Kโ€™ADDARA TAH

40

by @hauwaausmanjiddarh

'''K'ADDARA TAH!!!'''


    ๐ŸŒน

   ๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

 ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



      ~NAH~



*HAUWA A USMAN*

     _(JIDDARH)_




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿป*

     _(DASHEN ALLAH)_




_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦ™ai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_




DEDICATED TO 


UMMIEN FAUZAN

UMMY ONYOP

KHAIRTY (YA SHEIK) 

HAUWEE LOVE

UMMU FATIMA

FATIMA ZARAH




*EDITING BY MOMYN ZARAH*


40


A emergency room kuwa da kyar aka shawo kan Fa'iz, dan sai da suka b'ata lokaci sosai, turo shi suka yi zuwa d'akin sa, bayan nurses sun fita doctor ya kalle Fa'iz yayi murmushi yace " nasan idon ka biyu ka bud'e ido zamuyi magana, a hankali Fa'iz ya bud'e lumsassun idanun sa, ya sauke su a kan doctor, shima doctor kallon sa yake yi a hankali yace " Fa'iz ina baka shawara akan ka hak'ura ka mik'a dukkan lamuranka ga, duk wannan abun bashine zai fishsheka ba, idan Allah yayi yarinyar nan matar ka ce, to ka sani babu makawa sai ka aure ta, dan haka ka dangana ka nemi auren ta a wajen mahaliccinta, duk abinda kaga ya samu bawa daga Allah ne kuma da sanin sa, please brother kayi hak'uri ka maida komai ba komai ba, ka nutsu, ka maida hankali akan lafiyarka ka rink'a shan magungunan ka akan lokaci. 




Shiru Fa'iz yayi jikin sa duk ya mutu, tabbas yasan komai daga Allah kuma wannan ba kumai bane face K'ADDARA SU, ganin ya fara samun nasara ne yasa doctor din ci gaba, yace " kar sai ka gama kashe kanka, ma'ana ka bari cutar ta gama shiga jikinka taci k'arfinka sannan Allah ya baka Fauziyyah kaga alokacin babu wani amfani, da sauri ya d'ago kai yace " no doctor in sha Allah hakan bazata faru ba, " to idan baka san hakan ta faru sai ka rinka ragewa kanka tension da tunani, ka maida hankalinka kan neman lafiyar ka, ka rink'a shan magungunan ka, da sauri yace " I will try my best doctor, so please help me, murmushin jin dad'i doctor yayi yace " in sha Allah zan taimakeka, yanzu tashi in taimaka maka kayi wanka, da taimakon sa yayi wanka yayi sallah yaci abinci. 




Kafin 1 week da taimakon doctor Fa'iz ya murje yayi kyau yayi sumul, doctor ya zama tight friend din Fa'iz, dan tare suke yawa doctor yana d'auke masa kewa sosai, yana bala'il k'ok'arin akan Fa'iz, bayan Fa'iz ya warke an sallame shi, doctor ya tambaye shi ina ne gidan su, nan Fa'iz ya bashi labarin sa tun daga farko har k'arshe, amma bai gaya masa abinda ya shiga tsakaninsa da Fauza ba, doctor ya tausaya masa sosai, bayan ya tashi daga aiki ne, ya d'auki Fa'iz ya kaishi gidan su yayiwa Momyn sa bayanin komai, ita ta tausaya masa sosaiTa kuma k'arb'eshi hannu bibbiyu, da yake Momyn Doctor Adam mutance mai mutunci da sanin darajar dan Adam, sosai ta mutunta Fa'iz, yadda takeyiwa Adam haka take yi masa, in dai Doctor baya office to suna tare da Fa'iz tare suke zuwa ko'ina wani tym din ma har office, sosai Fa'iz yake jin dad'in zaman gidan su Adam. 




Tunda abinda ya faru gidan ya zama kamar gidan makoki, kowa yana d'aki yayi jugum, ganin halin da gidan yake yasa Abba yanke hukuncin d'aura auren Sadik da Fauziyyah, Baba ya samu yake sanar dashi hukuncin daya yanke, murmushi Baba yayi yace " bakomai ai duk 'ya'yan ka ne, Abba yace " idan ka shiga ya sanar dasu za'ayi meeting bayan sallar la'asar, "to kawai Baba yace jikinsa a mace, Abba ya lura da yanayin Baban amma yayi kamar bai ma san yana yi ba. 




Kowa ya hallara a babban parlon, Abba ya kalle Sadik yace " bud'e mana taro da addu'a, addu'a Sadik yayi suka shafa, Abba ya kalli Baba yace " Bissimillah, kayi musu bayani, gyaran murya Baba yayi yace " mun yanke hukuncin d'aura auren Sadik Da Fauziyyah, Aisha da Farouk, ranar asabar din nan mai zuwa in Allah ya yarda, yau lahadi kunga kenan saura kwana shida, satar kallon Fauziyyah Sadik yayi yaga ta zabura gaba daya ta gama fita hayyacinta, ya lura bata cikin farin ciki, duk ta zare, gashi tayi muguwar rama wayi bak'i sosai, ita ko Baba na sanar da d'aurin aurenta da Sadik gabanta yayi muguwar fad'uwa, da sauri ta d'ago kai ta kalli Baba, tayi rau-rau da ido zatayi kuka, Mama ma ita take kallo gaba d'aya hankalinta yana kan Fauziyyah, Aisha da Farouk duk sun sadda kai k'asa, alamar jin kunya. 




Shiko Sadik ya k'urawa Fauziyyah ido, baya ko k'iftawa aiko karaf suka had'a ido, k'ok'arin kuka take a hankali ya shiga girgiza mata kai alamar kar tayi kuka, itama kai ya d'aga masa tayi masa murmushin k'arfin halin, duk abinda ke faruwa tsakanin su Abba da Baba na lura, ita ko Umma hankalin ta yana kan su Aisha, Baba yace " kunji ko? Duk suka amsa da " eh!, yace " idan da mai magana yayi, kowa yayi shiru, Abba yace " Shikenan ku tashi kuje Allah yayi maku albarka, duk suka ce " Amin, Fauziyyah na fita da sauri-sauri ta shiga d'aki ta fad'a gado ta saki kukan da take dannewa, a hankali ya shigo d'akin, zama yayi a bakin gado ya kasa cewa komai sai da yayi kusan 20 munute, itama bata daina kukan ba, ajiyar zuciya yayi ya kira sunan ta a hankali "Fauziyyah!!! Wani irin yarrrr taji dan Sadik bai tab'a kiran sunan ta kai tsaye ba, shiru tayi bata amsa ba, a hankali yace " please if u don't love me, just tell me, babu komai zan kuma fahimceki, dan ina sanki bazai sa na tauye miki hakki ki ba, zan baki damar ki ki rayu cikin farin ciki da wanda kike so, so please tell me d true, bata iya ce masa komai ba, illa kukan ta data ci gaba dayi, " fauza hakan ma amsa ce, na kuma tabbar da baki so na, in sha Allah zanje nayiwa su Abba bayani yadda ya kamata kuma nasan zasu fahimta. 




Mik'ewa yana shirin fita da sauri ta mik'e tace" no yaya please karka fad'a musu komai nifa bance ban sanka ba, ta fad'a kanta a k'asa, hab'arta ya tallabo ya sunkuyo da faskarsa dai-dai tata ta kwaikwayi maganarta yace " to me kika ce? Murmushi tayi tace" kawai ina kuka rubuwa da Mama da Aisha ne fa, ta fad'a tana langwabar da kai gefe, " to kice kina so, " I love you dear, ta fad'a hawaye na zubo mata, murmushi yayi yace " I love you too baby, ya share mata hawayen yace " please stop cry, its pain me, ya fad'a yana dafe saitin zuciyar sa, dariya tayi tace " na daina, sai da ya lallab'e ta sannan ya fita zuwa masjid. 




Yana fita ta k'ara fashewa d saban kuka ta durk'ushe, duk abinda ya faruwa tsakanin su Baba na kallon su kuma yana jin su, tausayin yaran ne ya kamashi, amma babu yadda zaiyi, bayan Sadik ya fito daga masallaci ya kira abokansa yana sanar dasu d'aurin auren sa, haka ma a watsa a media, a shafin sa na Facebook, Instagram, Twitter, WhatsApp, duk ya saka ya sanar yana gaiyatar jama'a, nan fa Mama da Umma suka shiga shirya Aisha da Fauziyyah magunguna sosai Mama ke ba Fauziyyah saboda tana matuk'ar tausaya mata da K'ADDARAR TAH, shiyasa ta dage dan ganin ta share mata hawaye, maganin matsi, maganin ni'ima, laushin da santsin fata, Umma ko 'yan maiduguri tayiwa magana suka zo har gida suka shiga gyara, ga abu yazo a kurarran lokaci dan ma da kud'i a hannu duk abinda kake so zaka samu duk yawansa, aiko nan da nan Fauziyyah ta canja tayi wani mugun kyau na fitar hankali ga fari, dama abinka da farar fata dirinta ya k'ara fitowa sosai, musamman hips da breast dinta, sosai kamarta da Ashwariyya rai ta fito. 




Haka ma Aisha duk abinda akeyiwa Fauziyyah itama anayi mata maganin matsi ne kawai ba'a bata, saboda ita cikekkiyar budurwa ce, su kansu amaran sun san sun canja ga wata muguwar zuba da sukeyi wani lokacin ma Fauziyyah har pad (Always) take sawa, ga wani tsumi da Mama ke basu kullum, suma 'yan maiduguri suna bala'il k'ok'ari akan aikin su dan turare bak'aramin kama jikin su Fauziyyah yayi ba duk inda suka zaun ko suka shiga sai kaji yana kamshi, haka ma ko abu suka tab'a kamshin yake, suma sosai suke basu maganin mata. 



Ranar juma'a ana gobe d'aurin auren, Fa'iz na kwance yana chart yaga abinda Sadik yayi posting a Facebook, aiko da sauri ya mik'e ya duba sosai, tabbas idonsa ba k'arya yayi masa ba gobe ne, d'aurin auren Fauzan sa da Sadik, da sauri ya duba Instagram, nan ma yaga yayi posting haka ma a Twitter, aiko zumbur ya mik'e yana cewa " ina dat is impossible, Fauza tawace ni kad'ai wallahi baki isa ki auri wani d'a namiji ba sai dai in bana raye, kai da ganin sa kasan kwata-kwata baya cikin hayyacin sa, da nutsuwarsa, jin abinda yake fad'a ne yasa Dr Adam mik'ewa yana cewa " what is going on abokina? kasa bashi amsa yayi sai wani dube-dube yake kamar zararre duk ya wani haukace, sosai hankalin Dr ya tashi, fita Fa'iz yayi Dr yabi bayanshi yana tambayar sa meke faruwa bai iya bashi amsa ba sai wayarsa daya mik'a masa, shima Dr ya firgita sosai da ganin gobe d'aurin auren Fauziyyah, gashi yanzu dare yayi wajen 9:30pm, kallon Fa'iz yayi yace " subhanallah, dare yayi yanzu gobe kuma 10:00am za'a d'aura aure, we are too late friend, ai Dr na fad'ar haka yaji kamar an zubure shi yayi waje yana sambatu da gudu, dan ji yayi kamar Dr ya watsa masa Acid, bin bayansa Dr yayi, duk kiran da Dr yayi masa bai tsaya ba sai a k'ofar gidan su Fauziyyah, Aisha da Farouk ya samu a k'ofar gida, da sauri ya nufe ta, yana zuwa ko sallama babu yace " where is she? kallan sa Aisha kawai tayi, bata ce masa komai ba, yace " please sister help me to call her, I need 2 see her please, sosai ya shiga rok'on Aisha akan ta kira masa Fauzan sa, kallon Farouk tayi , yayi mata kallon ok no problem, kallan Fa'iz tayi tace " kasan dai idan Abba ya sani bazai barta ta fito ba, so u hv 2 be take care, dan yanzu ma k'arya zanyi ince inji mijinta ne Sadik, ji yayi kamar saukar aradu a k'irjinsa jin an kira Fauzansa matar wani a gabansa, a tsakar gida ta wuce Abba da Baba suna cin abunci kasancewar ba nefa. 





D'aki ta shiga ta samu Fauziyyah tace " Aunty wai kizo inji Yaya, "to kawai Fauziyyah tace dan ita a zaton ta Sadik ne tace " yana ina?  yana waje, tare suka fito tana fitowa wata mota ta dalle mata fuska, ai ba Fa'iz ba kad'ai har Dr sai da gabasa ya fad'i dan sun tsorata da mugun kyan da tayi, dan shi Dr a zaton sama aljana ce, ganin Fa'iz na nufarta yasa Dr rik'e yace " kai wai baka da hankali ne aljana ce fa, tunda kake ka tab'a ganin mai irin kyanta a zahiri, murmushi Fa'iz yayi yace " she my Fauza, she d 1 I love, kamar dolo Dr ya saki Fa'iz shi bai ma san mai yake ba baki bud'e yana kallon Fauza ajiyar zuciya ya sauke yace " wowwwwww she so beautiful, Fa'iz dole ka haukace a kanta harka kamu da ciwon zuciya. 




A gabanta ya zube da sauri ta sunya ta tallafo shi tace " dear lafiy........ Maganar ce ta mak'ale mata had'i da muguwar fad'uwar gaba a lakacin da tayi arba da fuskar Fa'iz....... 



*Alhamdulillah*




*MOMYN ZARAH*



BYE