SAKATARIYA TA

Chapter 7

by @azizat

Hankali kwance Farida ta ke hidiman biki. Anas dai ya kira ya ma ta faɗa akan tafiyarta, acewarsa kwana uku yai yawa sannan ya sanar da ita Najeeb ya koreta sai dai kar ta damu ta zo ranan Monday ɗin kafin nan zai roƙe shi. Ita kam ko ajikinta dan ta san abinda ta shirya wa Najeeb.


Ranan Jumma'a su Ummi su ka zo daga Jos, murna wajen Farida ba'a magana. Ranan Asabat aka ɗaura auren *Hajara Musa Wase da Haladu Iliyasu* sai *Salima Musa Wase da Jabir Muhammad*


'Yan uwa daga Wase da Giyaɗe duk sun zo, da ke Baffa Musa da Baaba Sabuwa duka 'yan Wase ne. Ita Anty Hanne kuma 'yar Giyaɗe ce.

Haka aka sha hidima lafiya, duk da an ɗan samu rikici ranan yini saboda magulmata wanda su ka tisa Baaba Sabuwa a gaba kan rashin auren 'yarta Maijiddah. Maijiddah ta yi kuka har ta ƙoshi duk da ta san akwai alamun kukan na ta ya kusa ƙarewa amma kuma madamar ba auren ta yi ba, ita ko Baabarta ba wanda zai samu sukuni...


.......................


Shigar Abaya ta yi mai adon duwatsu kalar gold. Gyalensa ta yi rolling da shi sannan ta ɗau jakarta ta fito, gidan dai an watse sai 'yan tsiraru. Ummi ma ta tafi jiya saboda aiki da za ta koma.


"Allah dai ya sa Sir Najeeb ya haƙura idan ba haka ba kuma kin gama aiki kenan a Najeeb constructions"


"Ya ma isa ya koreni. Lallai! ai Yakubu ka zuba ido kawai ka sha kallo amma yau ko ana ha maza ana ha mata bazan ajiye aiki ba"


Yakubu girgiza kai kawai ya yi ya tada machine ɗinsa su ka tafi...


 

Sandy mai goge office ɗin Najeeb ne ta cewa Farida Najeeb ya zo lokacin da su ka haɗu, za ta shiga lifter ita kuma Faridan ta fito.


 Ta na ajiye jaka ta wuce office ɗin sa. Yana duba wa su takardu ta shigo.

"Good morning Sir"

Ya ji shigowarta amma ya share ko ɗagowa bai yi ba.


"Sir akwai aikin da zan yi ne?"


Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta. 

"What part of my message did you not understand?"


"Sir na ga saƙo ta email ranan Laraba wai an koreni daga aiki"


Ya ɗaga ido ya ce "and?"


"Ban koru ba mana. Ba laifin da na yi sannan ko na yi laifi ma, tsarin da ka shirya min ya hana ka koreni"


"Listen Miss Salihu. Na san Saboda Anas ki ka dawo, but ki sani. This is my company, just like you Anas is my employee. So, na koreki ba abinda Anas zai iyayi akai. Now get out of this place bitch"


Fita ta yi daga office ɗin ba tareda ta ce ƙala ba. Minti biyu sai ga ta ta zo da takardu a hannunta


"Ga shi nan, wannan takardar shedar amincewarka ce da tafiyata. Wannan kuma kai ka amince zan yi aiki da kai na wata shida ba tareda ka koreni ba, idan har ka koreni to za ka dinga biyana salary har wata shida ta cika kuma......"


"Wait whats this? When did i sign this? I never signed this"


"Ka kalla dai da kyau Sir Najeeb Jibo. Ka san tabbas signature da ke jiki kai ka yi, you stamped and signed it"


"This is bullshit" ya faɗi tareda yaga takardun


Farida ta yi dariya ta ce " na nawa kuma wannan ma ba original ɗin bane. Original ɗin na nan, so ba inda zan je"


Ta fita daga office ɗin...


Anas ne ya shigo office ɗin ta da sauri "'yar uwa mi ya faru? Najeeb ya kira ni yanata kwarwa"


"Ce ma sa na yi bai isa ya koreni ba"


"Barin shiga na ji mi zai ce" ya shige office ɗin Najeeb da sauri...


  

Yadda Anas ya ɗau alamarin fa ba da sauƙi bane. Domin Najeeb faɗa ya ke ma sa kamar tsohon zaki, cewa yai ya kawo ma sa mahaukaciya, yarinyar ba ta ganin girma ko darajar sa.


"Amma Najeeb we've talked about this ai, na roƙeƙa ka bata wani chance ɗin"


"To hell with her. I dont want to work with her, can you imagine wannan yarinya ta creating documents ta sa na signing ba tareda na san miye a ciki ba. The girl is a crook, she's just...."


"Haba yallaɓai. Duk wannan tashin hankalin akan mace, ban sanka da haka ba"


Najeeb ya kalli Anas ido cikin ido ya ce " get her out of this office or i will use force, and you know i will do it"


Ganin yadda Najeeb ya bircike ya sa ya fita ya samu Farida ya ce dan Allah ta koma gida zuwa gobe idan Najeeb ya huce zai kirata sai ta dawo. Farida ta tafa hannu ta riƙe ƙugu ta ce "Ya Anas ba inda zan je. Ai yau idan bai haƙura ba zai ga haukata muraratan. Ba ri ma kaga"


Ta wuce office ɗin Najeeb.


"Ka ga Sir Najeeb kar ka bari na nuna ma ka haukata anan, kai shikenan ba dama mutum ya ɗan yi ƙaramin laifi sai ka ce kora, to yau ka gamu da gamonka. Ba inda zan je idan ka takura kuma na shigar da kai ƙara tunda da izininka na tafi hutu" ta san hakan zai iya faruwa shiyasa ranan laraba da ta zo ta typing documents ɗin ta haɗa cikin wasu da zai signing shi kuwa ko dubawa bai yi ba ya dinga signing ɗin su.




"Well lets see how tough you are" ya faɗi tareda ɗaukar waya ya kira security.

Anas da ya shigo office ɗin ya fara bashi haƙuri. "please dont do this. Ba girmanka bane wallahi. Za ta bar maka aiki amma banda koran walaƙanci dan Allah"


Farida ta ce " Ya Anas ka barshi, security ɗin su zo ina nan ba inda zan je"


"Farida ki yi shiru ki fita, i'll handle this"


"Yadda ya ke ji da taurinkai ni nawa ya ninka na shi. Mun fafata da arnan Jos ma balle shi"


Ana haka sai ga wasu murɗaɗɗun security sun shigo, dukkan su biyu da ka gansu ka san basu da mutunci da alama ma ba musulmai ba ne.


Najeeb ya tashi ya zo gaban Farida ya ce " for the last time, LEAVE"


"Allankatafir ba inda zan je"


Shi kam Anas baza ido kawai yai yana kallon wannan dramar.


Najeeb ya dubi securities ɗin ya ce " throw her out of my company, i dont want to see her here again"


Ɗaya daga cikin securities ɗin ya nufo ta yana ƙoƙarin  riƙe ta, aikuwa ta yi tsalle ta faɗa jikin Najeeb ta cukwuikuyeshi tana ihu tana faɗin wallahi ba zan fita ba ko za a kashe ni.

Najeeb ya rintse ido lokaci guda kuma hankalinsa ya tashi. Cikin zuciyarsa ya ke mamakin abinda ya faru, ba wai rungumeshin da ta yi ba, sai dai effect ɗin da rungumar ya jawo ma sa. He cant believe he got erection because of this crazy girl. 


Security ɗin ya kai hannu zai janyo Farida daga jikin Najeeb, Anas ya daka ma sa tsawa ya ce su fita daga office ɗin.


Najeeb har lokacin idonsa a rufe, ya rasa ya zai yi, he's afraid of pushing her away saboda Anas da securities za su ga yadda engine ɗinsa ta miƙe. He cant embarrass himself infront of this crazy girl dan haka cikin hikima ya sa hannu ya turata da ƙarfi before you knew it ya juya da sauri yai hanyar banɗaki.


Anas da ke recording abinda ke faruwa yai kan Farida da ta faɗi ƙasa warwas. " sorry 'yar uwa, tashi" da ƙyar ta miƙe da taimakon Anas saboda ƙugunta da ya bugu sosai...


Ya ƙara zuba ruwa a fiskarsa a karo na ba adadi. Ya kalli kan sa a madubi sai lokacin ya ga yadda jacket na shi ya ɓace da janbakinta.


"This girl is a witch. How could this possibly happen?"Rabon shi da shiga yanayi irin wannan ma ya manta....


"Oga ka fito ayi magana, ka haƙuran ne ko dai" muryan Anas ya katse shi.


Ajiyar zuciya yai sannan ya fito riƙe da jacket a hannunsa yadda ya riƙe ka ce kashi ne ajikin jacket ɗin. Yana fitowa Anas ya sa dariya.


"Get out Anas, i dont want to see anyone"


"Ka huta mutumina irin wannan al'amari sai da hutu ai"

Najeeb ya wurga ma sa jacket ɗin. Anas ya chafe ya ce " wannan jacket ɗin ta tarihi ce" 

Sai da ya kai bakin ƙofa ya ce " kar ka manta za ka saurari presentation daga Team D ƙarfe goma. Zan sa sakatariyarka ta tuna ma ka idan lokaci ya yi"


Najeeb ya ce " Anas i'll kill you"....


Anas na fita ya samu Farida ya ce " gaskiyar Yaks da ya ce ke da Najeeb fire and fire ne sai dai gaskiya ta ki wutar ta fi tasa zafi. Kar ki bari kowa ya shiga office ɗin sa sai nan da 1hr kafin nan ya huce"


Farida ta amsa da " ok"


Ko ajikinta dan ta san haƙarta ya cimma ruwa...


Yana zaune ya sa hannu a ƙirjinsa yana shafawa ashe yarinyar nan har cizonsa ta yi, da ya duba wajen a madubi yai wani jaa abinka da farin mutum.


"She'll pay for this, i'm not sending her away. Not until she suffer, i'll make sure she cry and cry and cry"



Yana zaune ya kunna laptop ɗin sa " lets see what the witch is doing" 


Tana zaune tana danna waya ga biscuit agefe tana ci. Har zai kashe sai ya tsaya saboda shigowar Khalidah da ya gani. " another bitch" ya faɗi a ran sa...



Kai tsaye hanyar office ɗin Najeeb ta yi Farida ta ce " Malama tsaya"


A gadarance Khalidah ta juyo "and who are you?"


"Idon ki dai bai makance ba ina?. Kin san dai aikin wanda ke zama a kujeran nan ko"


"Ya kamata ki sani, matsayin ki bai kai ya hanani shiga office ɗin Najeeb ba"


Farida ta taso " Sir Najeeb ya ce bai son ganin kowa sai nan da awa ɗaya dan haka. Ko ke wacece sai dai ki dawo anjima"


"Ki hanani shiga idan kin isa?" Khalidah ta faɗi tana ƙoƙarin shiga. Farida ta sa hannu ta jawota da ƙarfi.


"Ki riƙe matsayinki Malama, ko kuma wallahi ni da ke sai mun kwashi 'yan kallo"


"Ki matsa na shiga. Ke kin ma san ni wacece a kamfanin nan?"


"Najeeb constructions na gani ba Najeeba constructions ba dan haka duk matsayinki a ƙarƙashin mai kamfanin nan ki ke"


"Hmmm za ki sha mamaki yarinya, ko kwana ɗaya ba za ki ƙara anan ba Najeeb zai koreki, wanda su ka fi ki nitsuwa ma ba sa daɗewa balle ke shashasha"


"Eh na ji dai. A bi doka a zauna lafiya"


Khalidah ta yi tsaki ta fita. Sai da ta tafi Farida ta ja numfashi ta ce " wai! na sha da ƙyar. Wannan matar fa ta riƙe ni ba ƙaramin jin jiki zan yi ba. Allah ya yi halitta anan"


Najeeb da ke kallon komai ya ce "scary bitch"...



..............


Ƙarfe goma saura minti biyar ya fito daga office ɗin sa.

"Sir na biyo ka ne?"

Bai kulata ba ya fita bayan ya harareta.


Da ya tafi ta ce " ka ji dashi, ni kam kujeran nan tawa ce ina nan daram da kai"


Lokacin da zai dawo tare su ka dawo da Khalidah. Su na shiga office ta cigaba da bayanin abinda Farida ta ma ta sai dai hankalin sa ma baya gareta yanaga takardun da ya shigo da su.


"Najeeb ba ka ce komai ba"


"She's doing her job" ya faɗi ba tareda ya kalleta ba


"Najeeb yarinyar nan 'yar iska ce, ƙila ma 'yar ƙwaya ce kaga ɗazu wai za ta yi kokawa da ni idan na ce zan shiga office ɗinka"


"So?"


"Najeeb ka koreta, ina wancan Joseph ɗin nan da ya ke aiki da kai kafin na yi tafiya"


"Look Khalidah, i fire who i want to. For now that girl stays"


"Najeeb i demand you to sack that girl"


Da ƙarfi ya buga desk ɗin gaban shi.


"Look Khalidah, dan mahaifinki yanada 8% share a kamfanin nan doesnt mean you can make rules here. I owned 75%, i make the rules here. Understand that or ask your father, he'll explain to you. Now get the hell out of my office"


Khalidah ta fice fuuu cikin fishi.


.............


Cikin sati uku da Farida ta fara aiki a Najeeb constructions ba wanda bai santa ba. Wanda su ke tunanin ba za ta jima ba sai gashi har sati uku, shi kan sa Anas yai mamakin yadda Najeeb ya haƙura da Farida. A zuciyarsa kuma yana ganin kamar akwai lauje cikin naɗi.


Babban matsalar Farida a office ita ce Khalidah, a second floor ta ke amma kusan koyaushe tana third floor. Magulmatan kamfani su ka sanar da Farida cewa Khalidah son Najeeb ta ke, lokacin da ta zo ta yi service ɗin ta a Kamfanin ta haɗu da Najeeb tun daga lokacin kuma ta ƙi tafiya, da ke dama mahaifinta na da share a kamfanin sai ta samu ɗaurin gindi. Shekararta uku a Najeeb constructions amma ba alamar nasara sai dai ta ƙi haƙura...


Ta gaji da cin abincin canteen kullum sai kashe kuɗi ga abincin a zuba ma ka kamar kana roƙo duk da ma mafi yawancin lokuta Engr Mathew ko Arch Hamza wani cikin abokan Yakubu ke siya ma ta. Ba ma wannan ba abincin ma bai ma ta yadda ta ke so ba.


Ta zuba faten doya da ya ji ganyen alayyaho da kifi a plate. Gaba ɗaya ƙanshi ya baɗe office ɗin, ta na ci tana korawa da zoɓonta mai sanyi a haka Najeeb ya shigo. Bai ma ta magana ba ya shige office ɗin sa, yana shiga ta ji kira. Tsaki ta yi ta ce " yana gani fa abinci na ke ci" haka ta ajiye ta shiga office ɗin sa.



"Miss Salihu. The next time you eat in the office, 10% zan cire a albashin ki. Is that clear?"


"Ok Sir " ta faɗi ta fita tana ƙunƙuni...


.....................


Farida ta zaunar da Baaba Sabuwa ta yi ma ta bayanin abinda ke faruwa tsakanin AbdulWahab da Maijiddah. Da kuma ƙudurin AbdulWahab ɗin na son turo iyayen sa.

Baaba Sabuwa ta ce idan dai da gaske ne za ta sanar da Baffa Musa sai ya basu lokaci.

Farida ta ce " yanzu Baaba Sabuwa ba ki yarda ba kenan?"


"Farida na fi kowa damuwa da rashin auren Maijiddah, sai dai maganar AbdulWahab ɗin ne ta zo kamar almara"


"Addu'arta ne ya ƙarbu. Kin san tunda na zo gidan nan kullum dare Maijiddah sai ta fi awa ɗaya tana sallah tana roƙon Allah ya bata miji. Ko ba ta sallah sai ta tashi ta roƙeshi. To Ubangiji mai jin ƙan bayinsa sai ya kawo ma ta wanda ba ta taɓa tsammani ba. Baaba Sabuwa ki godewa Allah kawai ki cigaba da yi ma ta addu'a"


Cikin satin Alhaji Bello Hassan Kachako da wa su wakilan AbdulWahab su ka zo. Bakin Baffa Musa kasa rufuwa yai, shi ba dan ya gani zahiri ba ko lokacin da Baaba Sabuwa ta gaya ma sa bai gama yarda ba. Su zuwan da su ka yi idan an basu Maijiddah su na so bikin kar ya ɗau lokaci.


Baffa Musa kam zani ne ta tadda muje. Dan haka ya amince da sauri.

Sati na zagayowa aka kawo sadakin Maijiddah, dubu ɗari da hamsin. Wata uku aka sa biki su ka nemi a dawo da shi wata biyu Baffa Musa ya amince. Duk da kuwa bashida kuɗi a ƙasa dan ya gama kashe kuɗi wajen bikin su Salima. Sai dai ba zai bari damar da ya ke nema tun da jimawa ya kuɓuce ma sa ba. Allah na gani ya so a haɗa bikin Maijiddah da Farida sai dai hakan bai yiwu ba. 'Yan uwan Rayyan sun ce Rayyan yana so ya haɗa ginin sa kafin ayi biki...


Wannan babban al'amari ya sa kishiyoyin Baaba Sabuwa kowa yai tsit dan abin ya ba su mamaki, duk cikin yaran da aka aurar ba mai sa'an Maijiddah. A gaba ɗaya yaran ma Yayar Maijiddah wadda ita Maijiddan ta biyo wato Bilkisu ita kaɗai ta auri wanda yai boko sosai kuma ya ke da hali yana aiki a kamfanin insurance, sai gara-gara mijin Kulthum wanda shima ma'aikacin Kamfanin Airtel ne.


Abu kamar mafarki fa yadda su ke tsokanarta da Matar Custom sai ga shi har sadakinta an bayar saura a ɗaura aure kawai. 


......................


Tana kwance wayarta ya fara ringing tana ɗagawa ta ga Sir Najeeb. Mi zai sa ya kira a wannan lokaci? Ta dai ɗauki kiran.


"Miss Salihu, i asked you to send me a copy of the proposal before you leave. What happen?"


"Ya Allah! Na manta zan turo ma ka yanzu"...


Yana zaune yana sipping tea ɗin sa ta turo ma sa saƙon. Sai da ya duba ya ga aikin bai yi kyau ba akwai gyararraki. Nan ya sake kiran ta.

Tana amsa waya ya fara faɗa "Miss Salihu what is this? Mi ki ka turomin? Haka na ce ki yi?" Jin ƙorafin yai yawa ya sa ta ce


"Domin kai ƙorafi danna ɗaya, domin neman ƙarin bayani gameda aikin da aka maka danna biyu, domin magana da Aisha Farida kai tsaye danna uku...."


Ba ta gama ba ya kashe wayar.

Farida ta yi tsaki, " shi agidan ma ba za ka huta ba aiki, ya san da ya na yi wannan ɗin. Wallahi ba za ka kasheni da aiki ba"


Najeeb ya cillar da wayar yana cize leɓen sa na ƙasa. He's waiting for the perfect time ya aiwatar da ƙudurinsa, just a perfect time. Yarinyar nan sai ta raina kanta...