CIWON 'YA MACE

Chapter 9

by @fadilalamido

CIWON 'YA MACE

           By

    Fadila Lamido

   ADABI WRITER'S ASSOCIATION


   Page 17-18

Kallon kallo ne ya shiga tsakanin Poul da Mamma alokacin da ya tsaya a tsakiyar dakin, shigar da ke jikin su ya bi da kallo, ganin kaya irin na Hausawa ajikinsu ya cika da mamaki, Mamma ko tun da ta kalleshi sau daya ta dauke kanta tare da cigaba da tufke wa Helen kai, daf da su ya karaso tare da fadin, "Ina kuka je kwana biyu?"

  Cikin daure fuska sosai Mamma ta ci gaba da abin da take batare da ta bashi amsa ba, dauke kansa yayi ya maida wurin Helen domin wannan shine karo na farko da yaji nauyin sake jafawa Mamma tambaya, "Helen ina kuka je?"

     "Sunanta Zainab." Mamma ta fada fuskarta daure tamau. Cikin Sauri ya maida kallon shi ga Mamma, "Bangane ba Mamma" Poul ya fada hankalin shi a tashi tare da ware idon shi waje yana Kara bude kunnen shi.

    Cike da karfin haki Mamma tace "Eh abin da ka ji haka ne, ni da ita mun karfi musulunci yau...."

 Me ya sa mamma? Poul ya fada cikin tsananin tashin hankali tare da kara matsawa daf da Mamma ya na ware idon shi waje. "Idan bazaka iya za ma damu ba zamu tafi kauye mu zauna"

 Mamma idan wasa kike yi mini ki bari, hakan bazai taba zama gaskiya ba, idan kuma kin yi ne dan ki bata min rai wannan ba shi bane mafita, dan idan har kuna bin wannan addinin bazamu zauna inuwa daya ba, kuma bazan fita in nemo kudi inci da ku ba"

 "Poul babu wasa a idona, ni da Helen mun karbi musulunci, sabo da hankalina ya fi nutsuwa dashi, yanzun hankalina ya kwanta, na samu lafiya"

Sosai ran Poul ya baci har kana ganin wasu irin jijiyoyim da ke cikin kanshi saboda tsananin tashin hankali, idon sa kuwa wani irin ja yayi irin wadda be taba yi ba, cikin tsananin fushi ya ce, "Bazan zauna da ku ba, na ji ke da helen kun canza addini dan ku bata min rai, idan ni ne na mata miki rai ba wan ne mafita ba, da ga yanzun ko me kuke so ku fada min zan muku, amman bana son musuluncin nan, ko a mafarki bantaba tunanin zaki yi haka ba Mamma...."

 Poul ko me zaka ba ni bazan taba barin wannan addinin ba, rabon da na samu nutsuwar da na samu yau na jima sosai, bazan ma iya tunawa ba, na gane babu wadda ya kamata na dogara dashi sai Allah wadda ya halicceni ya halicci bayin da suka taimakeni; batare da mun hada komai ba, na samu nutsuwar da na rasa ko rabinta a gareka"

   Wanni irin kallo poul yaiwa Mamma, bayan ya gama kare mata kallo ya ce, "Shikenan, ku tattara duk wani abu da kuka san da gumina kuka siya ko na saya muku, ku aje min sannan ku barmin gidana, bazan sake zama tare da ku ba, bana son in sake ganinku a rayuwata.

 Bakin sa Mamma ta ke kallo a lokacin da ya ke furta wannan kalamin, sosai ya ke bata mamaki nan ta tuna yadda mazan gidan su Nur ke mutunta iyayensu, sannan ta tabe baki tare da daure fuska sosai ta ce, "Dare yayi amma idan mun wayi gari lafiya da safe zamu barmaka gidan ka."

  Kallon Mama Poul yayi sannan ya juya ya fita adakin, afusace ya ke tafiya tare da sake sake, wata zuciyar ce ta ce, "Ka korasu mana a daren nan" yin wannan tunanin ya sashi yaja ya tsaya, sannan ya waiga ya kalli hanyar tare da tuna fuskar Mamma, besan me yasa ba haka kawai ya ke ganin fuskarta a yau ta mashi kwarjinin, ita kanta da alama cike take da kwarin guiwa, dan haka yaji Sam bazai iya kallon idonta ya ce sai sun fita a daren nan ba, saidai zuciyarshi cike take da bacin rai har ya isa dakin sa, Yana shiga yasa makulli ya rufe dakin.

                      *****

Washegari da safe Poul ne zaune saman motar sa idonsa jawur, da ka kalli fuskarsa kasan ya na cikin baccin rai, tun da ga nesa ya hango budurwar yariya cikin Hijjabi har kasa, jajayen idonshi ya kara bazawa afili ya ce Nurr ce, ganin tana Jan akwati ya ji faduwan gaba afili ya sake cewa, "Wato akwai sa hannun yariyar nan aka shirya min wannan abin, idan ba haka ba me take a gidan nan? Yaushe ta shigo min gidan? Tun da sauran duhu nake zaune a wurin nan" Sakkowa yayi sama motar a fusace ya ke takawa jikinshi har tsuma yake, waige ya shiga yi domin neman madoki domin mudin yace zai dake Nur da hannu tana iya mutuwa, ganin babu wani abu da zai iya dokan Nur din dashi ya maida hankalishi wajen da suke tahowa, sai yanzun ya lura da dattijuwar da ke binta a baya, itama sanye cikin Hijjabi har kasa, bayan ya kare mata kallo ya ce "Mamma?" Adaidai lokacin da Mamma ke amsawa ya juya ya kalli yariyar da ke gefenta, Helen ce tsaye badan fuskarta ba kaikace Nur ce tsaye, sosai ya zuba mata ido tsayon lokaci sannan yai saurin saka hannun sa ya rike hijjabinta tare da fadin, "Wannan abin na Nurr ne ko?"

Da ga Helen har Mamma sun yi mamakin jin sunan Nur a bakin Poul, Mamma ce tai saurin girgiza kai tare da fadin "Banata bane, masallacin da mukaje jiya acan aka bamu."

 Lumshe Ido Poul ya yi sannan ya jawo Helen ya kai hijjabin hancinshi ya shinshina, dagowa yayi ya kalli Helen sannan ya cewa, "Na Nurr wanna, kenan gidan su ta kaiku?" Wannan karon ma cikin sauri Mamma ta girgiza kai alokacin da Poul ya ke cewa acikin zuciyarshi, "Amman zan nunawa yariyar nan ta yi kuskure mara kyau a rayuwarta, barinta da na ke tana shigowa gidan nan shine ya bata damar dauke min uwata da kanwata? Bazan taba bari hakan ya tabbata ba muddin Ina numfashi, saina koya mata hankali, da ma na lura da yariyar nan, akwai tsata me yawa a idonta, ko ma meye zan aikata domin in ga Mamma tabar wannan addinin da take kokarin jefa kanta acikin" zuwa can ya dago ya kalli Mamma cike da kwarin guiwa ya ce, "Ina zakuje?" Daure fuska Mamma ta yi sosai sannan tace, "Kauye, Ina ce kace in dai muna yin addinin musulunci sai dai mu barmaka gidanka?" Da sauri Poul ya dukar da kanshi kasa sannan ya ce, "Na sake tunani, zaku iya zama abin ku" Cike da mamaki Mamma ta kalli Poul, sanyin da taga yayi abin yai matukar daure mata kai, dan haka ta ce, Na gaji da zaman wulakanci da na ke yi a gidan nan idan har kasan zaka cigaba da mini abin da kake gara na koma kauye."

Lebensa na kasa Poul ya cize sanna ya ce, "Zan kiyaye." Karake maganar ya yi tare da amsan akwatin dake hannun Helen sannan ya juya cikin gidan, Mamma da Helen wadda ayanzun ta koma Zainab kallon juna suka yi sannan suka bi bayansh,i sai dai har yanzun Mamma ta kasa gamsuwa da sanyin da ta ga jikin Poul din yayi.

                        ******

Nur ce durkushe ta na wanke kayan makantarta bayan ta gama ta dauraye, bayan gidan ta nufa domin shanyawa, hannunta ta daga sama da nufin shanya hijjabin islamiyyarta, cikin sauri ta saki hijjabin ya fadi kasa, tare da waigen falin da ita daya ce tsaye a gurin, diriricewa ta yi gaba daya tana kokarin fita hayyacinta, daker ta iya lalubo jarumta ta nufi windows din dakunnan dake bayan gidan na su, ahankali take bin sautin har ta isa bakin window da sautin ke tashi, wani dutse ta dauko tasa a gurin, sannan tahau kan dutsen ta leka, saidai labulen rufe ya ke dan haka ta kasa kunne, tabass da ga nan sautin ke tashi, dan haka ta sauka akan dutsen a guje ta nufi cikin gidan tare da kwalawa Mamy kira.

  Saukowa a gado Mamy ta yi da sauri tana dafe da kanta dake sara mata tun safe, jin kiran da Nur ke kwala mata hankalinta ya kara tashi domin tasan babu lafiya.

  Aunty Saratu dake kicin ko fitowa ta yi tana cewa, "Nur mene ne haka, kin dai san bata jin dafi ko?" Zaman dirshen Nur ta yi a dakin tana maida numfashi, da ga Mamy har anuty Saratu afirgice suke tambayanta me ya ke faruwa?

   Cikin tsananin haki take cewa, "Mamy, Aunty Saratu ku je dakin Yaya Abdallah ku gani..."

  Anuty Saratu ce tace, "Meye a dakinsa? Me zamu gani acan din?"

"Mamy ku je ku gani wallahi ku yi sauri."

Mamy ce ta kalli Aunty Saratu sannan ta ce, "Saratu jeki gani"

"A'a, yanzun fa ya min sallama baya gidan nan, ina ga fa firgita take yi" juyawa ta yi ta kalli Nur ta ce, "Ke! ki nutsu dallah ki yi magana, mene ne kika gani a dakin?" Cikin numfarfashi Nur ta ce "Mace ce Yaya Abdallah ya shigo da ita cikin dakinshi...."

  Hannu Mamy ta sa ta dafe kirjinta tare da runtse ido, cikin daga murya ta ce, "Mace! Acikin gidan nan?" Ganin in da ta runtse ido tana dafe da kirji Aunty Saratu tabita da kallo cike da fargaban kar ciwonta ya tashi, ganin Mamy na kokarin ficewa a dakin afusace Aunty Saratu tai saurin riketa tare da cewa, "Karki je, ki bari ya fito dan Allah."

Bige hannun Aunty Saratu Mamy ta yi tare da cewa, Bazan iya tsayawaba Saratu, wannan iskancin har ina, tun munajin waiwai ace har takai acikin gidan nan yake damar da zai mana haka."

"Koma mene ne karkiji dan Allah, kindai san baki da lafiya, ki bari ya fito, ko Kuma a kirashi a waya."

 "Sakeni ina zuwa." Mamy ta fada tana kokarin zamewa daga rokon da Saratu tai mata. "Bazan sake kiba, ki yi hakuri bari na kirashi a waya"

"A dai dinga jin tsoron Allah, abin da baka son a maka kar bari amawa wani, ta yaya muna cikin gidan nan zamu bari haka na faruwa? Ina yar mu haka ta faru a kanta zamuji dadi? Saratu muna cikin gidan nan kuma kice wai in bari ya fito? Cikin sauri Saratu ta saki Mamy jikinta da sanyi sosai, afusace Mamy ta fice yayin da Aunty Saratu tabi bayanta.