Kโ€™ADDARA TAH

41

by @hauwaausmanjiddarh

'''K'ADDARA TAH!!!'''


    ๐ŸŒน

   ๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

 ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



      ~NAH~



*HAUWA A USMAN*

     _(JIDDARH)_




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿป*

     _(DASHEN ALLAH)_




_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦ™ai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_




'''DEDICATED TO'''


*FAUZA M BALA MY FAUZA*

*SARATU MRS ADAM 'YAR MUTAN KAGARA*

*MARYAM AHMAD PAKI*

*AISHA AR MACHIKA*

*AISHA SADA MACHI*

*AYSHA HAMZAT*

*REAL MISS J*

*NURUL JANNARH*




*EDITING BY MOMYN ZARAH*


41


Bakin ta na rawa tace " Fa'iz, dai-dai lokacin da Abba da Baba suka fito daga gida, Abba ya yunk'ura da sauri zaije wajen su, Baba yayi saurin rik'o shi ya dakatar dashi, kuka sosai Fa'iz ya fara " please my Fauza karki cutar da rayuwar mu nasan kina so na, kema shaida ce ina sanki please karki yi abinda zaki dawo kina kuka babu wani d'a namiji dazai baki farin ciki sama dani. 




Hannu ta d'aga masa tace " kaga malam ya isa haka waya fad'a maka ina sanka, ni a zato na ma miji na nane, dan idan da nasan kai ne babu abinda zai fito dani, k'ara matsowa yayi kusa da ita yace " k'arya kike yi wallahi kina so na, babu kowa a zuciyar ki sai ni, duk wanda kike ikirarin kina so k'arya kike ni ne kad'ai a zuyark....... 




Hannu ta d'aga masa tace " ni zuciya ta babu kowa sai Sadik nace ban san ka ko dole ne, tsayawa yayi cak da kukan shi ya k'ura mata ido yace " har kin manta da alkawarin da kika yiwa mahaifiya ta na zaki kasance dani duk runtsi duk wuya, kin manta kince mata zaki tallabi rayuwata, zaki kasance tare dani bazaki tab'a rabuwa dani ba, yanzu gashi bata raye amma kin karya alkawari, kuka Fauziyyah ta saka irin mai karya zuciyar nan, zubewa tayi a k'asa taci gaba da kukan ta mai sauti kamar ranta zai fita.




Shima durk'usawa yayi a k'asa yaci gaba da magana cikin sanyi " Fauziyyah ina sanki fiye da yadda nake san kai na ina sanki fiye da komai da kowa, Fauziyyah bani uwa ko uba, bani da wa ko k'ani ke kad'ai ke gare ni, laifi ne nasan nayi na kuma amsa laifi na, please kiyi hakuri ki yafe man ko Ubangiji muna yi masa laifi kuma mu naimi yafiya ya yafe mana, balle mu a tsakanin mu 'yan Adam. 




Fauziyyah idan duniya ba'a yafiya da an shiga uku, da babu wanda zaici gaba, nasan a baya nayi wauta da sakarci kuma wannan ba komai bane sai sakarcin iyaye na, da kuma kuruciya, please ki zama mai yafiya a rayuwarki koba akai na ba, ki kema fa mai laifi ce a wajen Allah, Fauziyyah dani kad'ai kika dace, idan na rasaki mutuwa zanyi, kece rayuwa ta, Fauza please kice kina so, sassauta kukan ta tayi tace " Fa'iz na dad'e da yafe maka abinda kayi man tun lokacin, saboda nima ina san Allah ya yafe man laifuka na, zancen alkawarin Momy kuma Allah ya sani bani da laifi akanshi saboda ba'a yanzu nayi mata alkawarin ba, alokaci dana yi mata ban san ainahin waye kai na, kai ne wanda ka karya alkawarin Momy ba ni ba, sai bayan nayi alkawarin sannan kai kayi komai, zancen so kuma ni ban san ka.




Ta fad'a tana mik'ewa tsaye, da sauri ya mik'e yana kallonta, kallon sa takeyi itama tace " eh ban san ka ni Sadik nake so, ta fad'a tana kawar da kanta gefe tana kuka, hawayen fuskarsa ya goge ya rik'e kafad'unta ya shiga jijjiga ta yana cewa ki killi kwayar ido na ki rantse min da Allah kice baki so, ki kalle ni ido cikin ido kice baki so na Fauziyyah ni kuma wallahi idan kika kalle ni kika ce baki so na, bazan k'ara shiga rayuwarki ba, kanta a k'asa tana matsanancin kuka tace " I hate you I really hate you ban sanka, sakinta yayi, yayi baya yana cewa " no Fauza wannan bake bace,wannan maganar ba daga zuciyar ki take fitowa ba iyaka cinta bakin ki, Fauza ko za'a kashe ni bazan tab'a yarda baki sona ba, kina fad'a ne kawai dan jin dad'in bakinki, wallahi k'arya kike, ke kin isa ma kice baki so na, sai kuma ya sausauta murya yace" look at me, kin kallansa tayi, yace " ki kalle ni ido da ido kice baki so, kin dago fuskarta tayi dafa kafad'ar ta yayi da d'aya hannunsa d'ayan hannun kuma yasa ya d'ago hab'arta a hankali ya d'ago kanta, idonta a k'asa ta kasa d'ago idonta su had'a ido dashi babu abinda take sai kuka. 




Yace " please ki kalle ni, a hankali ta d'ago red eyes dinta ta kalle shi, yace " kice baki so na, kuka ta k'ara fashewa dashe tasa hannunta tana tushe bakinta, k'ara rik'e ta yayi yace " please kice baki sona kona hak'ura dake na fita daga rayuwarki, kanta ta shiga girgizawa tana cewa " I can't I can not Fa'iz, idonsa ya lumshe hawaye na zuba yana murmushin jin dad'i, a hankali ya jawo ta fita kinsa ya rungume yana sauke ajiyar zuciya, bata hana shi rumgumarta ba, sai ma lafewa datayi a jikinta, sosai take kuka, kanta ya shiga shafa mata yana bubbuga bayanta su manta da a k'ofar gida suke cikin sigar shagwab'a yace " mai yasa kina so na, amma zaki aura wani zak bari a raba mu, cikin kuka ta bashi amsa mishi " bani keda kai na ba, kasan ina da iyaye kuma sab'a musu bak'aramin illah bane ga rayuwa ta ba, dole mu hakura da juna muyi wa iyayen mu biyayya, abu d'aya na sani na kuma rik'e shine ina san ka, babu wanda zan so kamar ka, babu wani d'a namiji da zanso, Fa'iz ruhi na yana wajenka a koyushe a koina, zuciya ta tana tare dakai, biyayyar iyye na ce kawai zata sa na auri Sadik, muyi hak'uri muyi masu biyaya idan Allah yayi ni matarka ce to babu makawa saika aure ni, koda duk duniya bata so, cikin sanyin Jiki yace " in sha Allah ke tawa ce, tace" nika haka nake fata na rayu da kai, yace " ki sani koda Allah baiyi auren mu ba ina sanki ina miki gumun so, nafi sanki fiye da rayuwa ta. 




Cikin kuka tace " nima haka, yace " I love you, tace " I love you too, ya sake ta yace" sai gobe in sha Allah zanzo, kasa sakin hannunsa yayi, ta rik'e hannuns gam, tana kuka dakyar ya kwace ya juya yana kaka.




suka bar wajen, duk abinda ya faru akan idan su Abba da Baba, sai Sadik dake ta faman zaman zubar hawaye, ji yake kamar kirjinsa zai fashe zuciyar sa ta fito dan duk a binda ya faru akan idon su kuma sunji duk abinda suka fad'a, kasa koda motsi yayi ya kyame a tsaye sai hawaye kawai yake, hannun Abba Baba ya kama ya shigar gida, shima yayi gida, ita ko Fauziyyah nan ta durk'ushe ta saki saban kuka mai cin rai, sai Aisha ce ta shigar da ita gida, haka ma Sadik Farouk ne ya kaishi har d'akinsa ya kwantar, Fa'iz zaune sai faman rusa kuka yake yana fad'in na cuci kaina, nayiwa rayuwa ta illah, ya Allah ka zama gata na ka bani Fauza, Dr ne ya dafa shi, shima duk jikinsa yayi sanyi yace " am so sorry friend na tayaka bakin cikin rasa ta, Allah yabaka wata wacce ta fita komai, Allah yasa hakan ne yafi alkhairi, sosai ya lallashe ya kwantar masa da hankali, haka kowa ya kwana babu dad'i. 




'''WASHE GARIN A WAJEN D'AURIN AURE 10:00'''




Guri yayi guri, dubbun jama'a sun taru dan shaida auren Sadik & Fauza, kowa ka gani a wajen yana cikin farin ciki bakin sa a washe, mutane daga ko ina, abokanan Sadik, da friend d'in Farouk, ga dangin Baba, dana Umma haka ma dangin Abba da Mama sunzo, ga 'yan uwa da abokanan arziki, da 'yan unguwa, Abba da Baba sunyi angon Shadda haka ma Sadik da Farouk, karfe 10:30AM dubbin mutane suka shaida auren....... 





*Alhamdulillah*




*MOMYN ZARAH*



BYE