GADAR ZARE…

18

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

_(united we stand and succed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers)_





Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 





***




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*




18




Numfashinta ya nemi d'aukewa cak... saboda rud'anin sautin muryar daya doki dodon kunneta cikin rawar murya ta bud'e bakinta dake rawa tace" my life kai ne? 


Shima cikin rawar murya yace" eh nine my heart, ya kike, ya su Momy da Dady?  

" duk muna lafiya, kai ya kake?  

Murmushin k'arfin hali yayi yace " Alhamdulillah, am sorry dear ban samu waya bane shiyasa kika ga ban kira ba sai yau, kuka ta fashe mishi dashi, da k'arfi Khamal ya runtse idonsa saboda bak'in cikin daya taso masa, babu abinda Khamal ya tsana kamar b'acin ran Fateeha, balle har yakai ga ta koka, sosai Fateeha ke kuka, cikin kuka tace " am sorry ya dear bazan iya cika maka alk'awarin dana d'aukar maka ba , bana san sa, bazan iya auren sa ba, bana jin zan iya rayuwa da wani d'a namiji a matsayin miji in ba kai ba, kai kad'ai nake so, kai ne rayuwa ta, kaine duniyata wallahi na yarda zan jira ka komai tsayen lokacin, amma Allah bazan iya AUREN dan'uwanka HAMZA ba kamar yadda kace . 



Da sauri ya bud'e idonsa dake rufe, gaban sa yayi masifar fad'uwa, kansa ya juye ya kasa fahimtar abinda Fateeha ke nufi, kalmarta ta k'arshe kawai yake maimaitawa _bazan iya auren dan'uwanka Hamza ba_ to me hakan ke nufi?

, bai k'arasa tunanin dayake yi ba yaji tace" wai ni za'a d'aurawa aure nan da kwana 5 kuma bada kai ba, I cant my love, I can't, am sorry, cikin rashin fahimta yace " Fateeha ban gane mai kike nufi ba, ban fahimta ba kin sani a duhu, waye zaiyi auren nan da kwana 5?



Cak ta tsayar da kukanta ta cire wayar daga kunnenta ta k'urawa wayar ido, jin Khamal nata "hello hello yasa ta mayar da wayar kunnenta tace " wai waye, bada Khamal nake waya bane?



"Eh nine mana my heart, please kiyi min bayani yadda zan gane ban fahimci zance ki ba, itama cikin rashin fahimta tace " kamar ya baka gane abinda nake nufi ba, ba da kai muke exchanging text ta layinka na Nigeria ba? " Eh bani bane ya akayi? "What!!? Fateeha tace da k'arfi, you means badai kai mukayi magana ba, ba kaine kace na auri Hamza ba? 




Cikin firgici da matsanancin tashin hankali yace " ni! yaushe? kinga please ki nutsu ki dawo cikin haiyacinki kiyi man bayani yadda zan gane, aiko Fateeha ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, daga k'arshe tace " this coming Saturday za'a d'aura mana aure, tab tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, nan take Khamal ya canja kamanni, idonsa sukayi ja, hankalinsa yayi mugun tashi, jikinsa ya d'auki rawa in bada huci babu abinda yake fitarwa, ita kanta Fateeha ta fahimci hakan dan tana jiyo hucinsa, ta cikin wayar .

Cikin rawar murya tace " my life kana nufin duk wannan shirin Hamza ne? 



Dakyar ya iya bud'e baki ya bata labarin abinda Hamza yayi masa, yace " koken d'in da aka kamani da ita a kaya na shine shi ya saka min a kaya na, ya fad'a mata duk yadda sukayi da Hamza, kuka Fateeha ta fashe dashi, saboda mamaki itama kasa magana tayi, Khamal yace " Fateeha, gabanta ne ya fad'i dan indai taji Khamal ya kira ta da real name d'inta ba lafiya ba, yaci gaba da cewa " mai yasa zaki munafurce ni, mai yasa baki sanar dani gaskiyar abinda ke tsakaninki da Hamza ba? Cikin mamaki Fateeha tace " kamar ya ban sanar dakai abinda ke tsakanin mu ba, me ke tsakani na dashi, koya ce maka akwai wani abu a tsananin mu ne? 



Shiru Khamal yayi baice komai ba, taci gaba da cewa ni dai abinda na sani shine, yayi tayi min nacin yana so na, yasha zuwa gidan mu, yasha rok'ona akan na so shi, ni kuma na fad'a masa ina da wanda nake so, a lokacin ban san alak'ar dake tsakanin ku ba, bayan na sani kuma shine ya hanani na sanar maka, ta fad'a masa zuwan da Hamza yayi gidan su, da yadda sukayi, duk cikin matsanancin kuka Fateeha ke magana. 




Ajiyar zuciya Khamal ya sauke da karfin gaske kana yace " lalle Hamza ya cika makiri maci amanar dan'uwa , wallahi tunda nazo k'asarnan banyi magana da kowa ba, sai shi ranar daya kira ni ya sanar dani shine yasa min koken a kaya na, cikin tashin hankali Fateeha tace " baka san ma Hajiya ta mutu ba kenan? 




"What Khamal yace da k'arfi, ya fashe da wani irin mahaukacin kuka ya dunk'ule hannushi ya naushi bango da karfi yace shikenan " ya kashe ta, ya kashe min ita dama yace sai ya kashe ta, Hamza ka cuce ni, wallahi kozan yafe maka komai banda jinin Hajiya , bazan tab'a yafe maka abinda kayiwa Hajiya ba, Allah ya isa tsakanin mu dakai, macuci, mugu, azzalumi, maci amana, mayaudari, mak'aryaci, ya k'ara fashewa da wani mahaukacin kuka, fisge wayar Ayuba yayi ya kashe, tuburan Khamal ya haukace agurin ya rink'a wani irin ihu yana hauka, ya fita daga hankalinsa, nutsuwarsa tabar jikinsa, Ayuba ya tusa shi gaba yana yi masa nasiha yana bashi shawarwari, har ya samu ya dawo cikin hayyacinsa. 




Fateeha na ganin an kashe wayar, tayi wurgi da wayarta, ta fita da gudu a falo sukayi karo da Momy da Dady da sauri Momy ta rik'e ta ganin gaba d'aya bata cikin nutsuwarta, kuka Fateeha take tana sambatu, a hankali Momy ta zaunar da ita, ta d'auko ruwan sanyi tabata tasha, sai da ta bari tad'an nutsu sannan ta kalle tace " mai ya faru? duk abinda ya faru tsakanin su da Khamal ta fad'awa Momy da Dady, sosai suka shiga cikin mummunan tashin hankali, Momy ta kalle shi tace " please Alhaji kayi wani abu akai mana, ajiyar zuciyar Dady ya sauke yace" tunani nake ta inda zan fara ne.



Cikin kuka Fateeha ta zube a gaban Dadyn ta tace " please Dady ka taimaka mana idan na rasa shi mutuwa zanyi please ta k'arashe maganar hawaye na bin fuskarta, cikin sanyin jiki ya kalli Fateeha yace " karki damu in sha zanyi iya k'ok'arina. 



Bayan kwana biyu Dady ya samu Fateeha har dakinta a gefen gadon ya zauna, ya kalle ta yace " kin nunuwa Hamza akwai wani abu? 

 kai ta girgiza masa alamar a'a, ajiyar zuciya ya sauke yace " yawwa gud girl, yanzu abinda za'ayi ki kira shi yazo gidan nan yau, dan nayi magana da commissioner of police, mun gama tsara komai, amma dole sai Hamza ya shigo hannu za'a iya fitar da Khamal, jikinta na kirma ta d'auki wayarta ta shiga kiran Hamza, bugu d'aya ya d'aga, sai da ta saita kanta sannan tayi k'asa da murya tace " hello my love, kusan fad'uwa Hamza yayi kasancewar yau ne rana ta farko daya ji makamanciyar wannan kalmar daga wajen Fateeha, da sauri yace " hello my everything, tace " please ina san na ganka ne, cikin zumud'i yace " yanzu ko sai anjima, " ah yanzu mana cewar Fateeha, da sauri ya mik'e yana cewa "OK gani nan zuwa. 



Da sauri Dady ya kira police d'in da suke magana yace " sun gama tsara komai, dan yana hanya " yes sir cewar police d'in, ya kalli Fateeha yace " ki shigo dashi har parlor, " to kawai tace, ba'afi 10 minutes ba Hamza ya kira ta yace ya k'ara so, yana k'ofar gida, umarni ta bashi daya shigo parlor aiko ba musu ya danna kai, fuskarta d'auke da murmushi ta fito. 



Da sauri ya mik'e tsaye yana kallonta, ido ta k'ura masa, yayinda wutar tsanarsa ke k'ara ruruwa a zuciyar ta, ya bud'e baki zaiyi magana yaji kan bindika a kansa d'an sandan yace " you are under arrest, kana motsawa zan fasa kanka da harsashi , suna cikin haka Dady ya shigo da 'yan sanda sama da 20, ido ya k'urawa Fateeha dake tsaye hard'e da hannayenta duka a k'irji tana murmushi hawaye na zuba daga idonta, a hankali ta tako har zuwa gabansa, cikin muryar kuka tace " kayi asara Hamza kaji kunyar duniya, ka rasa wanda zakayiwa haka sai d'an uwanka uwa d'aya uba d'aya, kallon ta yayi idonsa na zubar da hawaye yace " duk abinda nayi a kanki ne Fateeha, nayi-nayi akan na bawa zuciya ta hak'uri akanki amma na kasa, i love you Fateeha kuma wallahi banyi danasanin abinda nayi ba, bak'in ciki na d'aya na rasa ki da zanyi, amma matuk'ar ina raye bazan tab'a bari wani ya mallakeki ba, duk wanda yayi k'ok'arin hakan sai na tsinke masa numfashinsa. 



Murmushi Fateeha tayi tace " ni kuma duk duniya babu wanda na tsana sama da kai, bana sanka, ba kuma zan tab'a sanka ba , i hate you, ta tofa masa yawo a fuska, lumshe ido yayi yace " thanks my love, ganin yana b'ata musu lokaci ne yasa 'yan sandan tusa k'eyarsa suka saka shi a mota suka tafi office dinsu dashi, Fateeha ta durk'ushe a wajen ta saki kuka mai cin rai.




Ba k'aramar wuya Hamza yasha ba amma yak'i yayi magana balle a samu abinda ake so, sosai ran wani d'an sanda ya b'aci, cikin zafin rai ya shiga cell d'in da Hamza ke ciki ya damk'o wuyansa ya rink'a jan shi a k'asa har d'akin shocking, sosai d'an sandan nan ya rink'a ganawa Hamza azaba, sai da yaji wuya na neman kashe shi sannan yace " zanyi bayani, bayan an kyale shi ne kuma ya shiga raina musu hankali aiko a zuciye d'an sandan yaci gaba da gana masa azaba, wanda daga karshe aka saka shi cikin underground akayi masa me rad'a'di da muni wanda kusan duk wanda zakaga an sashi cikin underground laifinshi me girma ne sannan yasa taurin kai gurin rashin bada hadin kan bincike dakyar dai aka samu Hamza yayi bayani, Dady zaune a DPO office aka shigo da Hamza wanda gaba d'aya kamaninsa sun canja, Dady ya kalle shi yace " waye kace ya baka koken? 



Dakyar Hamza ke magana saboda wuyar dayaci yace " abokinka Abban Ja'afar, k'irjin Dady ne ya buga da k'arfi, gaske cikin firgici yace " what!!! wallahi k'arya kake sharri zaka yi masa, cikin k'arfin hali Hamza yace " idan da wanda zanyiwa sharri ai bayanka yake, tunda kake dashi ka tab'a sanin ainahin sana'ar da yake yi? 



Dammmmm!!! gaban Dady ya kuma fad'uwa, shiru yayi ya shiga tunani, shidai a iya saninsa bai san shi da wata sana'a data wuce business d'in kaya daga k'asashen waje zuwa Nigeria ba, Dady ya bud'e baki zayyi magana police yace " karka damu Alhaji zamuyi bincike sosai dan ganin gsky ta bayyana, yanzu munsa aje a taho,dashi kafin ya gama rufe baki sai ga 'yan sandan sun shigo da Abban Ja'afar, yana ta wani cika yana batsewa, murmushi d'an sanda yayi sannan ya sanar dashi zargin da ake yi masa.



Mik'ewa yayi tsaye yace " maganar banza maganar wofi ma kenan, ni zaku rainawa hankali wallahi idan bakuyi wasa ba duk sai na ja muku asarar rasa aikin ku, murmushi DPO yayi ya kalle Abba ya nuna masa Hamza dake zaune a gefe yace " kasan wannan? Abba yana ganin Hamza gabansa ya fad'i ya firgice ya shiga in'ina, ji yayi an dafa shi ta baya ya jiyo a firgice DPO ya gani tsaye a bayan sa yana yi masa murmushi, gumin dake zuba masa yasa hannu zai goge, da sauri DPO ya rik'e hannun ya mik'e masa tissue yace " goge da wanna, DPO na tsaye yana kallansa sai daya gama yace " zakayi mana bayani cikin dad'in rai ko sai nasa an tambaye ka,cikin tashin hankali cikin rawar murya yace " ni fa ban san kome ba, "agame da abinda ake tuhumata akai ba, "ok DPO yace, yaran sa ya kira ya kalle su yace " ku tambaye shi, ta yaren da zai fi fahimta. 



Sai da Abba yaci mugun duka da bak'ar wahala sannan yayi bayanin komai kan cewa dama can sana'ar da yake yi kenan sama da 30yrs, kuma shine ya bawa Hamza koken ya sakawa Khamal a kayansa, jinjina kai DPO yayi yace " dama can kasan Hamza ne?

 "A'a ban san shi b cewar Abba, DOP ya sake kallansa yace " yanzu tare kuke sana'ar? A'a wannan ne karo na farko dana sashi aiki, DPO yace " ya akayi ka san shi? 



Abba yace " wata rana ne naje gidan Alhaji Nasiru naga Hamza da Fateeha tsaye naji yana rok'onta akan karta sanar da Yayansa abinda ke tsakanin ta dashi, daga yanayin kallon dayake mata nagane yana yi mata mugun so, tunda daga nan nasa aka nemo min yaran, ban wani sha wuya ba ya amince min akan zan bar masa Fateeha ya aura, amma ni a raina bari nayi sai ana gobe d'aurin auren shi da Fateeha zan sa a kashe shi, ni kuma na lallab'i Dadyn ta kan kar a fasa d'aurin auren gobe sai a d'aura da d'ana Ja'afar.



A firgice Hamza ya d'ago kai yana kallon Abba, shima Abban shi yake kallo yace " eh Hamza niya ta kenan, to wai ma in banda abinka dan me nake san kawar da Khamal ai daman da Ja'afar ya mallaki Fateeha ne, tunda abin ya faru Hamza baiji nadama ba sai yau, jikinsa yayi sanyi idonsa ya fara zubar da hawaye cikin kuka ya kalli Abba yace " ka cuce ni, ina zaune lafiya da d'an uwana da kakata kasa na tarwatsa mana farin cikin mu da kwanciyar hankalin mu, tsawa DPO ya daka musu, duk sukayi shiru, DPO ya kalli Dady yace tunda duk sun amsa laifin ku, gobe sai mu kai su Saudian Embassy dake nan Nigeria, "ok kawai Dady yace saboda tsabar mamakin Abba. 



Jikin Dady a sanyaye ya zauna a kujerar dake kusa da Momy da Fateeha, da sauri Fateeha tace " Dady ya ake ciki? Cikin sanyin jiki ya shiga basu labarin abunda ya faru, dukkan su suka shiga jimamin Abba, had'i da jinjina irin san kai irin nasa, tunda Umma da Ja'afar sukaji abinda Abba ya aikata hankalin su yayi masifar tashi fiye da tunani, dukda Umma ba wani dad'in zama take ji dashi ba. 




Tunda Khamal yaji mutuwar Hajiya kwata-kwata yaji ya tsani duniya da abinda ke cikinta ya tsani Hamza fiye da komai da kowa dan da duk abinda Hamza yayi baiji ya tsane shi ba sai da ya kashe Hajiya, sosai Khamal ke kuka yana yiwa Hajiya addu'a, yayinda Ayuba yake ta faman k'ok'arin kwantar mishi da hankali. 



Ranar Monday Commissioner of police ya mik'awa Saudian Embassy Hamza da Abba, akan yarjejeniyar zasu saki Khamal had'i da wanke shi a idon duniya, washe garin ranar da aka mik'a su za'a wuce dasu zuwa Saudia, ranar Umma da Ja'afar suka samu Abba a Air port, ba k'aramin kuka Umma take ba, shima Abba cikin kuka ya kalle su yace " please ku yafe min, duk abinda nayi nayi ne domin ku dan ku kasance cikin farin ciki da wadata, cikin kuka Umma da Ja'afar suka rungume shi, dakyar aka raba su, suka rabu cike da bak'in, bayan sun isa k'asar saudia ne aka mik'awa gwamnatin k'asar su, tare da kwararan hujjoji, da sake kwakwkwaran bincike, sai da aka tabbatar da komai sannan aka yanke musu hukunci, shi Abba kasancewar ba'a kama shi da kayan maye a hannunsa ba, sannan ba'a k'asar saudiyya yake safarar muyagun kwayoyin sa ba, bai kuma tab'a aikatawa k'asar laifi ba, yadai bada koken ne kawai an saka a kayan wani dan haka suke tuhumar sa da laifin K'AZAFI, bai kuma wahalar da shara'a ba shiyasa suka yanke masa hukuncin 5yrs in prison had'i da horo mai tsanani bayan an datse masa hannu d'aya. 



Shiko Hamza kasancewar shine wanda ya saka koken a kayan Khamal,shine wanda ya shigo musu da koken k'asar su, tunda shine yasa a kayan, kuma ya aikata kisan kai, duk da laifin wa k'asar sa yayiwa, sannan Khamal d'an uwan sane na jini, shiya suka yanke masa masa hukuncin LIFE IN PRISON, sannan za'a datse masa hannayen sa duka biyun, had'i da huro mai tsananin gaske, ba k'aramin kuka Hamza yayi ba, yayi kuka kamar ransa zai fita, yayi danasani da nadama, shiko Abba godiya yayi tayiwa Allah dayasa hukuncin sa yazo da sauk'i. 




Khamal na zaune shida Ayuba yana ta faman sana'ar tashi ta kuka, wani d'an sanda yazo ya kira shi, bayan police d'in yabi, wani babban hall aka kai shi inda ya tarar da manyan mutu ne, da jami'an tsaro a kalla sun kai 50,umarni aka bashi daya zauna, bayan ya zauna ne aka fito dasu Hamza ganin Hamza yasa Khamal saurin mik'ewa, tsaye yana masa wani irin kallo me cike da tsantsar tashin hankali a gabansa Hamza ya zube yana rusa kuka yana rok'on Khamal yafiya, Khamal kansa ya d'aga sama hawaye nabin fuskarsa, Abba ma ya zube a gabansa yana bashi hak'uri a hankali Khamal ya sauke ajiyar zuciya yace " kaga yadda Allah yake ikon sa ko? kai da a tunaninka kaci banza, ai Allah ba azzalumin sarki bane, Hamza kaban mamaki, sannan ka bani misali ta yadda bazan k'ara yadda da kowa ba koda kuwa ni da kai na ne, ka tsora tani, ka cuce mu, ka tarwatsa mana rayuwar farin cikin mu, kasa na tsani kaina Hamza.




" mai yasa ka aikata mana haka mai yasa? , kasa zamu rayu cikin k'unci da k'unar zuciya ka tsinke min walwalata ka rabani da duk wata annashuwa ta?

, to amma ni na yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau, na yarda Allah ne yake tsarawa kowa rayuwarsa, shike aikata komai akan kowa a lokacin daya so, nasan haka Allah ya tsara mana, ni dai daga b'angare na na yafe maka duniya da lahira akan abinda kayi min, jinin Hajiya ne daka zubar bazan tab'a yafe maka ba, dan wallahi ko duniya zata tashi bazan tab'a iya yafe maka ruhin Hajiya ba duk ranar dana yafe maka jinin Hajiya bazan tab'a yafewa kai na ba, ya juya ya kalli Abba yace " kai ne tushen faruwar komai, kai ka tarwatsa mana ahlin mu, ka ruguje mana gidan mu, kaje Allah ya isa abinda kayi mana Allah yayi maka kai ma, da sauri Abba ya rik'o k'ofar Khamal yace " bazan yi maka musu ba, duk laifin daka d'ora min naji na k'arb'a, amma ka dubi girman Allah ka shafe min, jikin Khamal yayi sanyi ya kalli Abba yana goge kwallar dake zubo masa yace " na yafe maka, babban jami'in dake wajen ne yayi gyaran murya, kowa yayi shiru ya fara magana da harshen turanci " to dukkan mu dai mun san mai ya faru, dan haka mun saki Khamal sannan zamu wanke shi a ido duniya, bayan haka kuma gwamnati ta bashi kyautar 100 million naira, ido Khamal ya lumshe yana zubar da hawaye, a ransa yace " Allah sarki Hajiya kin sha wahala akan mu, yanzu kuma ga dad'i yazo sai dai baki raye, Khamal na gani aka tusa k'eyar su Hamza suna kuka. 



Shugaban wajen ya kalli Khamal yace " idan kana da buk'atar wani abu ka fad'a, hawayen dake zubo masa ya k'ara gogewa yace " alfarma d'aya nake nema a wajen ku, dan Allah ku taimaka ku duba cess d'in AYUBA kuyi masa adalci....... 




NASO NA NAYI K'OK'ARI NA GAMA MUKU LABARIN KHAMAL A WANNAN PAGE D'IN , SABODA LABARIN ZAID, AMMA NAGAJI GASKIYA AMMA IN SHAALLAHU NEXT PAGE ZAMU GAMA




MOMYN ZARAH