Kโ€™ADDARA TAH

21

by @hauwaausmanjiddarh

'''K'ADDARA TAH!!!'''


    ๐ŸŒน

   ๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

 ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



      ~NAH~



*HAUWA A USMAN*

     _(JIDDARH)_




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿป*

     _(DASHEN ALLAH)_




_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦ™ai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_




'''INA MATUK'AR JI DA KU, I REALLY LOVE SO MUCH'''


*K'ADDARA TAH FANS GROUPS*


*KAINUWA WRITERS FANS GROUPS*


~IYA WUYA ANA MUGUN TARE~

'''LUV U MORE MOST'''


*COMPUTER SCIENCE GIRLS RONI EX-STUDENTS 2012 GROUP*



~I NEED UR PLAYER AM NOT FEELING WELL (AM SICK) SERIOUSLY~




'''MY DEAR ALLAH YA BAWA OGA LAFIYA UBANGIJI YASA KAFFARA NE KARKI DAMU ALLAH NA NAN'''

*(MRS MAKAMAโคโค)*




21




*EDITING BY MOMYN ZARAH*




Director ne zauna a office d'insa, daga gabansa kuma Abban Fauziyyah ne zaune, gefensa Fauziyyah ce zaune, ta sunkuyar da kanta k'asa gyara murya yayi ya kalli Abban yace " a zahirin gaskiya ban so sanar da kai halin da ake ciki ba, amma dole ne sai ka sani saboda kai mahaifinta ne, a hankali ya zaro wayar sa ya kunna masa video ya mik'a masa tunda Abban Fauziyyah ya fara kallon video zufa ke karyo masa fuskar sa ta jik'e sharkaf da hawaye kasa k'arasa kallon video yayi da sauri ya mik'awa Director wayar sa, yana cewa " Fauziyyah kin cuce mu, kin b'atawa zuri'ar mu suna har abada, kin kunya ta mu, kin watsar da tarbiyyar danayi miki, kin sa na yarda dake, ashe ke fasik'a ce, mazinaciya ce, kin yaudare mu ni da mahaifiyarki, da ganin wannan rana gwamma mutuwa t...... kasa k'arasa maganar yayi saboda kukan dayaci k'arfinsa. 





Duk abinda akeyi Fauziyyah bata san ainahin laifin datayi ba, ba kuma tasan cewar ba aure sukayi da Fa'iz ba, cikin alamun mamaki fuskarta d'auke da alamar tambaya ta d'ago kanta ta kalli Abban ta da Director tace "meke faruwa ne? zubur mahaifin ta ya mik'e gami da shak'ar wuyanta, ya hau dukanta ta ko ina yana cewa " shegiya gwamma na kasheki na huta, ni zaki rainawa wayau, ni kike san k'ara yaudara, shegiya butulu, duk iyakacin k'ok'arina dana ke yi a kanku a she duk a banza ne, ganin yana niyar yin kisan kai ne yasa Director saurin mik'ewa ya rik'e shi " haba malam baka da hankali ne kabar ganin 'yarka ce wallahi idan ka kashe ta hukuma bazata kyale ka ba. 





"To sai me? ai gwamma na kashe ta nima a kashe ni, wannan lalatacciyar yarinyar ina amfanin rayuwarta, " haba bawan Allah saikace dai ba musulmi ba, kamata yayi ka zauna muji ta bakinta, dan gaskiya a hankalin yarinyar na da tarbiyyarta baza ta tab'ayin aikin irin wannan ba, dan nayi bincike sosai a kanta babu wani d'alibi ko malami daya fad'i aibu ko wani mummunan abu a kanta, kowa ma yabanta yake, ni gaskiya ina ganin kamar akwai wata k'ullalliya a k'asa ka sani ma ko ba'a cikin haiyacin ta take ba, ko saida aka bugar da ita sannan. 




Shiru Abban Fauziyyah yayi, kallanta Director yayi ya kira sunan ta, da kyar ta iya amsawa saboda kuka, tun shak'ar da Abban su yayi mata ta tsora ta, ta koma gefe ta rakub'e tana ta faman kuka, k'ara kiran sunan ta yayi, ya amsa yace " zo nan, a hankali cikin tsoro da rawar jiki ta je, video ya kunna mata ya mik'a mata, hankali kwance ta gama Kalan video tas, babu wani alamar tashin hankali a fuskarta, mamakinta d'aya yadda akayi har aka d'au video, kallanta Director yayi yace " kin san wannan yaron? " eh tace, "meye alak'ar ki dashi? a hankali tace "miji nane ta bada amsa kanta tsaye. 





Da sauri Abban ta ya d'ago kai yace what!!! mijin ki? hannu Director ya d'agawa Abban Fauziyyah alamar yayi shiru, murmushi yayi irin na manya, alamar yasan da wani abu a k'asa, yace mijin ki, kamar yaya, ta ya akayi ya zama mijin ki? tun daga farkon had'uwarsu da Fa'iz ta kwashe ta fad'a musu, bata rage komai ba, kaf ta basu labari, har marin da tayi mishi, da kuma yadda ta ganshi 2days ago, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai Abban ta yake maimaitawa, shiko Director kasa magana yayi, sai can ya d'ago kai yace " kaji ko ni dama nasan ruwa baya tsami banza, cikin tsananin b'acin rai da fushi Abban ta ya d'ago kai yace " ashe ke jahila ce, jaka, akuya tunkiya, iliminki na addini bai yi miki amfani ba bai k'are mu da komai ba, still Director ne ya k'ara dakatar dashi yace " haba yarinya ce fa she is 17yrs, kuma yayi amfani da basira, wayo, da tsoran da take dashi ne, shegen yaro ne yasan kansa sosai, kuma duk wanda ya girmeka ya riga ya girmeka, yayi amfani da basira ya cusa mata sanshi a ranta, kasan kuma so ko abu ba dai-dai bane yakan nuna dai2 ne, sannan yayi amfani da yarintar ta, yayi wasa da hankali ta da tunanin ta, ya had'a abin nana Hauwa'u da Adamu , ko babba ne za'a iya yi masa yawo da hankali, duk hankalin ko ilimin mutum idan akace maka yaro ne to kayi shiru kawai, musamman ma idan muka duba K'ADDARA. 




Fauziyyah yarinya ce k'arama bata da wayewa ko gogewa irin ta yaran yanzu, shi kuma babbane tunda yakai 27yrs kuma wayayye ne d'an duniya ne, cikekken d'an bariki, ya fita komai na rayuwa ya kuwa zai kasa yi mata wayau, kallan Fauziyyah yayi yace " ya cuce ki, ya yaudare yayi miki illa yabar miki taban da har abada bazai gogu daga zuciyar ki, Fa'iz yaudararki yayi Fauziyyah ba aure kukayi ba wayo yayi miki yayi zina dake, ya cimma burinsa a kanki tsakanin ku babu aure, k'arya yayi, haka yayi tayi mata bayani yana kawo mata hadith gami da ayoyin Qur'an dan ta fahimmata sosai, sai da ya tabbatar ta fahimta sosai karatun ya shiga kanta sannan ya kyaleta.





Tunda Director ya fara yi mata bayani ta fahimta sosai ta kuma gane Fa'iz yaudararta yayi wani irin kuka mai ban tausayi Fauziyyah ta saka, jikin sa a sanyaye ya kalleta yace " Fauziyyah kiyi hak'uri babu yadda zamuyi da K'ADDARA, dan ta riga fata, sannan ni kaina da da yadda zanyi da nayi, gaskiya ba k'aramar cuta Fa'iz yayi miki ba, dan kinga yanzu ya jawo miki barin makaranta dole, dole ne kumar makaranta ta d'auki mataki a kanku, shi ya riga ya gama karatunsa, ke kuwa dole ne a koreki, saboda horo, da kuma sauran students suma su hankalta su k'ara shiga hankalin su, kamar a mafarki taji Director yana cewa " FAUZIYYAH HUKUMAR MAKARANTA TA SALLAMEKI DAGA MAKARANTA MA'ANA AN KORE KI!!!!! wata irin k'ara ta saki dami da ihu daga nan bata k'ara sanin inda kanta yake ba. 





Ko kallanta Abban su baiyi ba sai Director ne ya mik'e cikin tashin hankali yana Subhanallahi, cak ya d'auke ta yayi mota da ita. 




*************************




Fa'iz na shiga d'aki ya wuce bathroom kansa ya sakarwa shower ko kayan jikin sa bai cire ba, yana tunanin maganganun Mom 


 _( "yarinya nitsatstsiya gata da hankali da tarbiyya, ina matuk'ar san yarinyar zan so had'a jini da ita ko dan nasamu zuri'a ingantacciya)_



A gaba d'aya wunin ranar babu abinda Fa'iz yake tunani kamar maganar Mom, ya kasa sukuni, da dai yaga tunanin na neman damun sa ya shirya ya nufi night club, yana cikin tuk'i yaji wayar sa na ringing da dai kamar bazai d'aga ba, daga baya kuma ya d'aga, Director ne ya kira shi, sanar dashi duk abunda ya faru yayi tun daga farrko har k'arshe har korar da akayiwa Fauziyyah daga makaranta, yace" wallahi kaji tsoran Allah kabar ganin babu abinda suka isa suyi maka dan iyayen ta bamasu hali ba, Allah bazai tab'a kyaleka kaci bulus ba sai ya jarrabeka ta inda bakayi tunani ko tsammani ba, wallahi Allah Fa'iz hak'k'in yarinyar nan bazai tab'a kyale ka ba yata bibiyarka kenan, sai ya hana maka kwanciyar hankali da jin dad'in duniya kasan illar cirewa budurwa budurcinta a titi kuwa, ka kuka da kanka duk abinda ya sameka kar kayi kuka da wani, ya kashe wayar.




Tunda Fa'iz yake rayuwar bai tab'a aika ta wani abu marar kyau yaji babu dad'i ba sai yau, sosai yaji abun ya dake shi musamman maganganun da Director ya sanar dashi, zuciyar sa ba k'aramar harzuk'a tayi ba da yaji abinda Fai'za tayi ba, dan shi ya tabbatar itace, zuciyar shi kamar zata tsaga k'irjinsa ta fito, har bibbiyu yake gani a haukace ya nufi gidan su. 




Cikin sauri Fai'za ta gama shirin ta na makaranta dan yau a k'agare take dataje makaranta dan taga abinda za'ayiwa Fa'iz da Fauziyyah, a hanzarce ta fito daga gida ta tare d'an a daidaita, ko ciniki babu ta hau, dan tsabar sauri, yana kaita ta sauka ta bud'e jakarta ta biyashi ita kuma tayi cikin makaranta, tana shiga makarantar ta bud'e jaka da nufin ciro wayar ta ta kira Fauziyyah dan taji komai, ga mamakinta taga babu waya, da sauri ta zazzage jakar taga ba waya,tunawa tayi da tayi waya da acikin adaidaitan, tana gama wayar ta ajiyeta a gefe, aiko da sauri tayi class wani ta samu ta karb'i a aran waya ta kira wayinta, a kashe taji wayar, wani irin bak'in ciki ne ya ziyarci zuciyarta data tuna da video su Fa'iz da Fauziyyah dake cikin wayar, shikenan dama ta kufce mata wani ne zai samu a banza, tasan duk wanda yaga video shima kud'i zai nema, "hmmmmm tace had'i dayin murmushi kome ta tuna oho............ 





*Alhamdulillah*




*MOMYN ZARAH*




KUCI GABA DA BINA DAN JIN K'ARSHEN FA'IZA DA FA'IZ, DA RAYUWAR DA FAUZIYYAH ZATAYI A GIDAN SU, SHIN YA MAHAIFIYAR FAUZIYYAH TAJI IDAN TA SAMU LABARIN ABINDA TAYI, MAI FA'IZA TA TUNA WANDA YASATA DARIYA, MEYE DALILIN SUMAN FAUZIYYAH, A IRIN SAN DA MOM D'IN FA'IZ KE YIWA FAUZIYYAH WANE MATAKI. ZATA D'AUKA IDAN TAJI LABARIN ABINDA FA'IZ YAYI MATA, IDAN FA'IZ DA FA'IZA SUKA HAD'U MAI ZAI FARU........