ARMAN MALEEK

P.7

by @autarmama

: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼



   *DAGA ALƘALAMIN*



SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️




  SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹)



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

    {R.S.W.A}


***

 *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




*P.7*




     Godiya yy sosai, kafin ya wuce tulin Escort dinshi na binshi a baya,kafin ma ya ƙarasa gurin Moto din shi an buɗe mishi mota, yana zuwa ya shiga da Bissimillah, rufewa aka yi, kafin suma duk suka shige motocin da suke bayan tashi da gaban tashi, a hankali suka fara tafiya cikin ƙwarewa.



     Asalin gidanshi da yake babbar Anguwar Shara-Mansir da take cikin Makkah suka wuce da shi, idanunshi na lumshe har suka ƙarasa tafkeken gidanshi da yake cikin Anguwar, gida ne babba na gani na faɗa,gaba daya gidajen da suke kewayen Anguwar gidan shine the number 1, z gurin kyau da tsari, har da wasu akwakun fitilu , masu kyau sai kaloli suke badawa.



     Sun danno kai gurin gidan gaba daya get din gidan mai kyau da tsari ya yaye yy sama, cikin natsuwa suka sulala da motocin cikin gidan , sun dan yi tafiya mai dan nisa kafin su iso Asalin cikin gidan wanda shima take dauke da wani get din, hon suka yi , wanda yasa da sauri Get man din gidan ya rugo ya bude musu get din.


 

    sulalawa suka yi ciki, suna shiga wani babban parking alot mai kyau da tsari wanda yake cike da motoci masu kyau kala-kala ya bayyana, gaba daya motocin a wajen parking alot din suka tsaya motar Yaa Shehi ce kawai ta samu guri cikin parking alot din.



     bayan Driver ya dai-daita parking a cikin parking alot din, aka bude mishi mota, a gajiye yake sosai, hakan yasa bai ɓata lokaci ba gurin fitowa daga mota, A hankali ya fito yana baza Alƙyabar jikinshi, cike da tsantsar gajiya yake dan lumshe gajiyayyayun idanunshi, tare da fesar da sanyayyiyar iska,haka har ya zo daf da ƙofar shiga cikin palon part din.



    tsayawa yy na yan mintuna, sai da ya ji takun Driver din shi kafin ya juyo, tattausan hannunshi ya miƙa mishi, brief case din shi ya miƙa mishi, karba yy kafin yace "Jazakhallahu bi khair..!", yana fadar haka ya juya ya shiga ciki.




     chan ciki yy sallama cikin muryarshi sanyayyayiya mai dauke da zallar gajiyawa, "Wa'ailaika Salama..!", wata Babbar Mace da zata iya kai wa 29 years ta furta cikin sanyin hali, idanunshi ya sauke akan fuskarta mai dauke da murmushi, ta gefenta ya wuce yana sauke numfashi, bata yi mgn ba har ya haye Upstairs.



     A hankali ta miƙe, kitchen ta nufa, bata jima ba ta fito da madaidaicin flask , da Ƙananan Cups sai kwalin Sugar da Tea spoon, saman ta haye, ƙofar farko ta kwanlwasa tare da tura ƙofar , haɗaɗɗen palo mai kyau da tsari ya bayyana, sanyayyan kamshi tare da sanyi ACn cikin palon ne ya haɗu ya gauraye Palon tare da bada wani ni'imtaccen kamshi mai sanyaya zuciya, tare da sanya natsuwa.



    kan daya daga cikin royal chair din palon ta zauna, tare da jaawo Center table ta daura tray mai dauke da flask da cups, jiranshi ta shiga yi, ganin an share 1 hour, bai fito ba yasa ta miƙe ta fita, tana fita ba da jimawa ba, ya turo ƙofar bedroom din ya fito, yana ta baza kamshi, yana sanye da Jallabiya fara tass da wando, kanshi yana luluɓe da hirami red da ɗigon fari, hannunshi zube cikin Aljihun Jallabiyar , sai zuba kamshi turaren huge boss yake, fuskarshi na fitar da wani Annuri da haske mai daukar hankali , yy wani fitinannen kyau , yana tafiya kanshi a ƙasa, yana tasbhi da baya rabuwa da bakinshi.




     zama yy kan kujera yana fesar da numfashi, jinginar da kanshi yy , tare da zame lips dinshi na kasa ya zamana yana cikin bikinshi, a hankali ya fara tsotsa cikin wani salo na musamman, wanda za'a kiranshi da Sexy moment , shi kuwa zallar gajiya da yunwa ce ta sanyashi yin hakan, dan rabonshi da abin ci, tun jiya war haka.



     Wayarshu ƙirar Iphone 13 pro, ya dauka a hankalin tare da daddana number, ring daya biyu a na ukku ta dauka cike da natsuwa tace "Assalamu alaika..!", "Wa'alaiki salam..!, Yunwa", ya furta da daddare.



    Yana ajiye wayar ta shigo sanye da hijab dark Blue , ta ziro siraran hannunwanta ta cikin hannun hijabin, fara ce sosai, sai dai tana da dan jiki ba laifi a shekaru ba zata gaza 16 years ba, colour ba Hijab din shi ya fidda Asalin kyan fuskarta, zagayayiyyar fuskarta ta fito rass ta cikin dan wuyan hijab din, tana tafe tana fitar da kamshin humra mai masifar kamshi.



    Sallama tayi,chan ciki ya amsa mata ba tare da ya bude idonshi ba, tana ƙarasowa tsakiyar palon ta cire zunbuleliyar hijab din jikinta, ta ajiye akan kujera 1 sitter, kyakyawar surar jikinta mai kyau da tsari da ta gama haɗewa cikin ɗamammum kayanta, masu kyau.

sanye take da riga fara body hug , sai black din wando skin tight ya bala'in dameta shima iya cinya.

gaba daya surar jikinta da ta kasance coca-cola a bayyane, jikinta sai glowing yake.



     ƙarasawa tayi kusa da shi, tare da dan zama ta shige jikinshu, a hankali ta furta"Shehi..!", idanunshi ya dan matse a hankali ta daura yatsun hannunta da suka sha jaan lalle akan fuskarshi tana bin sajenshi da yatsunta, tare da jaa mishi gemunshi.



     kyakyawan murmushi ya sakar mata tare da riƙe hannun yy kissing nashi .

yana bude idanunshi akam hannun, idanunshi ƙirrr akan yatsun na wasu mintuna, yana kallon jaan lallen da yy masifar yiwa hannun kyau sai sheƙi da ƙyalli yake, turo bakinta ta dan yi, tare da gyara zamanta sosai, gaba daya rabin jikinta ya zamana yana nashi, ta daura kanta akan kirjinshi, tana dan shagwaɓe mishi.



     "Waya miki..?", ta tsinci maganarshi a sama, "Ayyana..!", ta fada kanta tsaye, bai ƙara cewa da ita komai ba sai sakin hannun nata da yy yana gyara mata hular kanta mai gashi, wadda take kamar ta sanyi.



     zamowa yy da ita , tare da zama akan carpet, miƙewa tayi ta dawo gabanshi, tare da fara warware cups din da Ayyana ta haɗe gurin daya, daya ta ajiye, tare da bude flask , ta fara tsiyayo coffee sai tiriri yake, sai da tayi rafin cup din kafin ta barshi haka, sugar ta dauka kwara ukku ta zuba, tare da jujjuyawa.



     sai da ta gama ta kalleshi, shima ita ya kalla, sai ta kyarkyace da dariya, taɓe bakinshi yy bai ce mata komai ba, sai jawowa da yy shima ya fara haɗawa, sugar daya tal kawai ya sanya ciki tare da jujjuyawa, a hankali yy Bissimillah tare da fara skipping coffee .

tana gefenshi tana shan nata itama



      kafin ya gama sha tuni zufa ta wanke mishi fuskarshi, handkerchief ta dauka tare da fara goge mishi goshinshu, da yake fitar da zufa, sai da ya shanye tas kafin ya saki sanyayiyyar gyatsa, Hamdallah yy lokacin da ya tabbatar da cewar cikinshi ya cika .




      Sannu ta mishi, gyara zamanshi yy a inda yake zaune, kanta ta daura akan kafadarshi tace "Boɗɗi am ba zamu je gurin Affa ba ?", ta fada tana wasa da gashin kanshi, da yake har bayanshi, shiru ya mata , jaan gemunshi tayi, wanda hakan yasa ya lumshe idonshi, tare ƙara buɗesu sa boda zafin jaaan da ta mishi.



     Miƙewa yy, yana mikewa itama ta mike, da sauri ta nufi bedroom dinshi, bata tsaya ko ina ba sai gaban wardrobe dinshi, budewa tayi tare da zaɓo mishi wata baƙar Alƙyabba mai torch milk , fitowa tayi da ita a hannunta, tana zuwa ta rataya mishi, tana kallonshi, ƙarasa sawa yy , yana sauke numfashi bb karya ya gaji, amma idan bai wa wannan Yar rigimar tashi abun ya take so ba, baza ta bar shi kwanciyar hankali ba.



    trayn ta dauka , sai da suka zo in da hijab ɗinta take, ta dauka ta sanya suka fito, a kitchen din sama ta ajiye kayan suka fito, suna fitowa suka tarar da Zayn - Maleeq , tsaye da alama shigowarshi kenan, "na rigaka ai", ta fada tana dariya, tana ƙarasowa gurinshi suka yi shaking hands, shiru Yaa Shehi yy yana kallonsu, kafin cikin faɗa yace "ban hana ku wannan ɗabi'ar ba..?", ya fads cikin kakkausar murya, shiru duk suka yi, "uhmmm ya fada tana wucewa , da sauri ta bi bayanshi suka fita yana baza Alƙyabbar jikinshi.



     suna zuwa aka bude musu mota suka shiga, sai da aka fara tafiya, kafin ta zame daga in da take zaune ta koma kan jikinshi ta zauna, sai da suka dan yi nisa da gida yace ,"Ɗabi'ar banza ko.?, sau nawa ina miki gargaɗi akan hakan.? shi bake tuna cewar ke matar aure ce.? in ƙara ganin hakan zaki ga hukuncin da zan miki.", ya fada fuskar a kamile, "ba zamu ƙara ba, kuma gaskiya ni ba Matar Aure bace," ta fads cikin rigima.



     yana kallon bakinta yace "wace ke..?", tura bakinta tayi kafin tace "Yarinya mana, sai na girma zan aure", ta fads cikin zallar Yarinta, "Allahu yahdiki",da sauri tace "Ameeen", tare da lafewa akan jikinshi tayi shiru, har suka ƙaraso. ROYAL INTERNATION HOSPITAL da yake cikin garin Makkah bata ƙata cewa komai ba, dan hannunta ma na baki tana tsotsa, tuni na tuna da Munkhair dan kusan, Attitude dinsu iri daya ne.




    har mannewar konai kala daya, suna tsayawa ya zareta a jikinshi, tare da dan matsawa, ana buɗe mishi ya fito, cikin kamala da cikar zato, itama zagayawa akayi aka bude mata ta fito .



     Zagayawa tayi gurinshi, suka fara tafiya a tare,bayan ta gyara hijab dinta, ta rufe idanunta da niƙaf din jikin hijab din, idanuwanta kawai akr iya hangowa,haka suka shiga cikin Asibitin.


  

     bayan shigarsu cikin Reception din Asibitin suka nufi wani sashe na daban , sun dan yi tafiya , ƙafin su ƙaraso wani haɗaɗɗen sashe mai kyau, ƙofar Room  2, suka tura suka shiga bakinsu dauke da Sallama, Ayyana da bata jima da zuwa bace ta Amsa musu Sallama tasu, ƙarasa shiga suka yi cikin room din mai kama da gida , dan palo da bedroom ne , Zama Halimatu tayi kusa da ita tana mata magana, Yaa Shehi kuwa ciki ya wuce Abinshu ba tare da ya ko zauna anan din ba.



     duk da yasan ko yy Sallamar bb wsnda zai Amsa mishi amma haka yy Sallamar, tare da shiga ciki, bed din ya nufa, tare da raɓawa gefe ya zauna, wani kyakyawan Tsohon mutum dan ba'a ƙirashu da matashi ba dan zai haura 70years na kwanxe akan bed din, fari ne sosai wanda kalli daya zaka mishi kawa Yaa Shehi kasan suna da dangantaka ya jini sosai.



     ko dai Mahaifinshi ko kuma Yayanshi dan kamarsu har ta ɓaci, sai dai yana kwance ne , yadda kasan butun butumi, baya motsi, ban da idanunshi farare tar da suke jujjuyawa bb wata jijiya ta cikinshi da take harbawa, riƙe hannunshi Yaa Shehi yy, tare da mishi magana a hankali, duk da baya iya mgn Amma fuskarshi ta fallasa Asirin jin dadin ganin Yaaa Shehi da yy, dan sosai fuskar ta washe duk da va murmushi bane kan fuskar, kuma ya kafe guri daya da ido.



     Ayyana da Haleematou ne suka shigo cikin bedroom din, Yaa Shehi ne ya kalli Ayyana , cikin girmama Yayar tashu yace "Zaytun", ya fada ya a rike hannun Affa, matsawa tayi kusa da Drawer din da kaya yakw jere, ta dauko kwalbar Zaytun ta miƙa mishi, ƙarɓa yy tare da budewa ya tsiyaya, ya fara shafa mishi a hannunshi da yake tubus bb gautsi bb komai .



     kamar bayan kifi tsabar sulbi, na dauka hannun ne kawai, sai da naga har ƙafafunshi da yana shafa mishi haka yake taushi tuɓus, sai yanzun na gane dadewa ne a guri daya zaune, da tsabar gyaran da yake samu.




      sai 10pm suka shirya wucewa, suna fitows su Zayn na zuwa dan sune suke kula da mahaifin nasu da daddare, har za suyi shaking hands shi da Haleematou sai kuma suka tuna da gargadin Yaa Shehi suna juyawa suka ga ya tsaresu da ido kuwa......