AZIZAN BABA

Episode 13

by @zinariya0102



_______________Hmmm nikam har kin ba ni dariya Hajiya Hadiza yo Allah na tuba me akayi akayi dangin Miji mtsww, wai akan wannan kike ɗaga murya"

Mami ta ce" ba dole ba saboda Allah ina son waya da yarana amma tsabar rashin service na kasa samu" Hajiya Fatu ta ajiye hand bag ɗinta a kan center table ta ce" ai lefinki ne tun daga muka je gurin nan akayi miki aiki akan Mijinki sau ɗaya baki kuma komawa ba saboda Allah ba dole abu ya bi ya caɓe miki ba"

Momi ta ce"bari ki sha ruwa sai muyi magana, Hasiya!Hasiya!!" da sauri wata babbar Mace ta shigo tana amsawa" na'am Hajiya gani"

Momi ta kalleta a wulaƙance duk da Hasiya ta haifi kamarta, ta ce" baki ga nayi baƙuwa ba ne ko kullum sai na faɗa miki aikin ki"

"Ayi haƙuri Hajiya" ta tashi da sauri ta fita, drinks ta kawo mata da snacks ta fita.


Mami ta ce"kina ji kinsan dai yanda akayi na samu Alhaji ya dawo hannuna, amma duk da haka wani lokacin har tsoro yake ba ni, idan ya juye wallahi bai ƙi a mutu ba, taurin kansa yananan inda kika san jinjirin jaki wallahi har yau haka yake, shiyasa ban koma ba gaskiya"


Hajiya Fatu ta kurɓi exotic ɗinta ta ajiye sannan ta ce"to daman an gayamiki haka ake aiki da kinyi sau ɗaya shikenan tab to aikuwa ba haka ake ba, kinsan Allah idan kika dage ina tabbatar miki da cewa ko sunan ƙauyensu Mijinki ba zai so a kira ba bare har ya yi tunanin zuwa ko ya kwashe ƴaƴanki ya kai, sauro su zuba musu cuta mara jin magani" 

Momi ta ce" kai Hajja Fatu wallahi ba ki da dama, shikenan, kinga ina expecting tomorrow zasu dawo, amma zuwa jibi in sha Allahu zan kira ki sai mu je gurin, dan so nake ayi musu farraƙu da wannna tsinannan ƙauyen gaba ɗaya"

Hajiya Fatu ta ce "angama ƙawata hahhh" ta ƙarasa su na tafawa.



Kayan da ta ciko jaka da su ta buɗe ta na faɗin ki duba ga wasu fa, ƴan china ne, masu kyau ne, komai zam-zam zakiji" 

Momi ta ce"ke ki barni da wannan abubuwan pressure da ke kaina yanzu yawa ne da ita" 

Hajiya Fatu ta ce"a'a fa Hajiya ki kwantar da hankalinki ki bar min komai a hannuna nasan indai akwai Malam na ƙauyen bunkure matsalarki ta ƙare"

Haka ta sa Momi sai da tayi mata cikin dubu talatin sannan ta bar gidan.



"Hello Momi!ki na jina dubawa yayi ya ga service ya ɗauke.

"oh shit" ya faɗa yana dukan seat ɗin da yake kai.




Ummi ta dinga jan su Siyama da hira, kasan cewarta ƴar ƙauye sai hi hey take musu, babu wacce ta ke kulata sosai.


Daddy ya ce" naji saƙonki wajen Inna, ga wannan ki yi jarin da shi, wannan kuma ki yi buƙatun ki" ya miƙa mata rapper biyu na ƴan ɗari biyar-biyar, 100k kenan.Gwaggo Aliya sai ta sa kuka ta na ta godiya gami da yi masa kyakkyawar addu'a. Ya bawa Ummi dubu Hamsin ya ce su raba ita da ƴan'uwanta.

Mijinta kuwa Sama'ila dubu ashirin ya ba shi, suka tashi suka zasu tafi.Har ƙofar gida suka rako su.


Gwaggo Aliya ta ce "Allah ya kiyaye ubangiji ya tsare gabanka da bayanka mungode Yaya" Daddy ya ce" amin ƴar'uwata" ya hau motar suka nufi Mazoji.



A guje ta shiga gidan ta na uban haki, Baba Tabawa da take gyaran kayan miya, ta ga AZIZA a guje, "idan na ce yayi haƙuri Allah tsine min" ta tsaya ta na ta tafa hannuwa cikin masifa, Inna Gaji ta ce" to ke kuma ke da waye, oh la'ilaha'ilallahu yanzu haka kika yago kayan nan AZIZA" 

Baba Tabawa ta sa naman a colander ta nufi AZIZA ta na faɗin faɗan kika kuma yi ko" AZIZA ta nufi randa ta kandami ruwa ta sha, sannan ta ce" wai daga zuwa kan labi wajen su Ai shine Saminu ya tsokane ni kuma nayi masa duka, shi ne wai Maigari sai na ba shi haƙuri"

Inna da take tunanin a ina AZIZA ta koyi masifa, Baba Tabawa ta ce"yanzu akan ki ba da haƙuri shi ne kika gudu?"AZIZA ta ce "tabdijan alkur'an Baba ina da gaskiya bazan ba da haƙuri ba, ta cire kayan anan dafa ita sai pant ta zauna ta na faɗin yunwa nake ji" 

Baba Tabawa jiki na rawa, ta ɗauko mata ragowar abincin karin safe ta kawo mata.


"Ni za'ayi wa shegantaka Allah ai gatan bawa dan anganta marainiya kuma mace ai ba raguwa ba ce, kinyi dai-dai ƴar albarka" 

BABA ya shigo yana ta magana.

Sannu da zuwa Malam, ashe rigima ta janyo maka?"

"inji waye, babu wata rigima cutarta aka so ayi kuma ta ƙwaci ƴancinta" 

ganin ta na zaune ta na cin abinci ya washe baki ya ce" AZIZAN BABA, babu wanda ya isa ya taɓaki indai ina raye, Allah ya raya mana ke"

Hahhh ta sa dariya, zama tayi tare da Baba Tabawa ana suya ta na ci, sai da tayi ƙat.



Har La'asar Daddy bai dawo ba, BABA yana zaune akan dakali, dake gefen yara ne cike a wajen AZIZAN BABA na bikin ƴa, ƴar tsanoninta kusan guda biyar duk sun sa musu kaya, amaryar ta jingina da angon a jikin bango, sai kiɗa suke da bokitan su Inna.


Tun daga nesa, Abdul-AZEEZ ya gano haukan da ake a ƙofar gidan, Mudan ne yayi parking, Daddy na ganin BABA akan dakali ya sauko, BABA ya taso yana murmushi, hankakinsa ya kwance, yana kallon bidirin da su AZIZA suke.


Munnir ya ce" ɗan tsohu wai jiranmu kake yi ne?" BABA ya washe wawulun bakinsa ya ce"wa zan jira ni ɗana na jira ba wai ku ba"

Pretty ta ce " BABA ni kam wannan sandar nake so ka ba ni in tafi da ita" BABA ya ce" wannan sandar da kike gani ƙafata ce sai dai ki siya" Daddy ya ce "ku wuce mu shiga"

Abdul-AZEEZ da ya gama shan ƙamshinsa a mota ya fito, AZIZAN BABA ta taso hannunta duk ƙasa, ta ce "oyoyo Baban birni, ka ga biki muke yi, zan kawo muku abinci ma" Daddy ya ce"a'a wannan duk taron ne, ashe uwar amarya ce" dariya sosai AZIZA tayi, tana ƙaunar Daddy sosai.

Abdul-AZEEZ ya kalla da ya fito zai wuce " Abdul je ka can shagon ka karɓo min sweet da biscuits" Abdul-AZEEZ da ya san AZIZA za'a bawa ya ce" a ina Dadd?" BABA ya ce"nan nan shagon Hamisu akwai idan ka fita daga layin nan za ka ga shagon yana kallon kudu" Abdul-AZEEZ ya fara tafiya dan yasan umarni ne kuma da kuɗinsa za'ayi siyayyar.


A hankali yake tafiya duk da agajiye yake, ga yunwa da yake ji, yana tafiya ya na zagin AZIZA a ransa, wasu Jakai ne suka shigo da gudu layin ɗauke da mangalan ya shi, Abdul-AZEEZ bai ku ba kawai gani yayi sun yo kansa, da sauri ya tsallaka wata babbar kwalbati, ya bige da bango kasancewar a jikin katangar wani gida take.

Kamar zai yi kuka ya ji, yara ya gani suna ta langa a wani fili nan ya nufa, ya kira ɗaya daga cikinsu, yaron ya kalle shi ganin bai san shi ba, ya sa yaƙi zuwa, wani daga cikin su ne ya ce" kai jikan BABA ne fa daga birni ya ke" sai yaron ya je, har da gaishe shi, Abdul-AZEEZ ya ce"  a ina ake sai da sweet?" yaron ya ce "alkur'an bansaniba" dafe kansa yayi ya na tunanin me zai ce masa, sai kuma ya ce" to biscuit fa?" take ya ce " shagon Hamisu ana sai da wa" Yauwa zo muje   ka kai ni" yaron ya shige gaba Abdul-AZEEZ ya bi shi, katon ya je siya babu sai rabi ya samu hakama sweet two bags ya samu dan ɗan trader ne wajen.


Yaron ya ɗorawa su ka koma, AZIZA ta na cikin ƙawaye ana ta biki, Abdul-AZEEZ ya wuce ya shiga gida.


Ganin Daddy da sauran mutanen gidan suna cin abinci, duk da a tsakar gida ne, amma ƙamshin girkin kamar ba'a ƙauye ba.


Inna Gaji ta ce"sannu da ƙoƙari auta daga dawowarka naji ance an aike ka" murmushi yayi ya ce" sannu Inna" BABA ya ce"yauwa Abdul-AZEEZ ma za je ka ka rabawa ƙawayen AZIZA a ƙofar gida biki suke yi" Baba Tabawa ta ce"haba Malam a bar shi ya huta kawo nan ni na raba musu"

Abdul-AZEEZ ya ce "nagode Baba, wallahi na gaji sosai" Inna Gaji ta ce " ga azumi ma kanayi sannu autana" 

BABA ya ce " ba ni nan, kai yaro mu je waje" yaron da yake tsaye Abdul-AZEEZ ya ɗauko dubu ɗaya ya ba shi, BABA ya kwace ya ce" na me ye wannan kuɗin da ka ba shi?"

Abdul-AZEEZ ya ce"no na bashi ne kawai" 

"to mu ba ma wannan ɗabi'ar, ya zura kuɗi a aljihu ya ce"mu je kai ma ai zaka ci biskot da alewar ai" duk sun cika guri da hayaniya, BABA ya washe baki ya ce"ku hau layi a ba ku abun biki ko" 

Yara suka hau murna aka kafa layi, AZIZAN BABA ta kalli Jamila ta ture Mulaika a layi, ganin ta fita girma, ta na tsaye ana ta turereniya da hayaniya, ta ajiye ƴar tsanarta, ta tsaya kusa da BABA, aka fara ba wa yaron da ya siyo, ana ta rabawa aka zo kan Jamila, AZIZA ta ce, " ba za'a baki ba, ina kallo kika ture Mulaika yi nan"ta nuna mata hanya, BABA ya ce" wuce ki tafi mana, wai ke muguwa to ba za ki shaba tafi ki bamu guri" Jamila sai ta sa kuka, ta na fita a layin.

Abdul-AZEEZ da ya fito dan tafiya hotel yayi wanka ya samu ya ci abincin ya tsaya ya na kallon inda BABA yake ɗaurewa ƙarya gindi, Jamila na komawa gefe ya ce" ai ba ubanta ne ya siyo ba, zo ki ƙarɓa" ya sa hannu cikin kwalin da ke gefen BABA akan dakali ya ɗauko biscuit da alewa damƙowa kawai yayi ya ce "ungo" BABA ya ce "idan ka bata wallahi tallahi sai ranka ya ɓaci" Abdul-AZEEZ ya ce "karɓi mana" Jamila taƙi karɓa.

Tana kallon AZIZA wacce ta ke ta girgiza akai ta na ƙwafa, alamar ta karɓa ta gani kenan.


Jamila ta ƙi karɓa, ta na kallon idon AZIZA, ta san halinta yanzu sai ta sa fita ta gagareta, ƙawayen a gujeta.

Abdul-AZEEZ ya ga inda take kallo ta na girgiza kai.

Watsa musu abinsu yayi ya ce"shegiya mai baƙin hali, kowa ba ki bari ba" BABA ya ce " ka fita idona in rufe rasa kunya" AZIZA ta kalle shi, ganin yanda idanunsa mai kama da na kyanwa (cat) ta kwashe da dariya, ta kuma kallonsa ta kuma fashewa da dariya, ganin haka yaran ma suka hau yi masa dariya.


A zuciya ya nufo kan AZIZA ya na huci, BABA ya riƙe shi ya na faɗin " ai muddun tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba,to kuwa Jaki ba zai ji kunyar yi masa tutsuba ya tiƙa ɗan banza da ƙasa" AZIZA ta ce "ku tafi an gama bikin"BABA ya ce"to shige gida" ta na wucewa Abdul-AZEEZ ya kwace rigarsa ya bi ta har cikin gidan, ganin haka BABA ya ɗauke kwalinsa ya bi su yana sababi da masifa.


Yaran da ba'a zo kansu ba suka ƙi tafiya, sai suka hau Jamila da duka suna ita ta janyo musu,.faɗa ne ya rin caɓe tsakaninsu.


AZIZA na shiga kuwa ta nufi jikin Daddy ta na fashewa da kuka Abdul-AZEEZ ya shigo yama huci kamar wanda yayi faɗa da sa'ansa.


Daddy ya ce"me kayi mata?"

Abdul-AZEEZ ya ce" ni yarinyar nan za ta yi wa dariya,ni sa'anta ne, wallahi sai na kakkaryata" Baba Tabawa ta ce" idan ka fasa ka raina iyayenka"

Inna Gaji ta ce" fita ka bamu guri, kai na fuskanci babu wanda ka tsana sai AZIZA to ka kiyaye ni, me za'ayi da baƙunta irin taka"

Daddy ya na ta rarrashin AZIZA wacce kawai makirci ne ya sa kuka.


BABA da ya ji inda akayi masa cahhh, sai ya ji daɗi, ya ce "ko anan kasan AZIZAN BABA, ta fi kowa a cikin zuri'ar nan ta mu,zo ka fita ɗan duniya"

Abdul-AZEEZ da suya kawai zuciyarsa take yi, ya juya a fusace ta re da ƙara ɗammarar addabar rayuwar AZIZA da zarar ya dawo daga karatu.



Siyama ta ƙara naɗar rahoto dan sanarwa da Mami.

Ya na barin gidan , AZIZA ta tashi ta ce "kawo in ƙarasa ba su, kayan bikin" kamar ba yanzu ta ke kuka ba.


Tana dawowa kuwa taga anyi faɗa, ta fara ba su tana jin daɗi faɗan da aka taru akayiwa Abdul-AZEEZ ba ƙaramin daɗi ta ji ba, dan yanda ya tsaneta haka ita ma ta tsane shi........








Zinariya ce✍🏻