BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI?)

3 sakamako

by @zeeyyybawa

*BIBIYATA YAKEYI *

_(WAYE SHI?)_



*بسم الله الرحمن الرحيم*


 BY 

    ZAYNAB BAWA




Marubuciyar 

*BIBIYATA AKEYI*

*Y'AR FARI*

*YARIMA FAYAD* paid book 200

*ƘADDARAR RAYUWA*




Assalamu alaikum

Ina kuke manyan mata?


Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su

Virgin again

Tightening pills

Turaren ban mamaki

Sweetness agents

Wetness agents

Infection set da sauransu

Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern

***




*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*


INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!


  TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).


  WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI! 


 BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝


  PAGE 3



  Kallon Mama nayi naga tayi shiru tana saurarena ni take jira na bata amsa batareda bata lokaci na nace.


" Tace saboda mahaifiyarsu tabar gidan ta dalilinta." shiru Mama tayi sai can tace.


"Allah ya rufa asiri." Na amsa da 


"Amin." 


"Gobe idan Allah ya kai mu zaki koma dakin yayyunki da kwana, Saboda bai kyautu ace mu muna kwana da yaran mu daki daya su kuma suna can su kadai ba." Toh kawai na amsa dan nasan dole hakan zata faru. Mama nasake kiranta. Cikin kaguwa da tambayoyina tace.


"Mamee ki kwanta kiyi bacci yanzu dan bazaki fahimci lamuranda suke faruwa agidannan ba amma idan lokaci yayi zaki fahimta"


 "Zan kwanta Amma Mama yakamata izuwa yanzu ace kowa yayi hakuri tunda abun yadauki shekaru" kallona sosai tayi sai can tace.


 "Mahaifinku yana bukatar ganin iyalansa a hade waje daya baida burin daya wuce wannan, ki kasance mai son yan uwanki kada kitaba kullatar yan uwanki a wani dalili komai girmansa" Kai kawai na gyada tace.


 

 Dare yayi ki kwanta na amsa na lumshe idanuwana ina karanto addu'oi ahaka har bacci ya daukeni."



Washe gari na koma dakinsu da kwana, naji dadin zamana a dakin Saboda suna da wayar Android hakan ya sanya idanna bace cikin dakin ko motsina ba'a jiyowa barin ma idan na samu wayar da data na ringa bin labaran yan wasanni kwallon kafa kenan. Nafi amfani da wayar Fadeela dan tafi saukin kai saboda kwanaki kadan da muka yi da ita har mun saba da ita, kuma itace Babba dama. Zaman mu da ita yasa ta fahimci yanda nake masifar son wasan kwallo hakan yasa take download na wasannin koda na tafi hadda ta ajiye min. Aysha kam yawanci gaisuwa kawai ke shiga tsakanina da ita dan ita sam bama tada sakin fuska ba kamar fadeela ba."


 ———

Dawowar mu daga sallahr la'asar kenan babu wani malamin daya shiga mana, hakan yasa muka zauna muna ta hira nida kawayena muna dan hirar mu, Maryam ta dubeni tace,


"Mamee an duba miki results kuwa?" Da mamaki na dubeta nace. 


"Result ya fito ne? Kai Wallahi ban sani ba."


"Toh Yaya zakiyi ki sani tunda ke ba waya ce dake ba? nidai an duba min nawa kuma na haye, gabaki daya fa mu hamsin ne muka haye cikin mutane dari biyar."


Gabana sai da ya buga darram dan ni kaina nasan bani da kokarin da zan haye mutane dari biyar. Kuma Maryam ma ai bawani kokari take da shi ba tunanin ya fado min cewa ai baban Maryam yana da kudi sosai ko nawa ne zai iya biya dan Maryam ta haye jarabawarta. Maryam ta tabani tace.


"Wai ya haka ne daga cewa result ya fito sai jikinki yayi wani sanyi?"


"Uhm ai naji kince mutum dari biyar ne Maryam ina naga kwakwalwar haye mutane har haka? Kedai na miki murna Allah ya sanya alkhairi amma nikam nasan bazan wuce ba." Dariya tayi tace.


"Haba karki bani kunya mana har nawa mutane dari biyar suke?" 


"Uhmm keni kibarni tukunna ban san me zan cewa Baba ba har indai banci jarabawar nan ba." 


"Babu komai in sha Allahu duk yanda nasa kafata kema zaki saka taki da izinin Allah" 


Karfafa min guiwar da Maryam tayi ta yi ne ya sanya na dan ji sanyi amma jikina ya gama bani bazanci wannan jarabawa ba. 


Ganin yanda na dawo ya sanya Maryam yin dariya sosai ta dauko wayarta kirar iphone 7 ina kallon wayar nasan abunda zata yi hakan yasa nayi saurin sauke nikab dina a hakan Maryam ta dauki photon, nayi saurin fauce wayar na maida jakar ina fadin. 


"Ke baki da hankali koh? Idan aka sake kama wayar nan kinsan bazata fitoba, kuma wallahi ni dake duka sai munsha duka." 


"Toh wazai kama? Bayan duka malaman suna meeting.?" Mtsww naja tsaki nace. 


"Wancan karon ma waya san za'a kama?" 


"Oho dai nidai bani wayata" 


"Bazan bayar ba." Na fada ina sake ɓoye Jakarta. Bangama rufe baki ba malami ya shigo na dubeta nace. 


"Kinganni koh?" Shiru tayi bata kulani ba.


Malamin bai dade aciki ba ya sallama mu saboda lokacin tashi yayi. Sai da aka tashi kafin nabata wayar tata. Kamar munafuka haka na shiga gida dan nasan har indai Baba yaji labarin fitowar result to ya saka an dubo masa. Amma sai naji shiru hakan ya tabbatarmin da Labarin bai iso Baba ba.


 Washe gari sassafe na tattara kannena muka wuce Hadda dan banaso labarin fitowar result ya isko baba ina gidan.



Picture dinda Maryam ta daukeni a wayarta nake dubawa bada son raina akayi pic dinba amma ba karamin kyau nayi ba dukda kasancewar da nikab a fuskar sai yaba pic din nakeyi Maryam ta harareni tace.


 "Da jiya ba kin tsayawa nadauki pic din kikayi ba? Gashi yanzu sai kallo kikeyi inada tabbacin baki taba daukan pics mai kyawunsa ba" tsaki naja na mika mata wayar hadeda fadin "yar rainin hankali Allah yasa akarbe wayar" 


"Ba amin ba muguwa" ko kulata banyiba na tashi nabar wajan, mikewa itama tayi ta biyo bayana muka koma aji.


 Yau ba kamar kullum danake jiran lokacin tashi yayi kawai natafi gida ba. Yau lokacin nema banaso yayi. Saboda nasan komai ake ciki yanzu Baba yasan da zancen fitowar result kuma yasaka anduba masa. Hakan yasa nake ganin kamar lokacin yana tafiya dasauri. 


  Ganin gabaki daya Hankalina baya jikina yasanya maryam tace.


"Wai har yanzu zancen result dinne? Meyasa jiya baki sanarwa Baba ba? Nasan daya dade da sakawa an duba miki"


 "Hmm ke kibari wallh tsoro nakeji shiyasa dan aure zaiyimin idan banci ba"



 "Aure!" Maryam tayi exclaiming hadeda zaro ido. Toh har nawa kike ma?" Sai kuma ta tuntsure da dariya tana tsoanata amarya takaici ya sanya nakasa amsa mata.




Har lokacin tashi yayi ban kulata ba da aka sallememu saida gabana yafadi saboda bansan abunda zan taras ba agida ba. Banbi ko takan maryam ba jikina babu kwari natashi naje na hado kan kannena mukayi gida, Haka nashiga gidan kamar wata munafuka sai rabe-rabe nakeyi dan banaso na haduda Baba.



Ina shiga nasanu Mama zaune a falonta nayi mata sannu zan shige ciki tace min. 


"idan kin canja kayanki kije babanku yana kiranki." Tun datsu ya aiko yace idan kika dawo yana nemanki Sai da naji faduwar gaba. Na amsa na shige ciki na canja kayan Uniform zuwa kayana na gida. Haka dai na nufi wajan Baba jiki a sanyaye."



PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance, 

 account 0003075326

Zainab m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta *** da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan 

tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."

 Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike." 


✔️ote

Follow 

Comment 

Share please 



To be continued 


Zaynab Alabura 💕