GADAR ZARE…

12

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_



     ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*




Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh 


Gmail: *** 


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA'''





~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




12



Da yamma Khamal ya shirya ya d'au fitinannan wanka ya nufi gidan su Fateeha a bakin get yayi faki ya kwankwasa mai gadi ya lek'o yace " lafiya Malam? " lafiya dan Allah yimin magana da Fateeha, kallansa mai gadin yayi cike da mamaki yace " kunyi da ita zaka zo ne? "Eh cewar Khamal, " ita Fateeha ce da kanta ta baka izinin? Cike da k'osawa Khamal yace " nace maka eh, kai mai gadin ya jinjina sannan yace " ikon Allah, da mamaki Khamal ya kalle shi yace " ya akayi ne? 



Murmushi mai gadin yayi yace " abin ne ya bani mamaki, " mamaki kuma? cewar Khamal, " eh kasancewar yau ne rana ta farko dana ga hakan, dan kwata-kwata Fateeha bata kula samari, tun Fateeha tana yarinya nake aiki a nan gidan amma ban tab'a ganin wanda yazo yace yana sallama da ita ba sai kai yau. 



Murmushin jin dad'i Khamal yayi yace " Alhamdulillah, da sallama ya shiga falon ya iske Fateeha da Momy zaune suna aikin kallon, tare suka amsa masa sallamar tasa, Hajiya k'arama ana sallama dake, ido ta zaro tace " ni? Momy ko saboda tsabar mamaki ta kasa cewa komai, dan tasan halin Fateeha duk wanda yace yana santa tsiyatsiya suke rabuwa, da kallon Fateeha kawai take da Mamaki, Fateeha tace " je kace bata zuwa, har mai gadi yayi nisa sai tunaninta ya bata Kodai Khamal ne? 



Aiko bata san sanda ta kwala mai kira ba, tace " ce ne waye? Dawowa yayi yace " wai yace " Khamal ne, bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, cike da murna tace " shigo dashi d'akin bak'i, murmushi mai gadi yayi dan yasan bata isa tak'i amincewa Khamal ba, dan duk tak'amar kyan da takeyi Khamal ya fita, mai aikin su ta kira ta sata ta kaiwa Khamal ruwa da lemo. 



Ita dai Momy shiru tayi tan kallon ikon Allah, aranta kuwa cewa take wannan wanne mai sa'ar ne? d'aki ta koma ta shirya cikin riga da zani na atamfa, ta shafa farar hoda da lip glo, ta saka takalmi da mayafi 2 match ta feshe ilahirin jikinta da perfumes, ta nufi falo cike da farin ciki, da d'okin ganin sa, ita dai Momy ido kawai ta zuba, tana ganin ikon Allah.



A zaune ta same shi, da sallama ta shiga, a d'aya daga cikin kujerun ta zauna, kallon ta yayi his face with smile, yace " kinyi kyau, face ta ya mutsa tace " wannan itace kalmarka mafi tsada? murmushi yayi dan ya fahimci Fateeha ba k'aramar 'yar rainin hankali bace, hira suka d'an tab'a sama-sama tana yi tana bashi amsar rainin hankali, dakyar ta bashi phone number ta, harta kai bakin k'ofa zata fita yace " ya b aki bani amsa ta ba, juyowa tayi tana d'an yamotsa fuska tace " amsar me? "nace I love you, but u didn't reply me, tsaki ta d'an ja ta fita, mik'ewa yayi yana murmushi ya fita, k'ofar dayaga ta shiga yabi da kallo yana 'yar dariya, a hankali ta da fuskarta ta sakar mishi murmushi, dariya yayi mata yana cusa hannunsa cikin sumar kansa. 



A hankali ta motsa bakinta tace " I love you too, sai tin zuciyar sa ya dafe yana yi mata dariya marar sauti, haka kowannensu ya koma gida cike da farin ciki, da dare bayan ya gama duk abinda ya saba kan ya kwanta, sannan yayi dialing number ta, sai da yayi mata 2miss call, sannan ta d'aga, " waye abinda ta fara cewa kenan, murmushi yayi mai sauti yace " ur hubby, " what my hubby? ni bana da wani hubby, please waye? " ok Khamal ne, " wanne Khamal kenan, ni ban san wani Khamal ba, sai da ta gama raina masa hankali, sannan suka tsunduma hirar soyayya, ranar kowannen su yayi kwanan farin ciki.


Washe gari bayan sun tashi daga lactures, a gajiye likis ta fito tana ta had'a hanya, a gabanta yayi parking fuskarsa d'auke da murmushi yace " mu tafi ko? ba k'aramin kyau yayi mata ba dan haka bata san sanda ta sakar mishi murmushi ba, ba musu ta hau, suka tafi, a k'ofar gida ya sauke ta, sai da suka d'an tab'a hira sannan ta shiga gida, tun daga harabar gidan su take jiyo hirar mutane a falo, da sallama ta shiga falon Dady ta gani tare da Ja'afar d'an aminin Dady, ya dad'e baya Nigeria, a Malaysia yake karatun, lokacin dayake Nigeria he is her Best friend, da har iyayen su suna expecting soyayya suke, wacce ita a zaton Fateeha shak'uwa ce kawai ace shi a b'angaren sa, bahagon so yake yiwa Fateeha tun suna yara yake mata mugun so, da sauri ya mik'e ya nufe ta da murna, itama cikin farin ciki tace " Ja'afar yau she ka dawo? " yau dawowa ta kenan ko abinci ban ci ba nace bari na zo naga my Fatee nasan yanzu ta girma, cikin shagwab'a tace " amma shene ko ka gaya min, " sorry my Fatee so nake nayi surprising naki ne, " to yanzu nasan dai baka ci komai ba, ban some minutes in sha na d'an watsa ruwa, nayi sallah na fito sai na girka maka best food dinka, Dady ko baki har kunne sai fara'a yake, " ok yace, da sauri ta shige d'aki. 




Wacece Fateeha 


'Ya ce ga Alhaji Nasir, tsohon soja ne dan har ya kai matsayin mojor general kafin yayi retired, Hajiya Zainab ita kad'ai ce matar sa auren zumunci iyayen su suka yi musu, Hajiya Zainab macece mai hak'uri da kawaici, Alhaji Nasir mutum ne mai zafi yana da fad'a da kafiya, Fateeha ita ce kad'ai 'yar sa suka haifa, bayan ita Allah bai k'ara basu haihuwa ba, dan haka ta taso cikin gata da kulawa, amma duk da haka sun bata cikekkiyar tarbiyya, hakan bai sa sun saketa ko sun barta ta sangarce ba. 



Daf da magrib Fateeha ta fito daga d'aki tace " bari nayi sauri na d'an sama maka wani abun ko, tasowa yayi ya nufe ta yana dariya yace " no ki raka ni restaurant kawai, naga lokaci ya k'ure, " haba Jafy ka kadawo yau d'in amma ka ci abincin restaurant? " eh bakomai yunwa nake ji sosai muje kawai gobe sai kiyi min girkin kinji please, " ok tace ta shiga d'aki ta d'auko hijab ta zira suka tafi, da kallo Dady yabi su yana murmushi yace " Allah ya nuna mana lokaci, " Hmmmm Momy tace. 



A round about Khamal ya gansu danja ta tsaida su, gabansa ne ya fad'i, nan da nan yaji wani mugun kishi ya taso masa musamman yadda ya gansu tana zaune a gaban mota yayi dashi kuma yake zaune a mazaunin driver gaba d'aya ya karkata hankalinsa gare ta, sai dariya suke, danja na fasu hannu yabi bayan su, a Food Palace Ja'afar yayi parking, ya zagaya ya bud'e mata murfin motar, suka jera suka shiga, duk abinda ke faruwa akan idon Khamal, in banda tafasa babu abinda zuciyar sa keyi, parking shima yayi ya shiga a zaune ya hango su, gurinsu ya nufa d'aya daga cikin kujerun wajen yaja ya zauna ya sakar mata wani fitinan nan murmushi. 



Ido ta zaru tana kallonsa, alama tayi masa daya tashi, dariya yayi yace " ai da kika kira ni a waya kikace mu had'u anan nayi mamaki kasancewar a gida muka saba had'uwa, ya k'arashe magana yana kashe mata ido d'aya, zatayi magana service din gurin yazo ya fara gabatar musu da abinda suka bada Oder, gyaran murya Ja'afar yayi,.

 Shima Khamal yayi kamar bai san yana zaune ba.



Kallon Ja'afar Khamal yayi ya mik'a masa hannu fuska d'auke da fara'a yace " sorry ban lura da kai ba, kasan idan ina tare da my heart mantawa nake da kai na ma, shima fuska d'auke da dariya yace " gaskiya kam, murmushi tayi tace " Khamal wannan cousin d'ina ne sunan shi Ja'afar, ta kalli Ja'afar tace " wannan ne Khamal, shagwab'e face Khamal yayi yace " baki gaya masa waye ni ba, ta bud'e baki zatayi magana yayi sauri ya tare dan yasan tana iya bada shi yace " bari kawai basai kin wahalar min da bakin ba zan gaya mishi ya kalli Ja'afar yace " nine mijinta wanda zata aura very soon in sha Allah, yak'e Ja'afar yayi yace " masha Allah, sanin halinta ne yasa shi mik'ewa tun kafin ta kunya ta shi, ya rik'o hannunta a hankali yayi mishi kiss, ya kashe mata ido d'aya, yayi kamar yayi mata rad'a a kunne sannan yace " I love you too sweetheart, yayi saurin ficewa, itako mamaki ne ya hanata cewa komai. 



Tasan tsabar kishi ne ke yawo da Khamal shine yasa shi yin hakan, kasa cin abincin Ja'afar yayi, ko a mota sama-sama sukayi hira, a falo suka tarar da Momy da Dady zaune, kusa da Dady Ja'afar ya zauna, ya kasa cewa komai Dady ne ya lura da yanayinsa dan haka yace " lafiya dai, kaci abincin? " eh Dady dan har Khamal ma ya yazo, " waye kuma Khamal? cewar Dady " nima ban san shi ba, Fateeha ce tayi masa waya ya same mu acan, sai sannan Dady ya gane dalilin canjawar Ja'afar murmushi yayi sannan ya kalli Fateeha yace " waye shi? Dariya tayi tace " Dady wani ne kawai ta fad'a tana mik'ewa, shiru Dady yayi baice mata komai ba, ta shige d'aki tabar Ja'afar anan yana ta faman kumbure-kumbure. 



Sannu a hankali soyayya mai k'arfi ta rink'a shiga tsananin Fateeha da Khamal, had'i da muguwar shak'uwa, sosai suke mugun son junan su, ji suke kamar d'ayan su bazai iya rayuwa babu d'aya ba, kullum suna tare, idan ko suna gida to suna tare a waya, sunyiwa junansu mummunan sabo da juna, yayi da Ja'afar ke ta haukan son Fateeha dan ji yake kamar yayi hauka, sosai ya fara fita daga hankalinsa, kwata-kwata baya cikin nutsuwarsa, duk ya zama wane iri iyayensa sun kasa gane kansa, haka ma a b'angaren Hamza kwata-kwata yarinyar da yake so tak'i kula shi, yayi yin duniya amma taki bashi koda fuska ce, duk ya rud'e ya shiga matsanciyar damuwa ya rame yayi bak'i ya gode, ko abinci baya iya ci, sosai Khamal ya shiga cikin muguwar damuwa saboda halin da Hamza yake ciki, gashi yak'i nuna masa yarinyar. 



Hatta Hajiya kakarsu tana cikin damuwa sakamakon ganin Hamza cikin muguwar damuwa, duk sun tada hankalin su, sosai Khamal ke kwantar mishi da hankali had'i da fad'a masa in sha Allah zai mallaketa.



Ganin irin mawuyacin halin da Ja'afar ke cikine yasa iyayen sa tsare shi a d'aki, ganin a koyaushe suna iya rasa shi, da gaf yake da jefa kansa a halaka, Umman sa ta zauna kusa dashi tana shafa kansa, Abban sa yana gefe a zaune, Abban sa ya kalle shi yace " Son meke damunka ne, munyi munyi ka sanar damu damuwarka amma kak'i bayan kasan duk duniya babu wani mahaluk'i daya cancanci sanin matsalarka sama damu, ka sanar mana idan muna da abinda zamu taimaka maka zamuyi iya k'ok'arin mu dan ganin mun magance maka matsalarka, shiru yayi baice komai ba, a hankali Ummansa ta shiga lallashinsa, tana k'ara kwantar mishi da hankali had'i dayi mushi magiya akan ya sanar dasu damuwar shi, shiru yayi yana tuna sanda Fateeha take fad'a masa irin mugun son da take yiwa Khamal har ce mishi tayi idan ta rasa Khamal tasan rayuwarta bata da wani amfani bayan lokaci kad'an zata bar duniya. 



Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tuna irin maganganun Fateeha akan haukan son da take yiwa Khamal, gashi kuma iyayen sa sun saka shi gaba akan sai ya sanar dasu damuwar shi, yasan kuma idan bai sanar dasu ba, ran su zai iya b'aci, ba kuma zasu jure ganin sa cikin wannan yanayin ba, suna iya shiga matsala, dan haka ya yanke shawarar sanar dasu, a hankali ya furta " Fateeha ce damuwata, cikin zubar hawaye yake magana " wallahi Abba ina mugun son ta, akanta zan iyayin komai, zan iya mutuwa saboda da ita wallahi Umma da in rasa ta gwamma na rasa komai ciki kuwa harda rayuwa ta, sosai yake kuka yana sambatu akan Fateeha wanda shi baima san yanayi ba, murmushi Abbansa yayi yace " da akan wannan ka tsaya kana damun kanka?


"Karka damu kaji Son Dadyn ta ya dad'e dayi min maganar mu had'a ku aure nine nace kar muyi muku haka mu bare sai mun dai-daita kanku, da shi yaso ma tun kana Malaysia ayi auren, "Abba me yasa kak'i daka sani daka bari anyi, kanshi Umman shi ta shafa tace " kwantar da hankalinka Son koyan zuma lokaci bai k'ure ba, ko gobe kake son a d'aura auren ku za'a d'aura, " eh wallahi Umma na yarda a d'aura goben ma, maganar yake amma kwata-kwata baya cikin hayyacin sa, " don Allah Umma ina nema na rasa ta, ta fara mugun son wani, nan ya kwashe komai dake tsakanin Khamal da Fateeha ya sanar dasu " karka damu kaji Son wallahi koda zan k'arar da abinda na mallaka a duniya zan k'arar dan ganin farin cikin ka da walwalarka sun dawo, wallahi zanyi komai dan ganin ka mallake ta kaji Son, karka damu, maza tashi kaje kayi wanka kazo dining muna jiranka,  " please ku taimaka Abba, " nace karka damu gobe iyanzu Fateeha tana a matsayin matarka kaji, ya mik'e ya shiga bathroom, suka bishi da kallo cike da tausayawa, Abba ya kalli Umma yace " wallahi bazan tab'a bari nayi asarar tilon d'a na ba, ko kisa ne ya kama nayi zanyi, saboda farin cikin sa......... 




*MOMYN ZARAH*