kafin buk'atar junansu ta biya, suna kwance saman bed, sun rufe iya k'ugunsu da blanket,
kan Neelah saman k'irjin Neehal, tana shafa kwantaccen gashin k'irjinshi, while hannunshi yana shafa kanta, yace " bazan tab'a manta rayuwar da mukayi a d'akin nan ba,
ta d'ago idonta tana kallan kwayar idonshi tana murmushi tace " kasan me?
"A'a, " a lokacin mugun tsoranka nake ji, musamman idan naga ka bud'e min idonka kana yi min hayagaga, yayi kyakkyawan murmushin shi me bayyanar da kyan fuskarshi,
yace " shiyasa kike zagi na da fulanci ko?
Ta zaro ido had'i da cewa " ni?
"Kwarai kuwa ke!, ai Mamy ta fassara min abinda kike cewa, cikin mamaki tace " taya akayi Mamy tasan abinda nake fad'a,
" hummm ai duk abinda kike fad'a ina rubutawa, baki ta turo had'i da cewa " to ba kai bane a lokacin baka da aiki sai yi min fad'a ba,
" kin san me?
"A'a, wallahi tun a lokacin na fara sanki, sai na k'aryata kaina da abinda nake ji a zuciya ta, nayi zaton wani abu ne kawai,
shiyasa zakiga a lokacin ban iya dukanki ko kinyi min rashin kunya, sai na taho gadan-gadan, zan dake ki sai na kasa, baki ganin wani lokacin sai na d'aga hannu sai na fasa?
"Duk lokacin dana d'aga hannu zan dake ki sai naji gaba na yana fad'uwa, zuciyata ta tsananta bugawa,
" ni kuma a lokacin burgeni kake yi sosai, sai naji ina san na rink'a kallanka, naji ina san nayi maka magana koda zaka dake ni,
shiyasa zakaga a lokacin ina yawan tsokanarka, amma please lokacin daka fara sani na 'ya mace me kaji?
"Hummm Neehal yace had'i da sauke ajiyar zuciya, sannan ya cigaba da cewa " wallahi bazance miki ga takamaiman abinda naji ba,
na dai ji jikina ya mutu sosai, na rink'a ji na wani iri, dan nafi 1 month ban dawo normal ba, " to a Lagos tun yaushe ka warke?
Tuntsewa yayi da dariya sosai sannan yace " wallahi na dad'e sosai dan nakai wajen 2 months da warkewa, duka takai mishi cikin shagwab'a tace " to amma meyasa kak'i nuna min ka warke?
" Kawai ji nayi ina san zama dake, ban san rayuwa dake, " kai my heartbeat, shine kak'i nuna min, tab! ya za'ayi na nuna miki bayan kina yi min wanka da aski, hauka nake yi na nuna,
ta mik'e zaune tana dariya tace " au dama saboda haka kak'i numa min?
"Eh! mana yanzu ma idan da hali na ina buk'atar k'ari, ya k'arasa maganar had'i da d'age gira d'aya ya kashe mata ido d'aya,
yana rik'o ta, ta zame jikinta tana dariya tace " tab! dawa d'in?
"Dake mana, baki ji abinda Auntynki ta fad'a miki ba, tace ayiwa su Nawal k'anwa kin kuma san mijinki sharp shooter ne, ya fad'a yana lasar lips, ta d'auki pillow ta jefa mishi tana dariya,
shima ya jefa mata, suka shiga wasan jefe-jefen pillows, suna guje-guje suna zagaye bukkar cikin tsantsar so da k'aunar junansu,
yayi caraf ya rik'e k'ugunta da duka hannayenshi ya d'agata sama suna dariya, ta had'e bakinsu, cike da zallar madarar so.
Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
Tammat bi hamdulillah
Komai yayi farko yana da k'arshe anan na kawo k'arshen littafin Rabo Ajali, Allah ya nufa an fara lafiya an gama lafiya, kurakuran dake ciki Allah ya yafe mana, Ubangiji ya bamu ladan dake ciki gaba d'aya, nagode kwarai da had'in kan da kuka bani, nagode da soyayyar da kuke min, zanyi kewarku sosai masoyana, Allah ya barmu tare, Ubangiji yabar so, k'auna da zumunci, ina fatan wanda duk na b'atawa ta dalilin littafin nan ya yafe min.
Sai mun had'u daku a sabon littafi na *SAKI RESHE...! (CIGABAN GADAR ZARE)* amma shi na kud'i ne duk me so zata biya 300, in sha Allah daga kan Rabo Ajali na gama free novel, gaba d'aya littattafaina zasu koma na kud'i akan farashin 300, nayi novels biyar kyauta, Allah ya bamu ladan abinda akayi a baya, but ku sani littattafan Hauwa A Usman Jiddarh sun koma na kud'i daga kan Rabo Ajali.
Bye I gonna miss you dear❤️❤️❤️❤️
18/4/2020
MOMYN ZARAH