GADAR ZARE…

15

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_



     ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*




Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh 


Gmail: *** 


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA'''





~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDU*



15



Da kyar da taimakon Allah Hamza ya samu ya fizgo numfashinsa, a hankali a hankali yake bud'e idonsa harya samu yayi controlling kansa, dan baya son koda wasa Khamal ya fuskanci akwai wani abu tsakanin sa da Fateeha, ya daure ya doje yayi kamar ba wani abu, amma acan k'ark'ashin zuciyar sa ji yake kamar ya mutu da sauri k'irjinsa ke bugawa, mak'ogwaron sa ya bushe bakinsa ya rinka yi masa d'aci. 




Itako Fateeha bama tasan Allah yayi ruwansa ba, gaba d'aya hankalinta yana kan Khamal, kwata-kwata bata cikin nutsuwar ta, sosai ta matsa daf dashi ta yadda kowannen su yana iya jiyo numfashin juna cikin sanyin murya tace " please Khamal karka barni, kai kanka kasan ina sanka, karka d'ora min laifin daba nawa ba, ya d'an matsa baya kad'an yana aika mata wani irin kallo, yace " kinga please ki tafi gida, kai ta shiga girgiza masa cikin kuka tace " a'a Khamal please karka barni, bazan iya jure rashin ka ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi, ni kaina bansan ina yi maka wannan mugun son ba sai yanzu, Khamal kaine ruhi ne, idan ka barni tamkar ka tafi da rahi nane kabar gangar jiki na. 




" Tunda nake ban tab'a yiwa iyaye na musu ko gardama na sai akanka duk abinda suka umarce bana yi musu gardama hakan ne ma yasa Dady ya yanke ranar aure na ba tare daya shawarce ni ba, cikin muguwar razana Khamal ya d'ago kai ka kalle ta, aiko karaf suka had'a ido, alama tayi masa da idonta na eh, taci gaba da cewa amma a kanka na kunya Dady na tubure nace a'a, akan ka nak'i yi masa biyayya, na bijire masa, yanzu haka Dady ko magana baya man, a kanka farin ciki da kwanciyar hanklin da iyaye na suka gina shekara da shekaru ke neman gujewa dan yanzu haka Momy da Dady neman rabuwa suke. 



" Ashe duk tarin maganganun dakake fad'a min ba gaskiya, kasha fad'a min nice rauwarka, nice farin cikin ka, nice duniyarka, kace duk runtsi duk bazaka tab'a rabuwa da ni ba, Idan kasan baka sona mai yasa kace kana so, idan kasan bazaka iya rayuwa dani ba mai yasa ka koyamin yadda bazan iya rayuwa ba kai ba, idan kasan bazaka d'orewa so na ba mai yasa zaka koyar dani yadda zan soka, mai yasa Khamal mai yasa ta durk'usa a k'asa ta fashe da kula mai cin rai.



A matsayi na na mace mai kunya, daraja, k'ima, da Allah yayi min, na yarda jan aji na, na tako har gidan ku, amma duk da haka bazaka hak'ura ba, kai wanne irin mutum ne marar adalci wanda kansa kawai ya sani, baka damu da damuwar wani ba, taka damuwar kawai ka sani, wacce irin zuciya kake da ita mai kafiya marar yafiya. 



Jikin Khamal yayi mugun yin sanyi, zuciyar sa ta harba da k'arfi, yayin da yake jin santa na k'ara ratsa ko'ina na jikinsa yana bin kowacce jijiya ta jikinsa yana bin jininsa, ya runtse idanunwa da gam, k'aunarta na fizgarsa zuwa gare ta. 



Hamza ko zama yayi kamar ba mutum ya, ya sandare a waje d'aya, babu abinda zuciyar keyi sai bugawa, k'irjinsa nayi masa zafi, ji yake kamar ya mutu, dakyar yake iya controlling kansa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata tsage, a gaban idon sa macen dayafi fiye da kowacce mace a duniya ke kukan son Yayar sa uwa d'aya uba d'aya, wanda duk duniya bashi da kamar sa, a hankali ya share siririn hawayen daya zubo masa. 



Hajiya dake tsaye tana kallonsu, tausayin su ya cika mata zuciya, cikin sanyin jiki ta tako har inda Fateeha ke durkushe tana kuka, a hankali ta d'ago ta, takai ta kujera ta zauna ta shiga lallashinta had'i da bata hak'uri, a hankali Khamal ya tako ya durk'usa a gaban kujerar da Fateeha ke zaune, Hajiya ta shiga yi musu fad'a daga k'arshe ta zarce dayi musu nasiha, sosai nasihar Hajiya tayi tasiri a jikinsu, a hankali ya rik'o hannunwanta ya k'ura mata ido ya langwab'ar da kai yace " am sorry my life, murmushi tayi ta kama kumatunsa tace " bakai ne yace zaka iya rabuwa dani ba, " dariya yayi yace " wallahi pretending ne, ba gaskiya bane, dariya Hajiya tayi ta mik'e tace " ja'irai. 



Mik'ewa Khamal yayi ya rik'o hannun Hamza ya kawo shi gaban Fateeha yace " my cweet ga brother na, mama da Baban mu d'aya, mu biyu iyayen mu suka haifa, Hajiya kuma grandpa d'inmu ce, ita ta rik'e mu tun bayan rasuwar iyayen mu, bamu san kowa na mu sai ita, ya kalli Hamza yace " Bro ga my heart, sai lokacin Fateeha ta kula da Hamza aiko da k'arfi k'irjinta ya buga, cikin seconds ta shiga tension, da sauri Hamza yayi mata signs ya girgiza mata kai, alamar a'a, da sauri yace " yau dai Allah yayi naga amaryar mu, ya kalli Khamal yace " kai Yaya ka iya zab'e she is very beautiful, murmushi tayi tace " nagode irin wannan kod'awar haka. 




A dining Hajiya ta shirya musu abinci, suka ci, cikin raha da wasa da dariya kamar babu abinda ya faru, komai ya wuce an zama normal kamar babu abinda ya faru, da Fateeha zata tafi Hajiya ta had'a mata kayayyaki dakyar ta karb'a had'i dayi mata godiya, Khamal ya raka ta. 



Washe gari har gida Hamza yaje wajen Fateeha bayan ta fito sun gaisa yace " please Fateeha ki manta da batun soyayyar danazo miki da ita, a baya, saboda matuk'ar Khamal yasan kece wacce nake so ko sama da k'asa zata had'e Khamal baizai tab'a auren ki ba, nasan kece rayuwar Khamal shine tako rayuwar, shi kad'ai kike so, ke kad'ai yake so, nasan bazaku tab'a kasancewa cikin farin ciki da walwala ba matuk'ar bakwa tare, ina son Yaya na akan shi zan iya komai, murmushi tayi tace " bakomai Hamza, gabansa ne ya fad'i dan yau ne rana ta farko da Fateeha ta fad'i sunansa, ji yayi kamar tafi kowa iya furta sunansa, murmushin yak'e yayi yace " not Hamza bro, ok, murmushi tayi tace " ok. 



Kwata-kwata Khamal bashi da kwanciyar hankali burin shi kawai ya samu aiki, kullum acikin neman aiki yake dan ya sawa ranshi bazai tab'a k'ara taka gidan su Fateeha da niyyar neman auren ta ba har sai yana da abinyi, saboda yace koda zasu kai 10yrs a haka shida ita bazai tab'a auren ta sai yana da madagara. 



Babu yadda Fateeha tabayi ba dan ganin ta shawo kan Dady amma ina ya riga yayi nisa, abun yaci tura, sakamakon zuga dayake samu daga wajen Abban Ja'afar domin ba k'aramin ingiza shi yake yi ba, kullum cikin zuga shi yake aka kar ya sake ya bawa Khamal auren tilon 'yarsa ga mutumin da bashi da gobe, dan haka kullum abin k'ara kwab'ewa yake.



Dady da Abban Ja'afar ne zaune a falo suna tattaunawa yayinda da Abba sai k'ara zuga Dady yake, ya kalle shi yace " ni dai ina k'ara baka shawara karka sake ka d'auki tilon 'yarka ka bawa mutumin da yake zaman banza jobless, bawai dan Ja'afar d'ana bane, Fateeha bata dace da kowa ba sai Ja'afar shine kad'ai zai jiyar da ita dad'in dake cikin aure, shine zai bata farin ciki da kwanciyar hankali, saboda yafi kowa sanin darajarta kuma duk tsiya shi d'an uwanta ne, kaga kuwa ai ya bare, koba komai wannan had'in zai k'ara dank'on zumuncin mu, kasan wani abu? Abba ya tambayi Dady, kasa magana Dady yayi illa girgiza masa kanshi dayayi, murmushi Abba yayi yace " matuk'ar Khamal bai rabu da Fateeha ba sai na b'atar dashi, kai idan ta kama ma na kashe zan iya kashe wallahi, a hankali zugar Abba ta rink'a tasiri a zuciyar Dady har yaji ya tsani Khamal fiye da komai da kowa. 



Bayan tafiyar Dady ne Abba ya shiga gida, Umman Ja'afar dake zaune tana jiyo hirar su hankalinta yayi mugun tashi, ta shiga mummunar damuwa, gabanta sai fad'uwa yake dan taji abinda Abba yace, a haka Abban ya shigo ya same ta, mik'ewa tayi cikin sanyin jiki, ta shiga yi nasiha , " haba Abban Ja'afar, saboda tsabar san kai, wato naka d'an shine kad'ai d'a shi ba d'a bane, wannan wane irin zalunci ne, da rashin tausayi yarinyar nan tace batasan shi, ga wanda take so, shima fa d'a ne kamar naka, kuma shima iyayen sa suna sanshi kamar yanda kake son naka may be ma sunfi k son d'an su, yanzu Alhaji ashe zaka iyaye kisa, wata irin mahauciyar tsawa ya daka mata cikin fushi sai huci yake yace "bana son jin komai daga wannan banza bakin naki, shashasha kawai, banza lusarar mace, ke kin isa ki zaunar dani kina min wa'azi, ke kin isa ki fad'a min abinda ya kamata nayi, ok wato yadda baki sanshi baki damu da damuwar sa ba, nima so kike nayi watse dashi, wallahi badan akan ido kika haife shi da saina ce dan ba d'anki bane,dan haka na riga na gama yanke hukunci kawar da Khamal kowa ya huta " Alhji dan ina fad'a maka gaskiya kake jifana da wad'an nan maganganun, kadai tuna da mutuwa, da ranar tsayuwa, hannu ya d'aga mata kawai saboda ya kasa magana sai hhuci yake tsabar bak'in ciki ya wuce. 



Sannu a hankali rayuwa ke tafiya sabuwa suka dinka faruwa suna wucewa, cikin haka ne Khamal ya buga ball d'in k'asa, cikin sa'a da taimakon Ubangiji yaci ball d'in cikin k'ank'an lokaci Khamal ya farayin suna a Nigeria, cikin haka gwamnati ta zab'e a wanda zai jagoranci Nigeria, a worlds cup wanda a yi Saudia a garin Riyadh, aiko murna da farin ciki ba'a magana suman wajen Hajiya da Hamza. 



Khamal da Fateeha kuwa sunfi kowa farin ciki dan gani suke nesa tazo kusa, soyayyar su kullum k'ara gaba ji suke kamar su had'eye juna, kullum k'ara shak'uwa suke sunan su, Khamal da Fateeha na tsaye a harabar gida su, sai zuba soyayya suke suna sakarwa juna k'ayataccen murmushi, da tattausan kallo, cike da k'aunar juna, duk wanda ya gansu a haka yasan ko ba'a tamaya ba akwai tsaftacciyar soyayya, Abba da Dady suka fito, cikin zafin rai Dady ya nufe su, da sauri Abba rik'o shi, yace " mai yasa ka cika gagagwa ne, saura k'iris mu kai ga gaci, kai ka b'ata mana plan, ai na riga na gama shirya masa *GADAR ZARE*



Fateeha da Khamal zaune a Shagalin ku restaurant, Oder suka bayan ta abinci da drinks, murmushi d'auke a fuskar kowannensu, Khamal ya kafe ta da ido, iska ta hura masa tace " yadai wannan kallo haka? 


Dariya yayi yace " ba dole ba kin san bana gajiya da kallonki, ko a cikin b'akin ciki nake idan na kallonki sai naji na zama freshman, murmushi kawai tayi, suna cin abincin suna hirar soyayya cike da tsantsar so, kowannen su ji yake idan duniya zata tashi bazasu iya rabuwa da junan su, shauk'in k'auna ke fizgar kowannen su, duk wanda ya kalle su yasan ba k'arya akwai true love, sai lumshe ido suke, Ja'afar dake zaune a gefe yana shan coffee, ya sauke idonsa a kansu. 



Wani irin mugun kishi ne ya taso masa, zuciyar sa ta shiga bugawa da k'arfi, gabansa yayi muguwar fad'uwa, take yaji k'irjinsa na neman daina aiki, lokaci d'aya ya rud'e ya figa daga hayyacin sa, ya rasa abinda me masa dad'i a duniya, ya rink'a jin zuciyar sa kamar zata kama da wuta, idon shi ya rufe da sauri ya sake bud'ewa, ya sauke su a kansu, bai san sanda ya nufe su ba, yakai wajen 5mtn tsaye a kansu amma basu sani ba kasancewar sun da tafiya wata duniya, cikin zafin rai ya buga table din da suke zaune, a firgice suka mik'e suna kallonsa, wani wawan tsaki taja, ta watsa mishi kallan banza, ta kalli Khamal tace " please have a set my life, don't worry about him, a hasale Ja'afar yace " dama baki daina bin wannan d'an iskan yaron ba, zauna gari banza jobless wanda shi kanshi bai iya ci da kanshi ba balle ke, murmushi Khamal yayi baice komai ba, cikin zafin rai Fateeha tace" wannan shine zab'in rai na, masoyayi na, burin zuciya ta, kai da kake da aikin yi bana sanka bazan kuma tab'a auren ka ta, wai kai wanne irin maye ne jarababbe, nace ban san ka, ko dole ne, ana soyayya dole ne? 



Zuciyar Ja'afar ta k'ara yin zafi yaji kamar zai mutu, a harzuk'e yace " dolenki ki aure ni Fateeha matuk'ar kina raye ina raye baki da wani miji daya wuce ni, ya kalli Khamal wanda shiru kawai yayi zuciyar sa sai tafasa take, yace " kai kuma katon banza, matsiyaci zaman uwar me kakewa mutane anan, banza sakarai marar zuciya, uban yarinya yace bazai baka 'yarsa ba, amma dayeke kai maye ne ka nace, " dalla Malam rufewa mutane wannan k'azamin bakin naka, kai har zakayi maganar rashin zuciya, maye kawai wanda baison ciwon kansa ba, zuciyar Khamal ta k'ara hasala ganin yadda Fateeha ke ci masa mutunci akan Khamal, kuma yak'i tanka masa, ya kai hannu zai ci kwalar Khamal, cikin zafin nama Fateeha wacce bak'in ciki yayi mata katutu ta zabga masa zafafan mari,gaba d'aya hankalin jama'ar dake zaune yayo kansu, idonta yayi ja ta nuna masa hannu tace " wallahi koda maza sun k'are babu abinda zanyi dakai, ta nuna masa hanyar fita tace " get out from here, kad'an ya rage numfashin Ja'afar ya fizge tsabar firgicin daya shiga, lokaci ya d'auka yana kallanta da mamakinta, yace " ni kika mara akan wannan jakin matsiyancin, a tsawace tace " get out, da k'arfi babu wanda baiji ta ba, kai ya girgiza ya kalli Khamal yace " zaga ni, murmushi Khamal yayi yace " aini d'an gata ne, dan ina damai shigar min, kaga kuwa idan kana mayyi maka kai baka yi, tsaki Fateeha taja, ta rik'o hannun Khamal, sai da ta taka k'afar Ja'afar sunnan suka fice, suka bashi zuciyar sa kamar zata tarwatse.



Bayan kwana biyu zuciyar Ja'afar ta kasa akan abinda ya faru tsakanin shi da Fateeha, duk yadda yaso ya yakice ta daga zuciyar sa amma ya kasa, gashi idan ya kira ta a waya bata picking, babu abinda yake san gani kamar kyakykyawar fuskarta, ya rasa yadda zanyi, dan haka ya shirya a falo ya zauna kasancewar falon ba kowa, ya aika mai aikinsu ta kira amma fir tak'i zuwa, yayi aiken duniya tak'i zuwa, mik'ewa yayi cikin sanyin jiki zai tafi, Dady ne ya shigo falon ganin Ja'afar yasa shi sakin fara'a, da sauri Ja'afar ya nufe shi, ya gaida shi, ya kalle shi yace " yau she kazo, ko har kun gama da Fateehar ne? 



Murmushi Ja'afar yayi yace " yanzu nazo ban iske kowa bane shiyasa zan tafi, Dady yace " zauna bari na shiga ciki na turo maka ita, dad'i Ja'afar yaji dan ko bakomai ya ganta koda zaginsa zatayi, murmushi yayi had'e dayi masa godiya, a d'aki ya same ta yace " kije falo Ja'afar yana jiranki kuma minti 2 na baki, idan ba haka ni da ke ne, ya juya, direct kitchen ta nusa, sob'on (zob'o) da Momy ta had'a ta d'auko, ta nufi inda yake zaune, sanye yake cikin farin boyel da gani sabo ne, tana zuwa bata yi wata-wata ba ta juye masa zob'on a jiki, da sauri ya mik'e yana kallonta ta kalle shi tace " wai kai wanne irin maye ne marar zuciya, ko dai kare ya d'auke maka ne? 



Shiru yayi kawai yana kallonta, karka k'ara zuwa gidan mu idan kuma ka sake ka k'ara dawowa wallahi sai nayi maka abinda yafi haka dan harka mutu bazaka manta ba, murmushi yayi yace " ko k'in k'i ko kin so baki da wani miji daya wuce ni, kallon sa tayi shek'ek'e tace " wallahi matuk'ar Khamal yana raye bazan tab'a auren ka ba, a hasale yace " lalle kuwa Khamal zai mutu koda bai shiryawa mutuwar ba, lokacin barin sa duniya yayi, ke da kanki kikace idan baya raye zaki aure ne kinga kuwa dole ya mutu, ke da kanki kin jawo masa mutuwarsa kusa, bakin ki ya jawowa masoyinki mutuwarsa a kwana kusa daga yau daga wannan lokacin ki fara k'irga kwanakinsa na mutuwa, kin jawo masa bala'i sai saka shi kukan mutuwa, sai yayi tsere da mutuwar sa, sai na k'ulla masa *GADAR ZARE*, sai na ya tsani ratuwarsa, sai tsani duniya da abinda ke cikinta, wallahi hatta ke sai ya tsane ki Fateeha, kwalar rigar sa taci ta zaro idanuwa waje tace " wallahi k'arya kake Ja'afar babu abinda zai same shi sai alkhairi, Allah yana tare da, kuma ka sani komai za'a Khamal bazai tab'a tsana ta ba, kamar yadda nima ko rayuwa ta za'a cire min bazan tab'a rabuwa dashi ba. 



Dariya ya tuntsure da ita yace " akan wannan lusarin jakin kike wannan haukan, hannu ta d'aga zata kifa masa mari taji caraf an rik'e hannun ta baya, taji saukar wasu fitananun marika, kuncinta ta rik'e ta juya a firgice Dady ta gane tsaye a matuk'ar hasale sai huci yake, kamar mahaukaci zaki ya fara.......... 




MOMYN ZARAH