Kโ€™ADDARA TAH

27

by @hauwaausmanjiddarh

'''K'ADDARA TAH!!!'''


    ๐ŸŒน

   ๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

 ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



      ~NAH~



*HAUWA A USMAN*

     _(JIDDARH)_




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿป*

     _(DASHEN ALLAH)_




_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦ™ai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da kassai


27


" Assalamu Alaikum cikin rawar murya ya amsa sallamar, bayan sun gama gaiwasa ne Fa'iz ya sanar da Director buk'atarsa, shiru Director yayi na wani d'an lokaci sai yace "maganar gaskiya Fa'iz bazamu iya baka Admission ba, saboda abubuwan da suka faru, nan Fa'iz ya shiga rok'onsa, yana had'a shi da Allah, "ok to in sha Allah zanyi maka k'ok'ari in sama maka admission a BUK dayake abokina na Director makarantar, "nagode sosai Allah yasa da alkhairi, Amin yace ya kashe wayar. 




Malam kullum bashi da wata magana sai ta damun Abba akan yabar Fauziyyah taci gaba da karatu, shi kuma Abba ya kafi fir yak'i yarda, Malam Bala yayi da Abba amma Abba yak'i har Malam Bala yayi fushi dashi, shi kuma Abba ba abun ya fad'awa Malam Bala abinda ya faru ba, idan yayi haka kamar ya tonawa kansa asiri ne, hakan ne yasa dole ya kama bakin yayi shiru, amma ya k'uduri niyyar komai Malam Bala zaiyi bazai tab'a barin Fauziyyah ta k'ara ci gaba da karatu ba, Abba nan k'ofar shagonsa yana zancen zuci Malam Bala yazo zai wuce amma ko kallan Abba baiyi da sauri Abba ya mik'e ya bishi.




Rik'e hannunsa yayi yace " d'an uwa na fishi kake dani, kallon sa Malam Bala yayi yace " ina ni ina fishi akan abinda ba nawa ba, ba kuma ni da iko akai, Abba ya fahimci maganar Malam Bala murmushi yayi yace " kai ko kake da iko dashi, duk garin kano akwai wanda yafika iko da gida da iyalina, da sauri Malam Bala yace " bani da iko inda ina da iko na nemi alfarma a wajenka ka hana ni, Abba yace " wai ita Fauziyyahn ce tace maka tana san ci gaba da karatu? 




"A'a ko d'aya ni naga ya dace da hakan saboda kewa da damuwa sai yayi mata yawa, ajiyar zuciya Abba yayi yace " ni da a san rai na nafi san nayi mata aure idan taje gidan mijinta sai tayi karatun acan, Malam Bala yace "kana da tabbacin auren wannan zamanin? da anyi haihuwa d'aya shikenan, mazan yanzu mayaudara ne, shiru Abba yayi, Malam Malam yaci gaba yanzu babu gatan da zakayiwa yaranka daya wuce ka basu ilimi mai zurfi, ga ba 'yan uwanta nan su Fatima ba, mai ya same su, Abba ko a zuciyar magana yake "hmmmm dazaka san meya faru damu dakaima ka tsorata, Malam Bala yace "inata magana ka kyale ni, Abba yace " ba shuru nayi ba ina jinka, ai matsalar ni ban san kowa anan ba bani da hanyar da zan samata , murmushi Malam Bala yayi yace " bakomai ka bani takardunta in sha Allah zanyi iya k'ok'ari na, "to kawai Abba yace yana share gumi Malam Bala ya lura da hakan amma yayi kamar bai gani ba. 




Malam Bala yace " ai yanzu zamuje ka bani," to Abba ya k'ara cewa, ya wuce Malam Bala na biye dashi, sai da Abba ya shiga gidan shi kuma ya tsaya a k'ofar shagon saboda bai rufe ba, takardun Abba ya d'auko ya mik'awa Malam Bala hannu na rawa badan yaso ba, ya karb'a yana murmushi yayi Abba yace "nagode abisa mutumtani dakayi ka bani ragamar iyalinka, in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, kuma zakayi alfahari da hakan, shi dai Abba shiru yayi baice komai ba.




Malam Bala na tafiya Abba ya rufe shagon ya koma cikin gida a kicin ya samu Fauziyyah tana girki ya wuce parlor ya iske Momy zama yayi a gefenta ya zauna ya fad'a mata duk abinda ya faru tsakanin sa da Malam Bala cikin sanyin jiki tace " to Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi, Ubangiji ya tsare mana ita ya kare ta, "Amin Abba yace, sai kuma ya kalli Mama yace " kema kin goyi bayan hakan!? cikin sanyin murya tace " a'a ba haka bane kawai ina jin tausayinta ne, in banda islamiyya da take bin su Aisha bata zuwa ko ina, kuma kasan ajin 'yan hadda take da'an gama karb'ar hadda shikenan idan ta dawo gida ta shige d'aki bata fitowa, mu kammu iyayenta kunyar mu take ji akan abinda ya same ta, shiru Abba yana sauraron Mama sai yace " bakomai K'ADDARAR TAH ce haka babu yadda zamuyi muyi, illa mu dage mu taya ta da addu'a. 




Duk maganar da Abba da Mama keyi Fauziyyah najin su, wani irin farin ciki marar misaltuwa taji, nan take tayi sujjada ta godewa Allah, haka nan kuma ta dage da sallar dare da karatun Qur'an tana addu'ar Allah yasa a samu admission d'in, haka kuma ta dage da addu'a akan Allah ya tsare ta da fad'awa mugun hannu a karo na biyu, tun abinda Fa'iza tayi mata taji ta tsani k'awaye da maza kwata-kwata aure ko soyyaya basa gabanta, sai abu d'aya duk irin tsanar da tayiwa Fa'iz ta kasa mantawa dashi, da ta tuna maganar su da Momy sai taji gabanta yayi muguwar fad'uwa, sai dai kuma Sadik d'an Malam Bala ya hana ta sakat, tun ranar da Sadik ya ganta Allah ya d'ora masa bala'il santa, zuciyar sa ta hana shi sakewa, babu abinda Fa'iz zai nunawa Sadik sai dai farar fata da lulu eyes, sai dimples, amma shima Sadik ruwan tarwad'a ne dogo mai dogon hanci yana da k'irar zaki, irin su mata ke kira da handsome guy, dan shima kyakykyawa ne ajin farko, gaba d'aya ya hana ta sakewa da samun nutsuwa, da baya zuwa weekend sai k'arshen wata amma yanzu duk ranar Fridays yake zuwa, ko yaushe yana gidan su sallah kawai ke fitar dashi. 




Sadik yaro ne nutsatstse ga hankali da wadatacciyar tarbiyya ga sanin ya kamata,ga wadataccen illimi boko da arabi, tunda Sadik yake bai tab'a soyayya ba sai akan Fauziyyah, Ita kuma tak'i bashi fuska, dayake 'ya'yana Malam Bala basu da iya da gidan Abba ya kama su Fauziyyah basu da iya a gidan Malam Bala, dayake akwai kyakykyawar fahimta a tsanin iyayen nasu, duk duniya Abba da Mama basu da wani d'an uwa daya wuce Malam Bala da Matar sa basu da wani dangi daya wuce 'yaran Malam Bala, haka ma Malam Bala da Ramatu basu da kowa sai Mama da Abba, kuma kowa yana ganin mutuncin kowa, duk hukuncin da wani ya yanke a gidan wani to ya yanku babu wanda ya isa ya canja. 




*BAYAN WATA BIYU* 




Cikin ikon Allah, Malam Bala ya samowa Fauziyyah admission a ABU ZARI'A, an bata low zata karanci BARRISTER, tayi farin ciki sosai duk da ba course din da take so aka bata ba, Fauziyyah na kwance a d'akin su, taji wayar ta tana ringing tayi mamaki sosai ganin bak'uwar number tunda ta canja layi babu wanda yasan layin ta daga Zainab sai Farouk dayake shi abokin tsamar tane, suna wasa sosai, dan idan kaji dariyar Fauziyyah to tana tare da Farouk ne, dan wani lokaci idan ya shigo gidan tun safe sai dare, idan kuma yana makaranta ya dame ta da waya, sai kuma Fatima ('yar malam bala dan yanzu itace k'awarta itama da kyar Mama ta shawo kanta ta yarda saboda nacin da Fatima keyi mata, dita yanzu Allah ya sani tsoran k'awaye takeji) sai da mama tayi mata fad'a sosai, sannan ta fara d'an kulata sama2.




Da sallama ta d'aga wayar jin muryar ta yasa shi lumshe ido, bai amsa sallamar ba sai da ta k'aratana jin muryar sa ta gane, ido ta d'aga ta kalli Mama aiko karaf suka had'a ganin Mama na kallanta ne ya hana ta kashe wayar, "ina yini? "lafiya lau my love, fuska ta k'ara b'atawa tace "ina jinka, nan fa ya shiga yi mata hira sosai, ita dai ta rasa yadda zatayi ita ba abin ta kashe ba Mama tayi mata fad'a shi kuma ya dameta zancen soyyaya duk sanda yace mata my Fauza sai taji gabanta ya fad'a dan haka Fa'iz yake kiranta, shiko ya dage sai zuba mata soyyaya yake yana yi mata shagwab'a wai bata sanshi bata kula shi, dan ya kyale ta tace "to yanzu me kake so ya Sadik, da sauri yace "zuciyar!!! Pls ki so ni, shiru tayi ta kasa magana dan yadda yake yi mata magana duk ya kashe mata jiki, cikin sanyin murya tace " to ya Sadik, yace" ai ba shikenan ba, kiyi min promise duk sanda nakira ki zakiyi picking call d'ina, sannan ki daina ce min ya Sadik "I will tace masa, kiss yayi mata tacikin wayar ya kashe wayar ta k'urawa ido,ta tafi tunani Mama tace " waye? sai a lokacin ta dawo hankali ta cikin rawar murya tace " ya Sadik ne, Mama tace " cewa yayi yana sanki? baki ta turo ta b'ata face tace "eh!, harga Allah bak'aramin dad'in Mama taji ba, dan ta dad'e tana sha'awar yaran tana so ace ya auri d'aya acikin yaranta, dama ta dad'e tana zarkin hakan a ranta, amma yadda Fauziyyah ta b'ata rai da yadda take amsa masa wayar ya tabbatar mata da bata sanshi, kallanta Mama tayi tace " baki sanshi ko? shiru tayi batace komai ba, murmushi Mama tayi tace " Fa'iz kike so har yanzu ko?




Da sauri ta d'ago kai ta kalli Mama suka had'a ido sai kuma ta mayar da kanta k'asa, batace komai ba, "hmmm Fauziyyah ke yarinya ce, amma Fa'iz ba miji bane, har kina sa ran auren sa, kima cire shi a ranki dan bazaki tab'a auren sa, kunyiwa juna nisan nisa, na dad'e ina addu'a Allah yasa tsakanin keda Aisha Sadik yace yana san d'aya dan Sadik miji ne na nunawa sa'a, ina sha'awar yaran yana da hankali ga sanin ya kamata nan dai taita bata shawara tana nuna mata kyawawan halaiyar Sadik tana nuna mata illar auren Fa'iz, daga k'arshe tace "amma kiyi tunani, ta tashi ta fita ta barta, aiko maganganun Mama bak'amin tasiri sukayi a wajen Fauziyyah ba, dan takai 3:30 am ta kasa bacci tana tunani tana san gano aibun Sadik amma ta kasa, sai ma kyawawan halayen sa da take gani. 




Yau ce ranar tafiyar Fauziyyah makantar ABU ZARI'A bak'aramin fad'a Mama da Abba sukayi mata ba, haka ma, Malam Bala da Ramatu, jikinta ba k'aramin mutuwa yayi ba, Sadik ko ya dage wai shi zai kai ta makaranta, haka Aisha da Zainab da Fatima, gaba d'ayan su suka shiga motar Malam Bala yaja su zuwa zari'a, shiko Farouk yana can ya kasa zaune ya kasa tsaye Fauziyyah zata zo, duk bayan 20mnts sai duba agogon hannunsa yayi tsaki, sai kira ta yaji idan sun k'araso, haka dai har suka isa, Malam ya lura akawai wani abu a tsanin Sadik da Fauziyyah amma abinda ya kasa ganewa shine, yadda kuma Farouk ke kiranta a waya duk bayan 20mnts, haka ma ranar daya sanin dashi Fauziyyah makarantar su zata zo murna kamar ya mutu, shi dai yayi shiru yaga abinda Allah zaiyi. 




Fauziyyah an tsunduma karatu fafar, bata da lokacinta kanta Sadik ko ya damu gani kamar dan bata sanshi shiyasa bata san waya dashi duk ya damu ya kasa sakat, zuwansa biyu zari'a wajenta, 




Fa'iz kuwa bashi da wata damuwa data wuce ta Fauziyyah, ga makarantar sa an samu, har an bashi Admission letter, a BUK, cikin satin nan zai fara fara attending lacture's, amma gaba d'aya hankalin sa baya jikinsa, haka dai yayi ta rayuwa har Allah yasa fara zuwa makaranta, amma yanzu a nitsi yake shiga makaranta babu ma wanda ya sanshi a ajin su balle a makarantar....... 




*BAYAN SHEKARA UKU*




*Alhamdulillah*




*MOMYN ZARAH*



BYE