Chapter 11
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 21-22
Aguje su ke tafiya, duk irin magiyan da ta ke mu su basu juyo sun kalleta ba, dan haka ta daina bige bigen da ta ke ta zauna kawai tana kuka tare da magiyar su yi hakuri su sauketa.
Babu wadda ya juyo ya kalleta, tun ta na gane hanya har aka shiga in da bata ganewa, wannan ya sake daga hankalin Nur, tafiyan kusan awa daya sannan ta ga sun doshi wani katon get, wannan lokacin so tayi ta dauke numfashinta domin ta fara cire rai da duniya, gidane dandasheshen gaske, gani kawai ta yi get din ya bude batare da tasan waye ya bude ba, wannan lokacin raba ido kawai take da busheahen hawaye a idonta. Bayan motar ta faka a cikin harabar gidan matukin motar ne ya sauko da saurin sa, sannan ya bude bayan motar ya ce, "fito"
Jin hausarshi bata fita sosai ta da ga kanta ta kalleshi, baki ne katon gaske, damtsen hannunsa irin na masu da ga karfe, ga wani narkeken cross a wuyanshi, dauke kai ta yi da sauri ta waiga bayanta da take jin motsi, dayan ta sake gani a bayan ta shima da cross dinne a wuyansa, wannan ya tabbatar mata da su din ba musulmai bane, tafiya ta fara, ta na bin bayan daya kamar yadda ta lura abinda da suke so kenan, acikin zuciyarta ta shiga Kiran sunayen Allah.
Banda raba Ido babu abin da Nur ke yi, Cikin wani katun falo suka shiga, mutumin da ke zaune ya daura kafa daya kan daya tabi da kallo, waya ya ke dannanwa har suka durkusar da ita a gabanshi tare da cewa, "Gata" Da sauri ya dago kan shi ya kalleta tare da sauke kafar shi kamar zai taketa.
Ganin ya na kokarin sauke kafarshi tai saurin ja da baya, tare da dagowa ta kalleshi, "A fili ta ce, Innalilahi wa Inna ilaihir raju'un" Ido hudu suka yi da Poul dake tsaye a gabanta ya na mata kallo me cike da tsana, sunkuyar da kanta ta yi kasa tare da nemo dalilinsa na sawa a dauko mishi ita, ko tantama ba ta yi akan su Mamma da Helen ne da suka musulunta, nan ta ke hawaye ya fara zubo mata domin ta rasa abin yi, gaba daya jinta take a kidime.
Bata an kara ba ta ji an rike hijjabinta da karfe da alama shirin figeshi ya ke a jikinta, dan haka ta mike da sauri tare da cikuikuye hijjabin a jikinta tana fadin, "Duk abin da zaka min kamin da Hijjabina karka ciremin hijjabi."
Bece kala ba, ta bayanta ya miko hannun sa ya murde na ta duk biyun, cikin kankanin lokaci ya cire Hijjabin yai jifa dashi, bayan ta tabbatar da ya rabata da Hijjabin ne ta fashe da kuka tare da cewa, "Dan Allah ka bani hijjabina, ko kasheni zaka yi ka kasheni dashi a jikina." Tsaki ya ja sannan ya koma gurin zaman sa ya zauna tare da cewa, "Idan na kashe ki ma ai ban huce ba, aikin ku kenan hijjabi-hijjabi, can karshen naki zansa a yi fata fata dashi yanzunan, sai dai bakin ciki yasa ki mutu da kanki, kamar yadda ni ma kika dasa min bakin cikin da zai yi saurin hallakani."
"Babu ruwana, bani bace, su da kansu suka ka zabi hakan, ni ma daga sama na ji labarin." Mikewa ya sake yi a karo na biyu ya fara zagaye Nur tare da fadin, Koma mene ne ke kika sani wannan zai zama Jan kunne ne a gareki, dan da ga yau bazaki kara shiga gonata ba, ko ban shata miki layi ba."
"Wannan shine shata layin na ka ai, da ga yau bazan kara shiga gidan ka ba, dama Mamy ta dade ta na gaya min irin wannan."
Ba irin wannan take gaya miki ba, dan na tabbatar ita kanta da ace ta taba yin tunani irin abin da zai faru dake a yau zai iya faruwa ta dalin na da tuni ta rabaki da gidana, kamar yadda ni ma da ace nasan irin abin da kika min zai faru da tuni na rabaki gidan Koda ace binneki zan yi da ranki."
"Karka lalatamini rayuwa ka kasheni kawai"
"Ko na kasheki ban huceba, gara ki rayu da kunar zuciya, kamar yadda ni ma zan rayu da radadi acikin zuciyata."
"Allah bazai baka sa'a ba kan mugun nufinka akaina ba, Kuma Allah ya isa ciremin hijjabin da ka yi..."
Tun kafin ta rufe baki ya wanketa da Marin me zafin gaske, cikin sauri Nur tasa hannunta ta dafe gurin tare da runtse idonta, jin wann radadin Marin ya tuna mata zabar marin da Abdallah yayi mata kwanaki, yau ga kwatankwacin shi. Bayan zafin ya lafa mata ta bude idonta tare da kallon hannun da ta dafe kuncinta dashi, jini ta gani a hannun da haka ta Kara shafa kuncinta, jini ne wadda ke fitowa daga hancinta, dan haka ta mike a lokacin da Poul ke cewa "Kuje da ita."
Batare da wani bata lokaciba suka fara Jan Nur, ihu ta shiga kurmawa tare da cijewa, saidai duk da haka Saida suka yi nasaran shiga da ita wani daki me dauke da gado, kara rudewa Nur ta yi a lokacin da ta ga sun fara cire kayan dake jikin su, gaba daya su biyun suka cire, ya rage da ga su sai gajeren wando, ganin su manya-manya ta kara firgicewa, kayan makarantar da ke jikinta ta kalla riga da wando, kanta ta shafa dama hijjabi kawai ta sanya batare da ta daura dankwali ba. Hankalinta da maida gurin tika tikan maza dake shirin dufarota hawaye na tsiyaya a idonta take fadin, "Dan girma Allah ku yi hakuri, karku tabani, ko me kuke so mu je gurin Abbamu ya baku, dan Allah karku tabani" ganin suna daf da ita ta tsuguna akasa ta kurma ihu tare da sa hannunta ta kankame jikinta, sai dai duk da haka ji ta yi an dauktae cak, kamar an dauki riga an yi jifa da ita zuwa gado, dan haka ta shiga fadin, "Allah karka basu dama, ka tai makeni ya Rabbi, ya Allah ka kawo min agaji, dan darajan mazon Allah" cikin karaji take kiran suna yin Allah da manzonsa, gani ta yi dayan ya rike kafafunta yayin da dayan ya kwanta ajikinta yana kokarin fincike rigarta, duk da haka bakinta be mutuba, ihu kawai take tana Kiran sunan Allah.
Duk ihun da Nur ta ke a kunnen Poul, har yanzun ya na zaune a falo kafa daya kan daya, a wannan lokacin duk tabi ta dame zuciyarshi, ba ihun bane ke damun shi, Allah da Annabin da take maimaitawa ne ke hanasa sukune, aduk lokacin da ta ambata sai gabanshi ya yi mummunan faduwa, a hankali ya sauke kafarshi tare da mikewa da sauri, wannan lokacin yaran nasa ne suke bashi haushi domin bega dalilin da zaisa su barta har tana magana ba, dakin ya nufa da saurin sa, ganin shigowansa wadda ke rike da kafar Nur ya waiga ya kalleshi, cike da tsawa Poul ya ce, "Mene ne haka? Wannan yar yariyar ce har zaku kasa make bakinta ku barta taita mana surutu?"
"Oga duk ihun da za ta yi babu me jinta anan ai" Tsaki Poul ya ja tare da yi ma su alama da hannu akan cewa su fita a dakin, cikin sauri wadda ya danne Nur ya sauka tare da daukan kayanshi, shima dayan nasa ya dauka ya fici a dakin, tura kofar Poul ya yi sannan ya fara takowa zuwa cikin dakin tare da balle butirin gaban rigarshi ya na fadin "Ki rufe min baki idan kika sake magana saina zubar miki da hakora."
"Cikin muryanta data fara dashewa sabo da kuka ta ce, "Dan girma Allah ka taimakeni ka barni in tafi agida za'aga na dade."
"Babu abin da ya dame ni" ya fada a lokacin da ya cire rigarshi ya fara kokarin cire agogon shi.
"Addu'a Nur ta cigaba da yi afili, duk da cewa Muryanta ya fara dashewa Amman Yana jinta dan haka alokacin da ya ke kokarin hawa gadon yake cewa, "Ki cigaba da kiran Allah har inzo gurin in same ki, karki daina kiran Allah ki gani."
Gadon ya hau tare fincikar rigarta da alama yage rigar yake son yi bawai cireta ba, yana rike da kafarta yake fincike rigar, tuni ta fara yagewa haka yayi ta farka rigar kaca kaca har har ya ficiketa ajikinta; ya rage daga ita sai bra sai dogon waddon maka ranta, kallo ya bita dashi sosai, har yanzun yana rike da kafarta har wannan lokacin bakinta be mutuba, duk wata addu'a da tazo bakinta yi ta ke, tare da kokarin fincike kafarta, tana cikin wannan halin taji karan barkewan dogon wandon dake jikinta, dan haka ta kara gigicewa tare da fita cikin hayyacinta, alokacin da hankalinta ya dawo jikinta daker ta iya bude idonta, ganinta har yanzu acikin wannan dakin ta furta "Innalilahi wa Inna ilaihir raju'un" jikinta ta kalla, ganinta tube tai saurin jawo bargon ta rufe jikinta tare da waigawa tana kallon dakin kota wanni kusurwa, ganin babu kowa a dakin ta yunkura da nufin tashi zaune...