AZIZAN BABA

Episode 12

by @zinariya0102



_________________Ma sha Allah, Allah ya tsare hanya, ke AZIZA ina kuma za ki je,bayan yanzun nan Aminu ya ce ki zo kuje ku gaida iyayenki ki ka ƙi?" AZIZA ta ci gaba da ɗaure mataccen silifas ɗinta, ta na faɗin bikin ƴa ta zanyi yau, shine zanje in gayyato su Ai, da yamma su zo" BABA ya ce" to kar ki sa wannan takalmin ba ki gani ya mutu,ga sabo can haba AZIZA so kike a zageni ace bana kula da ke?" AZIZA ta ce "ni wannan nakeso ba na son sabon" Inna Gaji ta ƙwace talmin ta hau faɗa" to aikuwa ba za ki sa wannan mataccen takalmin ba, kuji ƴa da neman talaucin masifa" AZIZAN BABA ta kwaɓe fuska, BABA ya ce" me ye haka ne Gaji, ba ta takalminta wai meyasa ba kusan illar zubar hawayen maraya ba?" Inna Gaji ta ce"wallahi sai dai tayi kukan jini, ga yanda aka yi mata kwalliya saboda Allah kuma a barta ta sa wannan takalmi, ba ri ka gani, ta shige ɗaki da shi ta ɓoye.



AZIZA ta fara hawaye BABA ya hau sababi da bala'i sai an kawo takalmi, Baba Tabawa ce ta ɗauko wasu har guda uku masu kyau ta ce" sanya wani anan ungo goma nan idan kin fita ki sai alawa ma" AZIZA ta kalli kuɗin sannan ta ce "ni ashirin nakeso" BABA ya hau lalubar aljihu ya ɗauko ashirin ya ce" ga shi, du ki haɗa ma AZIZAN BABA ƴar gatan Mazoji rainon Tabawa da Gaji hahh ma za sanya ki tafi" 

Dariya ta sa tana sa wani plate baƙi na danƙo mai kyau ta karɓi talatin ɗinta tayi waje a guje.



Baba Tabawa ta ce"kai yaro yaro ne, Allah ya raya mana zuri'a" BABA ya ce "amin ya Allah, a ɗumamin ruwa ina son zan je faɗar Maigari anjima" Baba Tabawa ta ce"ai akwai ruwa a kan wuta" Inna Gaji ta fito, "kamarya akwai ruwa akan wuta, ku ji mata, ke kika ɗora ko kuwa girki na ne da dole ni zan ba shi ruwan wankan?" Baba Tabawa ta ce"haba Yaya dan kin bashi ruwan ai ba laifi ba ne" BABA ya ce "ku dai Allah wadaran wannnan hali tun da ƙuruciya kuke wannan kishin har tsufa mtsww Allah ya kyauta" Inna Gaji ta ce" eh da tsufan ma me aka fasa, tunda tana iya satar hanya ta shiga tukara wallahu babu wanda zan bawa ruwana, amfani zanyi da shi" ta koma ɗakinta.


Tun Yarinta Aisha(Inna Gaji) take da masifar kishi, duk da Maryam (Tabawa) farkon zuwanta ita ma haka take, sai daga baya ta ajiye nata ganin ta jima bata haihu ba, sai take bin Inna Gaji sau da ƙafa, amma wani lokacin dole sai anyi rigima.



Baba Tabawa ta ce "ai shikenan" ta ɗauko tukunya ta ɗora a murhu dan bata son ta sauke a rishon Inna ta hau faɗa, yau tunda Tabawa ta ƙarɓi girki sai Allah.


Tana ɗorawa ta hau gyaran gidan BABA da tsokana ya kira Tabawa "Tabawa, amarya ba kya laifi zo ki gani" Baba Tabawa tayi murmushi, duk sai ɓacin ran ya tafi ta ce"to Malam ta ajiye tsintsiyarta ta nufi ɗakin BABA,babu abinda zai nuna mata kawai dan ta huce ne.Yana tausayinta musamman idan yaga ƴaƴan Inna Gaji sun zo, tai tayin haba-haba da su, suma sun ɗauketa tamkar uwa, sai da uwa uwa ce, dole wani abun wane ita.



Inna Gaji ta ɗaga labulen ɗakinta ta ce

"Wallahi aka zalunce ni bazan yafe ba, daman ai da biyu ka ƙara auren sai da muka shekara ashirin ka jajiɓo min kishiya, ai dai ko yanzu ita ma tsufan ya tawo aikin banza kawai mtsww" abin ne ya bawa Tabawa dariya dan ita bata ga abin kishi ba, in banda Malam ɗin me take da shi a gidan ba ɗa bare jika.

BABA ya ce "Tabawa nasan kina haƙuri da yayar nan taki, dan Allah ki ci gaba da yi kinji, kinsan halinta da kishin jaraba, ko me takeyiwa yanzu kuma oho" Tabawa tayi dariya ta ce"hmm Malam kenan gani take har yanzu ina da sauran ƙuruciya shiyasa take, ban da abinta ina ma abun yake"BABA ya ɓantari goronsa ya ce" ke dai bari kinsan dai har yanzu da saurana ko,namiji ai baya daina haihuwa sai dai kawai a bari saboda zuri'a sun taru" gaba ɗaya suka sa dariya.



Dariyar da ta ƙara ƙular da Inna Gaji, sai da BABA yaga Tabawan ta ware sannan ya ce "duba min ruwan in samu in fita kafin su Aminu su dawo" 

Kai masa banɗaki tayi ta sanya masa kujera da kwandonsa na wanka, ta ce"na kai Malam" Baba ya dogaro sandarsa ya nufi bayi.


Inna Gaji ta ce" ke dai Tabawa anji kunya wai wannan tanƙwararren mutumin kike yi wa mtsww" Tabawa ta yi dariya ta ce"to ai yaya dole in ji da shi, tunda mijina ne, ki daina min irin haka dan Allah, shiyasa wani lokacin banaso AZIZAN BABA ta fita a gidan nan nasan ganin idonta kina iya bakinki" Inna Gaji ta ce " ki dai dinga tausaya masa dan ba shi da ƙarfi, kullum shine cikin ciwon kwankwaso dan jaraba sama da shekara talatin da auro ki amma kinƙi ƙoshi sai ka ce, wani sakamako kike bayarwa" 

Sanin goranta mata haihuwa tayi, ya sa Tabawa fashewa da kuka.


Ta nufi ɗaki tana ta kuka, Inna Gaji ta ji daɗi dan tarama baƙincikin da suka tusa mata ɗazu da suke dariya ita da Malam a ɗaki.

Duk da tasan ba wata tsiya BABA yake yi da su ba, amma kishin nan yaƙi barin zuciyarta ganinTabawa ta fita ƙuruciya sai tayi ta zargi. 


Sai da BABA ya fito ta kintsa ya sa turarensa sannan ya fito, ya na faɗin "to ni zan tafi, me za'a aiko a kawo muku?" Baba Tabawa ta share hawayenta ta fito da fara'a ta ce" naga su Siyama na son fura, a kawo kindirmo da sabuwar fura, sannan a siyo min naman shanuwa ayi musu shinkafa irin ta su, a kawo min wannna ganyen mai kama da kankana, yauwa yama sunan shi kabejo ko"

BABA ya ce "nagane, duk zan sa Yaro ya kawo, dan Allah kar ki ƙara kuka" 

"Kuka kuma Malam, ni kam banyi kuka ba" girgiza kai kawai BABA yayi ya ce"tun kina ƴar haka nake tare da ke Tabawa babu abinda ban karanta naki ba, nasan kina haƙuri dan Allah ki cigaba da yi kinji Allah yayi miki albarka"  

Amin adawo lafiya.



Inna Gaji ma ta fito ta ce"a dawo lafiya" 

Tabawa ta ci gaba da aikinta, can kuma sai Inna Gajin ta fito ta kama mata, kamar yanda sukeyi (daman zaman tare ya gaji haka) Baba Tabawa ta ce"Yaya nifa inaga da AZIZA zata yi hankali da mun barta ta bi Alhaji birni" Inna Gaji ta ce" hmmm Tabawa kenan, kin manta wace ce Hadiza, bata ƙaunar mu, ya za'ayi in ɗauki jikata in bata,Allah ya kyauta"

Baba Tabawa ta ce"yanzu shikenan mun sallama mata Alhaji, nikam gaskiya ba zai yuyuba, kinga fa ba ma samun zuwa yake sosai ba sai dai kullum ya kira salulan nan, ni da ɗana ne dole ya dawo nan wallahi" 

Inna Gaji ta harareta "eh saboda kina baƙinciki Allah ya watada ɗana ko, daman ke ba'a wanyewa da ke lafiya, abun kuma ya bar kaina ya koma kan Ɗansu ko"Tabawa ta ce"Allah ya baki haƙuri Yaya, ni dai daman shawara ce" to banaso ki riƙe tsugudidinki" 

Ta sakar mata aikinta ta koma ɗakinta.



Haka suke yau ayi daɗi gobe ayi tsiya, indai Tabawa ta larɓi girki, shikenan Inna Gaji ta dinga jin haushinta kenan.


(Kai AISHATU ku rage kishi)..


AZIZAN BABA na fita ta nufi bakin kan labi, inda yawancin yaran da ba sa zuwa makaranta suka fi zama can domin yin wasa, sahara tafi yawa a wajejen.


Su Ai'n Baba mai kalwa, da Haule da kuma, suna kan yashin kowa yana wasa da shi, cikin nishaɗi, AZIZA na ganosu ta washe baki ta ce"ahe kuna nan, kuwa kai Saminu dallah matsa daga cikin mata, banza kawai" yaron da ta kira da Saminu ya ce"ba za'a matsa ɗin ba, daga zuwanki za ki kama ni da tsonaka"

Bantan ubanka,AZIZA ta cakumi rigar Sammani ta keta,ta Faɗa ne ya kaure tsakaninsu Saminu ya yaga mata tata rigar, Ai da Haule na ta tsalle suna musu waƙar, ku casu arna ku casu ku casu ba mai raba ku" AZIZA tayi nasarar kayar da Saminu ta hau shi da duka da naushi.


Da ke namiji ne shima ya dinga ramawa a hakan, su Ai suka je suka ce "ku tsaya-ku tsaya, gaskiya kai Saminu ancuce ka" AZIZA ta ɗaga shi tana haki, gami da zagin Saminu.

Ƙasa haule ta ɗebo hagu da dama ta ce" Saminu ga ta tsiya gata arziki" ta nuna ta tsiya da ke hannun hagu ta nuna ta arziki da ke hannun dama.


Saminu ya zubar da ta tsiya, ta koma kan AZIZA ta nuna mata ta tsiya da ta arziki, ta zubar da ta tsiya, Haule ta yiwa AZIZA raɗa a kunne , kai AZIZA ta girgiza, a ka kuma kaurewa da sabon faɗa, shammatar Saminu tayi ta janyo ƙafarsa tim ta yarda shi a ƙasa, ta kama mafitsararsa ta dinga murɗewa, kuka Saminu ya sa yana ihu zai mutu, ganin haka ya sa su Haule murna, sannan suka raba faɗan.


Saminu yana kwance yana ta kuka, ya riƙe mafitsararsa, su Haule suka ce" ta so mu gudu" AZIZA ta kafe "babu inda zanje,uban wani ne ya ce ya takaleni"Malam Gambo mai rini ne ya zo wuje wa, dan rana ta take kowa ya fita harkokinsa, ya ga Saminu na kuka, ga AZIZA a tsaye tana ta bala'i.

"kai!kai ya ya me ya faru?" Haule da ta fisu girma da wayo ta ce" faɗa akayi"

Kama yaron yayi ya na ɗago shi gami da karkaɗe masa jikinsa, ya na masa sannu, Saminu ya ce "ta cire min abun fitsarina" wani mugun bugu zuciyar Gambo tayi, da sauri ya ce "innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun" ya na saɓule wandon yaron, babu abinda ya same shi, su AZIZA da ƙawayenta suka diba a guje.


Gambo ya dinga faɗa, yana faɗin meya kai shi cikin mata, hanyar gida ya sa shi, ya wuce yana yi wa AZIZA fatan shiriya.


AZIZAN BABA da ta ke haki ta tsaya ta ce" amma Haule kin iya mugunta, daman haka kike faɗa da maza?"

Haule ta sheƙe da dariya ta ce"ke nima ingaya miki ji nayi, Innar Habu tana faɗawa Innata, lokacin da za'ayi mata kihiya, Baban Habu yana dukanta,nan ta kama za ta cire shine fa ya suma, har aka je gaban Maigari, aka ce ya haƙura da auren, da ya ƙi haƙura, tun daga lokacin ya ke fitsarin jini, har sai da aka kai shi asibitin nan, na fatalwa, masu sa likkafanin nan"

AZIZA ta ce"na shiga uku Haule fitsarin jini yanzu Saminu zai dinga yi" Haule ta ce "iyi mana" AZIZA sai tasa kuka, duk rashin jinta akwai ta da tausayi.

"Wallahi ke kika ce in kama nan, ba ni ba ce"Haule ta ce" to ba taimakonki nayi ba, ke wallahi daman haka kike i......Mugun nashi taji a cikinta, AZIZA ta kamata da faɗa tana yi tana ba ni na sa shi ba, ke kika ce in kama nan, mutanen da ke kusa suka je rabasu, ganin yanda AZIZA ta ke kuka, ta na faɗin ita ce ta ce na kama nan, Haule ta gudu kar a ji abinda tayi.


Anas ya kwasa aguje zuwa fadar Maigari dan faɗawa BABA abinda ke faruwa."BABA,

!BABA ga shi can an taru acan ana faɗa da AZIZA anyi mata duka sai kuka take yi" jikin BABA ya hau rawa,ya na faɗin"a ina, wacce ƴar bantan ubance, Allah gafarta kana dai ji ko?" Maigari ya ce" Malam Inusa aje a tawo da su" angama ranka ya daɗe, ɗan aiken maigari suka nufi wajen, BABA ma ya tashi ya na dogara sandarsa tsabar sauri takalminsa da na Malam Liman ya sa zai tafi,Maigari ya ce" ka jira yanzu za su iso nan BABA" 

Ko sauraron Maigari bai yi ba ya bi bayansu yaro.



Kafin ya ƙarasa har an tawo da AZIZA tayi kaca-kaca babu takalmi dan yana can garin gudu ta zubar da su, "Idan na yarda kafuri nake, wace ta jibgeta" Ai ta ce "ba dukanta akayi ba faɗa sukayi da Haule da kuma Saminu" ya ce "mu je fadar yau za'a ga gatan AZIZA ba dai Aminu ya zo ba alkur'an sai mun kori ko wanne shege a garin nan" AZIZAN BABA ta ce"BABA wallahi ba ni na sa Saminu fitsarin jini ba, Haule ce ta ce in kama nan" sai ta kuma fashewa da kuka.


Ido waje BABA ya ce"fitsarin jini, na shiga uku ni Muhamuda AZIZA ya akayi?" Inusa ya ce"BABA mu ƙarasa rumfar maigari"ɗuuu da ƴan kallo aka ɗunguma gaban Maigari.


Ana zama sai ga Baban Saminu ya tawo kawo ƙara gaban Maigari ya tarar da AZIZA da BABA na nan, daman akan hakan ya zo.

Zama yayi yana zaunar da Saminu ya ce"Allah gafarta me AZIZA ta ke nufi da har zata iya kama zakarin yaro?"

"lah'ilaha'illahu....Gaba ɗaya fada ta ɗauka, AZIZA ta ce"wallahi Haule ce ta ce nayi" nan aka tambayesu abinda ya faru, kowa ya faɗa Ai ce shaida.


BABA yayi shiru jin abun ya fi ƙarfinsa, Maigari ya ce"Saminu fitsarin jini wai kake yi?" 

Saminu ya ce"a'a zafi na ji, kuma ya daina ma" anan BABA ya sami bakin magana, " kai wannan baƙinciki da hassadar da yawa yake, yanzu azo a ce wai AZIZAN BABA ta sa yaro fitsarin jini, to kai Zailani sai munyi shari'a da kai, ka ce fitsarin jini ta saka shi ko?"

Baba Saminu ya hau rawar jiki dan shi bai san zancen fitsarin jini ba, sai a bakin AZIZA da take kuka ta faɗa duk yanda akayi.


Ya hau ba da haƙuri yana faɗin " ba ni na ce ba, kawai na zo ne naji dalilin da ya sa ta kama masa zakari shi ne kawai wallahi BABA ba da wani manufa na zo ba" 

BABA ya ce" kawai ka ce AZIZAN BABA ta zama ƴar iska, tunda ga shi kazo jin ba'asi" 

Nan aka shiga neman Haule, wujiga-wujiga aka kamo ta, tayi tsuru- tsuru, zaneta akayi gaban maigari, aka ce AZIZA ta bawa Saminu haƙuri,nan fa ɗaya, ta kalli kowa a wajen BABA ya ƙara mata ido akan ta fece,ai kuwa ta ranta a na Kare, aguje ta bar wajen.


Kowa sai da ya dara hatta Maigari, nan aka samu aka sulhunta, Haule sai kuka take, duka biyu ga na AZIZA gana Maibulala.Daɗi sosai BABA ya ji, ya tashi yana yi musu sallama ya nufi gida dan ganin Iro ya kawo cefanan.



Tun da ga ganin yanda suke jagwab-jagwab a mota Abdul-AZEE ya san ruɓaɓɓiyar unguwa za su je.

Baya furta komai, sai kallon wayarsa da network ya ɗauke gaba ɗaya dan unguwar babu service.

Gwaggo Zainab na kulla kayan sana'arta manja da man ƙuli ta ji sallamar yayansu, cikin farinciki ta ce"oyoyo ga Yaya ga Yaya lale marbahabun sannun ku da zuwa" Daddy ya saki murmushi, ya na faɗin yauwa Maman Musa"suka  shiga ɗakinta tsaf da shi, dan Daddy yana taimakonsu sosai ba wani kaya ne a ɗakin ba, dan ta manyanta ita ma ba laifi, ta aurar da ƴaƴanta mata biyu sai samari da take da su da ɗan sha takwas da ɗan Ashirin sai auta ɗan sha shida. Umar, Muktar, da Aliyu.


Abdul-AZEEZ ma ya zauna akan tabarmar kabar da ta shimfiɗa musu akan ledar ɗakinta,duk suka zauna, ruwa ta ɗebo musu cikin kwano, ta fita maƙota ta siyo musu dambun tsakin masara ya sha zogale da mai ta kawo, sannu Daddy yayi mata ta zauna suka gaisa nan suka hau hira tsakanin ƴan'uwa abincin Daddy ya ci tare da su Mannir Abdul-AZEEZ kuwa ya ce azumi yake.

Kuɗi ya ba ta yace ta siyawa yara wanu abun, tai ta godiya har soro ta rako su, maƙota akai ta gaishe da yayan Gwaggo Zainabu.


Daga nan gidan Gwaggo Maimuna suka nufa nan ma ta karɓe su da murna, dake gidanta waje-waje nan, aka dinga shigowa ana gaisawa, kunsan ƙauye da kara, abinci aka dinga shigowa da shi kwano-kwano, sun ƙoshi haka sukayi godiya nan ma ya ba ta kuɗi ya kuma bata wasu ta rabawa maƙotanta,Abdul-AZEEZ kuwa tunda suka gaisa ya baro ɗakin ya koma mota ya zauna, gaba ɗaya ya tsani a ce wai waɗan nan sune ƴan'uwan Daddy'nsa.


Kwangwalan suka nufa da nisa sosai tsakanin Daura da Maikwangwalan, suna zuwa ana sallar azahar su Siyama ne suka shiga Daddy da Munnir da Abdul-AZEEZ da driver suka nufi masallaci dan akwai rijiya a wajen.

Ba tare da ƙyama ba Daddy ya zaga bayin da kowa yake shiga ya fito, ana ganinsa kuwa masallaci ya cika dam da mutane sanin duk sanda ya zo garin aka yi sallah da shi, to kuwa kowa sai yayi, samuwa, a masallaci, ana idar da sallah aka hau yi masa addu'a tare da iyalansa, nan ma ya ba da rapers ɗari biyar-biyar guda biyu ya ce a raba.


Su Siyama na shiga gidan suka tarar da Gwaggo Aliya tare sa ƴarta mai sunan Baba Tabawa(Maimuna) ana ce mata Ummi, ta zo gidan da ƴaƴanta, Gwaggo Aliya ta sansu sosai duk da ba zuwa ake da su ba, kuma suma ba wai sun cika zuwa gidan Aminun ba ne ganin yanda Matarsa ke kallonsu a raine.


Rasa inda zata ajiye su tayi, sai lale-lale take musu, ruwa ta kawo musu tare da tambayar ina Yayan yake? Siyama ce ta ce "sun tsaya a masallaci" nan ta aika ƴarta Husna, ta je shago da sauri ta siyo musu ruwan roba da lemon kwalba, Gwaggo Aliya mace ce mai son yi wa ɗan'uwanta kuɗin adashin mutane ta ɗauka ta bayar a siyo musu lemo.

Ruwa ta sa aka zuba musu, sukayi sallah, suna idarwa kuwa su Daddy suka shigo da sallama,kamar Gwaggo Aliya zata goya shi, tana ta murna ,hakama Ummi da yaranta,sai sannu da zuwa Kawu take faɗi, daɗi kamar ya kar ta, tana ta murnar rabo ne ya kawota gida yau.


Abdul-AZEEZ da ya ga gidan cike da yara, sai yatsina fuska yake, yana ɓata rai, Gwaggo Aliya da bata ɗaukar raini, ta ce "ni kam Yaya Abdul-azeez bai san ni uwarsa ba ce ba?" Daddy ya ce"hmmm ni bansan inda ya koyi wannna halin ba, kwata-kwata baya son magana wallahi" Gwaggo Aliya ta ce"to Allah ya kyauta, nan ma hira suke tayi, mijita ne ya shigo, har wajen da yake sana'ar kayan gona irinsu goruba, kanya, magarya, aduwa,kurma dasauransu, shi ne aka je aka sanar masa yayan matarsa mai kuɗi ya zo,shine ya bazamu.

Gaba ɗaya ya zube a gaban Daddy ya hau gaisuwa "ina wuni Yaya, ya hanya sannu da zuwa Alhaji" 

Daddy ya ga duk ya koɗe cikin tausayawa suka gaisa, akai ta hira da shi.


Sun sha lemon sosai, ruwan kaɗai Abdul-AZEEZ ya ɗauka ya fita da shi, mota ya koma ya sha yana ganin netwarok ya zo, da sauri ya kira number Mommy.


Tana zaune ta na buga lissafin business ɗinta da ke harkar sutura take, ganin kiran Abdul-AZEEZ ta amsa dan jin sun tawo ɗin, amma kafin ta ce komai, wayar ta yanke, ya na ta ƙoƙarin kiranta, ita ta na ƙoƙarin kiransa ƙarshe sai ta hau masifa "aikin banza ma malam ya kwashe min yara ya kai su jeji, tsabar tsiya ko arzikin network babu a gari mtsssw" wata ƙawarta ce ta shigo, irin haɗaɗɗun ƴan duniyar nan ne, Hajiya Fatu kenan mai sana'ar sai da kayan mata, 

"lafiya kike ta faɗa ke kaɗai?" 

Mami ta ce "ina fa lafiya, yarana na cikin ƙangin talauci" cikin rashin fahimta ta ce "kamarya?" 

Mami ta ce" dangin Ubansu mana........



Zinariya ce✍🏻