25
'''K'ADDARA TAH!!!'''
๐น
๐น๐น
๐น๐น๐น
๐น๐น๐น๐น
๐น๐น๐น๐น๐น
~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_
*EDITING BY MOMYN ZARAH*
25
"Tab! wallahi baku isa ba, wato ni ku ja min ko, ni da naje har gidan su gaban Maman ta na d'auka, idan wani abu yafaru wa za'a nema kudai canja wata shawarar wannan kam batayi ba,shiru kowannen su yayi sai can d'aya daga cikin su yace " to meye mafita dan ita ma tana da gaskiya idan kuma aka kama ta duk muma sai mun fito, shiru suka k'arayi sai can Fa'iza tace "ni yanzu zan shiga ciki Na shirya yadda muka zo sai mu d'auke ta mu kaita Hospital muce wani mai motor ne ya bugeta ya gudu, mu kuma tsintar ta mukayi shine muka taimake ta.
Gaba d'ayan su suka mik'e suka nufi d'aki, kallan su tayi da mamaki tace " ina kuma zaku ina magana baku ce min komai ba kun mik'e? gaba d'ayan su suka had'a baki suka ce " shiryawa zamuyi mana ai wannan shawara taki tayi, yadda taga sun had'a baki suna magana ne abin ya bata dariya tace " nima bari na shirya.
Bayan duk sun shirya wani ya sunkuya ya sungumeta sukayi waje da ita, a bakin wani private Hospital suka yi parking, duk kansu sunyi shiga ta mutum ci idan ka gansu sai ka rantse mutanen kirki ne, cikin alamun tashin hankali d'aya daga cikin su yayi cikin hospital d'in da gudu yana kwalawa Nurses kira.
Akan gadon tura marasa lafiya aka tura ta zuwa emergency room, ba'a tsaya tambayar abinda ya faru ba, taimakon gaggawa aka fara bata, sai da likitan yakai wajan 3hrs sannan ya fito, suna ganin shi gaba d'ayan su suka mik'e suka nufe shi, cikin fara'a ya tare su yace " maye dalilin faruwar hakan?
K'aryar Fa'iza ta shirga mishi harda d'an kukan ta, alheni Doctor d'in ya nuna a faskar sa yace "amma driver din nan bashi da imani, muje office dina, bayan sa suka bi, kuma kallon su Doctor din yayi sannan yace " to wa zai biya kud'in da akayi mata aiki? gaba d'ayan su suka ce aiki kuma?
"Eh! Doctor yace, yaci gaba da cewa " sorry banyi maku bayani ba, please have a set yace musu yana nuna musu kujerun dake office d'in, zama sukayi a sanyaye jiki ba kwari, Doctor ya yafara yi musu bayani " tana da ciki harna 3mnts amma sakamakon buguwar data samu cikin ya zube, sai da mukayi mata wankin ciki, sannan muka yi mata d'inkuna a ciwokanta, cikin razana Fa'iza tace " ciki? " yes of course, "Ok to yanzu nawa ne kud'in da za'a kashe gaba d'aya, "eh to idan har sallama ne zakai 155k "ok bani account number nayi muku transfer to account naku, "Ok ya fad'a had'i da fad'a mata number, kallonsu tayi tace " sai kuyi mishi transfer, "lyk how? wani yayi maganar, "excuse me, tacewa doctor ta fita suka bi bayan ta.
Can waje suka fita tace " ku zaku biya kud'in komai tunda kuka ja, sai kuje gayawa Fa'iz komai, in yaso sai ya biyaku kud'in ku,tunda na tabbatar cikin sa ne, bayan sun gama yanke shawara ne, suka koma office din doctor, suka biya kud'in, Fa'iza tace " to doctor mu zamu tafi amma ga wayar ta da muka tsinta tare da ita, ta mik'a mai wayar, amsar wayar yayi ya ajeyeta kan table nashi, su kuma suka fita, gida suka ajiyeta su kuma suka kira Fa'iz suka tambaye shi inda.
Ba'afi 20mnts ba suka isa middle night club d'in, da yake, zama sukayi kusa dashi ko kallon su baiyi ba, dayake miskili ne, sai d'aya daga cikin su ne yace " oga kasan me ya faru kuwa? ko kallansa baiyi ba yace " ina jinka, ya d'aga kwalbar yakai bakinsa, "oga kasan Fauziyyah tana da ciki kuwa?
Wata muguwar kwarewa yayi da jin abinda yaran nasa yace, sai da tarin ya lafa masa sannan yace "waya fad'a maka a ina kaji? labarin duk abinda ya faru tun daga har k'arshe ya bawa Fa'iz, cikin k'araji ya shak'e shi ya fara dukan su ta ko ina, yana zagi, "kunje kun zubar min da ciki, sosai yake d'aya murya yana magana, yakan ne yasa kowa yin tsit a club d'in aka daina kid'e-kid'en da akeyi hankalin kowa ya dawo kansu, yaci gaba da zagin su, yayi musu mummunar wulak'anci gami da korar kare ya tofa musu yawo a fuska yasa aka kore su kamar wasu karnuka yace "fuck you bitch ya fad'a yana zuba musu ruwan giya a jiki, sumi2 suka fita, tsabar bak'in ciki da jin kunyar abinda Fa'iz yayi musu a cikin jama'a yasa d'aya daga cikin su zama dirshen a k'asa yana kuka kamar wani k'aramin yaro, sauran muna bashi hak'uri, wani yace " yanzu ba lokacin kuka bane da mutum yayi maka abu ba,lokaci ne naganin dama idan kaga dama ka rama idan kaga dama ka kyale su.
Kallan shi sukayi, yace " eh bazamu kyale Fa'iz yaci lalai ba dole ne ya d'auki fansa da tafin hannunsa, wani kuma yace " to yanzu meye a binyi? "a binyi d'aya ne mu nemi Fa'iz mu had'e kai da ita kasan ance sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, wani ma yace " dole sai mun nemo Fa'iza cikin mu? "eh kusan dolen ne kasan ance kaidin mata daban ne, musamman ma ita da take 'yar bariki kuma itama da take neman hanyar d'aukar fansa a kanshi.
Haka dai sukayi ta tattaunawa daga k'arshe har suka yanke shawarar had'uwa da Fa'iza gobe, ita ko Fa'iza tana can kwance daga ita sai pant da bra tana sha sigarinta tana murmushi dan tasan zuwa yanzu makircin data had'awa Fa'iz da yaran sa ya tashi, dan ita ta shirya komai ita ta tura su su fad'awa Fa'iz komai daya faru dan nasan k'arshen zancen, cikin murmushi tace " na had'a tuggu na rabaka da gans dinka yanzu sun dawo nawa, dan na tabbar zuwa yanzu bomb d'in tana jefa muku ya tashi, gobe ko jibi da kan su zasu neme ni su kawo kansu hannu na dan mu had'a kai da hannu wajen yak'ar Fa'iz, ta tuntsure da dariya.
Shiko Fa'iz ya rasa mai ke damunsa mai yasa yayi musu haka dan kawai sunyiwa Fauziyyah haka, sun zubar da cikin shege cikin daba na halak ba,sai juyi yake a gado ya rasa mai ke damun sa, in banda tunanin halin da aka ce masa Fauziyyah na ciki babu abinda yake, yayi zurfi cikin tunanin sa, yaji magana sama-sama daga palon su, a hankali ya mik'e daga shi sai T-shirt da 3qtr ya nufi palon, "Subhanallah da gudu ya k'arasa inda Momy ke kwance cikin aman jini tana mik'a masa hannu a hankali tana kiran sunan sa, da gudu ya k'arasa ya sungumeta yayi mota da.
Wani irin mugun gudu yake kamar zai tashi masa, a cikin Hospital din yayi Parking, da gudu ya zagaya ya bud'e motar ya sungumi momy yayi cikin hospital da ita, yana shiga nurses suka tare shi, aka shigar da ita emergency, zaune yake ya had'a kai gwiwa yana tunani, jin Doctor nayi masa magana akai ne yasa shi saurin mik'ewa, " do....c........ to.... r... ya...... M..... Omy... na ya fad'a baki na rawa, Doctor bai amsa ba ya wuce office d'in sa yayi masa alama da ya biyo shi, sai da doctor ya shiga toilet ya feto sannan ya zauna, har a lokacin Fa'iz na tsaye bai zauna ba, " Doc.... t.. or ya momy? ya k'ara tambayar sa, kai Doctor ya d'ago ya kalle shi yaga duk ya fita a haiyacinsa ina kuma ga inya gaya masa matsalar da ake ci, cikin zafin rai ya dakawa Doctor d'in tsawa yace "nace maka ya jikin Momy, cikin sanyin murya doctor yace " kayi hak'uri ka zauna, sai da Fa'iz ya zauna sannan doctor yace " na rasa yadda zanyi in sanar da kai halin da ake ciki ne, amma magana ta gaskiya zuciyar Momynka ta gama lalacewa, takai matakin k'arshe da akoyaushe zamu iya rasa ta.
" innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Fa'iz ya fad'a yana dafe kansa yace " please doctor help me, I want her in my life, i need to continue my life with her, i don't have anyone, I don't know any person be side me only her I know and I have pls doctor ya really love her so much, ya k'arashe maganar yana kuka, kallan sa doctor yayi da tausayawa yace " I'm sorry, babu wani abu da zamu iya yi, tashi yayi jiki ba kwari ya shiga d'akin da aka kwantar da momy ya zauna a k'asa kan tails ya d'ora kansa bakin gadon hannunsa cikin nata yana rusa kuka kamar ransa zai fita.
Doctor ganin har washe gari su Fa'iza basu dawo wajen Fauziyyah ba yasa shi yin mamaki yana cikin mamakin yaji waya na ringing ya rasa daga Ina wayar ke ringing ya shiga neman wayar, wayar Fauziyyah ya gani, shi yama manta da wayar sai a lokacin ya tuna da wayar har wayar ya katse ba tare da yayi picking call din ba, sake kiran wayar akayi a karo na biyu, ganin an rubuta My dad ya tabbatar da mahaifinta ne ke kira da sauri ya d'aga wayar.Dan gudun kar wayar ta k'ara tsinkewa.
Da sallama doctor ya d'aga wayar daga b'angaren ma aka amsa sallamar, bayan sun gama gaisawa ne, doctor yake yi mishi bayanin abinda ya faru, a cikin tashin hankali Abba ya tambayi Doctor hospital din, cikin nutsuwa doctor yayi mishi kwatance, ba'afi 20mnts ba saiga Abba da Mama, Aisha sunzo hospital din, office doctor suka tambaya aka nuna musu, suka shiga da sallamar su, wajen zama ya nuna musu, suka yi mishi biyanin su waye su, shima bayanin da Fa'iza tayi mishi yayi musu, sannan yayi musu bayanin da yayiwa Fa'iza na zubewar ciki, daga k'arshe yakai su har d'akin da aka kwantar da ita, yace "tun jiya bata farka ba, ina san ran nan da few minutes zata iya farkawa, yana kaiwa nan ya fita.
Ganin halin da Fauziyyah ke ciki ba k'aramin d'aga musu hankali yayi ba, musamman da duk fuskarta an rufe mata ne da bandegi, kuka sosai Mama da Aisha suke, shiko Abba kukan zuci yake, nan suka zauna suka saba gaba suna kallo Mama na sharar wahaye, a ranta kuma tana mai godewa Allah a bisa zubewar cikin.
Sai da su Mama sukayi 43mnts sannan ta farka tana cewa "wallahi baku isa ku keta min haddi ba, Fa'iza tsakani na dake Allah ya isa, muguwa azzaluma, wallahi dakuyi zina dani gwara na mutu, tana maganar tana haure-haure, can kuma sai ta fashe da kuka tana kiran Mama da Abba, Aisha tana cewa " ku yafe man, mutuwa zanyi wallahi ba laifi na bane, makirci aka shirya man, da sauri dukkan suka mik'e suka nufi wajenta, suna bin junan su da kallan mamaki da jin abinda Fauziyyah ke cewa, a hankali Mama ta rik'e hannunta wata irin ajiyar zuciya ta saki, a hankali Mama ta fara yi mata magana "Fauziyyah mune bud'e idonki ki gan mu, meke faruwa dake, Abba cikin rawar murya ya rungume Fauziyyah yace " bakiyi mana komai ba, mun yafe miki duniya da lahira, Allah yayi miki Albarka, jin maganar iyayen ta a kusa da ita yasa ta bud'e idon ta a hankali, dishi-dishi take kallon komai kafin idonta ya k'arasa bud'ewa.
Ido ta zubawa iyayen nata, sai kuma ta saka kuka, ganin haka ya tabbatar wa Mama da Abba akwai abinda ke faruwa, a hankali Mama ta zauna kusa da ita ta lallashe tayi shiru, Abba kuma ya kira doctor ya sanar dashi ta farka, duddubata yayi yacewa nurse din dake niye dashi " ki saka bata magungunanta, ya fuce, magungunan ta bata ta d'an tada ta zaune ta jingina mata pillow ta fita, Fauziyyah ta fara magana cikin muryar marasa lafiya "Mama ashe Fa'iza shaid'aniya ce muguwa ce ta k'ara fashewa da saban kuka, Mama da Abba duk ido suka zuba mata can Mama tace "yi shiru ki sanar damu abinda ke faruwa, a hankali Fauziyyah ta kwashe komai tun daga ranar da suka fara had'uwa da Fa'iz, har had'uwar ya Fa'iza, da labarin da Fa'iza ta bata na duk makircin da suka shirya mata, har zuwa kai ta gidan maza da tayi jiya, ta fad'a musu, kowa mamakin abun yake, cikin kuka da jirin da yake d'iban ta fara shin mik'ewa da sauri Abban ya mik'e ya zaunar da ita yace "me kike so?
"Abba wata alfarma zan rok'eka, "ina jinki Fauziyyah ya fad'a cikin muryar tausayi, hannunshi duka biyun ta rik'e tace " Abba dan Allah mubar garin nan, please Abba karka ce a'a, wallahi Abba bazasu tab'a kyale min rayuwa ta ta zauna lafiya ba, bazasu kyale mu mu rayu cikin farin ciki da walwala ba, basu kyale mana kwanciyar hankalin mu ba, sunta samu a cikin masiba kenan, please Abba mu canja gari, rayuwa, komai namu, jikin Abba da Mama ne yayi sanyi, Abba ya juya kalli Mama dake ta faman kuka, sunkuyar da kanta tayi, juyowa yayi ya maida hankalinsa kan Fauziyyah, a hankali ya fara zame hannun sa daga cikin nata, aiko gam ta k'ara rik'e hannun tace "dan Allah, wallahi wata rana gawa ta za'a kawo muku, karki damu Fauziyyah zamuyi magana da Mamanki tukunna.
A hankali ta saki hannun mahaifin nata ta koma ta kwanta idonta na zubar da hawaye,Aisha taje tana goge mata itama tana kukan idonta ta bud'e tana halin da Aishan ke ciki, cikin muryar kuka ta shiga girgiza mata kai tana cewa " please sister karkiyi kuka itama tana goge mata hawayen dake zubo mata, " to Aunty idan kina so na daina kukan kema ki daina, cikin kukan Fauziyyah ta rungume ta saki saban kuka, tace " please sister karkiyi irin abinda nayi nasa iyayen mu cikin damuwa, please kona mutu ke ki zame musu 1 tamkar da 10, ki share musu hawayen dana zubar musu please sister, iyayen na kallon su suma zuciyar su kamar zata fashe.
*BAYAN SATI D'AYA*
Kwana biyu kenan da sallamar Fauziyyah ta warke sumul, mahaifinta ya yarda da shawarata ta su canja gari da rayuwa, sun sayar da gidan su, da duk wani abu da suka mallaka a garin katsina kayan sawar su kawai suka bari, suka had'a kayan su, sun yanke shawarar komawa garin kano ta dabo tumbin giya, an sai gidan da daraja har 2.5 daya had'a da kayan daya sayar sai kud'in suka tashi 3 millions naira,kasancewar yau ne wa'adin su damai gidan zai cika yasa su shiryawa suka nufi bakin titi dan neman abin hawa zuwa tasha.
Fa'iz zaune gaban Momy duk ya fita haiyacin sa, dan tun ranar daya kawo ta hospital bata farka ba har yau, kasancewar basu da kowa shine zaune wajen ta ko yaushe baya fita ko nan a can, tari Momy ta fara yi tana kiran ruwa da gudu Fa'iz ya fita ya nufi office din doctor, shiga yayi ko sallama babu ya kira shi, shima doctor a guje ya fito, sai da suka k'ara duba ta sosai sannan, doctor ya bada umarnin a bata ruwa, a hankali Fa'iz ya d'ago ta ya shiga bata ruwan, sai da tasha sosai ya ishe ta sannan ya maida ruwan ya ajiye, yana ajiye ruwan sai ta fara tari da aman jini na fitar hankali, da gudu Fa'iz ya yunk'ura zai fita kirar doctor ta rik'e shi, a hankali ya dawo ya durk'usa a gabanta yace " Momy doctor zan kira, "no need ta fashi amsa, a hankali ta saita tarinta tace"Fa'iz ni tawa ta k'are, zan tafi inda kaima wata rana dole zaka je, Fa'iz kaji tsoran Allah, Fa'iz kaji tsoran Allah idan ka tuna da ni da mahaifinka dakai muke rayuwa yanzu duk ina muke, ka tuna mutuwa ka tuna kwanciyar kabari da hisabi.
Dan tarin ta k'arayi sannan taci gaba " idan mu mun fad'a maka gaskiya kak'i yarda to duniya zata fad'a maka, kuma fad'awar duniya bata da dad'i, Fa'iz ka tuna komai daren dad'ewa wata rana kai uba ne, kuma inba mutuwa da tsofa, Fa'iz ina baka shawara Fauziyyah ita ce matar data dace kai, itace matar da zata kaika aljanna, ita ce matar da zata fitar mana da jikoki d'aiyaban, itace hanyar shiriyarka zuwa ga mahaliccenka, domin Fauziyyah macen kwarai ce, duk wuya duk runtsi karka sake ka bari Fauziyyah ta kufce maka, duk wahalar da zaka sha karka rabu da ita, karka yarda wani ya shigo tsakanin ku balle har ya samu damar rabaku, Fa'iz babban buri na a duniya shine naga ka aure Fauziyyah ka mallaketa a matsayin mata, please son kayimin alk'awarin cika min birina yana kuka yace " nayi miki mom, murmushin k'arfin halin tayi tace " nagode son Allah yayi maka albarka, Ubangiji ya kare min kai ya tsare min kai ya shirya min, sai kuma ta d'an b'ata rai "me? Yace cikin muryar kuka.
" son sakan bana san shaye-shaye da neman matan da kake yi ko? kai ya d'aga mata saboda kukan sayaci k'arfinsa, shima kayi min promise har abada naka k'ara yin zina da shaye-shaye, cikin kuka yace "nayi miki alk'awarin ban k'ara d'aya daga cikinsu mom never after, murmushin jin dad'i tayi sannan taci gaba da kwad'aita mishi auren Fauziyyah, tana nuna masa amfanin auren.
"Itace mace ta gari da kowanne namiji ke burin samu, mace mai nutsuwa, kamala, hankali, hak'uri, juriya tunani, sanin ya kamata, kawaici, wallahi Fa'iz idan kabari kayi asarar Fauziyyah a matsayi matar aure kayi babbar asara, kuma wallahi sai kayi kuka da idonka ba baki nayi maka ba, Allah yayi maka Albarka, Ubangiji ya shiryeka kan tafarki na gaskiya, Allah ya baka mata ta gari, 'ya'ya na gari zuri'a ta gari, Allah ya sanya albarka a cikin rayuwarka, Allah ya nutsar min dakai, yasa maka hankali da sanin yakamata a cikin ruhinka. Nasiha mai ratsa zuciya da shiga da rai tayi masa sosai.
Tana cikin magana tarin yaci karfinta da gudu ya fita, amma kafin ya kira doctor rai yayi halinsa, ihu sosai yake yana buga kansa a bango, yadda kasan mahaukaci haka ya koma ya rungume gawar Momy a kirjinsa yana kuka kamar ransa zai fita.
Fa'iz na cikin 'yan zaman makoki bayan an kai Momy makwancin ta, sanye yake da farin yadi, idonsa yayi ja, saboda tsabar kuka, wani ya shigo yace " Fa'iz yanzu naga su Fauziyyah zasu bar gari wai har sun sai da gidan su ma, wata irin zabura yayi ya fita a guje ko takalmi babu yadda kasan mahauci gudu yake sosai a titin Allah........
*Alhamdulilah*
*MOMY'N ZARAH*
BYE